← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 65

Sashe 63

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dauki Alqawari ko da zai rasa rayuwarsa ba zai iya rabuwa da Mansura ba!"Adams yayi laushi saboda shifa tsiwar Sahura na burgeshi amota ma Sai janta da Fira yake amma tayi Masa banza saboda haushin marinta da yayi d'azu!"

"Farin Cikin su mufeeda ya karou Alokacin da mudi Mai gadi ya wangale masu get,Murna suke har tumami amotar, da sauri suka fitou sanda motar ta tsaya!"

"Daga kofar falon Salim da Salima suka fito da gudun su, suna tarboun Mufeeda da Mufeed da iyayensu,"Cikin falon suka shiga cike Jin Dadi,"Yaran sunji dadin ganin sabon gidan nasu Mai kyau da tsari,"

"Suna shiga sukayi arba da Mommyn su ai da gudu suka fad'a jikinta suna murna....ita Kam Jalila harda hawayenta saboda murnar ganin gudan jikinta!" _Ayanzu kam Tayi nadamar barin gidan mijinta da yaranta_

"Umaima da Anty Talatu sai da idonsu suka canja launi,Akan tausayinsu...."Sallamar mu Saddiq CE ta katse hayaniyar da ake,"

"Maraba Umaima tayi musu ita da Jalila,suna Zolayar su da An gaida Ango da baran Ango"Gaban Ali ya buga baima San ta Ina zasu fara ba!"

"Sai yanzu Sadiq yaji wata fargaba ta darsu azuciyar SA,ya raba idonsa afalon sai dai ba Suhaila ba alamarta!"

"Anty Talatu da Rasheeda fatan alheri suka yiwa Sadiq din suna kokarin Tafiya....."Sai dai Aliyu cewa yayi Anty Talatu ki tsaya!A warware komai agabanki Domin wasu matsaloli sun kunno Kai ba'a daura auren da Mansura ba!"

"Wani Sanyi Jalila taji Azuciyarta Alhamdulillah ta fad'i tana Murmushi Wanda batasan ya fitou fili ba.."

"Meke faruwa aka fasa auren!? Umaima ta jefi Ali da Tambaya..."

"An daura auren Saddiq sai dai ba da Mansura ba Akan wasu dalilai!"kuyi Hakuri da abinda zAkuji da Suhaila aka d'aura auren....Inji Ali,"

"Wani kallo Umaima ta watsa masu tare da Tashi tsaye!"Tace Abban salim shin Wace Suhaila!?"

"Suhaila dai tamu kanwarki nine na baiwa baba Haliru kawun Sadiq aurenta Kinga kudin baiko da sadaki da Abokina kuma yayanta Sadiq ya biya!"

"Jalila ma tsaye ta Tashi da mamaki suka dubi juna ita da Umaimah tare da kallon Damen kudin da Ali ya ajiye agaban Umaima,"

"Anty Talatu da Rasheeda Dadi sukaji saboda Suhaila tafi mansura nesa ba kusa ba!"

"Suhaila Daga bedrum din da take kwance ta dinga jiyo muryoyinsu ahankali ta fito ganin kowa ita Yake kallo yasa ta Dan razana....Da sauri Umaima ta kamouta Tace Suhaila shin gaske NE ko wasa Wai Aliyu ya aurar da ke ga Saddiq batare da sanin mu ba!"

"A firgice Tace aure kuma!?"Ni Suhaila akai ma aure!?"Anty da gaske!?"Yaya Saddiq NE mijina...!?"

"Eh da gaske NE Suhaila Inji Ali da sanyin murya.. "

"Suuuuuuuu.....Suhaila tayi sai ajikin yayarta ta some!"Hankalin kowa ya Tashi afalon kokarin zuba Mata Ruwa ake," Umaima kaam har da kukanta saboda tashin hankali!...."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍

_Acigaba da Gashi fans, suya sai Ranar sallah, comments dinku na sakani nishadi, Kuma Yana Kara min fetur Wurin sambadou maku post, NAGODE da Addu'oin KU Alhmdllh...na samu sauki,Kusani Anatare Ni da KU masoyanah, na ciki da wajen Nigeria,"iya wuya muna tare, sai nazou kawo ziyarata Domin ku mutan Niger,Ghana,Gabon, Cameron,da Sudan Amma kune Zaku biya min biza😍😝NAGODE DA K'AUNAR KU_

[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

_ALHAMDULILLAH....._
______________________________________
"Gidan da Bimboy da ya saya ba laifi domin,"Da dadewa tun Yana cikin ganiyar KASHE kudin gadon SA,ya sayi wannan gidan, daki biyu ne da Falo sai Kichen da bayi,"

