← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 65

Sashe 28

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dariya mom tayi Tace naji SARKI tsari...Zanyi magana da aminin mahaifin ka Alh.malami sambo da Mainasara sai suje ayi duk abinda yadace..."

"Mom zan gayawa Abban mu domin Wannan Tafiya yadace ayi ta shi...Inji Saif cike da Jin Dadi..."

"Yawwa Saif hakan yayi Amma nifa Rana daya nakeso ku angance Kai da nakan...Ya zancen ita samhan naka?"Mom Tace tana kallon Saif

"Momy ay na daina zancen samha da dadewa saboda yarinyar sai ahankali batada kirki nagane samha batasan meye ya kamata ba, saboda"Samari ne da ita barkatai da nayi magana sai ta nuna min ban Isa ba!"RABUWAR mu shine mafita domin dukkan mu muna gadara da arziki..."Saif ya kammala zancen Cikin sanyin murya..."

"Jawad ya karbe yanzu dai zamu fara lalabou wata mom Sai ayi tare ko ba Haka ba!?Nawan...."

"Hakan shi yafi dacewa Inji mum tana Murmushi taqara da cewa nifa Kuna bani mamaki ga yam Mata Nan kamar janfa ajos sai Kun darje!"AKWAI Yayan arziki da talakawa akwai Kuma masu tufin asiri...Amma garin ruwan idonku na banza har KU kwasowa kanku maras *TARBIYYA* ko da ruwa baya tsami banza..."

"Mom abar zancen aymu Duk mun daina komai yanzu Inji jawad."

"Allah yasa mum Tace."

"Saif yace Amin... "

"Nan SUKA Cigaba da tattaunawa akarshe mom tashi tayi ta barsu suna fira ita Kuma waya ta dinga yi da hamshaqan kawayenta Kuma Abokan business dinta gold."

"Daga Nan Alh.malami sambo ta Kira WATOU aminin marigayi mijinta All.Husamaddin tayi Masa bayanin SOSAI akan neman auren Dan su Jawad."Sai da ya Bata tabbacin gobe zai dawo daga Abuja Amma jibi zasu shigo ayi zancen komai Sannan suje neman auren."

"Fatan adawo lafia tayi Masa tare da GODIYA ta musamman Sannan sukai Sallama..."Murmushi mum tayi tare da kallon gilashin wayarta tana tunani Tabbas Alh.malami sambo akwai mutunci Kuma ya rike su da amana tamkar jinin Abba."

"Bayan mun Gama lectures din mu duka direct office din Yaya Saddiq na nufa..."Sai dai akulle yake Bayan Naga motarsa a parking place na admin din..."Fitowa nayi tare da jinginawa ajikin motarsa Bayan mintuna sai Gashi Yana sauri tace Kai shige mutafi..."

"Duk da Kasancewar bana Jin dadin jikina tamkar Mai zazzabi Duk jikina yayi zafi!"Ga wata fargaba da ta darsu araina!"Bai hanani hango bacin Rai a fuskar Yaya Saddiq ba!"Da alama kamar an tabou shi a office din da yafitou..."

"Gudun fitar hankali yake shararawa a titi kamar Mai Shirin tashi sama ko kallon Inda nake baiyi ba!"Sai Nan da Nan yaja tsaki tare da duka sitarin motar...."Na tsorata matuka domin ban taba ganin shi a irin Wannan yanayin ba!"Tsorona da fargaba ya ninkou!!"Domin kamar muyi karou a hanya Nan take cikina ya shiga kugi abukace nake da shiga bayi Shiyasa na kosa na ganni agida..."Addu'oin tsari nake jerowa Allah ya sauke mu lafiya Dan Tuni kwallah yafara min zuba saboda tashin hankali...."Ajiyar zuciya nayi alokacin da na ga mun shigo layin gida tare da fadin Alhamdulillah...."

"Waigowa yayi ya kalleni...bansani Ashe zancen zucine ya bayyana...Dai dai gidan yayi parking yace ke matsoraciya fice Dan Allah ki dauki ledojin nan ki shige da su Ni zan tafi masallaci...."

"To nace jikina na rawa saboda zawayi da ya matse Ni da kyar na kwashe kayan da jikata na nufi gidan...shi Kuma juya akalar motarsa yayi izuwa hanyar masallacin da ke Cikin Estate din...."

