← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 65

Sashe 13

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mom taji dadin zantukan Baba"Ta CE Ba komai Baba yiwa Kaine domin azatonta ko wani dattijo ne mai shekaru." batasan cewa wahala da rashin hutu tare da cutar talauci ne ya tsofar da Mallam Balarabe tun Wuri."

"Innerei Tace Hajiya ayni nasamu yarana masu son mu,Su jawad kaam Akwai mutunci."

"Raaas gaban mom ya Fadi domin Innerie CE,mutum ta FARKO da ta ambaci mutunci tattare da su Jawad."

"Mom mamaki take yadda su Jawad suka canja suka koma kalar kirki tun Daga shigarsu gidan har kawowa yanzu...Ba suyi wani abin rashin mutuncin ba!"Ko meye sila!?"Amma dai Akwai wata akasa Tunda har taga sun Sanya sutura ta mutunci,Wato Kaftan da hula..."Abinda Bata taba ganin sun sanya ba!"

"Jawad ne ya dawo da mom Daga duniyar tunanin da take."Ya ce mom mu wuce Koh!?"

''Dariya tayi tace"To mutafi Baba Allah Kara sauki Kudi ta bashi 10k Daman sun shigo da manyan ledojin kayan fruits ahannunsu sun ajiye."Tace aci da Hakuri Allah ya baka lafiya ya tsare gaba!"

"Ameen,Baba yace Yana ta jera GODIYA da fatan Alheri wa mom da yaranta."

" Saif yace to Baba sai mun dawo fira jibi."Yana Dariya

"Malam Balarabe yace yawwa saifullahi sai na ganku fa Hajiya angode Allah ya saka da alkhairi,Muhammad sai kunzo cewa da Jawad."."

"Ameen..mom Tace."

"Jawad yace Baba sai mun dawo,"

"Innarei tace gaskiya kuna kokari mun gode ay ba Haka ake ba!"Gashi 'yarta taki tana makaranta har yau ba ta dawo ba."

"Mom Bata fahimci me Innerie ke nufi ba.."Yake kawai tayi ta shige suka bita Abaya..Nan suka isa Mota Baba har can ya rakasu Yana masu GODIYA."

"Innerie Koh Daga zauren gidan ta tsaya tana musu Sallama."Tare da tunanin kirki irin na wad'annan mutanen..."Tsoronta daya kada Nadiyatou ta dawo asamu matsala!"Koh da yake tana da yakini akan halinta kuma a yadda sukayi Mata tarbiyya bazata taba girgiza masu ba!"Bare Jawad baida aibu ko makosa ko kadan."Domin ya nuna masu halin kirki yaron kirki ne kawai zai fitou agefen da Jawad ya bulkowa lamarin!!"Da tunanin ta shige Daga cikin gidan tana Cigaba da ayyukan ta."Tana yiwa Allah GODIYA da yakawo haske arayuwarsu."

"Baba Yana ganin tashin motarsu Jawad, shagon unguwar ya nufa domin sayen abubuwan da suke buqata, Daman kudin sun zo masu alokacin da suke nemansu."Shiyasa ubangiji ya kawo masu su Jawad a sanadin tufin asirin su."Ikon Allah kenan da Amfanin Kai Kuka awurinsa, Allah kenan Al-ahad Al- samad."Sai ya kawo mafita ba zato ba tsammani da zancen zucin Malam Balarabe ya isa kantin ya fara sayen kayan da yake bukata!"

"Dab da magriba suka iso kofar gidan su...Horn suka yiwa Mai gadi ya bude gidan Mom suka sauke sannan suka shiga masallacin gidan domin an fara Kiran sallah."

"Mom shiga tayi tafara watsa ruwa sannan tayi sallah tana dawowa falon, suna shigowa..."

"Daning place suka nufa domin abincin dare ya Dade da kammala."Har an jera komai akai."

"Da mom da su abincin suka bude kowa ya zuba suka fara ci..."Suna taba fira.

"Nan mom ta kalle su ta fahimci suna cikin farinciki."
"Tace Saif.."

"Na'am mom ya amsa."

"Nace wai...meye sirrin? ko dai mun fara Yar boyen sirrine da KU?.."

"Yace kamar ya mom!?"

"Kun fara neman aure Banda Labari ne..!?"

"Jawad yace aure fa mom!?"

"To sarkin tsari...Ba da Kai nakeyi ba da Saif nake."Inji mom tana hararen Jawad

"Kansa ya Sosa Yana murmushi.."Tare da cigaba da cin abincinsa."

