← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 65

Sashe 11

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_SANARWA!SANARWA!!SANARWA!!!IINA MASOYAN OFFICIAL NABEELA DIKKO,INA MAKARANTA NOVELS DINA...DUK INA GAYYATAR 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI DA KUMA MASOYANA ZUWA AUREN KANWATA TA KAINA ❤ PRINCESS YASEERA DIKKO👰🏻 WANDA ZA'AYI ON 28/DEC/2019 ,BAN DAUKEWA KOWA BA NA NESA DA NA KUSA AZO LAFIYA ALLAH YA KAI MANA RAI AMEEN._😍
______________________________________

"Har yanzun Yaya Saddiq Bai Kara min zancen komawata Hostel da Zama ba."Har nayi sati daya agidansa." domin na kula yaya Yana Jin dadin ganina agidan.Shakka babu Tabbas an samu canji agidan mussaman agefen girki,ina yiwa yaran abincin safe kullum suje da shi makaranta, kuma duk kalar Wanda su keso shi nake girka masu."Sannan idan na dawo da Wuri Ina daura sanwar dare,Ina tuwon semo,shinkafa da miyar taushe da kubewa da sauran su"mufeed da Mufeeda suma yanzu suna jin dadi sosai sun sake da Ni sosaii, sun daina hayaniya atsakanin su,sunayin Kuma sun iya gaida Mutane idan sun gan su, har iyayen nasu yanzu suna gaidawa safe,Rana,da yamma Yanzu kam kowa agidan ya fahimci yaran sun samu canjin RAYUWA Gashi kuma Ina kokarin koyar da su karatun Islamiyya da na boko."Yaya Saddiq Yana jin dadin yadda nake kulawa da taimakon da nakewa yaran, aransa sai fatan Alheri yake min,Yana son zamana gidan sosai Domin farin cikinsu ya karou dani ta kowanne fanni,Gashi Yana sakewa da Ni sosai tamkar kanwarsa ta jini,komai mukeso Ni da yaran Yana saya Mana,Haka kullum suke ganin kamar kada na tafi saboda canjin da akasamu agidaan Kuma kowa na nuna min kulawa cikin Yan kwanaki Anty Jalila ta sake min komai na gidan."

"Anty Jalila sai dadi take ji aranta tasamu ma'aikaciya agida,Iyakacinta tayi bacci,ko Kuma Kallo daga nan ta wanke goma ta tsoma biyar"KOMAI ni nakeyi agidan idan dai banje makaranta ba da Wuri,ko Kuma kafin na tafi tun Wuri sai na kammala aikin duka Sannan na wuce saboda wataran da karfe goman safe ko da Rana ko Kuma karfe hudu na yamma nake fita."Daga Baya ne kawarta Subbyh ta shiga atsakanin mu alokacin da tazo gidan tasameni,Shine ta hurewa Anty Jalila kunne,akan na bar gidan kada na aure Mata miji."Duk da Ina Mata biyayya Ina kula da yaranta,Bai hanata daukar shawarar aminiyarta ba,saboda tana da tsananin kishi!"Akan Yaya komai zata iya aikatawa."Hakan akayi domin kuwa Anty Jalila ta takewa Yaya Saddiq burki dole saina bar gidan na koma Inda yace Mata tun farko zan zauna!"Ba domin sunso ba,shi da su Mufeeda."Yace na tattara kayana zan koma makaranta da Zama,A cewarsa acan zanfi karatu,Sayayya yayi na koma hostel da kwana.."Sai dai kullum mu kanje ofishinsa Ni da Abokina Naseer mu gaida shi."Wataran ya bamu kudin abinci Wataran Kuma bama samu saboda yau da gobe sai lillahi."

"Na kwantar da hankalina sosai Ina karatuna yadda ya kamata Kuma Ina ganewa sosai."Dan kuwa muna group discussion da Naseer da abokinsana Deeni."

"A hakan na Cigaba da tafiyar da rayuwata akwalejin shehu shagari.."Sai dai Banyi sa'ar abokan kwana ba, wato Yan Dakin mu da yake mu hudu NE adaki daya."Hali na ya babbanta da nasu."Hakan Rayuwata ta fita daban acikin tasu."

"Su uku ne Esha Hayat wato (Aisha Hayatu)sai Kuma Deejah Yak(Khadija Yakubu) sannan Deeyarh Bas(Badiya Basiru) sai Ni Nadiya BB da yake ko Nan ma hakan suke Kirana wato Nadiya Balarabe Bello."

