← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 65

Sashe 36

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_"Yaa 'yan uwanah Muyi kokari mu kasance masu zuciyoyi da ayyukan alkhairi, Mu gujewa bakin ciki da Hassada domin babbar halaka ce, Mu so Yan uwa, muyi zumunchi domin Allah, Idan Cigaba ya samu Dan uwanka ka Taya shi Munna domin Allah, Haka idan zamuyi ibada da aikata aikin Alheri muyi domin Allah, Fatana Allah ya dauramu Akan tafarkin gaskiya Ameen."_ _____________________________________
***********$$**
"Bayan sun taimaka min na shigo da kayan nawa,Tayani gyara su, sukayi tsaf a mazaunin su na da"Domin har yanzu ba kowa a dakin sai su,Tun Bayan tafiyata,Abinci Deejah ta zuba mana tare da su muka ci sosai,Wanda Rabona da in ci abinci da yawa irin yau har na manta."

"Bayan mun kammala magunguna na fito da su nasha,Sannan na gabatar da sallar Isha."

"Alkibla na fuskanta Na Dade Ina jera Addu'oin tare da neman mafita da sauki arayuwata."

"Wayata Na dauka Na Kira layin Babana,Cikin Sa'a ya D'aga muka gaisa ya hadani da Innata mun Sha fira sosai da su,Har suke tambayana su Anty Jalila da yaran."

"Nace lafiya qlaw."

"Alkawarin da Na daukarwa Yaya Saddiq ya Sanya Ni Jin karfin boye masu damuwata har muka Gama wayar da su, Addu'oin fatan Alheri da nasarar karatu, Iyayena suka min."

"Cike da Jin Dadi nayi masu godiya nan mukayi sai da safe."

"Da murna tare da saukin kaunar su na ajiye wayar,sai Kuma Hawayen!da ke min sintiri a fuska,Tabbas ba kamar Iyaye Aduniya!"Wanda ya rasa Iyaye ya zamo abin Tausayi."Gashi yanzu naji Dadi da nutsuwa dalilin jin sautin muryar su."

"Kawayena na Duba, suma dukkan su Ni suka zubawa ido,Tausayina NE kwance afuskar su,sai Zaman jirana suke domin na kwance masu kullin abinda ke faruwa..."

"Inda suke na zauna,Ina fuskantar su na labarta musu komai Daga farko har karshe"Akan abinda ya faru da Ni."

"Deeyart Tace"A GASKIYA Anty Jalila Bata kyauta ba!"To ita wa ya Gaya Mata hakan...!?"

"Esha Tace shine fa tunda ke Naddy kince ko da zata fita bukin lafiya kalaw Kuka rabu da ita!"

"Nace gaskiya hakane Bata nuna min komai ba! har fa abincin da Zan dafa sai da ta fad'a min,me Zan girka kafin ta wuce,nayi mata dawo lafiya.."

"Deejah ta nisa tare da cewa to Naddy Ina ganin kamar awurin bikin birthday Nan aka hure Mata kunne, Sannan aka dasa makaman tsanarki da zarginku azuciyarta!"Dole mu binciki lamarin nan duk wacce ta hadaku tana da manufa akanki ko Kuma ta tsani Zamanki gidan!"

"Nima hakan nake tsammani Inji Esha.."

"Hakane gaskiya,Amma Ina ganin kamar kanwarta Rasheeda ce! saboda Bata wani yina sosai,Gani take na tare Mata komai agidan,Ada can rabin zamanta duk agidan NE!"To Tunda na dawo da Zama gidan, ita Kuma tayi hijira ta daina zuwa,Sannan kunga Anty Talatun nan Itama masifaffiya CE,tun farko ma ita ke kishina!A gidan bama Anty Jalila ba!"Nasha kamasu suna nunawa Anty Jalila illar zamana agida Suna yawan gulmata,cewa sukeyi tayi sakacin barina agidan!Ay yanzu an daina barin Yan matan Wannan zamani su zAuna maka agida,To inaga sunci galaba Akan Anty Jalila ne!"Amma Allah NE masanin gaibu ."

"kun san wani Abu? nifa duk tsanata da suke wallahi ba komai yayi min zafi ba!"Sai kazafin da sukayi min, ita da Yan uwanta...nan take muryata ta kama rawa saboda kukan da ya zo min."

"Kiyi Hakuri Naddy Allah zai saka maki!"Da ace Yaya Saddiq Bai dauki mataki Akan Jalila ba!"Wallahi da sai munyi maganinta mun ta da rashin mutuncinmu ita da shegun Yan uwanta jahilai duk sai sun gane KAWAI Daga Jin zance sai su hau kai!"Wataqila labarin wasu ne ma suka jiyo agidan bukin zasu huce kanki Inji Deeyart tana huci!."Tare da dafani tana rarrashina.

