← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 65

Sashe 34

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Police station din suka nufa, karasawar su ke da wuya sai ga Ali ya qaraso shima da sauri..."Saddiq yace Yawwa Ali Dan Allah ka wuce min da yaran Nan gidanka su ci abinci suyi wanka Sannan ka dawo, su Kuma yaran kabar su can..."

"Ali yace gaskiya banji Dadi ba Saddiq..Wai meke faruwa ne!?"

"Babu lokacin Wannan bayanin Ali..Ni dai kafita da yaran Nan daga wurin Nan..."Sai ka dawo kaji yadda abin Yake.."

"Ba damuwa,yace tare da Jan yaran suka wuce!"Jalila idonta na kansu aharabar station din, sai dai ba halin magana. Dan ta lura ko da wasa Saddiq Bai kalleta ba!"Gashi dazu Akan ta Kula Mufeed Hajiya ta Mata fad'a wai ta fita harkar yaran dan Saddiq din zaifi Jin haushi..."

"Wuri aka tanada kowa ya zauna nan Officer ya karanta Duk statement din da aka dauka Akan abinda Saddiq ya aikata..Tare da tambayar Saddiq din hakane!?"

"Abinda Ya san ya fada ya Kuma aikata yace hakanne abinda ba gaskiya ba Kuma ya karyata..."

"Ali NE ya dawo shima Wuri yasamu ya zauna kusa ga Tahir..Jalila da Rasheeda sai hararensa sukeyi..."

"Officer yace meye dalilinka na dukan matar ka batare da tayi maka laifin komai ba!?"A karshe Kuma ka hadata da guzurin saki!"

"Saddiq yace ranka ya Dade neman kisan Kai!"tayi shine nayi kokarin hanata!.."

"Kamar ya kisan kai!"

"Gyara zamansa yayi Cikin ilimi da dabara Saddiq ya zayyane wa Officer Duk abinda ya faru!"Daga FARKO har karshe...Ya qara da cewa idan Kuma tayi musu..."Ina da shaidu yanzu Haka yarinyar akwai raunukan da sukayi Mata ita yayarta da Wannan marar kunya ajikinta,ya nuna Rasheeda.

Sannan ina so muje asibitin da aka kwantar da yarinyar a nemo file dinta..nasan zaku samu dukkan bayanai daga bakin likitan da ya dubata..."

"Yau ma tayi yunkurin hallaka yarinyar Shiyasa nayi kokarin hanawa har na daketa, yallabai ina ma son akafa shaida anan domin ta ci alwashin sai ta kashe yarinyar!"Daman Ina niyyar kawota Kara koda ita Bata kawo zancen nan ba!"ta fita harkar Yar mutane abinda take zargi ba haka bane,k'anwata ce Wallahi duk abinda ya sameta itace. akafa shaida nan.."

"Tahir...yayi sarou saboda shi Sam bai san sun daki yarinyar ba!"Kallon su yayi duk sunyi wani zuru-zuru.."

"Hajiya Kam sai fidda ido take!"

"Tuni Cikin Rasheeda ya dauki ruri sai murdawa yake.."

"Cikin tsawa Officer yace Ke Jalila kinji bayaninsa hakane!?"Ko akwai abinda Baki yadda da shi ba!?"

"Hawayenta ta goge da gyale..Tace nasan mun daketa dai..."

"To kince sai kin kasheta!?"Inji Officer

"Wallahi Ni ba da gaskiya nake ba barazana ce!"Officer taya can Zan iya kashe mutim!"Dan Allah kuyi Hakuri wasa nakeyi.."

"Officer....yace Kai rubuta.."Nan Mai rubutawa ya rubuta Duk bayanan..."

"Kallon su officer yayi yace to naji Duk bayanan KU...Kai Saddiq Ina yarinyar..!?"

"Yallabai dazu da naga Jalila taso ta halaka Shiyasa na mayarda ita hostel Daman kanwata CE tazo karatu ne ba ANan garin take ba!To yanzu da Naga masifar tayi yawa ga rauni ajikinta!kuma Ina gudun Jalila tazo Daga baya idan bana gidan ta Ida nufinta..."Ta kashe Yar mutane...Shiyasa da yamma na mayarda ita makaranta tana can.."

"DakAta masharranci!ka daina hada diyata kisa!"Inji Hajiya afusace tana goge gumi da mayafinta!."

"Officer yace"Hajiya! karki manta diyarki tayi furuci kuma ta amsa mu Kuma mun dauki report Dan watarana.."

"Yanzu Saddiq zAka fad'a Mana abinda ka kashe...na jinyar ita Nadiya zasu biya ka ko nawane..."Sannan kuma zasu bayarda naira dubu goma ta Cigaba da Shan magani..."Tarar da akaci su saboda sun daketa batare da hakkinta ba!"

