Sashe 61
Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A hankali mallam BALARABE ya numfasa tare da cewa"Dukkan abinda ya faru ya faru NE,A matsayin kaddara!"Da son zuciya!"Ba abinda zance face duk mu hakura da komai ya wuce!"Hajiya kiyi Hakuri ki yafe Masa!"
"Momy Tace"Yaya Zan yafe Masa Amma Ina da sharadi!?"
"Meye sharadinki Khaltumi,!?"Hajiya Maryam ta tambaya,"
"Ajiyar zuciya tayi tare da cewa sai Idan jawad zai saki Nadiya!?"
"A firgice ya dubi momy bakinsa na rawa Yana zubda kwallah!......Arazane ya Kama kafafun Mallam BALARABE Yana cewa Dan Allah Baba ka baiwa momy Hakuri na tuba......"
*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍
_Tukuichi neh gareku masoyan TARBIYYA kuyi Hakuri na jina shiru nayi typing ina kokarin maku post sai ya goge!Wannan ma nayi ne Domin farinciki ku,Ayi hakuri da kurakure!Banyi edit ba😭_
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*PEN WRITERS ASSOCIATION*
*SHAFI NA 51-60
___________________________________
"Cikin yardar ubangiji su Sadiq suka sauka Argungu Lafiya inda suka sami Yan uwa sun tarou agidan suna Taya gwaggo yunin Bukin,Suna ganin Ango sai tsokanarsa suke cike da Raha har da hotuna akayi cike da Jin dadi"
"Bayan sun huta abinci suka ci Daga bisani Baba Haliru yayiwa Mallam Musa bayanin Komai yadda abin ya faru har da asirin mansura da Bimboy ya tona!"Da irin cutar da take dauke da ita,"
"Da farko Mallam Musa yaso ya ga laifin su, Amma Daga bisani da ya fahimci komai, Hamdala yayi tare da godewa ubangiji da Bai kaddari kaddara ta gittah!"Akayi auren ba!"
"Godiya sosai yayiwa Aliyu sannan ya karbi Lambar wayar umman kano Acewarsa zai kirata ya Bata Hakuri Akan auren bazata!"Da akayiwa Suhaila,"
"A lokacin da Labarin auren ya zo kunnen gwaggo Murna tayi sosai tare da sanya Albarka,"Nasiha suka hada Baki dukkansu su kaima Sadiq Mai ratsa zuciya!"Akan adalci da rikon Amana,da Sauran Jan kunne,"
"Daga Nan kayan Mufeed da Mufeeda gwaggo ta had'a,da 'yan tarkacen kayan yaji da daddawa tace akai ma Jalila,"Yaran sai Murna sukeyi sun ga Abbansu," Gashi Kuma zasu ga mommyn su,"Da farin ciki suka Kama hanya,sai dai Aliyu Yana Jin nauyin yadda zai sanarwa Suhaila ya aurar da ita!"Agefe Kuma bai san yadda Umaimah da Umman kano zasu dubi abin ba!"Amma shi Kam baya da haufi ko kwankwantou akan dacewar Sadiq Domin namiji NE da Kowacce maccen kirki Mai Hankali ke burin mallaka,"
************ "A gidan Jalila ko tun su na jiran shigowar Yan jere har suka debe Rai saboda yamma likis,tayi basu ba labarinsu,"
"Sha'anin su suka cigaba da gudanarwa da hidimomin su,"Umaimah tace Jalila ta sake sabon wanka, kwalliya Mai kyau Suhaila tayiwa Jalila ta tarbon Ango,"
"Duk da haka kawai taji yanayin jikinta ya sauya yayi sanyi lakwas ga faduwar gaba na damunta"Amma daurewa tayi ta Koma yiwa jalila kwalliya. Dan ta k'asa sukuni A daddafe! Dai"ta kammalawa Jalila light make-up,ta wuce dayan Bedrum din ta kwanta tare da fad'a masu kanta ke ciwo,A Lokacin da su ka tambayeta.
Da sigar damuwa! Jalila ke faman jerawa suhaila sannu saboda tana son ta, Kuma ba komai ke burgeta da ita ba sai halayenta na kirki da nutsuwa.
Magani da Ruwa Rasheeda ta kawo ma Suhaila Tasha ahankali wani bacci Mai nauyi ya dauketa!"
