← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 65

Sashe 25

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk da nayi kokarin boyewa Saudat damuwa ta Amma a hankali sai da ta fahimta...A karshe dai KAFIN mu Isa gidaa kwashe komai na labarta Mata...Hakika ta tausaya min Amma tabani Hakuri saboda shi Mallam Bai taba furta min kalmar so ba!"Sai dai ya nuna min Alamar hakan..."Sannan ta fahimtar da Ni shi mutum NE Maison ganin dalibi Mai hazaqa Sannan Tace min Ni Kaina nayi wauta da na fad'a Sonsa har na kamu da yawa hakan...Gashi Nan shi ya canja wata da Ni Kuma batare da ya damu bah!"Na shiga tashin hankali sosai Amma yanzu Naga darasi domin nagane kuskure na."( _Hattara Yan Mata da yawa kuna wauta irin ta Nadiya,Sai kiga saurayi Yana nuna Miki so Amma ya kasa furta miki,A maimakon kema ki share sai ki fad'a so,shiyasa sonki zai fi nashi son to akiyaye domin gujewa wulaqanci_)

"Bayan RABUWAR mu da Saudat gida na shiga,dakina na nufa...."Ban sanda na fashe da Kuka bah!"

"Sai da nayi Mai Isa ta na koshi Sannan na fito bansan meke min Dadi bah!"Na kasaci da Sha zuciyata taimin nauyi!"A hakan na hakura na Cigaba da ayyukan gidan..."Saboda tun jiya mama ta gaya min zata fita unguwa..."

"Ko da ta dawo ta sameni Ina aiki Amma Raina ba Dadi!"Idanuwana sunyi jajur...ko da ta tambayeni lafiya!"Nace Mata ba komai bacci na tashi..."

"Kyaleni tayi duk da ta fahimci da wata aqasa Amma tasan cewa a hankali zata San meye damuwata..."

"Da Rana ma Yaya Saddiq ya shigo da yaran sa sunyi Mana bankwana zasu koma sakkwato..."

"Mama ta bada kayan yaji da SAURAN tarkace akaiwa Anty Jalila."

"Kamar Kar su wuce naji!"Nan dai Nima na shirya Naje Gidansu Saudat.''

"Ban jima ba!"Aka turou min sakou kamar kullum na gaisuwa tare da fatan alkhari Wanda akarshe ake rubuta ... min Daga mesonki M.JAWAD."Banyi mamaki ba domin idan da sabo na Saba..."Tun ban mayarwa har nafara mayar Masa da reply na NAGODE."Fira mukayi sosai ni da saudat tare da bani shawarwari akan Jawad da Kuma Juyawa malam yunus baya."

"Tuni na dauki alqawarin mantawa da soyayyar Mallam.. sai dai Nikam bana Jin masoyin boye amatsayin masoyi domin bazan iya Sonsa ba."A yanzu da ace za'a bani zab'i da Abokina Naseer zan zaba domin shine mukafi dacewa da shi."

"Mommy zaune a bedrum tana ninke kayan ta....sai Gashi ya fadou ba ko Sallama...duk da ta Dan tsorata akan baiyi Sallama ba!"Amma sai ta share shi...''Yace mum gani!"

"Jawad!!"Daman Ina son muyi magana Mai muhimmanci da Kai!"Zauna anan ta Nina Masa gefenta."

"A gefen gadon shima ya zauna Yana fuskantar mahaifiyarsa..."

"Jim tayi na wani lokaci Sannan ta dubeshi shi da sanyi Tace"Jawad ya kamata muyiwa Abba Adalci!Lokaci Yana Tafiya fah! yanzu Naga hankalinka ya dawo jikin ka kayi hankali!ka daina shashanci ka fara Zama yaron kirki Mai Kamala kamar yadda Abba Yake son kazamou Mai *TARBIYYA*...Sanadin neman auren Yar gidan *TARBIYYA* ya canja kaf rayuwarka ta Daa yanzu ta dawo sabuwa kamar kowane D'a nagari Mai *TARBIYYA*"Yanzu NE Ya kamata mu Ida nufin Abba..."Ina son muyi kokari mu fara neman abinda ya Sanya agaba kafin mutuwarsa!..."Mu Idar da aikin da ya kawo shi wannan kasa ta Nigeria,Kaga kakannin ka suna can suna na jiran tsammani!."

