← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 65

Sashe 41

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Umaima Tace to Allah ya kawo ku lafiya, Duk da Ina kishi!" Amma gwara Naga Wace iri CE,Kar dai batada kyau, SABODA da wuya asamo kamar mu, anaso Ana Kai kasuwa,gama ta zakuyi KU dawo hanya Domin sai da tsohuwar Zuma akanyi magani eheee..."

"Sai dai kin ganta 100% Hajiya ba ta da makosa ko a gurin ku Yan sa ido komai iya kushewar ku zaku yaba da Mai kalar fanta kirar Coca-Cola Saddiq yace Yana Dariya tare da shiga motarsa ya tada injin."

"Ali da Umaimah dariyar suke Masa,Tace lalle ka shige da yawa Toooo....Allah ya kyauta,ta fice abinta Cikin gidan,Shima Ali Sallama sukayi da shi,yabi sahun Gimbiyar SA."Ko ya gajiyar fita unguwa Bai mata ba."

*********** "Sai kusan magrib,Baba ya dawo da murna na tarbeshi tare da karb'ou ledar hannunsa ina gaishe shi,"

"Shima yaji dadin ganina tare da nuna farin cikinsa,Yana min sannu, da ya makaranta ya karatu,"

"Nace duk lafiya law."

"Yace to Allah ya bada nasara muna nan muna Addu'oi."

"Nace Amin Baba to mungode."tare da barin wurin."

"Yace"Innarei kin ganni sai yanzu?"

"Shi ne Mallam daga kaje ka dawo,"

"To Innerie kesan batun duniya baya karewa,Ina can Mallam Musa ya rikeni,Yana bani labarin Matar Saddiku,Ashe batada kirki,ita Nadiya Bata Gaya Miki ba ko?"

"Rassss!gabana ya Fadi Jin abinda Baba ke fad'a,sai da kofin hannuna ya subuce ya fadi kasa."

"Dauke kofin nayi na wanke, tare da k'arasa cikon butocin, da nakeyi."Buta d'aya ta Baba na d'auko tare da ajiye Masa gefensa Domin yin alwala."Saura kuma a hanyar bayi na jera su,"

"Baba ya CE"Wallahi Innarei malam Musa na Gaya min abin ba Dadi saurare Ashe Saddiqu yazo makon can,Yake Basu labarin komai, Ashe batada mutunci,hakuri yakeyi sai da yaron nan yabani tausayi,Yanzu haka in karashe maki zance bata gidan sun rabo!"

"Subhanallahi!"Innerie Tace"tare da buga kirji,ta kalleni inda nake zaune gefen su,nayi tsuru-tsuru,Tace"Amma ke Nadiya wace iri CE,Ashe jalilah Bata gidan!"D'azu Mallam muke zancen su da ita,harda yabonta Yar nan keyi Wai sunce a gaishe mu Aiko zakiyi zurfin ciki bazaki boye Mana Dan muma Sadiq ya zamo danmu sai mu kirashi muyi Masa fad'a mu bashi hak'uri yanzu watakil Yana dubinun san komai ,"

"Mama bansan Bata gidan ba!Nima Yanzu nakeji wurinku"saboda da lokacin jarrabawa yayi, Makaranta na koma da zama Domin karatu,kuma daga makaranta nadawo ban biya ta gidan ba!"Yaya Saddiq din Bai kaini ba!Kuma ni ba komai nasu na Sani ba,amma gaskiya nikam banji Dadi ba!"Nayi maganar kalar tausayi,"kamar gaske,sai Addu'a nake Kar su gane komai,"

"Baba yace"To ALLAH ya sauwaqa Daman malam Musa yace min shi tun farko baiso Saddiq ya auri yarinyar ba,Dan diyar macece Sam basuda mutunci Amma ya Nace sai ita,Yanzu Haka nuna min yayi da ba'ayiwa Nadiyatu Miji ba,Da mun hadasu aure da Saddiq din, nicce to ai tuni gurbi ya b'ata shaa Dan an baiwa yaron nan."

"A firgice Nace Baba aure fa!?"Wallahi nikam Wannan masifaffiya ko makiyina bana fatan ya zauna da ita! har Yan gidansu basu da mutunci."Ai sai su kasheni!"

"Innerie Tace"Yo Ashe Kinsan HALINTA Amma ko da wasa Baki taba aibata ta ba!"

"Sai lokacin nagane tsoro da fargaba ya Sanya Ni subul da baka,"Allah dai ya gyara, iya Nan na tsaya."Nace ni ai batayi min ba Kuma batayi Masa a gabana na dai San yayarta da kanwarta Suna zuwa gidan Yan bala'i ne.

