← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 65

Sashe 52

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daman falonsa babba aciki Bedrum dinsa yake Sai kofar da zata sadaka da gefen Jalila d'ayar kofar kuma gefen Amarya sannan Dakin Yara Wanda Duk acikin Babban falon suke,"Gidan Kam ba karya yayi kyau,komai an kammala,gefen Amarya NE kawai ba'a kawo kaya ba!har yanzun acewar su sai Ranar aure zasuyi jere!"Da angama akawo Amarya,"kada ayi mata barbade Kafin tazo( _Hakan neman magani ya gada,A duk lokacin da kakeyi ganin kake anayi maka,Allah ya tsare mu da fadawa halaka!Amin_)

"Cikin tashin hankali Yake driving Yana tunani da zancen zuci! kamar zai kife ya Fadi daga Cikin motar,Gudu Yake shararawa na fitar hankali!!kamar zai Tashi sama ya kosa ya isa Kebbi!"Domin yayi arba da Mansura!"

"Ranshi sai suya Yake,Yana cikin damuwa da tashin hankali!"yadda mansura zata yaudare shi!"Lalle bazai taba barinta ba!"Sai dai kowa ya rasa Wallahi Domin ya shirya fallasa komai ya tonawa kowa asiri Akan zancen Auren,Abdul-Rahman(Bimboy)kenan tsohon saurayin Mansura,"

"Tun da yamma tayi kowa ya shirya acikin ado da kwalliya Mai kyau,Wurin da ake event din kowa ya hallara ba laifi komai ya tsarou Domin harka CE ta Yan karya,Kuma wayayyi,"A hankali wani sassanyar sauti ke Tashi Wurin,"Komai an bajewa Mutane a table,"Suna hiding suna motsa Baki,zuwan Amarya da ango da sauran kawayenta kawai ake jira wasa ya fara,"

"Ganin har 6pm ta gota yasa jikin mansura yin Sanyi,Gashi an damesu da Kira su karasou tarou ya fara Basu,"Nan dai ta hak'ura suka Isa Wurin ita da kawayenta!"Sai karairaya suke Ana rangwada kamar za'a Kare!"Bayan ta zAuna awurin da aka tanada Domin Amarya da Ango,Wayarta ta fitou da ita tana kokarin Kiran layin Saddiq,"

"Hayaniyar da taji anayi kusa ga Angonta yasa ta murmusa Domin tasan cewa shi da abokansa NE,watakila ma sun karasou,"Sallamar CE ta dawo da ita hayyacinta,"

"Tace"Nace har Yanzu Banga Kun zo ba!"Kuna hanya NE,Dan Allah my kuyi sauri Wallahi Mutane sun taru Kuma kune ake jira...mansura ta Gama zancen da sangarta da nuna damuwa tamkar Yana agabanta!"

"Sauke Numfashi yayi yace"kiyi hakuri Daman Yanzu nake Shirin kiranki,Gaskiya BAZAMU samu zuwa ba!"sai dai goben ki bawa kowa Hakuri wani uzuri ya gitta Mana... sannan Umaima ma batajin Dadi Shiyasa bazata zou ba!"Kuma......"

"Datse kiran Mansura tayi batare da k'arasa Jin me zai fad'a ba!"wasu Hawaye NE suka zubou Mata!"Ranta Idan yayi dubu ya baci!"me Saddiq ke nufi da ya canja Mata hakan,kwana biyu,dole NE ta dauki matakin Kare Dangi akansa!"

"Sai ware Ido take tana kallon Mutane!"ranta ba Dadi!"Can sai ga kawarta Hindou ta karasou Yar fara lukuta da ita,Mai manyan mazaunai,tana tambayar ta yadda Sukeyi da Saddiq,"

"Mansura labartawa Hindou komai tayi,"tana kokarin Kuka!"

"Hindou Tace to meye aciki mansura ki Masa uzuri Mana! muje mu chashe kawai kinsani da rawa kamar mazari!"Kiyi Hakuri!muje Ayi pics share hawayenki..!"

"Har sun Kama hanya sai ga Sahura tana rangwad'a ta tare su,"Hindou Daman ba shiri take da su Sahura ba, Shiyasa ta sake hannun mansura ta Kama gabanta! Domin ta dabance acikin su ita tana da kirki,"

"Sahura tambayar mansura tayi ya ake ciki!"

"Mansura ta Gaya Mata yadda sukayi da Saddiq din Sarai ranta abace!"