👍🏼Share👍🏼 comments👍🏼My fans

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 20*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

_Wannan safin kyauta ce,mallakin ku ne my people's😍_

_Zulaihat Abadany_

_Maimuna Ladan_

_Ummu Alisha_

_Momy Jega(Zeeman)_

_Mummy Yusuf(Fattyh)_

_Hindou Alqali_

_Aysha Bagudu_

_Ayush Iliyas_

_Nabeeha Ameenu(Sareena)_

_'Yar Father_

_'Yar Hussai_

_Hadiza Yusuf Buzu_

_Duk ina mika saqon gaisuwata agareku nagode irin sosain nan_❤

*Jinjina da gaisuwarki daban ce Babbar Yaya mai kamar Oummah😍 Allah yaqarou arziki da nisan kwana YAYA RALEEYAH MUHAMMAD AMINU,Allah yayi miki jagora ya zamou gata agareki Amin...Muna yinki Over*👍🏼👍🏼👍🏼
______________________________________

"Alh.Malami Sambo da mom ne zaune afalon tare da Jawad da Kuma aminin Alh.malamin,Suna tattauna akan zanjen neman auren Jawad..."Mom kudade ta BAIWA Alhajin Amma fafur yaki karba tare da daukarwa Jawad alkawarin zai zame Masa uba kamar Marigayi Husamaddin..."Alh.malami sambo ya Kara da cewa komai shi zaiyi na auren..."

"Mom da Jawad sai GODIYA suke Masa..."

"Ya ce ku daina GODIYA iyalan marigayi sun wuce GODIYA a ko'ina ba girmanku bane domin arziki da kansa jinjinawa Humaddin yake Sannan Alheransa NE ke bibiyar ku in shaa Allah Bazaku taba wulaqanta ba Aduniya domin marigayi mitum NE Kuma ya dasa alherai Aduniya

"Wasu Hawaye masu zafi!"suka zubowa momy habar gyalenta tasa ta share!"Tace hakane malami mun gode DUK da hakan da ka riqe Amana.."

"Jawad ma Idonsa ya kada yayi jajur!"Saboda tuna baya Tabbas sun Rasa wani bangare na rayuwar su sai dai Hakuri!"

"Alh.malami yace"yanzu kubamu address din gidan gobe sai muje...."

"Nan Jawad yayi musu gamsasshen bayani har suka fahimci komai kana sukayi Sallama da mom suka wuce...Jawad har parking place yayi masu rakiya cike da girmamawa...."

"Hannu Alh.sambo yaba shi sukayi musabaha..."Ya ce a gaskiya Muhammad Jawad naji dadin ganin irin sauyin da kasamu arayuwa inama ace marigayi zai dawo duniya yaga yadda nasa ya zamo kamili Mai cikar kima dA haibs kamar yake buri...."Ko kaifa jawad baka ga sauyi arayuwarka ba!?"Rayuwarka ta baya Bata Dace da Kai ba kuma batada amfani...Amma shigar mutunci da Kamala,sanin girman manya da mutunta su tare da amfani da ilimin nan biyu shine gishirin zaman duniya Duk Wanda ya ganka zai San kana da hankali da ayanzu.....Allah yayi maka Albarka ya shiryar suwa...."

"Amin...Abba nagode...Jawad yace Cikin sanyi da ladabi..."

"Nan SUKA wuce shima sashen sa ya nufa cike da mamakin zantukan Abba malami..."Ya Rasa ma Taya zai fassara Wannan shin wa'azi ne ko Jan kunne....Tsaki yayi tare da haye gadonsa wayarsa ya dauko Yana Kiran Nadiya Bata zuwa akarshe Baba Balarabe ya Kira tare da shaida Masa gobe magabatan sa zasu zo Inda yake..."

"Malam Balarabe cike da Jin Dadi yace to Allah ya kawo su lafiya ya Sanya Alheri...Nan SUKA taba hirar su Sannan sukai Sallama..."

"Sauya Kiran yayi zuwa layin abokinsaa saif...tare da labarta Masa Duk yadda sukayi da su Abba malami sambo..."

"Shima Saif din fatan samun nasara yayi masu...tare da yiwa Jawad Albishir din aikin M Bala na shehu shagari ya kammala dazu ya Kira shi ya tabbatar Masa da komai ya daidaita..."

"Dadi Jawad yaji SOSAI tare da dariyar mugunta yace aikin mu Yana kyau kace an kusa cimma wurin Baba.."

"Tabbas Nawan an kusa Mata shakar dambu..Inji Saif Yana kyalkyala dariya..."Fira suka dinga yi Jawad har da labartawa Saif nasihar aminin mahaifinsa...."

"Saif yace Basu San tubar mazuru CE kayi ba!"

"Jawad yace Duk da hakan nagane zama mutumen kirki wani Babban jigone arayuwa komai iliminka da kudinka da kuma wayewarka idan bakada tarbiyya Kuma Bata wadaci Rayuwarka ba saif Ashe ba ZA'A daraja ka ba!"A gaskiya idan nayi watsi da komai Banda halin kirki da na koya ayanzu.."Domin shine burin iyayenah nazamo nagari

"To Jawad Allah yasa MUDACE halayen sunyi karamci arayuwar mu..."Saboda bama koyon su Koda an koyarda MU..."Inji Saif.."