"Sanin kanka ne...Abba ya barmin wasiyya!"Ya Kuma barmin amanarka da ta dukiyarsa ka da Kuma ta aikinsa." Ina son ka cika Masa burinsa jawad lokaci yayi da ya kamata na warware maka komai yadda zaka gane Wanene Kai meye asalinka da kuma Danginka..."

"Ajiyar zuciya yayi yace"To mom zanyi kokarin hakan."Nagode Allah da ya kawo Wannan lokaci da na Dade Ina jira..."

"Yawwa,Jawad zan Gaya maka komai nidai kayi kokari kayi aure domin shine mabudin warware maka abubuwa kamar yadda Abba ya tsara da Yana Raye!!"

"Ba komai mom aure kamar gobe NE,zanyi da yardar Allah."

"Masha Allah Tace tare da sauke ajiyar zuciya so da kaunar tilon danta Yana fizgar numfashinta."

"Cike da kauna tare..yanzu ya zancen Nadiya ne!?"Jiya saifullahi yace min ta dawo tana gida hutu take."

"Tana lafia.....mom Eh...na manta na sanarda ke tafa dawo."

"Yaushe zaka kawo min ita na ganta."

"Duk Ranar da kikeso mum."

"To...kamar Jibi akawo min ita zaifi."

"An Gama mom,zan kawota...."

"Shi kenan Allah yayi maka Albarka."

"Amin...my Dear.."

"Tashi yayi Yana kokarin fita...mom taqara da cewa Nifa na kosa ne inga surukar tawa saboda nidai Tuni na yaba da tushenta nasan cewa Nadiya yarinya CE Tagari wacce nutsuwa Ta wadaci rayuwarta..."

"Haushi yaji acikin zuciyarsa saboda ya tsani! yaji ko da sunanta NE!"A fili Yake yayi yace"Hmnnnnn mom kenan Lalle kinaji da yarinyar nan..."

"Kwarai da gaske Jawad."

"Duk da Kasancewar ta Yar talakawa!?"mom

"Ayni Tuni Na daina tsanar talakawa Tunda na hadou da ahlinta Jawad saboda mutuncin su ne ya saye son duniyata..."mum taqare zancen tana dariya."

"Dai dai KOFA ya juyo ya Kara kallon mom..Yana murmushi Sannan yace"To Allah yasa ta soki itama kamar yadda kike sonta."Domin Ni nafara KISHI!"tun ba a ganta ba!An fara santi hakan..."

"Amin...Jawad Ayna San yarinyar kirki CE zata so ni kamar me.." mom Tace alokacin da yake kokarin fita daga Dakin."

"Cigaba tayi da gyara Kayanta aranta ta kosa taga ko Wacece Nadiya..."

"Shi Kuma Yana fita wani tsaki yayi tare da cizon yatsa!"ya ce azuciyarsa"hmnnnn Nadiya ta shigo hannu kawai sai tayi Kuka da hawayenta Wallahi!sai tayi Dana sanin kirana da abinda ta ambata Abaya wani Hawaye ya zubou Masa Mai zafyh!"Hannunsa yasa ya goge tare da jera ajiyar zuciya."

"Sashensa ya nufa wayar Saif ya Kira..."Nan sukayi waya Mai Dan tsayi kana suka rabou da zummar zasu hadou an juma da yamma."

"Tunda Naje Islamiyya da yamma na canja domin ko kallon malam yunus Banyi ba!"Na daina sakewa da KOWANNE malami..Abinda ya kaini shi nakeyi na dawo daga Ranar na canjawa kowa."Kullum Ina waya da Naseer..."Da su Esha,Deeja,Da Kuma Deeyart ayanzu ba abinda ke damuna domin na jingine duk wani son malam yunus gefe..."Saudat da kanta sai da tayi mamakin irin dakiyata ta Kuma jinjina min..."Saboda Sam batayi tsammanin zan debe komai araina da Wuri hakaan."

"Haka na Cigaba da rayuwar Hutuna lafiya qlaw Bani da damuwa domin Naseer ya Gama min komai mun Kara shakuwa sosai awaya."

"Hakan agefen Jawad ko yaushe Yana turo min text Nima Ina tura Masa Sannan muna waya sai dai ba sosai ba!"

"Na fahimci Jawad mutum NE Mai hankali ilimi da Kuma tsari Wanda gayu da kwarjini ya wadaci rayuwarta Wanda Kuma alamun cikar kima da hankali ya bayyana agaresa duk da bamu San juna ba!"Amma halayensa da Yake nuna min awaya ya Sanya naji Yana burgeni..."Sai dai har yau Babu Sonsa ko da kwayar zarra azuciyata."