"Eshaa Kam idonta ya cika da kwalla!"Tace Yanzu Naddy kina ganin ba matsala!?"zaman ki a nan.da kinyi Hakuri kin Koma tunda an d'auki mataki akanta.

"Bazan iya Zama gidan Nan ba!Esha,Ina ganin hakan da nayi shi ne kwanciyar hankalina!"Amma ko da Yaya Saddiq, yayi min fad'a Zan Amsa laifina! Kuma na nemi afuwarsa, Amma fa Daga baya kenan!"Saboda na nuna Masa Ina son nadawo banga ya ce dani komai ba."

"To Allah ya kyauta Inji Deejah.

"Ameen,suka CE dukkan su, Daga Nan Kowacce tafara Shirin kwanciya, jiki dai ba Dadi! saboda an tabou Rabin ransu Naddy."Ko wayar da sukeyi tsawon dare da samari yau Kam an kasa!"

"Tunda misalin karfe goma na safe Kiran mansura ya shigo wayar Jalila wacce ke kwance tana tunanin duniya.!"

"Hello,Ta Daga wayar."

"Anty Jalila ko bacci kike na Tashe ki?"Kiyi Hakuri!

"A'ah mansura na Tashi.."

"An Tashi lafiya ya gida Ina Yara da oga!?"

"Hmnnn Nidai Ina lafiya sauran kuma ban San awane hali suke ciki ba!"

"Waro Ido tayi waje!Da mamaki Tace Anty Bangane ba!Meke faruwa!?"

"Jalila gyara Zama tayi ta labartawa mansura komai har da Karin Dan gishiri,cike da nadama take zancen har da Kuka Wai domin mansura ta tausaya Mata, ta taimaketa!"

"Mansura kamar tayi gud'a dan murna,Amma kannewa tayi,Tace Yanzu ya sakeki akan Naddy fa Kika CE!?"Allah ya rabamu da sharrin wasu yan Matan zamani!"Ta zo gidanki ta fidda ke!Lalle Naddy bazata Gama lafiya ba,kuma ta cika maciya Amana!"Mansura Tace murya na rawa!"

"Jan majina tayi alamun Kuka take,tare da canja murya zuwa kalar Tausayi Tace"Anty Jalila kiyi Hakuri in shaa Allah zaki koma gidanki!"Yanzu kiyi kokari kije gidan anjuma da yamma ko gobe,Da sunan kayanki Zaki dauko na sawa kingane!?"Hello Anty!kina jina!?"

"Eh mansura Ina tare da ke!"Inji Jalila tana sheshshekar Kuka!"

"Yawwa Anty,Idan kinje gidan sai ki turaren da maganin Duka,Amma fa ki daidaita time din da baya nan,Sannan kiyi zamanki agidan sai lokacin dawowar shi Yaya Saddiq din yayi,ki shafa Wanda akace kisa ajikinki,Ki tabbata ya shaki duka biyun,na jiki da na gidan."Sai ki dauko kayanki ki dawo."Sauran bayani zai biyo baya."

"Kai!Kinfa kawo shawara Mai KYAU,Nagode kanwata Kinga ko tun Jiya na kasa bacci Ina tunanin ya zanyi!"Da maganin nan Amma gashi kin Samo Mana mafita Nagode."Jalila Tace cikin Jin Dadi da gamsuwa,

"Haba!Anty Jalila ba komai,Sai jibi Zan shigo Ina ne ma unguwar ku!?"

"Nan Jalila ta kwantata Mata tare da Kara Mata godiya ta datse kiran.,Sai yanzu tasamu karfin jiki, Tashi tayi domin ta watsa ruwa,ta Sami abinda zata jefawa cikinta."

"Mansura ko Ina ruwan kankara ta fad'a domin Dadi abinda takeso ya samu godiya tayiwa Allah Sannan ta dinga Shirin fita class cike da Jin Dadi."

"Hayaniyar da taji anayi afalon gidan NE ya sanyata fitowa,Ko Mai Bata shafa ajikinta ba!"Jallabiya KAWAI ta sabo ta fito da faduwar gaba!,Tahir ta samu afalon Yana ta zuba,Har da Marin Rasheeda!"Anty Talatun ma Sai sa'in sa suke da ita, tatas yayi musu tun kan Hajiya har Rasheeda."

"Da sanyi tace Wai meye hakaTahir!?"

"Ke munafuka kimin shiru ko na babballaki!"Sakarai! Wallahi kinyi asarar Miji!Baki sani ba!"Kuma sai kinyi Kuka,Wanga da kikeyi ba kuka bane!Har da danasanin ki,ya na nan tafe!"Kun san baku da gaskiya."Zaku wani tasani gaba na biku,To Gashi Nan munji kunya!"Wallahi naso ahada da ku, ukun nan ayi muku dukan tsiya arufe KU sai Kun ji ba Dadi..."

