← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 65

Sashe 58

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********** "Akai-akai tana yawan duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta,"Cike da fargaba!"Lokaci take dubi ko an daura auren Saddiq,"Jim tayi a Bedrum dinta na Dan lokaci Bayan ta kammala sallar Azzahar,"Wasu Hawaye ke Mata zuba ahankali ta Daga hannunta sama tana roqon ubangiji Domin ya kareta daga sharrin shaid'an ya yi Mata maganin kishin da ke neman zame mata wahala arayuwarta!"

"A hankali ta dafata Tace"Jalila Kuka!fa!?"Fuskarta dauke da damuwa!"

"Dan zabura tayi tare da goge hawayenta,ta shafa Addu'arta, Sannan ta dubi Umaima wacce ta zuba mata Ido cike da tuhuma,"Tace Haka Kawai nasamu kaina da kukan batare da son zuciyata ba!"Amma kin San me!?"sai Naji Sanyi araina!" Tace cike da sanyin murya,"

"Yake tayi tace Jalila kenan nan,"komawa tayi bakin kofar Bedrum din,tare da sakawa kofar Dakin key,"Sannan ta dawo, kusa gareta ta zAuna suna fuskantar juna!"

"Tace Ina son kibani aron kunnenki da hankalinki ki saurareni Kuma ki fahimceni!"Shawara Zan Baki ta karshe Akan dukkan lamarin Nan,"Fatana ki d'auketa,saboda Ni na daukeki amatsayin Yar uwata!"

"Abu na farko shi NE, ki yadda da kaddarar ubangiji,"Ki karbi rayuwa aduk yadda zata zo maki,Ki dogara ga Allah,"Sannan ki sani Duk fa abinda Kika Gani arayuwarki tsarin ubangiji NE,"

"Kisani tun farko bakin kishinki shi ne ya rufe maki Ido,har ya kaiki ga Danasani,To ko yanzu sai kin shirya kin neme makaman yaki da shi,"

"Dole NE kiyi Hakuri,ki rufe idonki,da Duk abinda Zaki Gani agidan Nan saboda Yanzu komai zai canja!"Ba kamar da can baya ba ne!"

"Sannan da Mansura da wata can daban Duk matsayin su daya awurinki kodai ki daukesu kishiya ko Abokiyar Zama,"InA son kisan cewa Duk kwarkwasar mansura sai kin Bata fuska zata rainaki!"Ki dauki girmanki da mutuncinki shi ne kin waye!"Sannan ki kula da tsafta,girki,kwalliya,da iya magana mai Dadi,ke dama Duk sauran abinda kikasan ya Dace kiyiwa mijinki dole sai kin dage.

"Jalila...Sai fa kinsou zaki baiwa mansura makami da kofar sanin Waye mijinki, Domin ke kin Dade da sanin sa halinsa da rayuwarsa da Duk abubuwan da yakeso da sabanin hakan,"Ita Kuma Yanzu tasa kafa karatun acikin karatun rayuwarsa," kin ga ke kin Dade da wuceta akaratun bazata tab'a kamo kafarki ba!"Sai abinda kikaso kika sanarda ita sadaqa.

"Amma fa Idan kinji Zaki iya,"Dan Haka Ina son ki cire komai aranki ki fuskanci rayuwar gidanki da yaranki,"Mansura ki d'auketa Abokiyar Zama, ba abokiyar gaba ba,Idan ta cutar da ke can baya Yanzu asirinta ya tono Allah ya bayyanata,Kuma ko Yanzu kin huce haushinta Domin kina zaune agidan da take ikirarin nata NE,Kuma ta fitar da ke, sannan zata zo taga abinda batayi zatou ba,wato ganin ki acikin gidan,Kinga Idan Allah nayi maka fad'a baka fad'a,"Gaki ga mijinki da yaranki,"To meye aibu ko abin bacin Rai,"Kudi fa ya zuba maki a dakunanki gana Fadan Kishiyarki da yabaki to meye matsala?!"Kiyi tunani Mana komai ake saddiq ya maki shi Jalila,"

"Ajiyar zuciya Jalila tayi cike da nazari ta Kara share hawayenta,"

"Abu na karshe da zan gaya miki, Jalila...Shine ki zage damtse akan *TARBIYYA* yaranki,"Domin *TARBIYYA* na farawa NE,Daga garemu iyaye,Haka Idan *TARBIYYA* ta lalace iyaye na da Nasu kamisho,Khairan ko sharran,"

"Ka da kizamou uwa mai son Kai,"Mai nunawa yaranta so da qauna,Kuma mai nuna b'acin Rai!"Akan Duk abinda za'ayiwa yaranki,"

"Kiyi kokari kibi hanyoyin da ake bi Wuri ladabtar da yaro tun tashin sa har zuwa girman sa saboda icce tun Yana danye ake tankwara shi,"Matakan gyaran ta Kuma sune, *TARBIYYA* Sanya Ido, kula da abokan su,da kuma Addu'ah,"

"Kizamo Mai lura da ilimin su,Addinin su da Duk wani motsi nasu,"

"A karshe Ina maki fatan alheri,sannan ba mansura ba!"Ko macce uku zai auro yau karki ji komai,Aranki ki shirya Yadda Zaki Zauna da su,"Iyakaci ki Kare martabarki da mutuncin ki agidanki...."