"Umaima da Anty Talatu share gidan sukayi tsaf tare da gyara ko'ina turaren garwashi Dan maiduguri da na Tsintsiya akasa Nan gidan ya dauki kamshi,"Haka Uwar gida ran gida an Sha wankan less Dan Dubai sai zuba kamshi take kamar anyi barin humra ajikinta,"
"Yanzu Kam komai yayi tsaf, zaune suke Ana jiran zuwan Ango ko Ahlin Amarya,"Domin Uwar gida ta KASHE dauri Yana kallon kudu masu yamma,agefe Yana dubin Gabas maso Arewa,duk hanyar da aka bullou agidanta tana maraba,"
**********"Duk da Nasan Jawad ya aikata laifi Amma hukuncin sakin Nadiya ba shi NE maslaha ba!Wanda kike son d'auka khaltumi!"Inji Alh.malami Yana dubanta.
"Hajiya Maryam Tace"Wannan gaskiya NE!Alhaji,"Dole Hakuri zamuyi Hajiya Kar arabasu!"tunda Abin ma tuwo na Mai na ne.Allah ne ya gadasu jini D'aya ko Dan sanadin su aka San juna ya kamata ki ajiye zancen sakin nan.
"Momy Tace Haba ya kamata ku fahimce Ni Mana!Jawad ya zalunci yarinyar Nan, Daman na gaya Masa sai ya saketa! saboda Ba sonta Yake ba! auren manufa da huce haushi yayi!sannan burinsa ya cika ayayinda ita ya tarwatsa natan!to me yayi saura!?"sai ya sallameta Mana, Makaranta Zan sata tayi karatu Mai tsawo,!"Daman na fahimci itama Nadiyatu biyayya ce tasa ta karbe shi amatsayin Miji....!ba sonsa take ba hasalima hamayya ce a tsakanin su"Auren Biyayya tayi ba Auren so ba,ya kamata ai Mata adalci a Bata dama ta karshe Kar mu cutar da ita akan Wannan Dalili na jini D'aya.,"
"Wani Sanyi naji araina Alokacin da kunnuwana sukayi arba da zantukan mommy,"Share hawayena nayi tare da ajiyar zuciya," _Na yadda Idan Allah nayi maka fad'a baka fad'a_
"Alh.malami sambo yace agaskiya ba za'ayi hakan ba!kuskure dai Anyi shi Amma yanzu jini ya had'a Dole a hakura!"tayi karatun agidansa,"Wannan shi ne abinda ya Dace Hajiya khaltum.
"Tayaya za'a hakura Alhaji!?"Dole NE atambayi ita Nadiyatu idan har tana sonsa da buqatar zaman aure da shi!"ko kuwa!?"Momy ta tambaya akufule saboda ta kawo iya wuya Domin tana son taga iya gudun ruwan Jawad Amma an hanata!"
"Na fahimceki khaltumi Domin ciwon 'ya macce na 'ya macce NE!?"Hajiya Maryam Tace tare da dubina Tace"To Nadiya gareki...kinji abinda momynki Tace"Shin kina buqatar Zama da Jawad ko kuwa araba auren KU.....!?"
"Dan Allah Nadiya kiyi Hakuri Wallahi Ina sonki!ke jinina CE!Kanwata karkice arabamu!"Bazan Kara wulaqanta ki ba!"Na yadda na amince Ni maras *TARBIYYA* kamar yadda Kika fad'a a baya. Wanda sanadin sa na cutar da ke.
Amma kisani haduwata da ke ya canja min halayena da dama!"Har aka dinga kirana Mutumen kirki idan Kika barni zan Kara lalacewa ke alheri ce.
"Nadiya ke haske ne arayuwata!"Dan Allah ki Soni, matukar kina son Marigayi Husamaddin ya samu labarin ganin jininsa, da mukayi akushewar sa to ki min rangwame.
Akwai aure atsakanin mu Amma Momy naso ta rabamu karki Bari Dan Allah....."Na yadda na amince ki kirani da Koma meye har sai kin gaji Zan amsa..."
kamar mahaukaci haka Jawad ke rokona Yana Hawaye!"
"Saif wani Dadi yaji aransa tare da tausayin sa Amma fargabar SA Daya Kar Nadiyatu Tace "Bata son Jawad din!"
"Hajiya Maryam Tace"ke muke saurare NADIYA....."
"Hawayena na goge tare da kallon Babana da Mamana Nace Ni Banda abinda zance face abinda iyayena suka zartar dama can nabi umurnin su na yarda da aurensa!"Yanzu ma ashirye nake da daukar duk wani hukunci da suka yanke akaina!"Bazan gaji da masu biyayya ba!"
"Hawayena na kara gogewa!Nace Mama......Baba na shirya amsar umurnin KU a Karo na biyu !nikam bani da zab'i sai naku....."Duk yadda kun ka zartar ashirye nake zanbi,"
"Innerie Tace"Haba Nadiyatu ai ke ce Zaki zAuna shi bamu ba!"Ki Fadi abinda kikeso saboda ayanzu kina da damar zabin abinda ranki ke so Domin gujewa Danasani! ta karashe zancen a Dan hasale!saboda ranta ya sosu da irin cin kashin da su Jawad sukayi min,"
"Duk Wanda ke falon ya fahimci inda zancenta ya dosa musamman momy da Jawad Amma Sam ba Wanda yaga laifinta!Domin D'a Cikin Rai Yake!Kuna duk Wanda aka cutarda nashi ba zaiji Dadi ba!"