"Jawad yace na Kira mutuniyar wayarta akashe.."

"Wa Kenan..."Saif ya tambaya

"Matar faansa!!"Jawad ya bashi Amsa..."

"Dariya Saif yayi yace to may be batada caji!"

"Ita tasani...."

"Kodai me sonta yasani ba.!"

"Tsaki jawad yayi tare da datse Kiran yace banza night!!!"

"Jifa yayi da wayar gefen gado...cike da haushin zancen saif Nan wani Sabon takaicin Nadiya yadawo Masa sabou..."

"Bansan yadda akayi sai gani na nayi kwance a gadon asibiti....Kallo nabi Dakin da shi..."Tare da Salati ahankali na dubi gabana Yaya Saddiq NE,A tsaye ya hade hannuwa Yana kallona agefena yaran NE tsaye suna Hawaye!"Wasu Hawaye NE suka dinga min zuba ahankali na tunano abubuwan da suka faru da Ni!!!"

"Hannuna na motsa tare da yiwa Yaran Alamar su zo...Nan suka matso kusa Dani...Da yake hannuna daya ansa min drip!"Da dayan na dinga share masu Hawaye..."

"Anty Naddy sannu...mufida Tace."

"Kallonta kawai nake domin ko magana bana iyawa!saboda axabar zafin da nake ji akaina Wanda aka nadiye da bandeji!!"

"Mufeed yace Anty Naddy kiyi Hakuri ki yafewa momy da su Anty Wallahi sun ci amanarki...."

"Da sauri na rufe Masa baki tare da Girgiza Masa Kai Ina Hawaye...Nan na Rungumesu muna ta Kuka..."

"Tausayin yarinyar ya Sanya shi zubda Hawaye!!"Kallon su Yake cike da tausayin su day Kauna!"A zuciyarsa Yana Allah wadai da halayen Jalila!"Sam Bata cancanci Zama uwa ba!"wacce zata iya kula da yaran

"Dr.ne ya shigo yace"Saddiq ta farfadou NE!"

"Eh...Dr.ta farfadou.."

"Hannu Dr.ya bashi yace congrts Saddiq...Anyi nasara gaskiya saboda dogon Suma NE tayi."
"Wurina Dr.yazou yace sannu..."

"Da kyar na kada Kaina Alamar Amsawa..."

"Kallona yayi na mintoci tare da janye yaran jikina...yace kingane su!?"

"Nan ma Banyi magana ba!"sai Alamar da nayi Masa..."

"Kallon Yaya Saddiq yayi..yace"Ina ga ba wata damuwa Saddiq kamar zafin kanne Yake hanata magana..."Abin yazou da sauki tana gane komai...saboda ta Bugu SOSAI akai..."Inji Dr.yana murmushi."

"Masha Allah..."Dr.mun gode.."

"Yanzu muje office Sai na rubuta magani...Ina ga Nan zuwa gobe ZA'A iya sallamar KU..."

"Ok!Yaya Saddiq yace tare da bin Bayan Dr.."

"Har ya Kai KOFA ya dawo tare da dubina yace sannu Nadiya!"Ki Hakuri kinji..."

"Mufeed KU jirani asayowa Anty magani...Banda surutu kunji ko..."

"To Abba sukace Sannan ya fita...su Kuma dawowa sukayi kan gadon suka zauna sunata faman jera min sannu...."

"NIKAM na kosa nabar asibitin Tuni na kudurta abinda zai fiddani..."Domin gujewa halaka da haukar Anty Jalila...A hankali Hawayen ke kwaranyo min a fuska...Wani Abu nakeji idan na Tuni kazafin da tayimin tare da mugun alkaba'i da tayi min...Allah ya saka min nace Wanda ya fitou fili..."

"Ameen Anty naji yaran sunce....Nan na kama bakina nasa Masa linzami..."

"Haba Anty talatu Ni Wallahi ba Inda nayi nadama...Akan Wannan Dan Abu kima daina Wannan zancen Dan Allah."

"Jalila kinsan kaddara ake gudu!"Anty talatu tace
"Kaddara da kanta tsorona take..."Inji Jalila

"Rasheeda ta karbe Nima fa Da farko na tsorata!"Amma yanzu nasan da sauki domin idan anji shiru lafiya CE!!"

"Tsaki Jalila tayi Tace kamar da ba jinin umma ba!Naga yanzu tsorou ya shiga jininku Ni Wallahi ko ajikina Allah yasa ta mutu! sai me!?"
Chapter 28 · 0% Book details