← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 65

Sashe 56

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Haka Zama da Abokin kirki da marar kirki Yake,Domin Kodai mutim ya Zama Mai kyawawan dabi'u ko Kuma sabanin hakan,"Allah ya sauwaka, Mallam Balarabe Kai da Fatima kuyi Hakuri da abinda danku ya aikatawa Yar mu,"Hajiya Maryam ta karashe zancen da damuwa!"

Dukkan su ba Wanda yace uffan Domin kowa da abinda ke Cin zuciyar sa falon tsit yayi na lokaci.

*******************
"Bayan an kammala Salati waliyin Amarya mansura ya baiwa Adams waliyin Abdul-Rahman (Bimboy)Auren Mansura Akan sadaki naira dubu goma Sha biyar,Fatiha jama'a suka shafa!"Kowa na fadin ALBARKACHIN bakinsa,"Daga cikin gidan mansura ko kide-kiden da ake da raye-raye da hayaniya ya hana suji sautin sanarwar auren da Marok'a keyi awajen gidan,"

"Jiki Babu k'wari jama'ar Wurin ke kokarin tashi,yayin da Adams da Bimboy farinciki ne faal aransu Domin shirinsu ya tafi za Dadi,"

"Kamar Daga sama Saddiq ya karbi abin magana(microphone)"Ya ce jama'a Dan Allah kowa ya DakAta!"Nima AURENA za'a daura KU Sanya Albarka,"

"Nan kowa yayi cirko-cirko suna mamaki!"Lalle kallo ya koma sama,"Aliyu da mamaki yace"Aure fa Saddiq to da wa Kuma!?"

"Hannun Ali ya Kama yace"Dan Allah ka taimakeni,Ina son na nunawa Jalila Ni mijin macce Hudu ne! Idan na koma ba tare da aure ba! Burinta zai cika na Lalle tafi karfin ayi Mata kishiya!duk da ayanzu nasan tayi laushi!"Amma Ina son na nunawa Mata masu ganin sunfi karfin ayi masu kishiya!"Karyar su.

Domin Allah ne, ya bamu ikon Karin auren ba su ba!"Inji Saddiq Cikin yanayin damuw!"

"Ali yace Yanzu me kake so NE Saddiq!?"

"Ina son kazama waliyin Suhaila kabani aurenta Wallahi Ina sonta Kuma tun Ranar da nafara ganin ta agidanka naji ta shiga Raina!"Zan baka naira dubu asirin na baikoh sannan Zan bada sadaki naira dubu Hamsin yanzun Nan,ga Kawu Nan waliyina..."

"Numfashi Aliyu ya sauke yace"TABBAS Ni Mai bada auren Suhaila ne,Amma to bamu sani ba ko zata soka banason asamu garaje!"Kuma umman kano bata sani ba!"zan ba da auren Suhaila,"

"Saddiq yace"Aliyu na dauki alqawarin da zarar mun je Suhaila Tace Bata Sona ko wata matsala ta kunno Kai ta gefenta ko danginta Wallahi Zan sauwake Mata!"Nidai Ina son burina ya cika na zamou Mai Mata Ayau!na koma gidana a matsayin Ango,"Itama Jalila labarin mijinta ya taba aure Bayan ita ya kasance acikin tarihinta"

"Da kyar da magiya Aliyu ya amince...Nan jama'a suka koma shafa fatihar auren Saddiq da Suhaila Akan sadaki naira dubu Hamsin,"Godiya sosai Saddiq yayiwa liman da jama'ar Wurin har iyayen mansura tare da labarta masu komai da Mansura tayi Masa,"Sannan akarshe Hakuri ya Basu,"Nan suka nufi motarsu Domin zuwa Argungu,"

"Amota ma Ali Sai tunanin yadda zata kaya yakeyi... Saddiq Kam murmushin Jin Dadi Yake Saboda ya tabbata Suhaila zata so shi!"ko Domin yawan Kallonsa da take cike da kunya idan sun hadou!"A Mota kawunsa nasiha Yake Masa sosai tare da tsara duk yadda za'a bullowa lamarin... Domin Mallam musa Sam baisan da batun fasa auren mansura ba!"yace dai asanarwa iyayenta duk abinda ke faruwa Don gaba!"

"Hankalin Aliyu ya k'asa kwanciya Shiyasa ya kira wayar umman kano kusan sau uku ba'a Daga ba Nan ya Kira layin Umaimah shima shiru,kamar hadin Baki na Suhaila baya zuwa,Dole ya hakura har su karasa!"

"Jiki Babu k'wari Yan uwan mansura suka bar kofar gidan,"Sauran mutanen gari sai magangannu sukeyi Akan Wannan auren da akayi Angon kwarai yace ya fasa,sai wani Mai guntun Wanda aka daura da shi.