"Baba yayi dariya yace"tsorou kamar farar k'ura Ni Kaina naji dadin hakan,saboda Bazasu nemi Alfarma agareni na kasa masu ba,Amma Kinga Yanzu Jawad ya raba gaddama, yace Yana Dariya."Alwala ya fara Yana gamawa ya wuce masallaci,"

"mama kam ta dinga mamakin Jalila,Nima dai bayani na Kara Mata saboda nasan zata tuhumeni ko Jalila na kuntata min zamana gidan,Gaskiya na Gaya Mata yadda zaman mu yake,sai dai na da na gaya mata."Muna zaune lafiya."

"Nan nace mama Wai shi Wannan Jawad din naku bazai zo in ganshi ba,naji Baba yace"An yi mini Miji !?"Har an Basu ni kenan?"

"Dariya mama tayi har da tafawa Tace Kai kurci dangin hauka!"Nadiya to Dan ankawo kudin shiga gidan,sai an Gaya maki,Yanzu da Kika dawo ai Zakiji komai,shi jawad din Bai Gaya Miki ba!?"

"Daure fuskata nayi harda hawaye na,Nace Ni ba Wanda ya Gaya min,nifa ko saninsa Banyi ba mama,"

"To ki yafemu laifin mu NE ko Nadiyatu,Lalle wannan zamani abin tsoro,mu da aka yiwa auren ko mijin bamu sani ba,Amma Kuma muka zAuna sai ku yaran zamani!?"To shi kenan bari Mallam yadawo zamuyi magana."

"Riketa nayi tana kokarin Tashi!Nace Mama Kiyi Hakuri Duk abinda kukayi dai-dai NE,Allah yasa hakan NE Alheri." tare da share hawayena."

"Amin Daman Haka ake son D'a Nagari,Muje muyi sallah,"

"Tashi mukayi zuwa daura Alwala muyi sallah,"

"Mama dakinsu ta nufa Nima nawa na shiga Domin idar da sallah."

"Ina kammala Sallah Nan wurin na zauna Ina Hawaye!"Wannan wane irin aure NE,Ikon Allah Ni Nadiyatu Naga ta Kaina,Cigaba da kaiwa Allah Kuka na!"Nakeyi ahakan na kwanta wurin Ina jiran Kiran sallar Ishaa."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 29*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*SADAUKARWA GA:" ZURIYATAAH, KUMA DANGINAH, FARIN CIKINAH,DIKKON KEBBI & MADAWAKIN KEBBI FAMILY'S HAK'IK'A INA ALFAHARI DA KASANCEWA GUDAN JININKU A RAYUWATAH,ALLAH YA QARA HAD'A KAN MU YA SANYAWA ZURIYA ALBARKA,ALLAH YAQAROU DANK'OU K'AUNA DA ZUMUNCHI MAI D'AUREWA AMEEN, FATAN ALKHAIRI.''😍*

*KYAUTAH CE,GA:"NANCY, MAMAN NANA,SAI KUMA FAUZIYYA HAMZA SHEHU NAGODE DA K'AUNAR KU ALLAH YA SANYAWA RAYUWA ALBARKA AMIN."😍*
______________________________________

Bayan mako biyu

"Wannan Rana ta kasance min bak'ar Rana arayuwata!Ranar bak'in ciki agareni!"Ranar da bazan manta da ita atarihin rayuwata!"Ranar da na sha Kuka!har nagodewa Allah,Tun lokacin da akai min waya aka shaida min Wannan labarin nake gunjin Kuka!"Mai shiga Rai!Hakuri mama ke bani tare da mita Amma naki na hakura,Baba ma yayi iya yinsa akarshe fita yayi yabar gidan Domin na k'asa hakura,"

"Bazasu gane irin rad'ad'i da tuk'uk'in bacin Rai!da bakincikin da nakeji arayuwata ba!"Da ace nasan Banyi karatu ban mayar da hankali ba,aka kadani jarrabawar Nan!"Ba zanji ciwo ko zafi ba!"Amma Nasha karatu Nasha wuya nayi iya kokarina Ina da Tabbas Akan karatuna,Yanzu Rana tsaka akirani a shaida min banci jarrabobina ba!"Kai duniya Wannan cin Amana da zalunci yayi yawa arayuwar mutane!"

"Wannan abin shi yafi komai damuwata,Duk wani buri nawa Akan karatuna ya rushe,Nayi Kuka har muryata ta disashe! Idanuwana sunyi luhu-luhu sun kumbura har wani ja fuskata tayi,Duk Wanda ya ganni Ranar sai ya tausaya min Shiyasa mamana Kuka har da hawayenta,Ba abinda ke damunta sai yadda taga naki na dangana da ikon Allah tayi bani Baki da nasiha Amma naki barin kukan!"