"Sahura zarou ido tayi waje!"cike da mamaki Tace"Wallahi ke lusara CE,mansura da har kinka Bari Saddiq yafi karfinki,Har da Masa Hawaye!?"Kinga nikam bazan Baki Shawara ki biye masa ahaka ba,Kina mallakar cutar d'a namiji!"Ay namiji da kike Gani mansura,ba Dan goyo bane,Kuma allurar guba NE,Gashi yasaki bakin ciki tun Yanzu,Wallahi idan kin dauki Saddiq uba to karshenki Zama marainiya!"Bari kiji SHIFA Namiji tuwon kayane,miyar allura ka gutsira ya soke ka,ka hadiye Kuma sai lahira,"Yanzu muje ki fuske kamar komai Bai faru ba!"Duk Wanda ya tambayeki Ango kice suna hanya motarsu ta lalace,yace"zasu sauya Mota suna tahowa!"Ni kuma An juma zanje gidan malam na Kan tudu na amso maki Mai kankat,Dariya Sahura tayi ta shaidanu...Tace Daga Nan Hajiya Mansura Labari zai canja,saboda zakiyi maganin iskancinsa,Ai yayi kadan ya samu bakin ciki,"Muje tawan...Badai AKWAI dumus ba,Ai magana ta Kare,"

"Ajiyar zuciya Mansura tayi Cikin Jin Dadi tabi kawarta wacce tafita Zama guba Sahura kenan, Uwar daba lamba Daya!"

"Yadda Sahura ta tsara hakan CE,ta kasance Nan akaci akasha aka chashe Duk da har Yan gulmace-gulmace anyi na rashin zuwan Angon," Nan dai aka Gama cin taro ya watse,"Daga Wurin event din Sahura Bata zame ko'ina ba sai gidan nakan tudu,"Kudi ta zuba Masa shi Kuma Babban Asiri ya bata Wanda Mansura zatayi amfani da shi,Idan Saddiq yazo gobe d'aurin aure,"( _Hmnnn..Daga kin gaskiya dai sai bata inji yar mutan Dikkawa_)

"Bayan na farka na samu Jikina yayi min sauki a daddafe na karaso falon inda momy tare da gaidata itama ya jikin take min,Nan na zauna kusa da ita akasa,Duk da ba yadda batayi na hau kujerar ba,Amma na k'asa,"Shiyasa momy taji Dadi tare da yabawa da halayena

"Abokin kuka!" akace shi ake fadawa mutuwa!"Tun fitar su momy Daga gidan Jawad ya Kira Saif sun Dade gidan suna neman yadda zasu shawo kan Matsalar!"Wanda akarshe gidan na momy suka nufa domin su bata Hakuri Alan Duk abinda ya faru!"

"Ina zaune Ina kallo Amma Rabin hankalina na Kan tunani,momy mita ta dinga yimin Akan na daina tawan tunani,"Ana hakan naji kukan motar Jawad,"Zumbur na Mike nabar falon Wanda hakan da nayi yayiwa momy Dadi,saboda batason Jawad ya ganni!"

"Gyara zamanta tayi tare da hade girar sama da ta k'asa!"

"Da Sallama suka shigo falon sum-sum da su kamar barayin masallaci,"

"A can k'asan makoshi momy ta amsa, batare da ta kallesu ba!"

"Saman kujera kowannen su ya zauna suna gaidata."

"Harara ta watsa masu,Tace to marasa *TARBIYYA* Ni a saman kujera kuma samanta,to Ni Bari na sauko sai KU zAuna yadda Idan anzou za'a iya bambance Waye karami acikin mu!"

"Da sauri suka dawo Kasan!tare da sunkuyar da Kai!"

"Saif yace"Daman Momy mun...mun...munzo Domin mu roke ki....Dan Allah ayi Hakur...."

"DakAta saifullahi fita idona na rufe!tun ban Saba maka ba!"

"Idan Hakuri Kuka zo bani! to maza ga hanya KU fita...Domin Ni bani aka nemi kashewa ba!"KU nemeta!KU bata Hakuri..."

"Momy Dan Allah kiyi hakuri Naga kamar ranki ya baci...!''Ay Jawad Bai karasa ba!"sai Jin saukar Mari yayi a fuskar SA!"

"A hasale!momy Tace"Jawad yaushe ka koma marar Hankali wato ma Kama...ne ko!?"To saurareni kaji Raina ya baci ba Kama bane!"Kuma nayi Allah wadai da halinka..sai yanzu na yadda da Duk abinda ake Gaya min nakasa Ganewa"

"Wato rashin imaninka har ya Kai,ka nemi aikata kisa!"kanaso ka kashe Nadiya! Duk bangon jaridar duniya yayi ado da fuskar ka akai!?"Kanason Ace Kai Kuma ka kashe matarkA!?A yayata ka a bakunan mutanen duniya,Kanason a fallasa Dukkan asirin ai mana kazafin abinda bamuyi ba!?"To ka kyauta Kuma na godewa Allah da burinka Bai cika ba!Ya tufa min asiri"Abinda nakeso da Kai ka rubuto takardar sakinta ka kawo min,Tunda baka sonta Toni da iyayenta muna sonta!"KU Tashi kubar min gidana kuje gaku ga duniya!"