"Y'allabai....."

"DakAta! Hajiya nasan me nakeyi..."Ai hukunci na lalama ne nayi maku.

"Ke Kuna Jalila zamuje asibiti kema aduba ki!"Saddiq zai biya duka kudaden da za'a kashe maki..."

"Ke Rasheeda ke da yayarki da ace tun Ranar da abin ya faru ne aka kawo mana labari!to da sai mun kargameku a cell har wannan jalilah!"Saboda kunyi kokarin kisan Kai!"Kuma Kun taka doka!"Daga yanzu Baku ba Nadiya munyi maku kashedi na karshe!"

"Yallabai da subar kudin kawai saboda na fiso akashe zancen Inji Saddiq.."

"Duk abinda nace shi za'ayi Saddiq Wannan shine dai-dai. saboda mu bama sabawa doka!"Kai ma karka k'ara daukar hukunci da kanka!

"Bakin Hajiya ya Kara tsini... Rasheeda ta Matsu subar wurin tun ba'a tasa kiyarta cell ba!"Jalila Kam taga ta kanta Baki Mai yanke wuya domin tana Cikin tsaka Mai wuya.."

"Daga Nan asibiti suka nufa aka Duba Jalila tare da rubuta magani Saddiq din ya biya, tare da Basu dubu goma na Shan magani..."Amma fir Tahir yaki karba yace ya rikesu kudin tarar Nadiya."

"Hajiya Kam ta kasa cewa komai taga Sami taga Rashi! Daman Talatu tayi masu gudun hakan.. "Gashi akarshe Sune da kunyar!"Da jin haushi da takaichi!"

"Saddiq dubu biyar yaba Officer da yaransa tare da Masa godiya suka wuce..."Ko duban su Hajiya baiyi ba!"

"Hajiya Tace DakAta Saddiq idan Kai Dan halal ne!ka Ida sakin Jalila yanzu ba sai anjuma ba!"

"Murmushi Yayi tare da cewa kiyi Hakuri Hajiya iya sakin da Naga damar yimata kenan..."motarsa ya shiga, Ali ta da nashi motar yayi Nan SUKA wuce suka bar su Hajiya na daddalar sayyada horn sukayi masu na sai da safe suka wuce abinsu..."

"Tsaki Rasheeda tayi Tace shegu wa zakuyiwa karyar Mota..."

"Ke Mana banza! ke sukeyiwa?keda gaki Nan akafa...wallahi sai na karyeki wato kunsan kun daketa, kukasa na zo Ashe bakuda gaskiya...Tahir yace Yana kumfar Baki.."

"Dan Allah kubar ni da zancen haushi da wanne zanji..."ke Kuma sakarya Sonsa ma kikeyi ko!?"marar zuciya yace bazai sakeki ba!"ke bakisan kalar rashin mutuncin da zakiyi Masa ba!Har ya hasala ya sakeki!"

"Shiru Jalila tayi Amma azuciyar ta tasamu sauki da ba'a Ida daga Mata red card dinta ba!"kamar yadda Hajiya ta so."Sai da sukayi Tafiya Mai nisa Kasancewar dare yafara Sannan suka Sami abin Hawa kowanne da bacin ran da ke damunsa..."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍😍

*2020*✍🏼
*Share & Comments*
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 25*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

*DAN TSOKACHI..."A duk lokacin da masoyana ke min Wannan tambayar na kanyi😄Wai Dan Allah Nabeela Dikko 'yar mutan katsinawan Dikko ce?"My Fans Ni Yar KEBBI ce, Ba 'yar katsina ba,Kamar yadda kuke tsammani😍 Nidai 'yar jihar kebbi ce a garin ARGUNGU,Nagode sosai fans,Da kulawar ku, da Kuma soyayyar ku,Allah yabar zumunchi Ameen,Duk Wanda zai zo kebbi Inda nake, ina maraba.*😄

_A koda yaushe mu masu kuskure neh awurin ku,Mu writers muna fuskantar kalubale awurin ku readers, Dan Allah idan munyi ba dai-dai ba amatsayinku na fans ku fitou ku bamu shawara, ba kuyita zagin mu ba,Kusani laifin mutum daya zai iya shafar kowa,Sannan ta wani gefe kuma Kuna bayarda goyon baya Akan abinda ke faruwa,FATANA Allah ya yafe Mana ya daura mu akan tafarkin gaskiya Ameen,Anatare iya wuya fans_
______________________________________
*************
"K'arar Wayata ta sani karasowa da sauri!"Inda na sanyata caji na nufa,Ina kokarin d'ebeta acajin!"Sai dai Lambar da ta bayyana da sunan Wanda ya kirani ajikin wayar ya sani tsorata!"Juyowa nayi na kalli Esha da tsoron Ina fadin Yaya Saddiq NE!"

