← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 65

Sashe 20

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bayan ya fito ya sameni zaune Ina jiransa..."Firar tambayoyin mukeyi da yadda malamin ya rikita Mana lissafin saboda tambayar a hikima yayita idn mutum Bai fahimta ba sai ya fad'i."Daga nan Dakin karatu muka shiga muka Duba Wasu littafai acan nabar Naseer saboda munyi da su Esha idan Sha biyu tayi zamu hadu muje Inda Yaya Saddiq."

"Banyi wahalar samun su ba domin nasan Inda sukafi yawan Zama.Nan nasamesu sai ciye_ciye kayan kwalaam suke maza da Mata."Da nesa na tsaya ayko Nan take suka tashi suka sameni...Kallon su nayi ba laifi duk jallabiyoyi suka saka..."Sukayi rolling da mayafin rigunan."Sunyi kyau sosai da yake ba karya dukkan su Sunyi kyau da yake suna shafa mayuka masu tsada kowacce sai sheki take Sunyi tatas da su."

"Deejah tace min muje Malama Naddy."

"Esha ta ce"Ya test din ko da yake nasan ku masu kwanya ne zakuci..."

"Murmushi Deeyart tayi batace komai ba."

"Bamuyi doguwar Tafiya ba suka isa admin din."Office din Yaya Saddiq mukayi knocking..."Sai da naqara yin wani sannan yace Mana Yes come in (Alamar mu shiga)"

"Da Sallama muka shiga office din.. "A hankali ya amsa Mana tare da ajiye wasu files a side drower dinsA."

"A hankali muka gaida shi..."

"tuni su Esha suka sha jinin jikin su saboda kwarjininsa da cikar zati." wani da wani irin Kallon Nan na ba yabou ba fallasa da Yaya Saddiq ya bimu da shi."A lokacin da ya dago kansa ya ganmu..."Tare da amsa gaisuwar adakile!"

"Da sanyi nace Yaya Daman mun zo mu gaishe ka ne.."

"Yawwa to kun kyautah..."Ya karatu!?" ya tambaya

"Lafiya qlaw....nace da shi"

"Wad'annan fah!"yace tare da nuna su da hannu.."

"Rass!"Gabana ya fad'i!"Cikina ya dauki duri kada ya wulaqanta su..."

"Da...Daman 'yan Dakin mu ne!"nabashi amsa."

"Okay...yayi KU Nagode Kuna iya Tafiya zanyi magana da ita."

"Kamar jira suke kowaccen su ta miqe Daga kujerar da take zaune.,sum sum suka fita jiki na kyarma!"Saboda duk iskancin basa wasa da irin su Yaya Saddiq."

"Suna fita ya kalleni...sama da kasa!"Ya ce"Da kyau! haba biri yayi Kama da mutum...Shiyasa naganki kin wani canja Ashe da marasa *TARBIYYA* kike rayuwa!"

"Kina ganin kinyi wa iyayenki Adalci Nadiya!?"To wallahi bazan lamunce ganin ki da wadan Nan 'yan iskan yaran ba!"Sai dai ki koma gida da karatu saboda Baba Ni ya baiwa amanarki!"

"Meye alakarki da su!?"Ya tambayeni a fusace!"

"Kuka!nakeyi yayin hawaye na ke malala a fuskata!"Nace wallahi Yaya Sam bana rayuwa irin tasu Dakin mu ne daya!"Kuma nifa ko yawo bamayi tare ko yanzu Dan kace nakawo su ka gansu ne..."Naqarashe maganar muryata na rawa.."

"Saboda naga kin canja ne ya sanyani tuhumarki!"Shiyasa na nemi ganin su.."hankalina ya tashi alokacin da na hango wayewa da canji a kwayar idonki...sannan tsadar chocolates dinda suka baiwa su Mufeed ne ya bani mamaki...domin Ina sayen irinsu nasan kudin su..."Amma ace Wai kawayenki. Zasu iya KYAUTA da su amatsayinsu na dalibbai."

"Daga yau karna Kara ganinki da yaran nan saboda lectures da dama sun nuna min su amatsayinsu tsagerun makaranta."Duk makarantar Nan ansan da labarinsu da Zaman da suke school dinnan."Kina tunanin ba za'ayi muku dauka daya ba!?"To kisani babu ke babu su!"Kuma na baki Nan zuwa yamma ki tattara komai naki Zaki koma gidana da Zama saboda ko an raba maku daki nasan zasu iya binki har Inda kike su canja makin rayuwa...."

"Dai-dai Nan nakara fashewa da Kuka saboda na shaku da su Eshaaa,Ban son rabuwa da su..."Jin kukana!ya tsananta yasa Yaya Saddiq yace na fice nabashi guri karfe shidda ya sameni bakin get din hostel da kayana."

