← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 65

Sashe 17

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaune nake Ni kadai adakin mu Ina dafa abinci Ina karatu da yake yanzu mun fara gwaji(test)."

"Shigowa sukayi Dakin ko sallama basuyi ba da yake yanzu sun daina kulani sosai kamar baya."Ko kallon su Banyi ba!"Na Cigaba da karatuna."

"Esha CE Mai raha acikin su."Tace Sannu Malama Nadiya."

"Yawwa,Sannunku Nace da ita!"

"Baiwar Allah Naddy Karatu,kawai ake ta sha..."Inji Deejah tana dariya.

"Banza nayi Mata..tashi nayi na Duba abincina shinkafa da wake ce,Na had'a ta da Mai da yaji,zubowa nayi da su Nace suzo muci,Ba kunya Esha da Deejah suka zauna mukaci tare Dan ba kunya da zuciya ne da su ba!."Deeyart Ita dama akwaita da Jin kan tsiya Kuma bata wani yina sosai Tunda taga bana layin su."

"Nan muka dinga cin abinci suna bani labarin yawon su da suka fito dana samarin su na malamai da Yan makaranta har na cikin gari ba'a barsu Abaya ba...nidai Daga Eh,sai Ehimnn ke hadani da su,Ina cin abincina su Kuma sunata zuba"Har muka gama nan ne nake basu Shawara akan su dinga shiga aji suna karatu,saboda idan har suka cigaba da hakan Sam basu yiwa iyayensu adalci ba,"Idan dai Haka rayuwar su zata cigaba''

"Deeyart da ta cika faam tace"Ke Malama kisani mufa ba yara ba NE!"Da Zaki wani zo kina Mana surutun banza to ki ajiye gaskiyar ki agefe!"watarana zatayi Miki amfani."Naga kina Mana kallon Wasu iri!"Me kike nufi Nadiya!?"Mu sakarai ne marasa TARBIYYA!?"To idan bakisan Wacece Badiya ba bari na sanar maki Kuma idan har zakiyi min adalci to Zaki iya Kirana da Mai *TARBIYYA* wacce iyayenta sukayi Mata *TARBIYYA* Mai kyau,Sai dai tuni ni na ajiye masu kayansu agida kafin na koma na DAURA Daga Inda na tsaya."Domin naga anan bazatayi min amfani ba!"Ni Badiya na kasance yarinyar kirki Babana limamin unguwar mu ne,Duk garin gwadabawa ba wanda Bai San shi ba,Haka mamana Malama ce matan aure take karantarwa Ni da yayye na duk malammai ne."Ko da na shigo makarantar nan da mutuncina da *TARBIYYATA* sai dai haduwata da Esha yasa nafara canja rayuwata saboda wannan CE mafita agareni matukar inason in Zama babbar yarinya kamar kowa Nan muka hade da Deejah."Ba komai yasa Ni canja rayuwata ba!"Illah!nagane a jami'a idn baka budawa kana wanka,to Kai ba kowa bane!"Kuma ba Wanda zai San da zamanka..malammai ma da kansu basa kula ka bare ka nemi Alfarma ayi maka da sauri."Amma ki Duba yanzu hakan bama shiga aji Amma muna da sakamako Mai kyau ajiye Wanda ma yafi naki ke Mai ikirarin kinzo karatu Kuma kinayi.Ki zauna ki gani zama amshi Takardun NCE lafiya law."Batare da Wani wahala ba!"Ko ba Haka Eshaa."Deejart Tace tana kallon abokanta cike da bacin rai!"

"Tabbas Hakane Deeyah Domin Ni kaina gidan mu an min *TARBIYYA* sai dai ni ban dauka ba tun farko,Ni tun Ina gida Nike sharholiyata kuma da taimakon mamana,Sai dai Tace min Aysha ki kula, saboda tana Sona batason bacin Raina ko Baba yaso hukunta Ni ita ta ke tarewa."Kullum cikin kareni take Domin ganin kar aga nayi laifi!"Shiyasa Duk abinda nake tana sane Domin da taimakonta."Kuma idan nasamu kudade na kan tsakura na sammata."

"Shiyasa da nazo makaranta na Cigaba da harkokina!"Na fahimta kokarinka da dagewarka bashi kesa ka ci jarrabawa ba!"A wannan zamani saboda tun Ina sakandare nasan da hakan,Wannan ne dalilina da yasa nake abinda Raina ke so."Amma Nadiya ki gane mu ma fa kamar ke muke muna da ilimin mu ki daina Mana kallon maras *TARBIYYA*"Esha taqare zantukan ta tana dafani."cike da gamsarwa."