"Kiyi sauri ki dauka mana!Inji Esha"
"Da sauri..Na d'aga tare da Sallama hannuna na rawa da muryata!"

"Ki fito bakin hostel din ku, Ina jiranki,Shine Naji adodon kunnena,Dif Kuma ba'a Kara cewa komai ba!Wayar na duba Ashe ya datse kiran."

"Idona ya kawo kwallah!Ina kokarin yiwa Esha bayani me yace,Sai ga Hindou ta rum 6 da maman hostel abayanta sun shigo Dakin."

"Bayan mun gaisa da su,"Maman Hostel tace"Nadiya kiyi sauri!Tun dazu nake neman Dakin ku Bangane ba! Mallam Saddiq ke nemanki,Yana waje Yana jiranki!"

"Da kyar na hadiye kukana!Nace to mama Gani Nan!"Juyawa sukayi suka fice!"

"Ni Kuma Esha na duba!"Ko Zaki rakani!?"

"Ni Naddy?Allah ya kiyaye!wato na karaki asirinki ya tono!kina son ya gane muna tare har yanzun ko!?"

"To Ay yanzu Kun canja Daga yadda ya sanku Adaa can baya Eshaa!"Kuma Duk Wanda zai tambaya zai fad'a masa hakan!"

''Amma ba damuwa bara na tafi nace Muryarta na rawa! na sab'a hijab Dina,na nufi hanyar waje!"Tun Daga nesa na hango motar sa, Addu'oin nake idan na Kama Wannan na manta karshenta, na dauko wata har na Isa jikin motar,"

"Tsaye nayi Ina kallon su saboda duk glass din motar arufe Yake ko sallamar da nayi basuji ba, sai dai nasan sun ga baki na Yana motsi,kusan mintoci Basu fito ba!Ni Kuma Ina tsaye!"Nan Kuka ya zo min na hau shafe Hawaye na da hijab."

"Daga Cikin motar kuwa,Ali,yace ko Yanzu an horata nikam agaskiya ta bani tausayi,ka dubeta Wallahi duk atsorace take!."

"Saddiq yace"Daman halin ta NE, Kuka ba!"

"Fitowa sukayi Daga Cikin motar ahankali nayi kasa da murya ina gaida su,

"Yaya Ali ya Amsa min tare da tambaya ta ya makaranta ya karatu?"

"Lafiya kalau nace Masa"

"Yace"Nadiya Daman mun zo mu duba shin ko kina makaranta?"Alhamdulillah,Mun sameki,Amma Meyasa Zaki fita batare da iznin Saddiq ba!?Bayan kinsan amanar kula da ke tana hannunsa!"A gaskiya Baki kyauta ba!"Ay ba'a hakan! da kinyi Hakuri idan ya dawo Daga masallacin, kice ya mayar da ke hostel din!"Sannan komai ya wuce kiyi Hakuri kinji!?"

"Sunkuyar da kaina nayi nace to Nagode,"Na Kara da cewa Yaya Saddiq nasan nayi laifi Dan Allah kayi hakuri!"

"Duk da ya yaji ciwon abin da yarinyar Nan tayi Masa Amma Akan ta bashi Hakuri sai yaji wani Sanyi aransa."

"Yace ba komai Nadiya Allah ya tsare gaba Yanzu anan kike son Zama kenan!?"

"Eh....!"Yaya nafi son nan saboda Ina shiga library karatu,gashi anfara Mana (C.A) Ina bukatar Samun nutsuwa Domin karatu"

"Ya CE to Shi kenan Ali kaji yadda Tace.."

"Ali yace to ba damuwa,Nadiya Allah ya taimaka,Ayi ta karatu banda wasa, ya dauko kudi acikin aljihun sa, ya bani yace ga Wannan ki sayi sabulu."

"Amsa nayi Ina GODIYA tare da nunawa Yaya Saddiq din."

"Shima godiya yayiwa Ali."Yana murmushin jin dadi Sannan

"Ya kalleni a wane daki kike Zama!?"

"A dakin da nake Ada!na bashi Amsa cike da tsoro,

"Ba Nace kibar Zama da yaran Nan ba!?"

"Yaya Wallahi sun daina komai Yanzu karatu NE agaban su Kuma ka bincika!"

"Ay gurbi ya Bata Sha,Domin ko sun gyara ba za'a daina masu Kallon banza ba!Kuma idAn an ganku tare dauka daya za'ai maku ba ayi b'ari a kwashe daidai ba."
Chapter 34 · 0% Book details