"Fita nayi cike da kunci azuciyata!Nasan bana rayuwa irin ta su Eshaa Amma Ina da burin cetou su daga halinda suke ciki!"Ban Kai ga cika burina ba!"Yaya ya yanke min kuduri!!!"Tafiya nake Batare da nasan Inda nake kada kafata ba!"Banyi aune ba sai Jin nayi karaf an rikemin hannu."

"A zabure na dubi gabana ...wani ne. Wanda ga alamu kamar malami ne.."

"Hannuna na kwache a nasan tare da bashi hanya ya wuce!"

"Murmushi yayi yace"Yammata Kuka Bai kamace ki ba!"Kina da kyau hakan har za'a ga hawaye kwance a fuskarki Kuma kina 'yar jami'ah..."

"Ya Kara kallona Yana murmushi yace ki gayamin damuwarki zan taimake ki wanene ya kadake!? ko ya cuceki!?"

"Takaici ya bani bansan sadda nayi tsaki ba!"Na wuce abina saboda yabani haushi tabanin da yayi!"

"Tsaye yayi Yana kallona...."Yace Kai!Ni wannan yarinyar zata yiwa tsaki!"Hmnnnn zan nemoki yarinya Zaki shigo hannu...Tabbas watarana za San waye malam Dan Bala!"Ya wuce office dinsa Yana mamakin yadda Mai kyau ta masa tsaki duk yadda yake jin kansa."

"Ko da na fitou fili Banga su Eshaa ba!"Duk da muna lecture 4_6 ban tsaya ba hostel na wuce saboda ban San abinda ke min Dadi bA!"

"Na Saba da rayuwar hostel tsawon watanni biyu..."Naji dadin rayuwa acikin mutane!"Na fara iya mu'amala da mutane da yadda AKE zama da su Naga wadanda suka fini *TARBIYYA* ilimi,da addini har Ina kwaikwayon su Amma yanzu Yaya Saddiq Yana son ya rabani da su!"Saboda su Eshaa da nasan a mazaunin da na ajiye su arayuwata."

"Da tunanin na isa Dakin mu....Gabana ne ya fad'i alokacin da na kalli fuskokin su...kowacce ba fara'a ita Deeyart har da hawayenta..."

"Banyi kasa agwuiwa ba!"Nace Eshaa, Deeyah, Deejah Dan kah kui hakuri da abinda Yaya Saddiq yayi muku kunga koni yanzu yayi min wannan halinsa ne KU kanku kunsani Kuma kunji aschool ana fada!!!"

"Ba komai duk abinda yayi Yana da dama domin mu muka Kai kanmu!"Inji Deeyart cije da bacikin Rai!"

"Eshaa tace wallahi saboda ke mukaje Naddy..."Kuma Dan kawai kince mu rakaki ne!"

"In dan badomin Hakan ba! me zai kaimu!? mu da sai ma an gayyace mu muke shiga office! Mutim ko provost sai ya nememu muke zuwa bare shi waye shi!?"Me Kuma ya dauki kan sa"

"Deejah kenan."KU daiyi hakuri koma menene nice sila!"Nace da Deejah wacce ta gama zancenta tana cika tana batsewa.."

"Shiru sukayi Ni Kuma tashi nayi Ina had a kayana..."

"Eshaaa tace Naddy Ina zakije Naga kina had a kayanki ba dai akan wannan maganar ce zaki bar Dakin ba!?"

"Hawaye masu zafy!suka fito min nace Eshaa Yaya Saddiq yace"Gidansa zan koma da Zama duka...!!"

"Menene!Naddy!?cap lalle bawan Allah nan anyi mugun gaske,!"Saboda kawai yaga shi aka baiwa kalihunki shine yayi Miki hakan..."Inji Eshaa

"Ni kaina Ina son zamana anan Eshaa Gidansa bazan sake ba!"Bazanyi karatun kirki ba!"Amma ya zanyi Ina gudun ya Kira Babana ya Gaya mashi wani Abu akaina ran iyayena ya baci...Dole nabi umurninsa..."Nace Ina Kuka!!"

"Hmnnnn...Tabbas zai Gaya masa kin lalace Tunda kina rayuwa da mu lalatacci!"Inji Deejah

"Ba Haka bane Khadija...."DakAta Naddy Wallahi hakane!"Saboda kowa a makarantar nan ya ajiye mu amarasa *TARBIYYA* da kamun Kai!"

"Tabbas hakane Deejah!"Nidai duk Wanda ya zarge mu akan abinda bamayi Allah ya isa!Domin baka shaidun mutum Ayau!"