"Deeja dariya tayi Tace nikam agaskiya idan Nace iyayenah sun min *TARBIYYA* To hakika banyiwa kaina adalci ba!"Saboda Ni ko gidan *TARBIYYAR* ban taso ba bare nagani anayi na koya."Iyayena rikakkin Yan boko ne."Duk abinda mukeso agidan mu shi mukeyi Daga mu har iyayen mu kowa sha'anin gabansa yake."Shiyasa Ni da kannaina Duk abinda mukeso shi mukeyi."Kowa Yana da right tamkar rayuwa akasar turai hakan rayuwar gidanmu take,Nifa ko Islamiyya bana zuwa agida anan makaranta na koyi ibada saboda masallaci da muke zuwa idan muna Nan,Kuma anan nakejin karatun alkur'ani da waa"Azi."Kinga nikam amakarantar nan na fara koyon *TARBIYYA*

"Shiyasa Tunda na taho na samu su Esha da Deeyah amatsayin kawayena sai muka dace da JUNA!"Babu Mai Jin kanmu muna zaune lafiya qlaw, harkar mu mukeyi Kinga kowa ya ganmu yaga manyan yara,mun samu sutura,Kudi,wayoyi masu tsada ki Duba kigani kowaccen mu iPhone 11 take riqe da ita."Muna business wata anan har iyayenta take taimakawa."

"Hmnnnnnn yanzu motoci ne kawai suka rage Mana mu saya!"Kwanan zamu Kama gidan kanmu Domin munfi karfin zama hostel."Kuma Nan da kike ganin mu Duk abinda muke iyayenmu basada Labari musamman Ni da nake a zamfara."Yanzu zamani ya canja abubuwa da yawa mukeyi Batare da sanin su ba."Domin kuwa sune suka haife mu Amma mun fisu wayo da davaru."Ko karatun mukayi karshe kadamu za'ayi abaiwa wasu can da basa karatu muna Kallo,da musha haushi gwara mu bada haushi Nadiya."Kedai da kikaji Zaki iya rayuwar jami'a a Haka kamar bagidajiya da Kyaunki da kyaun jikinki sai kiyi."Amma kisani Nadiya zamanki ahakan bakida Wanda zaiyi making tsaye a makarantar Nan babban hadari NE."Saboda kowa amakarantar Nan yasan halin Wanda kike ganin ya isa gareki!"Shifa daban NE acikin lectures din makarantar Nan."Yana Daga cikin Yan tsirarun mutanen ake ganin masu mutuncine Kuma ake mutuntasu.."Sai dai Yana matsala Baya neman Alfarma ga kowane malami Kuma Baya yiwa kowa Alfarma."To ta Yaya Mallam Saddiq zai taimake ki ahakan Nadiya.!"Kina ganin Zaki iyah cinye jarrabawa ahakan Bayan akwai iri irenmu da akeyiwa alkawarin sakamako Mai kyau!?"Me kike so kicewa iyayenki idan har ba ki ci jarrabawa ki ba!?"Duk da mun fahimci Duk acikin mu iyayenki sunfi namu rauni!"Ba kuda shi ku talakawa NE!Amma gashi Allah yayi Miki baiwa bakya amfani da ita Dan kawai akiraki Mai *TARBIYYA* Mai mutunci Mai kokari Mai kamun Kai."Kisani acikin duniya akwai na kwarai kuma akwai Dan iska,Duk yadda ka zama bazaka wuce zagi ba awurin mutane!"Yanzu hakan ke kanki Nady akwai masu zaginki..Dan Haka kowa yayi abinda yakeso Kuma yake ganin mafitace agare shi,Wannan Shine nasara arayuwa Nadiya."

"Numfashi na sauke Mai nauyi!tare da kallon su tabbas wadan su zantuka na su hakika gaskiya ne,Kuma sunyi tasiri azuciyata ganin yadda rayuwar makarantar take tafiya..." Sai na kasa cewa komai!"Kallon junan su, sukayi suna murmushi..."Tare da Cigaba da zantukan da zasu janyo hankalina garesu."A karshe hannunsa suka aza tare da yimin inkiya na daura nawa akai saboda suna Sona sosai."

"Duban hannayen sau na Duba tare da Kawar Kaina!Tuni na nutse a cikin kogin duniyar tunanin zamanin mu ayau."Shiru nayi na Dan lokaci Ina nazarin amsar da zan basu saboda karatun Yanzu sai da dabaru ko mu hade da su!?"Ko Kuma mu raba hanya da su!?"Shi nake tunani, Domin ina Gudun watarana."Yanzu meye mafita agareni na shiga tsaka Mai wuya Ina son karatuna sosai,Amma Kuma Ina Jin asarar watsi da *TARBIYYA* ta!!Daman da kokarina da Kuma taimakon Yaya Saddiq na kwantawa gashi ance Baya neman Alfarma Ni ya zanyi Yanzu!!"