"Ko da suka karaso gidan, su Dan iska sun share gidan tatas,Har sun zuba kayan furnitures sun jera kamar Mata,"Bayan sun gama suka sallami direban ya wuce,"

"Sahura ta dan ji dadin Ganin gidan Saboda Yana da damar SA,"Kallon yadda aka aza gadajen da kujeru tayi sunyi kyau sosai,sai dai babu fenti da tails,An dai shafe ciki da wajen gidan da sumunti,"Mansura Kuka take kamar ranta zai fita,sanda ta gama kallon ko'ina na gidan, dan burinta ya wuce rayuwa a irin wannan gida,Dan ita tasawa sabon gidan Sadiq rai Dan kuwa sunje zagaya gidan yafi a kirga.mafarkinta ta rayu agidan daula karyarta ta karu Amma Wai karshenta Nan gidan....Inaaa bazata sab'ou ba Kuka ta dinga rerawa tana toshe bakinta da mayafi...Sahura Hakuri take Bata Amma Taki tayi shiru.,"

"Duk mutan unguwar Gwuiwa sunji dadin auren na Bimboy,domin zasu samu sassauci Dan ko Yana cikin manyan shaidanun unguwar Masu Tara Yan Mata da samari.

"Abin ci da drinks Dan iska ya kawowa sahura,"Yace Ranki ya Dade ga abinci inji oga Adams kuci ku koshi ke da amarya sai ke ki fitou mun Tashi komawa za'a saukeki Kebbi,"

"Sahura yunwa takeji Haka ma mansura na buqatar abincin,Shiyasa ta karbi abinci,"Tana zabgawa Dan iska Harara,Tace dama hanyar Mota da ta jirgi daban...KU wuce abinku nasan hanyar garin mu,"Dariya Dan iska yayi har shewa yace kanki akeji Yar Shan miyar Amarya, sannan ya wuce abinsa,"Nan Sahura ta bude abincin Fried rice da nama ne acikin kowanne takeway,Sahura Zama tayi ta ci shinkafar, kana ta aza lemon fanta,"Mansura Kam cin dole NE take ma abincin Domin maganin yunwa,"Bayan sun gama Sauran kayan gidan Sahura ta gyara,sannan Tace to Ni mansura Zan tafi!Kiyi Hakuri har muji me Mallam na Kan tudu zaice,"

"Share hawayenta tayi,Tace Sahura karki manta....da zancen karye asirin Nan, Saboda na fahimci duk yadda Mallam ya fada Mana saddiq Zaiyi,Kinga shi NE Bimboy ke nuna min,Idan har asirin yayi akansa akwai matsala!"Saboda Ina son nayi Masa rashin mutuncin da zaiyi zucia ya sakeni!" Kinga idan maganin nan yaci ba yadda zai fusata har ya sallameni.

"Karki damu mansura za'a warware asirin sai ayi Masa Wanda zai sakeki Ido rufe!"karki damu...Kuma in shaa Allah Sadiq zai gane kuransa!"Kedai KAWAI Inji dumus....."

"Jikkarta ta dauko da kyar ta had'a dubu Sha UKU,Tace Kinga Wannan Sahura ki kaiwa Mallam dubu goma,Wannan ukun Kiyi na Mota!"Kinsani Banda sauran Kudi yanzu,Duk Bikin da na samu awurin kawayena da dangi, sune na hada na baki Kika amso min wancan kwallin..."Yanzu dubu biyun nan da kike Gani su kadai NE ragowa, Zan ajiye su hannuna har Naga yadda Tafiya zata kasance!" _(Asarar duniya da ta lahira naga masu neman magani bazasu taba tara komai ba,Allah ya shirya amin,)_

"To ba Komai mansura Zanyi masa bayani idan yaso Daga baya in kin samu ragowa kudinsa,Kuma aikin yayi kyau,sai ki biyashi Sauran, kinsan na Kan tudu da kudi, baya kananan aiki Daga ashirin zuwa sama ne..."Sahura Tace cikin Alamar rashin Jin dadin kudin..."

"Ba damuwa Sahura inji mansura,tana kallon kawarta, sannan tace"kije gidan mu ki duba min mamana...."Nagode Inji mansura Alokacin da take kokarin ma Sahura rakiya...."

"A kofar gidan Dan iska NE...zaune sun tare hanya Saboda tsarou..."Yace madam akoma gida hakan ke Kuma umma ta gaida Aysha,"

"Tsaki Mansura tayi ta wuce!Azuciyarta Tace Hmnnnn....wato gadinta ma akasa wad'annan Yan daba suyi,"Sahura Koh sum sum ta wuce abinta tayi tafiyar ta, Domin ta fahimci Su Dan iska Basu da mutunci..."