"Nagode Umaima... Jalila ta katseta...,Tace in shaa Allah ayanzu Babu sauran fargaba ko tsoroun kishiya azuciyata ko wacce iri CE tazo ashirye nake!,Daga Yanzu na saki kowa na Kama Allah,zan zamou kainuwa dashen Allah awurin mijina da gidana,Nagode Allah yabar zumunci,"

"Ameen kin wuce hakan awurina,"Inji Umaima tana Murmushi..."

"Jalila Tace"Yanzu muje Falo naji Anty Talatu na kirana, Bari na Kara gyara makeup Dina,na baza turare!"..."Umaima Tace" Kinga zuwa Anjuma kadan, sai ki Kira saddiq idan an daure sai mu sauya sabon wanka,"Fitowa falon sukayi suna dariya kowa su Yake kallo," ko da suka karasou Ashe kawayen Jalila ne mariya da ikilima suka zo yunin buki, Jalila tayi mamaki ganinsu matuqa,ko da yake ance gayyar sod'i ba gayyatar su ake ba,"Saboda ita Kam Jalila Tuni ta watsar da su Saboda ba qawayen kirki bane,"Batasan ma ko wa ya gayyatou su ikilima ba!''Hidimar aka cigaba da yi,"Yan uwa da Abokan arziki,"sai taya uwar Gida sarautar Mata Jalila murna tare da fatan zaman su zauna Lafiya a gidan,"

********** "Tun sanda ya dauko su Baba Balarabe da Innerie gabansa ke fad'uwa har suka karasou kofar gidan,"Tsoroun sa,Kada momy ta tona masa Asiri,"Haka agefen na hannun damansa saif tsoron yakeji shima,"Innerie da Mallam Balarabe sun k'osa su ga fitowar Nadiyatu,"

''Bayan Mai gadin ya wangale masu get din ne,suka kunno hancin motarsu izuwa mazaunin da aka tanadar Domin ta,"Fitowa sukayi nan suka wuce hanyar Babban falon gidan,"Jawad key yasa ya bude suka shiga,Wurin Zama ya baiwa iyayen Nasu,"Inno Mai aiki ya kwalawa Kira,Da sauri ta fito ta Fadi tana gaisuwa,"

"Jawad yace ki kawo masu abin Sha,sannan ki gayawa momy tana da Baki afalon Abba,"

"To,Inno Tace tare da Tashi da sauri, ta fadawa Hajiya sannan ta kawowa bakin abin motsa Baki da Ruwa,"cike da tray,"

"Saif Jiki ba kwari ya Tashi yana tsiyayawa su Baba lemun yabasu..."

"Innerie da Mallam Balarabe sai kallon Gidan sukeyi,A zuciyar su,suna mamakin irin Wannan arzikin nasu Jawad Amma basa nunawa,"Sam Basu dauki kansu komai ba gasu da mutunci da sanin girman mutane"

"Duk zatoun momy Alh.malami sambo ne yazo,Domin tayi waya da shi Yace suna hanya shi da matarsa Hajiya Maryam duba jikin Nadiya,"Sai dai tana shigowa taga su Jawad,da iyayen NADIYA, ne zaune akatafaren falon Abba"

"Fuska asake ta tarbesu tana murna," ko kallon su Jawad batayi ba!"

"Gaisawa momy takeyi da su Innerie,tana kokarin Zama,sai ga su Hajiya Maryam sun karasou nan falon ya karade da gaishe-gaishe,"

"Daga Jawad har Saif k'asa suka dawo da Zama,suna wani kame-kamen Jin kunya saboda sun san Dole Abba malami yayi fad'a Daga ganin su duba Jikin Nadiya suka zo,"

"Ay ko kamar Daga sama sukaji Mallam Balarabe Yana Korou bayani tare da ba momy Hakuri akan ta daina ganin laifin Jawad saboda yafi Nadiya gaskiya,"

"Murmushi Mai ciwo momy Tayi tare da kallon su Jawad din da suka sunne Kai, Sannan tace Mallam BALARABE duk abinda wad'annan gamammun hauru suka sanar maku babu Gaskiya aciki,"Amma Bari na kira Nadiya tazo kuji Daga gareta,nikam ba yadda banyi da ita ba!"Amma Taki Gaya min Komai da ya faru Bayan Wanda mukaje idonmu ya Gane mana...."