"Baba Yana fita gidan mallam Musa ya nufa tare da shaida Masa abinda ke faruwa,wato abokan karatuna sunje sun dubo jarrabawa da aka manna Amma duk sunci amma ance Nadiya ta fad'i"tana Daga Cikin korarrin makaranta ma"

"Mallam Musa Sam baiji Dadi ba!"Nan ya Kira saddiq ya shaida Masa,"

"Saddiq ya shaida masu Naseer abokina yaje tun jiya ya sanar Masa Kuma yayi iya kokarinsa,na Riga da na Fadi jarrabawa sai dai ayi hakuri na koma a NCE ONE,"Rai Babu Dadi suka ajiye wayar,Mallam Musa Hakuri yaba Baba,

Baba yace,Bakomai Haka Allah yaso,yanzu Kam Nadiyatu tayi Hakuri da karatu tayi aure,"Duk da Mallam Musa, baiji dadin faruwar hakan ba,Amma DAUREWA yayi Yana ba Babana hakuri,"

"Jiki Babu kwari Baba ya dawo gida ya samu mama a madafa tana sama Mana abincin dare,Zama yayi saman turmin da ke wurin tare da yiwa mama bayanin komai."Itama Bata ji Dadi ba Akarshe Addu'a sukayi min."

"Da dare Bayan Baba ya kammala cin abinci mama tana gefensa tana dama Masa fura,Daga dakina na jiyo shi Yana kirana,"

"Da kyar na Tashi saboda matsanancin ciwon Kai da jiri da ke debana,Ina had a hanya na fito Daga Dakin a INDA suke zaune na durkusa Ina kukan zuci!"Domin nasan Duk abinda zai fito daga garesu to ban hakuri ne!,"

"Baba"Ya dubeni da kulawa yace"Nadiya Ina son kiyi Hakuri,ki yarda da ikon Allah,ki duba ki Gani mu fa iyayenki NE,Amma mun hakura bare ki,kinsani da Dadi da ciwo mun hada abinda Muke da shi kinje makaranta,To Dan ance baki ci bae,me zamuyi,Kisani mun yarda da kaddara Kuma BAZAMU ja da ikon Allah ba!"Kema ki bar komai Allah yayi Miki mafita,D'azu nakira Sadiq ya Gaya min yayi iya kokarinsa,sai dai ki koma ko aji daya,niKam bana goyon Bayan ki koma,matsawar ba cigaba zakiyi ba,A gaskiya bamada wad'annan kudaden kin sani,Dan Haka kiyi Hakuri mu saurarin hukuncin ubangiji..."

"Mama ta amshe zancen Baba tana cewa"Wannan gaskiya NE Mallam Nima tun d'azu nake Bata Hakuri,Amma da Yake kafiya da saka Abu Rai gareta,Taki hakura!Mu Kam ba Dadi mukaji ba!saboda cigabanki shine farincikin mu,Allah yayi maki masanya ta Alheri,"

"Ameen Innerie Baba yace Yana kuskure bakinsa da ya Gama Shan fura,"

"Tunda suka fara maganar su hankali na ya Tashi mussamman da naji maganar NCE1 wani Kuka Yazo min da kyar na hadiye shi!Kar iyayena suga kasawata!"Bayan rarrashi na da suke!"

"Mama Tace"Ga ganta Nan har abinci Bata ci ba!saboda Kuka!"

"Ungo Wannan Sha,Baba ya Miko min langar furarsa tare da tsare gida ranshi abace!"

"Jikina na kyarma!"Na Amsa tare da kafa Kai,Allah sarki Babban ma'aji ba'a Masa garaje Domin baisan Babu ba(CIKI)Nan take ya dauki Kuka Yana amsaemr saqo,Sai da Nasha sosai na ajiye kwanon,Ruwa Baba ya bani Nasha sannan yace kar na sake Jin ance kinki cin abinci ko kinyi Kuka!"

"To Baba in shaa Allah na daina,nace muryata na rawa,Tashi yayi ya shiga Dakinsa fitowa yayi da magani Panadol ya balla ya bani,yace kisha Tunda kinyi Kuka har kin godewa Allah,Amsa nayi Nasha."

"Mama Tace"Ai ka taimaketa Mallam da baka barta ta kwana Bata ba CIKI ba,Ni nasan Daren farin zai hanata bacci,Dole ta ziyarci talle."

"Tashi nayi tare da masu sai da safe,"

"Ina shiga dakina wayata na bude wadda na kashe tun lokacin da kawayena Yan sokoto suka kirani suka Gaya min sakamakona,wadanda bazan manta da bakin labarin su ba!"
Chapter 41 · 0% Book details