"Saif ma dariya suka bashi yadda suke wannan da mom..."

"Na dawo kanka saif kasan bana son wasa ko to kagaya min Gaskia meye alakar KU da wadan can mutanen..?"Anya kad'aiwa ce kawai!?"Wannan hankali da kukayi asanadin su!?"Na k'asa ganewa Domin naji Wannan matar tana fad'in yartawa Bata Nan kaina ya daure saiku min Bayani..."Inji momy

"Kallon Jawad yayi da ke cin abincinsa ko ajikinsa." sannan yace"mom kiyi Hakuri a gaskiya Jawad ya fad'a son yarinyar gidan ne." me suna Nadiya..."To har yanzu Bai sanarda ita ba!"Iyayenta dai sun sani,Saboda ance halin kirkine kafara neman macce awurin iyayenta kafi Ka sanar da ita,"To yanzu dai su sun san da maganar Kuma Jawad aurenta Zaiyi ba da wasa ba!"..."Daman muna son ta dawo Daga makaranta ya sanarda ita ne Daga Nan idan ta aminche sai mu sanarda ke!"Amma kiyi Hakuri mom...Inji Saif Wanda a cikin sigar rarrashi yake maganar da kunya."

"Wani Abu Jawad yaji tamkar an cika Masa mashi ak'ahon zucia..Alokacin da yaji Amininsa na fadin waaai...ya kamu da son wacce yafi tsana adunia! wacce ya tsani ganin ko da Mai sunanta ne!Wacce yake burin daukar mummunar fansa akanta!"Wacce yake da kudurin ya wulaqanta dukkan rayuwarta!!!"Tuni Idonsa suka rikid'e zuwa ja abincin ya ture tare da tashi ya fice yace ka sameni part dina saif kaina na min zafi zan kwanta!!!"Jawad yace tare da tafiyan sa abinsa..."

"Da yake saif Dan duniya ne Tuni ya hango bacin ran abokinsaa!!!"Sai ya fashe da dariya yace su kunya manya bawani ciwon Kai....sai dai nazon..."

"Ya kalli mom yace"Ai mum yau kin hada rigima saboda munyi da Jawad sai Nadiya ta aminta za'a sanar maki."Kinsan mutumen nawa yanzu fushi NE yayi saboda na gaya maki Gaskia alkawari ne."

"Murmushi mom tayi Tace"A Gaskiya naji Dadi wannan zancen idan har da gaske Jawad na sonta Kuma Zaiyi auren da gasken...zanyi murna da hakan Saif,domin na k'osa Naga kun Zama mutane kunyi aure ya fiye muku wannan shirmen banza da kukeyi!"

"Yanzu dai mom karki damu In shaa Allah mun Zama mutanen kirki..."saboda mun fara hankali..ki dai tayamu da addu'a Allah yasa muyi nasara."

"Saif zanyi maku Addu'a da fatan shiriya, sannan idan ta kama har ni zan shiga zancen domin ganin ya samu abinda yakeso, duk da ba Yar gidan talakawa naso ya aura ba!"Na ci buri akan auren Jawad naso ya samu Yar gidan manyan mutane masu Kudi na asali ya aura mu daki JUNA da naira,Nayi had'ashi da yaran qawayena, da 'ya'yan Abokan marigayi Babansa d'iyan masu Kudi Amma kana sane Saif duk yace baya son su.." sai Wannan
zaice Yana so!?"

"Mom may be ita ce zabin da Allah yayi Masa."

"Hakane Saif,Allah yasa ita CE Alheri,Zanyi munna da hakan Daman shine burin mahaifinsa,yaje da burin son ganin auren Dansa."Mom ta karashe zancen cike da damuwa."

"Allah ya gafartawa Abi."

"Ameen Saif..."

"Shima abincin ya ture tare da Shan ruwan faro da ke ajiye...yace mom Bari nasamu nawan..."Sai da safe."

"Yawwa Saif ka gaida Mamie Kwana biyu bamu hadou ba Amma muna waya sai na shigo..."

"Yawwa zataji mom.."

"To sai da safe Nagode sai naji yanda dik kukayi adinga sanar min."

"To Mom zakiji saif yace ya nufi sashen Jawad ."

"Mom abincin ta Dan ci kana ta Kira Inna tare da Bata umurnin ta kawo Mata kayan fruits."

