← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 65

Sashe 65

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Kwanciyar hankali da arziki da wadata ya wadaci rayuwar Alhaji sadiq Wanda ayanzu commissioner of Education ne na jihar sokoto,"Arzikinsa ya yawaita ga Mata Nagari Allah bashi da zuriya dayyaba Mai albarkaa,Domin yaransa sun taso ahade ga ilimin addini dana zamani ba laifi sun Zama mahaddata kur'ani,"Domin sun samu *TARBIYYA* Mai kyau awurin iyayen su,"Komai Yake nema Aduniya ya samu burinsa ya cika. Domin ya Sami iyali Nagari masu nagarta ga zuriya na yawaita agidan SA sai GODIYA,"Tuni ya ginawa iyayensa da shi kansa katafaren gida a Argungu Kuma Yana taimakawa danginsa sosai"Duk wani Abu ya taso sallah ko buki ya Kan kwaso iyalansa suzo ayi hidima da su sannan su koma, Suhaila da Nadiya an Zama kawaye Jalila ma ta roki Nadiya gafara Haka dai komai ke Tafiya babu matsala,"

"Daman ance komai nisan jifa k'asa zai dawo haka duk nisan dare gari zai Waye!"Bayan duk mun gama tasko da wulaqancin da mukewa Jawad na koma gidan da dadewa tun lokacin bukin auren saifullahi da saudat,"Ko Bayan na koma na wahaladda shi sosai Kafin na ba da kai,"Haka muke rayuwa kamar komai Bai faru ba!"A Yanzu na fahimci soyyayar da Jawad kemin ya nunka Nawan ba Adadi ya samu aiki a Abuja,"A can muke rayuwa da yaran mu,"

Tsawon shekaru goma da suka wuce a baya,nayi karatu Burina ya cika Ni da mijina Dan kuwa shi burinsa na Zama barrister Ni kuma Burina nayi karatu.

"BARRISTER NADIYA BALARABE kenan hamshakiya Kuma matashiya Wanda ayanzu gwamnatin tarayya ke damawa da ita,"

"Duk wani burina ya cika Domin da taimakon mijina nayi karatu Mai zurfi har na zamou Barr.Nadiya ga shi na samu haihuwa uku Duk twins ne",Akhram da Ikhram wato (Muhammad Bello da Fatima Batula) sai Hanif da Hanifa(Khaltumi da Husamaddin) Wanda Duk sunan iyayen mu, sai Auta Juwairiyya.

Alhaji Jawad ne yayiwa iyayen mu takwarori da tagwayen mu biyu,"Yaran Masha Allah fafare tatas masu kyau, wad'anda iyayen mu keso da kauna da sosai,"Musamman momy da na lura duk soyayyar da takewa Jawad ta daurata akan yaran,"

"Sadaut ma tana lafiya ita da Saifullahi Wanda ayanzu suna jigawa acan ya samu aiki CBN zaman lafiya suke ga arziki ya daure,yaranta biyu maza mah'mud da Almustafa,"Itama tana aikin asibiti acan jigawa din ko da yaushe tana turowa mahaifiyarta da kannanta Sak'o harma da su baba laraba da baban su tana TAIMAKA masu sosai,"

"Umaima da Aliyunta suna zaune qalau shima ya samu Karin girma,suna zaune lafiya da yaran su,"Salim,salima,Salma da Salman sai autansu Saiman,"

"Mansura da Bimboy Yanzu Kam da sauki Domin ya samu an dauke shi aiki a local government,Ana Masa albashi sai dai baya wadatar su....Da sauki dai akan da can baya,itama ta samu tana karantarwa a sakandaren Mata,tana albashi, suna zaune lafiya Bayan watanni ya Kan d'auketa da yaran ya Kai Kebbi su Kwana biyu su dawo"Haka suke zaune Asiri tufe Ana Hakuri da juna,"Yaran su ZAINAB da Maryam (Ummi) sun tasa ba laifi,'Duk abinda ta samu Yana ciki ga lalurorin Yara sai ahankali,"Da kyar mansura ta samu haduwa da Jalila ta roketa gafara, Nan ma take Jin labarin suna Nadiya suna Abuja, Yanzu ma basa Nigeria sun fita kasar waje(U.S)hutun karshen shekara,","Duk da taso taga Nadiya ta roketa gafara Wanda akarshe Lambar wayarta ta amsa awurin Jalila domin ta kirata,ta roketa,"Nan Jalila da Suhaila su kai ma mansura goma na arziki,Domin ta Basu Tausayi sosai,ko suturar jikinta Dana yaran abin kallo ne,"Tufafin su Dana yaran suka had'a mata,"Tana godia har hawayen ta tabar gidan cike da kunya da danasani da Kuma nadama,"

"Tuni Rasheeda ta KASHE aurenta Domin zaman gidan Yan bala'i ya gagareta Bayan wuya da azaba ga dukan da take Sha awurin su,"Tahir Kam Yana zaune lafiya da matarsa safina ya samu MD a company da Yake aiki,yaran su uku Yaseer,Yaseera da Yasmeen,"Shine rike da Gidansa da kuma mahaifiyarsu Yana taimakawa Yan uwansa sosai,"