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA GOMA*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

_____________________________________

"Kimanin wata D'AYA da barina gidan,Anty Jalila ta shiga damuwa saboda Duk ta daina ayyukan da ta saba da yai sanadin zamana agidan,sai Yanzu ne ta gane cewa tayi wauta! na cewa na koma hostel da Wuri,Akan zance subyh saboda basu ko ga yaya Saddiq Dinma yace Yana Sona, hasashe ne kawai na zucia,meye ma Habibinta zaiyi da Ni karamar yarinya!"A gaskiya subyh tayi Mata asara Domin gashi Dan hutawar da takeyi ta daina aiki ya dawo Mata sabou!"Hakan gefe yaran sun damu da akai su wurina sosai.Shiyasa Yaya Saddiq Ya shirya ranar lahadi suka kai min ziyara wuni sukayi min a hostel,Su Esha sai yawo suke da su Mufeed block by block suna nunawa Yan faculty dinmu Wai ga yaran malam Saddiq."Da yake yaran barkallah akwai farin jini Domin sun biyo haske da kyaun maman su."Sai hotuna ake masu."Nidai Ina daki suka dawo da su,Kayan kwalam su Esha suka baiwa Mufeeda da Mufeed."Masu yawa har bakin get suka rikamu, nida su muka nufi office din Yaya Saddiq."

"Da isar mu muka samu Yana rufe office,Masinja ya baiwa keys din office suna sai da safe da shi."Kudi Yaya ya bashi da munna ya Yana godiya.."Da gudu suka karaasa wurin Yaya tare da nuna masa kayan da aka basu na chocolates masu yawa.. "suna cewa Abba kawayen Anty Nadiya ne suka bamu."Itama Kudi tabamu tare da nuna masa Yan hamsin da na basu na naira dari."

"Kallona yayi yace su waye kawayen naki!"Fuskarsa a daure."

"Daman ba qawayena bane Yaya!"Dakin mu D'AYA da su."

"Gobe ki Kawo su office Dina na gansu."KU Kuma KU shige Mota mu tafi."

"Mota yake kokarin shiga ni kuma Ina bayansu gefen Mota, yaran sai hannu suke Daga min."Suna yaushe zAnzo,nace sai wani sati zAnzo weekend."Ina masu Bye kamar kar su tafi!"

"Wayar Yaya ta dauki ruri Ina kokarin tafiya..A zuciata Ina Jin tsoron Kawo masa su Esha saboda sunyi popular sosai a school din."Nasan sarai Raina zaiyi mugun baci."

"Ke tsaya!"na ji Yaya yace da Ni."Har na fara tafiya."

"Juyowa nayi Adan razane!Rass!!!Kirjina ya buga na karaso gareshi..."

"Ya ce"Amsa Allah!Wannan yarinyar ce,Fitinanniya!!!!ta dameni kamar batasan bakida waya ba!"Ki gaya mata karta Kara kirana banson damuwa!!"

"Amsa wayar nayi jikina na rawa ko ba'a fad'a nasan mansura CE."

"Da Sallama na Kara waayar akunne nah!."

"Amsa,min tayi cike da iyah yi."

"Tace"Alo kawas ya kike ya karatu?.."

"Lafiya qlaw.."nace agajarce!"

"Bayan mun gaisa nace mansura mata itama ya nata karatun?."

"Lafiya qlaw,Nady nayi missing dinki da na Yayanmu kina Ina NE sai ki kwatanta min zan zo?"

"A tsorace nace Mata Ay Ina zaune a hostel."Nan dai na kwatanta Mata."

"Tace yawwa zan shigo mu gaisa...."

"Ke ban wayata bAnson shirmen banza..."Yaya ya katseni."Haushi ya Kama shi aransa Saboda shi Sam ya tsani Wannan heqaqqiyar yarinyar Mai Kama da figaggiyar kaza."Zaiyi kokarin ya raba Nadiya da ita domin kareta da miyagun kawaye!"Ka da su lalata Mata *TARBIYYA* Mai kyau."

"Da sauri nAce mansura karki Kara Kirana da layin Yaya zan kiraki da Lambar Yan dakinmu nagode sai anjuma.."

"Ban jira amsarta ba!"Na katse Kiran tare da ba Yaya wayarsa Wanda har yayi nisa cikin tunani...Kallon tuhuma ya bini da shi."
Chapter 17 · 0% Book details