"Jiki na rawa Inna ta dauko su afirijin Daman ta gyare su sun dauki sanyi...ta kawo ta ajiyewa Mom..."Sannan ta wuce dakinta..."mom falon ta dawo dauke da filet din ta,kallo takeyi tana chat da kawayenta tana Shan kayan lambun."

"Horn yayi kusan sau uku Alamar da yake masu idan ya dawo..."Sannan yayi parking motar a Inda yake ajiyeta..."Aykuwa fitowar mu ke da wuya sai ga yaran da gudun su.."Suna oyo yo Abba."

"Ganina yasa suka daka tsalle da kuwwa suka rugumeni Anty Nadiya oyo yo..."Cike da murna suka dinga daukar Yan kananan kayan da suke iya saukewa abut din."

"Mufeed da Mufeeda sai munna sukeyi...ganin hakan yasa naji Dan sanyi araina na sake fuskata...Saboda a hanya Yaya Saddiq yayi min tatas tare da kashedi da sharudda akan na kiyaye na kula da kaina "A karshe Baba ya Kira awaya yabani shi muka gaisa har nace yabani mamana yace Yana kanti wurin sayayya."Kuma Daga can masallaci zaije alokacin."

"Da taimakon yaran na kwashe duk kayana Yaya Saddiq Tuni ya shige gida yabar mu..."Rufe motar nayi Bayan mun kammala."A Lokacin da na shiga gidan naji wani iri araina.."Hakan dai na adana kayana adakin yaran nadawo falon."Ina tambayar Anty Jalila?" tana wanka Inji yaran."Nikam zaune nayi shiru sukuma sai zuba suke.."

"Tana wanka ta dinga jiyo hayaniyar yaran suna fadin sunan Anty Nadiya..."Nan take taji wani sanyi aranta..."Tuni ta manta da wanka take ta dinga tikar rawar India har da su shoyki tana Alhamdulillah gobe zanyi baccin safe, Addu'ata ta karbou."Nan da Nan ta watse ruwan ta fito ko Mai Bata shafa ba tafito Sanye da jallabi.A falon Inda muke."

"Yaran na jikina suna surutu ta karaso cike da fara'ah Tace A'ah Nadiyatou CE Wai... "

"Nace"Eh.....Anty Ina wuni,tare da sunkuyawa Daga kujerar.."

"Ta ce"Lafiya qlaw,ya makaranta!?"

"Nace Alhamdulillah."

"Kallona tayi Tace anzo Mana kwanaki NE?"

"Eh,nace."Da sanyin muryata

"Anty tace Nadiya to yau ake zuwa weekend NE! jiya sukace zaki ko Ranar jumma'a?"

"Eh,Anty,Daman naso nazo wani sati weekend ne,Yaya ne dazu yace in shirya ya wuto da Ni."

"Tooo....Anty jalila tace tana Murmushi Domin murnarta taqasa boyuwa,"

"Nace,Anty... Bari nayi sallah muna hanya akai sallah..."

"To sai kin fito ga Tafiya can kichen sai ki zubo ku ci idan kingama idar da sallar"

"Nidai na koshi gaskiya Anty domin na ci abinci a hostel."nace Mata saboda nikam bana son komai ayanxu."

"Mufeed Ina Abba!?"Anty Jalila ta tambaya."

"Ya tafi masallaci Mufeeda ta baiwa maman su amsa."

"Tashi nayi yaran SUKA bini sai dadi sukeji kamar an gafarta masu."Alwala nayi tare da tada sallar magrip da ishaa da yake lokaci yayi muna hanya akayi sallah gashi motar mu tayi faci ahanya muka samu tsaiko..."
"Ni da yaran mukayi sallar magrip sannan Ishaa...Bayan mun kammala Azkhar mukayi Ina koya masu...Nan SUKA dauko littafan su suna nuna min ayyukan da aka basu da taimakona sukayi aikin..."Sannan nace suje falon suyi kallo Inda mamansu saboda nikam Ina bukatar hutu mussamman da na tuna da qawaye na su Esha Nan naji Wasu zafafan Hawaye na zuba a idona."

"Duk sai naji komai ya fita Raina!!!"

"Amma ahakan zan hakura na Cigaba da Zaman Hakuri agidaan Yaya Saddiq...."

Kui hakuiryh fans Ina ganin comment naku Ina godia zakuji Ni hiru a Yan kwanakin nan cos zan shiga busy ana auren kanwata Amma idan nasumu time zan Dan tsakurou muku ko read more 1 ne,Ina neman Addu'oin KU wa auren Habibartynah😍

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*
*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 11*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_
Chapter 13 · 0% Book details