Lalle mansura ta ga isharar rayuwa Wasu ma gwai suke cewa Dan batada mutunci,"Kan kace me zance yabi gari,Dan duk mazan da suka hallara taron sun bazu acikin unguwar su na yayatawa nan wasu idan sunji suyi Karin gishiri su sanarwa wasu,"Nan da Nan gidan buki ya cika timjin da Yan sai mungani da Yan sa Ido,da wadanda Basu barin labari da Yan Allah ya Kara!"

A hankali aka dinga gulma Ana dariya wasu na alhini acikin gidan,sai dai ba'a Samu wanda zai fadawa Uwar buki ba wato Halima da yaranta,"

"Nan yarou ya shigo Wai Ango na Sallama da Mansura,"

"Yaya fariza da sauri ta Kara feshe amarya da turare har wani fari da Ido ake koyawa mansura,bayan ta sauya Kaya, sannan Sahura ta rakata har falon gidan Ana Tafiya kamar za'a karye!"

"Sai kallonta Mutane keyi wasu da suka San da labarin har dariya sukeyi!"

"Lullube da mayafi ta Isa falon Sahura na biye da ita,abaya,Sahura CE tafara cin karou da su zazzaune Akan kujeru kusan su shidda ba Mai fitar arziki,tsaki tayi cike da tsiwa tace''ku KUma Daga Ina!?"Dan Allah ku bamu Wuri zamuyi baki!"Idan abinci kuke jira zansa yarou ya kawo maku Yan yunwa kawai ku jira a kofar gida....!!!"

"A fusace Adams ya zabga Mata Mari!"tare da nunata da yatsa yace''ke banza Kinga munyi Miki Kama da Yan yunwa!?Yanzu Zanyi maganin iskancin ki!"

"Mansura gabanta ya fad'i!"A hankali ta yane gyalenta...yayinda Sahura ta rike kuncenta tana huci!"

"Tana kokarin mayarwa Adams da martani sai dai jin sautin muryar mansura arazane ya tsayar da ita!"

"Mansura Tace Bimboy tare da Kallonsa Ido Cikin Ido,Shikam wani sonta da kaunarta ya ninku azuciyar SA!"

"Yace Amarya mansura kenan,Kinga Allah yayi nine mijinki!"duk da kin yaudareni kinci kudina,wanda akarshe kinka gujeni har da boye min aurenki,To Kinga hukuncin Allah rabou ya ratsa sai me shi!NAGODE Allah da yasa na sani kafin a daura. ba Dan hotunan ku na aure da nagani a media Suna yawo ba da ba zan San Anyi ba...Inji Bimboy Yana murmushi Yana Kallon sahibar SA,"

"Wayar hannun Sahura CE ta subuce Mata ta Fadi kasa,Nan take ta tarwatse!"

"Mansura kunnuwanta ta danne da hannayenta!"Cike da tashin hankali tace"Bimboy ka ajiye zancen wasa agefe Yanzu ba Wannan lokaci ba NE!"nasan na yaudareka Amma Kayi Hakuri! Shi lokaci baya jira saika jira nakan Yana zuwa,domin ka makarou Ni matar wani CE!"Dan Allah ku fita kada suzou su sameku!"ran mijina ya b'aci!"ka bani kwana biyu Zan biyaka duk kudaden ka da naci.

"Dariya yayi tare da jifanta da wani mayen kallo...ya CE"Mansu Baby kenan wallahi nine mijinki da aka d'aura maki Aure da shi yanzun Nan,"Saboda Shima Wanda Zaki aura kin yaudare shi,yace ya fasa aurenki domin kece Silar rabashi da iyalinsa!....."Ni Kuma Daman nazo da shirina Ashe ke rabona CE sai aka d'aura Dani shima tsohon saurayin naki an daura nashi da wata Suhaila,"zancen biyana kudina Bai taso ba Dan Bana Zaki iya ba,sannan Wanda like tunanin ki shiga gidansa ki tande ya Zama mijin wata,Ni Nan nine zaki zauna tare Dani ba kowa ba.

"Wani jiri ya dinga kwasar mansura!Hawaye ke Mata zuba tace "Sahura me hakan ke nufi!?"Da GASKE! ne?"kice min mafarki nake!?"Na Tashi da mugun baccin da nakeyi...."

"Cikin karajin Kuka Sahura tace "kyaikayi ne ya Koma Kan mashekiya!!Mansura," kenan asirinki ya tono awurin Saddiq!" Amma Sam ban yarda da ya fasa aurenki ba!"Wad'annan tsamaye karya sukeyi!!!"

"Adams ya jimke hannu ya Kaiwa Sahura Duka da sauri ta sunkuya k'asa yasha iska!"Yace"Da naso na samu jibgegen bakin nan naki da Kinga aiki!"Tunda bakinki da Sauran magana!Yar bakin CIKI.."To aure an daura da Bimboy kuje KU tambayi duk uban da zaku tambaya shine Ango!"Sai Hakuri kananan Yan bariki..."