"Bimboy da Abokinsa Adams ne zaune awani Babban zaure...."Bayan wani lokaci Mutumen ya Gama rubutu da Zane ature mai kasa sannan ya dubesu yace"Samari kunzou da nasara an daureta...babu ita Babu fita har abada matuk'ar ba Kai ka Bata umurni ba!"Kai Wataran da hannunka zaka tura keyarta waje ta rigeka dawowa Cikin gidan,Na kafe maka ita agidanka sai yadda kaga dama da ita,"sannan na rabata da kowa nata matuk'ar ba masu sonka ba ne,"

"Dariya Bimboy yayi yace Nagode Dan mallam... hakika kayi min maganinta...Adams yace Shiyasa muke yinka Dan mallam...."

"Kudi suka bashi sannan suka wuce suna murna Domin da yardar Allah sun gama da Matsalar mansura,"

"Bayan an zuba ma suhaila ruwan Sanyi ta farfadou ahankali take kallonsu,"Nan aka samu kowa ya zauna,Yaran ko Dakin su aka tura su suje suyi wasa, Anty Talatu ta kira Hajiya Atika,"

"Falon ya cika da Yan uwan jalila duk sun karaso,Hajiya Atika,Tahir da Mahmud,"suhaila sai kallon su take ta rasa me ke damunta arayuwarta tsoro!fargaba!ko Kuma farin cikin samun Sadiq da take tunani akowacce Rana,"Domin halayen SA da kirkinsa na burgeta,"Amma Bata taba Jin Sonsa arayuwarta ba!"Burgeta KAWAI Yake,"

"Umaima da Jalila suna zaune awuri Daya Kowacce da tunanin da takeyi aranta,"Haka Sadiq da Ali tunanin Mafita suke fatan su Allah yasa Kar asamu akasi!"

"Hajiya Atika ta numfasa tace''Aliyu KU sanar Mana meke faruwa!?"Tayaya ka daurawa suhaila aure batare da saninta ba!!?"Sannan ita mansura Meyasa aka fasa aurenta!?"Duk Ajere Hajiya ta antayo masu Wad'an nan tambayoyin...."

"Gyaran murya Ali yayi yace"Hajiya kamar yadda kuka sani mansura ta cutar da Sadiq shiyasa yace ya fasa aurenta,Kuma akayi sa'a ma Ashe mansura na dauke da cutar HIV sannan ta yaudari wani saurayinta shine ya tona Mata Asiri,Kuna yace zai sanarwa kowa matuka ba'a daura auren da shi ba,"Shi kuma Sadiq ganin an daura auren mansura da wani,Shiyasa ya nemeni alfarmar Akan nabashi auren suhaila Yana sonta,Kuma ya yaba da nutsuwarta, hankalin ta,"Yasan cewa In shaa Allah zasu fahimci juna da Jalila Kuma zataso yaransa,"Ban yarda ba Sai da yace"idan har Suhaila ko Yan uwanta Basu amince ba zai saketa!"tun Kan wani kunne yaji,"Nan dai Ali yayi kokarin masu bayani tare da kwantar masu da hankali har ya fahimci sun gamsu sosai da bayaninsa..."

"Da kan shi ya Kira wayar umman kano,Cikin Sa'a ta d'auka,Ali fannin tsara zance ba baya ba!"zaune yayi ya labartawa surukar SA komai tun farko har karshe,"Inda ya Bata Hakuri Akan rashin tuntubar ta amma ya shaida mata ya kira Alokacin sai dai Kash!ba a dauki wayar ba!"

"Umman Kano Tace ba komai Ali,zanyiwa dangin Babanta bayani, Yanzu Nan Mallam Musa ya kirani yayi min bayani tare da rokona alfarmar na fahimci lamarin.

saboda Haka na amince da auren Allah ya Basu zaman Lafiya,sai dai ta zAuna agidanku har Yan uwanta suzou ayi taron bukin akawo furnitures dinta,"Sannan ta tare kaga ayi walima hakan,"

"Godiya sosai Saddiq yayi ma umman kano,Hajiya Atika ma wayar ta amsa suka gaisa tare da Mata bayani Nan dai suka tattauna sannan aka KASHE wayar,"

"Ali ya dubi Suhaila Tace"to kinji yadda mukayi da Umman kano saboda Haka Kiyi Hakuri Suhaila ki amshi Wannan auren Amma har Yanzu kina da dama,Kodai ki yarda ko Kuma ki bijire!"Kiyi tunani akai Wannan ita CE kaddarar KU,"

"Suhaila sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zoben hannunta..."Ta rasa yadda zatayi da kunyar Sadiq da Anty Jalila,"
Chapter 63 · 0% Book details