"Inno....momy ke Kira...da sauri ta zo ta zube agabanta!"
"Tace,Hajiya Gani,"

"Yawwa Inno kije Dakin Nadiya ki gaya mata tazo, sannan ki kawowa su Hajiya Maryam Wasu cups su sha, Ruwa,"

"To Hajiya, Inji Inno ta Tashi tana Kokarin fita,"Zuwa sashen momy,"

"Alh.malami sambo da Hajiya Maryam Sai faman mita suke yiwa jawad Akan rashin kyautawarsa Saboda duk abinda matarsa tayi Masa Bai kamata ya daketa ba!"Fad'a sukayi Masa sosai,"

"Nan dai ya sunne Kai Yana Basu Hakuri, Mallam BALARABE Kuma sai faman gyaran lamarin Yake,Innerie taji sauki aranta, duk da Nadiya ce batada gaskiya Amma Sam dukan baiyi ba Sam bataji Dad'i ba!"

"Momy in Banda Harara da take zabga masu ba abinda takeyi!"

"Jawad mamaki Yake yanda momy ta canja Masa duk kulawa da soyyayar da take nuna Masa,Amma Yanzu har takai ga zabga Masa Mari da Harara oh!Duniya kenan,"

"Shigowata Cikin falon ya katse Masa tunani,kallona Yake nakara fari sai dai na rame sosai,Sanye nake da katon hijab,Da siririyar muryata nayi Sallama,"Ido ya zuba min Tunda Yake arayuwarsa baitaba yimin kallo irin na hau ba!"

"Wani Abu yaji aransa shin Tausayi NE ko Kuma Dadi ya k'asa ganewa Saboda yayi missing duk wasu hidimomi nata,"A Yanzu hakan gidan Nasu ganinsa Yake kamar kwafai,Amma yafi dangana abin da kalmar Nan ta sabou turken Wawa,"

"Ganin iyayena azaune naji Sanyi araina sauri nake domin nakarasa na gaisa da su,"

"Mamana sai kallona take cike da tausayi da kewata, agefe tana Jin haushin rashin mutuncin da Jawad yace na aikata Masa,"

"Baba Kam k'asa Hakuri yayi da sunkuyar da kansa,Dagowa yayi Domin ya dubeni,sai dai caraf......Idonsa yayi arba da wani tangamemen hoton da ke manne ajikin bangon falon,Wanda Yake FUSKANTA Daga Gabas din Dakin,"

"Da sauri ya Mike tsaye ya Kama hanya,Nikam na dauka Baba inda nake ya nufo,Ay da guduna na isa gareshi na Rungume shi Ina Hawaye!"

"Sai dai hankalinsa baya Jikinsa,janyeni yayi Daga gareshi Tafiya Yake Idonsa tsaf akan hoton har ya karasa,"

"Bugun zuciyar momy ya karou!ganin inda surukin nata ya nufa!"

"Jawad ma ya shiga tashin hankali!"

"Shiru falon ya d'auka Babu Motsin komai,Ba tare da kowa yayi tsammani ba sai ganin faduwar Mallam Balarabe akayi yana dafe da zuciyarsa da ke mugun buga Masa,''

"Da gudu Dukkan su sukayo Kan SA Amma Ina Babu Numfashi,"Nan falon ya hargitse da hayaniya da Addu'oi,"Alh.malami da hanzari ya nufi fridge ya dauko Ruwa,Saboda matan duk sun rud'e,"Ruwan ake yayyafa Masa,Duk kowa yayi jigum nikam sai Kuka nakeyi,"Ni Nadiya da wane zanji arayuwata!"Rashin masoyin kirki!?ko kuma uba!?"Allah yayi min mafita!!!"ya agaza min,"

"Wurin Kam ya cika timjin da jama'ah kowa ya hallara,"Ango da iyayensa Kawai ake jira Wanda har Yanzu basu karasou ba!"Gashi saura mintoci goma Sha biyar lokacin dauri auren ya cika,"

"Bimboy da Amininsa Adams sun Sha wankan kananun Kaya,sunyi kyau sosai acikin shigar gayu masu wankan sukari,"Kusan Mota uku ya ciko da Yan iskan Abokan shi,"Maroka da makida sai aikin su sukeyi,"taron daurin aure yayi taro gwanin sha'awa.

"Bayan Yan sakanni sai ga Mota D'aya kacal ta kunno Kai, A harabar kofar gidan,"Nan Marok'a ta mawaka sukayi dandazou da microphones dinsu suna fadin JAMA'A GA MAI GAYYA UBAN TARO ANGO YA QARASOU!!!"

"Aliyu da Saddiq ne suka fito sai kanin Mallam Musa mahaifin Saddiq su uku NE,"Nan suka Isa wurin da aka tanadar Domin su,"
Chapter 58 · 0% Book details