"Mallam BALARABE gyaran murya yayi, sannan yace NADIYA hakika mungode, da yarda da kuma amincewa da kikayi damu, da kuma zabin mu A baya!"Sannan muna Baki Hakuri da jajanta maki Akan Duk abinda ya faru!"Ina son ki manta da komai ya wuce duk abinda kinka samu ko Kika rasa!"hukuncin ubangiji NE!"Nasanki da kawaici da alkunya,Ina son ki Kara hakuri akarou na biyu!"Kibi umurni na,ki Koma gidan D'an uwanki Jawad,"
"A firgice na dubi Babana idona taf da kwalla!"
"Mamana b'ata fuska tayi tare da Kara kumbura ta cika fam Dan haushi!"wato Mallam ya goyi Bayan dansa ita akashe Mata yarinya Lalle bazata sabou ba...."
"Jawad wani Sanyi ya ziyarci kokon ransa ya washe baki...wani kallon so ya jefini da shi,"Bansan sanda na watsa Masa muguwar Harara ba!"tare da hade fuskata babu Alamar annuri atattare dani.!"kirjinsa ya buga...saboda shi Yanzu wani tsoron ta Yake da gudun bacin ranta!"Dole a lallaba Kar liqi ya kwance!"
"Masha Allah,shi ne abinda Alh.malami, Hajiya Maryam da saifullahi ke ta nanatawa Cikin Jin dadi,"
"Momy Kam son tayi sai an gara Jawad yayi laushi sannan,Amma ko yanzu tana da dabarar da zatayi Wanda bazata koma da Wuri ba!"Sai ya gane shayi Ruwa NE,Domin kaunar da takewa Nadiya Daga Allah NE,"
"Mallam Balarabe yace nasan dalilin da yasa Nace ki Koma Nadiyatou,saboda Ni aganina abin kunya NE na raba aurenki da Dan Husama,ke da shi jini Daya NE!"Dukkan KU 'ya'yana ne,"Babu bambancin atsakanin KU....."Sannan Wannan hadin Allah ne ba namu ba!"Dan Haka ba abinda mukeso sai mu ga Kun zAuna lafiya,"Fatana Allah ya baku zaman lafiya da ZURIYA dayyaba...."Kamar yadda muka taso da Husama acikin soyyayar juna hakan nakeso zuriya ta da Tashi su kasance!"Hawayen Idonsa ya goge tare da kallon su yace kuyi hukuri da hukuncina nasan wasun KU basuji Dadi ba!"Amma nasan saboda Baku San Waye Bello da Husama bane,"BazAn manta rayuwata ta baya ba!
*WAIWAYE*
*ASALIN MU*"Ni da Husamaddin Yan kasar *SUDAN* ne, A garin Kharfum, muna zaune a unguwar Al-kubrih...sunan mahaifin mu Abu sufyan As-sultaan,Sai umman mu da ake kira Rajjah, "Mu shidda ne iyayen mu suka Haifa Aduniya; Ni Muhammad Bello nine na farko, sai Kanwata Awadiyah, sannan Husamaddin, da Sausal, da kuma wisam sai autar mu Abrar,"Daga Ni sai Husamaddin ne,maza awurin iyayen mu,Dukkan k'annai na baqaqe ne,sai dai Baki Mai haske irin na Yan asalin Sudan,sana'ar safarar Kaya shine sana'ar gidan mu,"muna dauko abinda babu Wannan kasar mu Kai Wannan kasar,"Umman mu ma sayarda zinarai da azulfa shine kasuwancin da tayi fice da shi agarin,"
"Tun muna Yara iyayen mu suka Gina rayuwar da ilimin Muhammadiya,"suna kula damu da Kuma *TARBIYYAR* mu sosai,"
"A lokacin bamu wani damu da ilimin boko ba, Shiyasa kannaina Mata na tasawa akayi masu aure ya saura Daga Ni sai Husamaddin,"
"Tun da Husama ya Zama saurayi ya nuna Yana son karatun boko, Wanda da kyar Assultaan ya amince ya turashi Bahri karatu...."Ni dama ban damu da son karatun boko ba!"Nan na Cigaba da Zama Ina taya Assultaan kasuwancin sa,"Da maman mu Rajjah,Ina Cigaba da neman ilimin Addini.
"Ana Cikin hakan naji Ina sha'awar siyasa a lokacin Ina matashi, Kuma Mai ilimi da dukiya.