"Kullum Yan Dakin mu ganina suke ban waye ba a matsayin Bagidajiya!"Sune suka waye suka San duniya da Abin da duniya take ciki."Ni Kuma Ina masu kallon Wasu iri,A ganinsu saboda bana shigar banza irin tasu Kuma bana kula maza Bana Wannan shirmen soyayya kamar yadda sukeyi shine ban waye ba,A Kullum kirana suke gara ko ustaziyya"Su Esha sam basu da kamun Kai da yake na lura mafi yawa hakan yam matan suke na kwarai masu hankali da kamun Kai"Kalilan ne acikinsu abin mamaki har matan auren ba'a barsu Abaya ba a Wannan zamanin me cike da tsoro,yadda mafi yawan Mata suka ajiye sure gefe suna abinda ransu keso bare yammata sai dai har gobe akwai na Nagari b'ata gurbi ne sukafi yawa!"Wannan halayen da nake gani yasa na Kara yarda da kuma gasgata Maganar Mallam yunus Dina,Da ya CE"Jami'a gidan kowa da kowa ne."Nako gani saboda akwai shege akwai Dan banza Sannan akwai nagari aciki,kowacce kalar rayuwa akwai Kuma ko da me kazo amfika."Na tabbata hakan."gidan ban Kashi ce,"

"Rayuwar mu da su wata iri Cce suna tasu nikuma Ina tawa koyaushe SU Esha cikin Kudi suke, da sayen sutura masu kyau da tsada,Har gasar wanka da saka manyan Kaya masu tsada sukeyi da sauran d'alibai" ga su duk sun San manyan mutane da malammai suna shiri da su sosai,da duk wani Mai fad'a aji acikin makarantar." Iyakacin su,Fashion da budawa amakarantar,Ba karya sun iya wanka naji nagani na fada,saka mayafi Bai damesu ba,ga kayan suna kamesu sosai tare da fidda tsiraicin su, Amma su aganinsu wayewa ne Wannan fitar ta rashin mutunci ita ake yayi,"Shiyasa suke fita yawon su,Abinci mai kyau sukeci su Sha Mai kyau,Ina ji Ina gani nazama doluwa Yar Kallo acikinsu." ko sun ce min in zo muci abinci tare da su banaci hakan bana nuna bukatar komai Daga garesu."Ba yadda basuyi ba domin su ga na shiga acikin harkar tasu Ayta sha'ani tare,Amma naki!"Sun nuna min sutura saboda sun fahimci banida ita da yawa Mai kyau."sun nuna min kud'i sun bani abubuwan kwadayin duniya duk nayi banza da duk abinda suka bani."Nace da su nagode banaso Domin nafison abinda nasamu ta dalilin iyayena!!"Hakan Na Cigaba da karatun da ya kawoni makaranta." saboda su na gane basu damu da wani karatun ba Kuma basu da niyyar yinsa." sharholiyar su kawai sukeyi ta duniya."A kullum fatan shiriya nake masu."Su kuma suna min kallon lusara Wacce batasan komai ba bagidajiya Yar kauye."

"Saifullahi Aminin Jawad ne sosai Kuma Abokin shawarar sa."Sun shaku da JUNA sosai sai dai shi Saif yafi Jawad dama Amma dai dukkan su yan gatane."Sun taso acikin so da kauna." Saifullahi shine karami agidansu,Saboda duk yayyensa Mata ne su biyar shi kadai ne namiji Kuma auta agidansu yayyensa Duka manya ne,Haka iyayensa manyan Mutane ne,Kuma yayyansa suna auren mazaje masu kudi.shiyasa ta ko ina,yake damawa da kudade son ransa Dan gata ne Dan auta Kuma autalele Sha leleh awurin iyayen sa da yayyensa ."

*************
"Yanzu kimanin sati biyu da zuwan su wurin Mallam Balarabe wato mahaifin Nadiya Tabbas sun Sami karbuwa kwarai da gaske agurin Baban nata Haka kawai yaji jininsa ya hadou da Jawad kaunarsu na ratsa jini da jikinsa,Duk da ya kula yaron sai ahankali Amma dai ya karbe su hannu biyu kuma ya gamsu da kudurinsu."Aykuwa sunji Dadi sosai sai dai sun fahimci Baban bayada kwadiyin Abin duniya."saboda sun bashi masa kudade yaki ya karba ranar."