"Hakane Deeyart!"Inji Esha wacce ta tashi Daga Inda take zuwa wurinda Dan firijin dinsu karami yake!"Ta bude tare da dauko lemun kankana Mai sanyi ta kurba kana Tace" mudai Allah ya wanke mu,Daga zargin da ake Mana!"ke Kuma Naddy kiyi hakuri ki yafe Mana domin Zama da mune yasa ake ganinki kema kin lalace har aka Bata maki Rai!"Daman Zama da madaukin kanwa ke Sanya farin Kai!"

"Nidai Har ga Allah Nady Ina sonki Kuma Ina kaunar Zama da ke Inji Deejah..."

"Kuka ne ya kwace Deeyart da yake akwaita da saurin Kuka da hasala!"

"Tace"Yau akan mu ake kokarin Naddy da Zaman hostel!"Tabbas Akwai gyara arayuwarmu saboda shaidun duniya shine na kiyama..."Hakan da akayiwa Naddy ya zame Mana izinah!"Kenan babu masu Mana shaidar kirki!"Mun b'ata record dinmu Tunda har mukayi watsi da *TARBIYYAR MU* tun farko yanzu ko mun so mu nunawa mutane abinda suke zargi ba shi bane ba bazasu taba amincewa ba!"

"Hakane Deeyart mun makarou Inji Eshaa itama tana zubar da hawaye!!"

"Deejah kam tuni jikinta yayi sanyi..."Tana nazarin rayuwa!!"

"Nace kuyi hakuri kawayenah!Kusani na shaku da KU bazan iya barinki ba!"Muna tare yanzu ma naji Ina son zumunchi daku!!"Sai dai Kusani shi Zaman duniya iyawa ne Kuma duk abinda zakuyi kuyi nazari kuyi amfani da *TARBIYYA* da kuma addininku...Saboda idon mutane ma'auni ne...Shiyasa tun farko nake kokarin sanarda KU gaskiya gashi yanzu kowa Yana zarginku alhalin KU abinda ake nufi da KU ba Haka bane!"

"Wallahi Nady iyakacinmu mu ci kudin samari muyi sayayya da su muyi shiga irin yadda ranku ke so Amma Sam bama watsi da mutuncinmu.."Sannan farin jini ne Allah yayi Mana Iyakacin mu rashin mutuncin anan ya tsaya!"saboda mu aganin mu wayewa CE!"Inji Deejah."

"Na dubeta!Nace Babu wayewa Deejah sai tsabar halaka!"Wacce yanzu sanadinta ana maku kallon marasa *TARBIYYA* Allah dai ya yafe Mana yasa mugane ."

"Ameen..."Deejah Tace.

"Nan na kammala shirina tsaf acikin akwatina..."Lokacin Tafiya ta kawai nike jira.."

"Tsittth!!!!Dakin yayi kamar wadanda ke Zaman makoki....Mun Sha Kuka!"Har mun gode Allah"Sai yanzu nagane su Eshaa nada kirki!"Hakan Suma sai yanzu suka Kara tabbatar da mutuncina..."

*'YAR MUTAN DIKKAWA*

[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*
*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 13*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

___________________________________

"Wannan karon zamana ya sauya a gidan Yaya Saddiq saboda na daina sakewa sosai da shi!"

"Bana son muna yawan haduwa da shi a gidan,Sai dai idan zamuje karanta ko mundawo,Idan Yaya Saddiq Yana falo bana Zama!"Ina Dakin mu Ni da yaran."

"Hakan yayiwa Anty Jalila Dadi,Ganin yadda nake nisanta kaina da mijinta."

"A gefe ban bar komai da nakeyi ba agidan,Sai dai Idan bana Nan Ina makaranta."Kuma yawanci kafin na fita sai na kammala dukkan ayyukana.."Shara! mopping da girki,da yake wanke2 tun acikin dare nakeyi."

"Su Mufeeda da Mufeed ba laifi akwai soyayya sosai atsakanin karatun boko da na zamani Ina koyarda su.."Musamman gefen sallah da *TARBIYYA* duk Ina kula da su sosai."A yanzu kwakwalwar su ta bude ga ladibi da biyayya da suka samu agurina."

"Yaya Saddiq Yana jin dadin yadda al'ummara ke Tafiya agidan sa..."Dawowata agidan ya kasance sanadiyyar farincikinsa Haka kawai yaji ya Sami nutsuwa da kwanciyar hankali arayuwarsa."

"Kimanin watana HUD'U da kwanaki a sakkwato birnin shehu Ina karatuna a kwalejin shehu shagari."A yanzu hakan mun kammala (C.A) din mu duka sai batun fara zana jarrabawar zango na D'AYA wato(FIRST SEMESTER)."Saboda hakan ne na Kara mayarda hankalina akan karatuna."
Chapter 20 · 0% Book details