"Ana hakan kwanaki sai Tafiya sukeyi har lokacin komawa na sokoto yayi domin hutun mu ya kare har naqara mako biyu...Shiyasa Yaya Saddiq ya Kira Ni Yana fad'a Nan NE iyayenah suka tattara abinda suke da shi nayi Sayayyar Kaya na koma makaranta..."Sai dai Wannan karon karatu NE agaban mu domin mun fara darussa masu wuya shiyasa na ajiye komai nafara FUSKANTar karatu na haikan ba da wasa ba."

"Saif da Jawad NE Cikin shiga ta Alfarma..kokarin fitowa sukeyi Daga hadaddiyar motar su..."Dai dai Inda aka rubutawa Admin suka nufa tare da want malami Wanda ga alama Dan jagoran su ne...."Ba da wani jimawa ba suka Isa kofar wani office da aka rubutawa M.BALA da farin fenti...manne akofar."

"Knocking sukayi Bayan an basu damar shiga Daga ciki...Sai suka shiga Bayan sun gaisa..."

"Wanda ke tare da su yace Mallam Bala wadan Nan sune samarin da kuke waya da su Jawad da saifullahi Daga kebbi."

"Dariya Wanda aka Kira da Bala yayi irin ta rashin mutunci Sannan yace"Ba dai kace sun jika ba ko sahabi?"

"Sosai...ko ay manyan yara NE ranka ya Dade Wanda aka Kira da sahabin yace Yana murmushi da zumudi."

"Gud...malam Bala yace Sannan yakara da cewa naji duk bayanin KU awaya Sannan sahabi ya fad'a min komai...Wannan bukatar taku duk Mai sauki CE...matukar zanji damen kudi atafin hannuna to zan iya aikata komai Aduniya..."

"Sahabi ya karbe Tabbas hakane oga ai duk fadin makarantar nan Babu Mai ja da kai.."Duk Wanda yaja da Kai xaici kasa..."

"Dariya yayi tare da zuqar tabar hannunsa kana ya hurou hayakin waje cike da gadara yace ku nuna min hoton yarinyar zansa anemo min facultyn su da duk wasu details nata duka Nan zuwa jibi komai zai wakana sai dai KU saurari sakamakonsa aikin ku..."

"Da sauri Saif yasa Hannun sa a aljihu ya dauko hotonta biyu ya mikawa sahabi ya duba da kyau kana ya baiwa M.Bala..."

"Ido ya turou fili tare da zuge gilashinsa sa yaqara mannawa Yana kallon hoton...dariya yayi Sannan yace Wannan yarinyar sunanta sorry...Domin Ni Kaina ta taba min rashin kunya ko da Baku kawota wurina nasan watarana zamu hadou da ita a makarantar nan....Kenan yanzu can hada Mata zafy! biyu saboda Nima Ina da takaicinta!!!"

"Jawad yace mudai aikin mu kawai muke bukata kayi Mana kuma ya tafi daidai."

"Saif yace saboda akwai Dan uwanta ko Mallam Saddiq bama son ya shiga Cikin lamarin Nan yakawo Mana cikas...."

"Haba yaro ay duk farin makarantar Nan ta shehu shagari ka bincika Babu Mai fad'a aji kamar m.Bala Nan da kake ganinsa shaidani NE ko shaidan da kansa yana Sara Masa Kai duk makarantar Nan tsoronsa sukeyi har provost da kansa Sara Masa yake...saboda Yake mutum a halaka wurin bokaye Bakomai bane awurinsa...Sahabi ya karashe zancen cike da Jin Dadi da Kara Koda da kambaba ubangidansa."

"Kallon JUNA sukayi sannan Jawad ya zarou Damen kudaden da shi kansa baisan adadin su ba ya ajiyewa M.Bala..."Saif ya Mike tsaye yace to Mallam mu zamu KOMA sai munji Daga gareku..."
"Sahabi washe baki yayi shi da M.bala Ana rige rigen daukar kudi Tuni M.Bala ya kwache ya tura aljihu shi Kuma sahabi cewa yayi haba yallabai ay sai kabari na kirga Dan gudun kuskuren biyana kudin aikina..."
Chapter 25 · 0% Book details