"Shiyasa suka canja dabara ta hanyar Sayayyar kayan masarufi sukai masa yau,Saboda sun Kwana biyu basuje gaida shi ba!"Kuma wannan Yana Daga cikin shirinsu...Shiryawa sukayi tsaf acikin jallabiyoyi da huluna farare tas sunyi kyau kamar larabawan Sudan da yake dukkan baqaqe ne masu Dan haske."Da misalin karfe hudu na yamma hanyar tudun wada suka nufa kamar yadda suka Saba, Bayan duk kwanaki uku sukanje da sunan kawo gaisuwa ta mussamman agurin mahaifin Nadiya ko Yanzu hakan CE ta kasance."

"Tun Malam Balarabe na sanyi-sanyi da su har ya Fara sake masu saboda ya lura yaran na da kirki,da sanin girman na gaba dasu shiyasa suke girmama shi Kuma suka dauke shi da muhimmanci, Wannan NE yasa Mallam Balarabe ke ganin mutuncin su, tun Baya amsar abubuwan da suke kawo masu har ya fara amsa har cikin gidan suke shiga su gaida mama fad'imatou(Inneirei) suyi fira sosai da ita har take masu zancen kewar Nadiyarta, Haka sukeyi dai har aka Saba da JUNA."Kamar kullum yau ma zaune suke rashe rashe agidan Bayan an kammala shigo da kayan da suka kawowa su Mallam Balarabe." Sannan suka cigaba da firar su daga bisani suka fito."Mama Da Baba sai albarka suke saka masu da dimbin GODIYA."

"Dariya sukayi alokacin da suka fad'a Mota,suna tafawa Jawad yace"Wallahi da farko sai Naga kamar bazan iya ba!"Saif

"Hakuri ne bakada shi Jawad Shiyasa.. Saif yace Yana Dariya."

"Yanzu nafara koyon hakurin adalilin daukar fansa!"

"To Jawad yanzu dai kaga Shirin mu Yana tafiya dai-dai."

"Haka NE faa...Wai kasan da kyaar na tsara momy na d'aurata akan layin iska,Domin ta daina zancen zuwa ganin mutumen Nan da na Mata Bayani na karya...."Sai da nagaya Mata yaji sauki munje dubashi Baya gari yayi tafiya kauyen su..sannan NE fa ta hakura Tace sai yadawo ta tafi."Nace Mata to da kanmu zamu kaita har gidan."Inji Jawad dake tuki cike da kwarewa,"
"Kace munyi arziki da mummy Bata B'ata mana shiri ba!nji Saif yana dariya

"Kai Baaba...Ai kuwa da ta tab'a komai nifa na rasa Ko Meyasa mom ta damu da taje, ai idan ta dage sai taje sai ta wargaza Mana shiri."Jawad yace."Saif Kam muryar wakar Davido dake tashi amotar ya Kara tare da rawa Yana tafawa...yace bazamu rasa yadda zamuyi Mata wayo ba!Domin mu Yan zamani....yace yana Cigaba da bin wak'ar."

"Tafiya suke suna Hira da shewa,Saboda a yadda Shirin nasu ke tafiya, kamar yadda suka tsara."Daa kamar wuya Nadiya ta kubuta Daga tarkonsu."Sai dai ta zama Abin tausayi a hannun su, Domin Bata sani ba, ta tafi makaranta tabar Baya da kura."

*************""""
"Zaune nake Ni kadai adakin mu Ina dafa abinci Ina karatu da yake yanzu mun fara gwaji(test)."

"Shigowa sukayi Dakin ko sallama basuyi ba da yake yanzu sun daina kulani sosai kamar baya."Ko kallon su Banyi ba!"Na Cigaba da karatuna."

"Esha CE Mai raha acikin su."Tace Sannu Malama Nadiya."

"Yawwa,Sannunku Nace da ita!

"Baiwar Allah Naddy Karatu,kawai ake ta sha..."Inji Deejah tana dariya.

"Banza nayi Mata..tashi nayi na Duba abincina shinkafa da wake ce,Na had'a ta da Mai da yaji,zubowa nayi da su Nace suzo muci,Ba kunya Esha da Deejah suka zauna mukaci tare Dan ba kunya da zuciya ne da su ba!."Deeyart Ita dama akwaita da Jin kan tsiya Kuma bata wani yina sosai Tunda taga bana layin su."
Chapter 11 · 0% Book details