"Duk inda hankalin Jawad Yake yayi mugun Tashi...tun Kam Marin sa da Momy tayi, abinda Bai taba faruwa ba!"Har zuwa kalamanta da suka D'aga masa hankali!"

"Kuka Yake Yana rokonta Amma banza tayi Masa akarshe barin falon tayi!"Cikin takaicin halayen Jawad

"Saif ma Sai da yayi Hawaye! saboda tsabar tashin hankali!"Hakuri yake ba Jawad Amma ya k'asa yin shiru Domin Bai had a kowa da momynsa ba!"Haka suka fita daga gidan Basu ko San Nadiya tana Nan ba!"

"Shawarar zuwa gidan Mallam Balarabe sukayi Domin su sameshi su bashi Hakuri Akan abinda ke faruwa,"Daga Nan su ga Nadiya su Bata Hakuri ko momy zata huce!"

"A zuciyar Jawad Babu sauki! Domin haushin Nadiya yama qara ninkuwa,A ganinsa sanadinta ya samu matsala da farin cikinsa wato momy,nadamarsa daya bacin ran momynsa!"Amma ba Domin hakan ba,Shikam ko a aljihun wandonsa,Domin ya huce haushinta!Da takaicin bakinta da ya kirashi da kalmar da ta tsaya Masa arai.

"Saif Addu'a yake Allah Yasa kada Jawad ya saki Nadiya, domin burinsa shi da Saudat agyara komai Amma Gashi Abu sai qara lalacewa yake!"Allah dai ya shiga lamarin, ya shirya shine Addu'ar saif da fatansa Wanda tuni jiki ya d'auki raw'a!"Saboda akwai SA ahannunsa acikin ta'asar,"bayaso asirin su ya tono.

"Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba,"Domin harda wata k'aramar liyafa aka hada ta jin dad'in agidan Jalilar Saddiq,"Wanda akayo masu oder a Hilton Restaurant,"

"Madam Jalila Ita da Yan uwanta da Saddiq da Umaimah da mijinta kowa yaci gayu an canja tufafi anyi kwalliya,sai da aka bude tarou da Addu'oin da fatan Alheri,"Sannan aka Soma jawabai da nasihohi sannan aka Fara kwasar gara,"Jalila Kam an sha kyau Cikin wani hadadden material sabo dal Wanda Umaimah ta Bata shi kyauta,Domin ta dinka Bata SA ba!"gashi Anje saloon an wanke Kai,tayi parking dinsa,ga makeup an zuba na ji nagani na fad'a,sai kamshi ke Tashi gidan,"Domin batada maraba da Amarya,"Dan tuni ta d'auki aniyar kawo gyara a rayuwar ta Musamman tsafta,kwalliya,da iya girki Wanda umaima ce tayi Mata lacca mai zaman kanta Kuma jalila ta dauka Dan ko yanzu sai kamshi take zubawa.

"Saddiq da Ali Sai murna suke har sun manta da wani dinner ga Babban Dinner anayi agidan uwargida Mai gayya Babban gorou sai magogin karfe,tsohuwar Zuma maganin cuta!"Jalila kainuwa dashen Allah Maman Mufeed da Mufeeda,"

"Fad'an irin farin Cikin da Jalila take ciki bazai misaltu ba, sai dai fatan Alheri,Su Anty Talatu, Rasheeda da su Tahir sun koma gida Cikin jin Dadi,"

"Haka Aliyu da Umaimah gida suka wuce,"

"Bayan fitar su ne Jalila ta Rungume Saddiq tana bashi Hakuri akan Dukkan abinda ya faru,"

"Share Mata Hawaye yayi tare da Kallonta ta koma Masa sabuwa har wani kyau tayi,"Yace na yafe maki Jalila Allah yasa MUDACE,"Daga Nan Tashi yayi,ya shige Dakinsa Domin ya samu ya kebe Nan ya Kira mahaifin SA Mallam Musa,Sun Jima suna tattaunawa Cike da fahimtar JUNA Wanda akarshe sukayi sallama,"

"Ko da ya dawo falon Bai Sami Gimbiyar ba! hanyar kofar da zata sadashi da gefenta ya nufa,yana shiga rufo kofar yayi Daman sun rufe komai nasu da bakin suka fita,Mai gadin gidan ma Yana bakin aikinsa mudi kenan Dan dashi aka dawo Kuma yaji Dadin dawowar Hajiya Domin ya fahimci ta sauya yanzun zai samu Abinci yadda ya dace,Fatan Alheri ya yi masu da asuba tagari.

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*

_ZAFAFAN COMMENTS NAKESO FANS,KAMAR NA KASHE MAKU KUDINKU👌🏻_
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*
Chapter 52 · 0% Book details