"Sororo Jalila tayi tana kallonsa bata da halin magana saboda yadda yake tujara duk Wanda yayi magana zai iya mazgeshi Dan ba mutunci ne da shi ba!"Daman tun suna Yara ita ke Shan wuya hannunsa,saboda shi ke Binta"Kuma Tahir akwai zuciya Amma fa sai antabo shi!"Mutim NE Mai son yin rashin mutunci da hujjarsa!Shiyasa tayi ruf da bakinta."

"Hajiya a fusace Tace Tahir ka fita idona na rufe! Iskancin ka ya isheni!Ita Rasheeda idan kanwarka ce!To Talatun da Jalilan ba yayyenka bane!?Sunji sun gode!" kaje ka bani guri yanzun Nan, tun ban maka rashin mutunci ba!"

"Hajiya ai kin san ba ku da gaskiya!"Da Yake ba sonta kike ba!shine ni Zaki ga laifina Bayan ga 'yan ta'adda nan agabanki!"

"Tatas!tas!tas! sautin saukar Marin da Hajiya ta saukewa Tahir ka keji!"Wanda sai da ya ga wuta!Tace naji Nagode fita daga falon nan,tare da nuna Masa hanya."

"Idonsa sunyi ja! yace Zan fita Amma Daga yau bani ba shiga sabgar su! Tunda su basu tsare gaskiya! kuma ahakan kike goyon bayansu,Ni nafi son inyi masifa da dalili! da Kuma hujjata!"yadda bazanje inji kunya ba!kuma ba ZA'A Raina Ni ba!" Ke kuma duk kika Kara dauko gulmarki to kada ki dosoni,Yace ma Rasheeda Cikin fushi ya wuce Dakinsa tare da bugo kofar da karfi."

"Ina nan tsaye Ina kallon Dan wahala!"Rasheeda Kam sai Kukan Marin da Tasha take,Anty Talatu da zagi ta bishi tana zatayi maganin rashin mutuncin SA!"

"Hajiya Tace"KU barni da shashasha!"Ay mu ba kyalewa zamuyi ba!"Dole ne mu dauki mataki!Nan dai ta Cigaba da borin kunyarta ta gama!"

"Kichen din gidan Jalila ta nufa,domin samun abin Kari,Sai dai kunu tasamu, bata fuska tayi cike da haushi!"Ta Dan diba a cup,ba ko suga!bare kosai!"Tana Sha sau daya ta aza hannu aka! Tana Hawaye!Saboda rabonta da shi tun tana jego!"Amma gashi yau Shi take Sha bako kosai!"Amma gidan Saddiq sai abinda Ranta keso Mai Dadi take ci ta Sha har ta aikowa Hajiyar ta."

"Gashi ba halin magana ko korafi yanzu Hajiya tayi mata cin mutunci saboda ta lura tun Jiya tafara canja mata,saboda ita Hajiya idan dai ba bata zakayi ba!To zaku Sami matsala!."Idan Kaine zaka nema awurinta

"Saddiq kam tun Jiya ya kasa sukuni,Abubuwa sun taru sun Masa yawa,shiri yayi, ya nufi gidan Ali, Domin ya ga yaransa."Ya samesu sun baje afalon gidan, basu da wata damuwa sun hade da yaran su Ali, Salma da Salim sai wasa suke da Yake duk tsara NE,"Numfashi ya sauke tare da basu sweets da ice cream din da ya saya masu da gudun su suka nufi bedroom Inda matar Ali take Umaimah suka nuna Mata!"

"Amsa tayi ta rarraba masu da murnar su suka wuce wurin wasar su,A hankali ta tashi daga gaban madubin,mayafi ta yafa ta nufo hanyar falon.."A sannu take Tafiya saboda tsohon Cikin da take dauke da shi."

"Da fara'ah ta samesu suna fira Tace"Manyan Baki sannu da zuwa."

"Saddiq yace"Yawwa,Umaimah ya gida, maman Yara,Inji basa rigima!?"

"A'ah basa rigima aini Kasan teacher ce nasan ta Yara.."Umaima Tace tana Dariya."

"yace"Daman nazo na tafi da su ne!"Nasan su da rigima Gashi kina fama da kanki!"

"Ina zaka Kai su Saddiq Idan ka dauke su Daga nan!?"Bayan ka Gaya min bazaka mayarda Jalila ba!?"Kuma Nadiya ta koma hostel!Kaine zaka zAuna da su ko kuwa!?"Inji Ali
Chapter 36 · 0% Book details