"Hannu mansura ta aza aka ta fashe da mahaukacin Kuka!"Da gudu ta kwasa Cikin gidan,tana Kai kofar Dakin mamansu ta Fadi kasa somammiya!"Cike da tashin hankali akayo kanta,Ana fifita!"da yayyafa mata ruwan Sanyi!!!" har ta farfadou!"Sahura ma Kuka takeyi,"Kowa ita ake tambaya meke faruwa!?"Sai dai shiru tayi domin ita Kam ba za'aji mutuwar sarki abakinta ba!"

"Mansura na farfadouwa Cikin Kuka ta Tashi zaune kamar zautacciya!! da tashin hankali take Maganganu barkatai......da sambatu sai da Yaya Farida ta rufe Mata Baki Ganin ga Mutane, najin yadda take tonawa kanta Asiri!"

"Kanen mahaifin ta ne,ya zo ya fara labarta masu komai,ba tare da ya rufe ko ya sakaya ba!"Daman can haushin su Yake!"da muguwar mahaifiyarsu da ta rabasu da Dan uwanka su,"Nan gidan buki ya koma na Kuka Saboda yayyan mansura da mamansu sun fashe da Kuka ga kunya!"

"Cikin mintoci gidan buki ya watse!"Baban su mansura ya shigo gidan ransa ajagule yaqara warware masu komai!"Har cutar da Mansura ke dauke da ita ta HIV.,"

"Tashin hankalin Mansura ya karou Cikin Kuka!take rokon Babanta tare da cewa karya ne!?"Ita Kam lafiyanta qlaw,"idan Anyi musu atafie asibiti ayi gwaji,wallahi Bimboy kazafi yayi Mata!"

"Daga Hajiya Halima har yayyenta kanta sukayo Saboda haushi sai jibgarta sukeyi suna zaginta,har bakinta ya fashe!"Domin ta Bata masu suna!"Yanzu shi kenan mazan su da mutanen duniya sunji komai!"

"Tun mansura na iya Kuka har ta kasa,sai gunji ta ke Tashi...."Sahura ce ta kamata tana rarrashi!"Saboda kowa ya watse agidan har Sauran kawayen su!"Daga Dangi Sai Yan Ganin kwakwaf,"

"Baban mansura da ya fita waje NE ya shigo gidan,A fusace Yana Kiran sunan mamansu da karfi!"Fitowa Hajiya Halima tayi Daga Dakin ta Tana sharar kwallah!"

"Yace"Ina son yarki ta hada Komai nata tabi mijinta!Domin nagaji da ganinsu akofar gidana nace su tafi sunce amarya suke jira!"

"Haba Alhaji Tayaya hannunka zai rube ka yaaaar!"A gaskiya nikam zan kaita asibiti ayi mata gwaji!"Domin tabbatar da gaskiya lamari!"sannan Wannan auren baiyi ba!Tunda Bata Sonsa harfa Suma tayi!"Ai dole ya saketa....ko Yana so ko...Bayaso...Dan Ina son 'yahtah."

"Cikin ikon Allah yau Allah ya baiwa Alhaji Sa'a da damar mayarwa matarsa da Yake tsorou kamar wuta amsa......"Da tsawa yace"Wallahi kinyi kadan Halima ba Ruwana aciki!"Tama mutu Mana aike CE da asara!"Yanzu basai anjuma ta shirya ta fitar mini Daga gida!"Tasan batason SA zatayi mu'amala da shi!"Meyasa Bata Kama kanta da mutuncinta ba!?"To Bari kiji Halima bakin aurenki matuk'ar mansura Bata bi mijinta ba...."

"Ba Hajiya Halima ba!"Har yaranta sun razana!da zantukan MAHAIFIN su!"ganin yadda ya sauya harda Samun yancin surfa ruwan masifa!"Sun shiga tashin hankali Domin komai ya jagule."

Juyawa yayi abinsa ya koma waje tare da baiwa mansura mintoci ta fitou tabar Masa Gidansa..."

"Hannu mansura ta aza aka tana karajin Kuka!kamar ranta zai fita! Yayyenta ma sun tausaya Mata!Haka Hajiya Halima Kuka takeyi!Domin kasuwa ta watse ba uwa ba riba!"

"Sahura ta tausayawa kawarta kwarai da gaske nan ta TAIMAKA mata Wurin parking din Kayanta Amma azuciyar mansura ta kudurta guduwa!"Tabar Bimboy Domin idan Yasan wata baisan wata ba!"Dole ta dauki fansa akan mugun kazafin da yayi Mata Domin wani tabou NE arayuwarta!"Kowa yanzu Yana Mata kallon Mai kanjamau.
Chapter 56 · 0% Book details