"Bayan su Barrister Nadiya da Ambassador Jawad sun dawo gida Nigeria,"Suka dunguma su da iyayen su zuwa kasar SUDAN inda suka gana da Yan uwa da Abokan Arziki,Nan Jawad da Nadiya suka ga gwaggonin su Wad'anda suke Kama da su, watan su daya suna zaga Dangi gari wa gari,"tamkar kada su dawo sai dai ba yadda zasuyi hutun yaransu ya Kare,"Haka suka dawo tare da alqawarin duk Bayan Lokaci zasu dinga kawo masu ziyara," Amma su Innerie da momy da Baba suna can SUDAN din acewarsu sai Bayan sati biyu ko uku zasu dawo,"Domin dai mutan Sudan su rikesu kamar kada su dawo,"

"Bayan sun dawo gida Nigeria da sati uku su momy suka dawo cike da kewar Dangi,"Ba'a Dade ba!"Sai ga ciwon ajali ya Kama Innerie,Wanda aka wayi gari babu ita adunia!"tashin hankali marar Adadi iyalanta suka shiga Wanda akarshe Hakuri ne magani!"

"Nasha Kuka!har nagodewa Allah shi kenan na rasa Mamana ,Ba yadda Zanyi sai Addu'a Fatana da Innata mu hadou Aljannah fiddausi,"Ganin zaman gidan babu Dadi awurin Baba da momy wani baranbaran,Shiyasa su Mallam Musa da sauran dangin mu na Sudan suka hada Auren momy da Baba,"

Day farko Momy ta so ta bijire a ganinta tayaya zata auri yayan mijinta,Amma Yan uwanta da Hajiya Maryam sun Nuna Mata bakomai bane,gashi ta jima batayi sure ba gwara ta tufawa kanta Asiri.

Shi Baba Daman yasan ya halatta Shiyasa Bai damu ba a hakan suka amince akai aure Suna zaune Lafiya da girmamata juna. na samu Sanyi araina Domin momy ta rikeni kamar Yar cikinta,tana kula da ni sosai,"Haka rayuwarmu ta kasance cike da farin ciki da Jin Dadi agefe Ina maraicin Mamana,"Yaran mu sun girma ba laifi suna karatu a makarantu masu kyau,"sun taso acikin kulawar mu na k'ara haihuwar namiji akayiwa baba malami takwara (Abbati)"Ina fita aiki a higher court Abuja yayin da ayanzu mijina ya samu Ambassador na Nigeria,"Shiyasa baima cika Zama Nigeria ba!"Yana Camaro idan Anyi hutu muna bin shi tare da zaga kasashen duniya.

"Anty Talatu ma ba laifi ta sake haihuwar da namiji Ibrahim, Daga shi Bata Kara ba, Saboda dama can tana da uku Mata ga yaran da aka bar Mata marayu biyu maza,"Shiyasa ta hadesu da Duka ta rike cike da Amana da kauna,"Anty Talatu ta zamou uwa Tagari awurin yaranta Domin ta Basu *TARBIYYA* kamar Kowacce uwa Tagari Mai Nagarta"ke kokarin baiwa yaranta Domin su taso da ladabi, Biyayya da nutsuwa,"

" _Ikon Allah akace sai kallo Domin tun duniya kake Gane illarka,wani ko Allah Yana raga masa sai alahira,"Duk abinda mutim yayi Khairan ko sharran shi zaya girba,"Allah yasa MUDACE mu aikata ayyukan ALHERI,"_

" _Anan na kawo karshen Wannan littafi na *TARBIYYA* abinda na rubuta dai-dai Allah ya bani Lada,Abinda nayi kuskure Allah ya yafe min Ni da KU Baki Daya,"_

" _Masoyana KU sani Ina sonku kuma Ina Jin dadin comments naku,Anatare Ni da KU iya wuya,"_

_A karshe Wannan LITTAFIN na *TARBIYYA* na rubuta Shine Domin fadakarwar da ilimantarwa sai nishadantarwa,"A dauki darasi Mai kyau azubar da abinda baya da kyau,"_

" _Iyaye Mata da maza Musa Ido Akan *TARBIYYAR YARAN MU*,mu Kula da ibadarsu,mu'amalarsu da abokansu mu sa Ido Akan duk wani Motsin su,"Mu daina nunawa Yara tsantsar so da kauna,Idan Anyi musu hukunci mu daina nuna bacin ranmu,"TABBAS iyaye Mata musani mune kashin Bayan rayuwar yaranmu Domin idan sun gyaru mune Kuma zamuyi alfahari da su,"Tayaya!?_

" _Ta hanyar basu " *TARBIYYA* Mai kyau,"_

" _Allah ya taimake mu ya daura mu Akan tafarkin gaskiya,ya shirya Mana zuriyar mu,yasa Mana hannu akan *TARBIYYA* yaran mu *AMEEN*_

_GODIYA MARAS ADADI 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI_

_MASOYAN TARBIYYA GAISUWAR KU TA DABAN CE_👍🏼👍🏼👍🏼

_TAMMAT BII HAMDULLAH......_

*YAR MUTAN ARGUNGU CE*😍

*2020*

_"SANIN GAIBU!...." COMING SOON IN SHAA ALLAH_

👍🏼👍🏼👍🏼PEN WRITERS ASSOCIATION
Chapter 65 · 0% Book details