← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 65

Sashe 21

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alaqata da kawayena su Eshaa,Dejeeh da Deeyart tana Nan daram ba Inda ta canja sai dai aboye nake zaune da su.."Ina zuwa faculty su da dakin su a hostel."Muna zumunci sosai Ni da su saima ayanzun kawancen mu yaqara tasiri azukatan mu."Duk yadda muke mu'amala da su munayi ne aboye saboda Yaya Saddiq ya Sanya Abokina Naseer da saka idanuwansa akan duk wani motsina a makarantar ya sanar Masa."Shima Naseer Tuni ya daukarwa Yaya Saddiq alqawarin Gaya masa gaskiya in dai akan su Eshaa ne saboda ya tsani ya ganni tare da su."A ganinsa lalatacci ne wadanda beraye suka gama wankewa idanu."Bai kamata aganni da su ba!"Musamman ayanzu da zuciyarsa ta Dade da tabbatar Masa da ciwon Sona da ya kamata!"sai dai har yanzu ta kasa furtawa abin sonta saboda labban baki sun ki bayarda wata kafa ta furuci!"Sai dai Tuni idaniya suka nunawa abin sonsu me zucia take nufi!"

"Hakan na cigaba da rayuwata da ciwo da Dadi Ina karatuna tare da taimakon Naseer...."Kuma Ina ganewa sosai."

"Wayar hannunsa ya ke latsawa ga alama lambar da aka rubutawa My man ita ce yake Kira...."tare da karawa a kunnensa.."

"Hello!"A kace adayan BANGAREN."

"Kai kana Ina ne Kai nake jira fah.."

"Oh!sorry man gani a low-cost Mami ta aikeni na karbou Mata sako!"

"To,Ya za'ayi!?"

"Ka jirani Ina zuwa yanxun..."

"Ok!"Sai ka shigo."

"Yawwa"

"Tnx...Ka gaida Mommy

"Zataji.."Yace agajarce tare da katse Kiran.."Zaune yayi Yana duban wayarsa tare da kallon tsintsiyar hannunsa domin Duba agogon da ke daure a hannun nasa Mai kyau da tsadar gaske."

"Bayan mintoci talatin da dakiku sai ga Kiran abokin nasa ya shigo...Iska ya furzar tare da manna bakin gilashinsa a fuska Wanda ke Kara fito da Masa da kyawunsa kamar irin na bakaken fatar Nan ta kasar Sudan."

"Dakin ya rufo tare da Daga wayar yace gani Nan sannan ya kashe tare da fita Daga sashen nasa duka..."A harabar gidan ya Sami Saif tsaye ya hade hannayensa a kirji yana kallon Amininsa da yayi kyau matuka wata Muhammad Jawad Husamaddin."

"Tafawa sukeyi tare da gaisawa sannan suka fad'a a SABUWAR motar Jawad PRASO kalar kasa Mai kyau."

"Tafiya suke suna sauraren M Sharif ta SAREENA."Saif hadda bin wakar cike da sauki."Jawad da ke Driving kallon titin yake..."Yana Dan fira da Saif.."A hankali ta karya kan motarsa a kwanar Tudun wada layin gidan su Baba Balarabe suka."Ba suyi wata Tafiya suka karaso kofar gidan."Tsayawa sukayi kana suka fito.."

"Da Sallama suka karasa Daga ciki.. "

"Innarei ce ta Amsa alokacin da take kwashe tuwon dawa da ta kammala tukawa."

"Tarbarsu tayi alokacin da suke gaidata..."Tabarma ta SHIMFID'A masu tare da kawo masu fura da ruwan leda da Baba BALARABE."yake sayowa agidan ruwa da ke saman tudun layin nasu."

"Bayan Innerie ta ajiye masu daki ta shiga tare da gayawa Mallam gasu Jawad Nan..."Kimtsawa yayi fito da yake ya Dan kishingida NE."

"Innerie ko tuwon ta ta Cigaba da kwashe tana adana komai a mazauninsa..."

"Su Saif Tuni aka bude Sabon babin fira da Mallam Balarabe kamar yadda suka saba."Tun suna kyamkyemi akan abuncin gida har suka daina akan dadi da dandanonan bincin gashi sun yaba da tsaftarsu matuka..."Nan Innerie ta zubo masu tuwon dawar da danyar kubewa Kore Shar da Tasha kayan kamshi da daddawa da busheshshen kifi..."Ay Nan su Saif aka hau kwano ana ci ana Santi,Jawad sai Kora furar Nan Mai Rai da lafiya ta shinkafa kabawan kanta yake."Mai Dadi da gardin gaske Wacce akayiwa damun kyale mouda."

"Suna cin abincin suna yabawa Innerie akan dai abincin yayi Dadi."

"Innerie tayi dariya tace mu da abincin namu miya sallaba CE,Ba Nama aciki ai abincin masu kudi yafi namu Dadi...."

"Ina mama fatyh da yake hakan suke kiranta...Saif ne katseta yaqara da CEwa a gaskiya mama abincin Nan ko gidan shugaban kasa Albarka... Saboda duk Wanda ya ci ba zai fahimci ba Naman dawisu ko jimina aciki...Ai mun dauka da giwa kikayi miyar Nan Mama..."

"Jawad ya amshe zancen...ya ce mama a gaskiya Ni vanma fahimci ba nama aciki bah...Saboda kamshin miyar sai ya nuna nama da kifi ne suka yalwaceta..."

"Baba Dariya yayi kana yace zaku gama santin KU Yan nema masu salo...Ai kuwa 'yahtah Nadiyatou tafi ta iya Miya saboda ta kware sosai agurin girki kunga ko Sabon hannu yafi tsohon hannu...."

"Innerie ta karbe zancen tana dariya ta ce da dadin miyar kake tutiya Kuma da shi aka reni yarta taka...kaima anjuma kadan zaka daura santin naka daga Inda su Jawad suka tsaya..."

"Dariya sukayi cike da jin Dadi dukkan su...Nan a dauko firar Nadiya..."Baba ya shaida masu saura mako biyu na dawo a yadda Saddiq ya sanar Masa da sukayi waya ajiya."Saif yace agaskiya Baba da Nadiya ta dawo hutu sai dai kayi Hakuri zamu saya Mata waya..."

"Jawad yace "Duk da na fahimci baka so Baba Amma ya kamata ka hakura saboda tana fama da kewaemu a sanadin wayar!"

"Ajiyar zuciya Baba ya sauke yace''Abinda yasa bana son Nadiya da waya shine saboda kula da *TARBIYYAR* na Duba nagani rashin Amfanin wayar yafi amfaninta yawa!"Tana batawa yara *TARBIYYA* Haka yara da yawa sukan fad'a wata rayuwa sanadin waya!"Sai kuga yaro Yasan abubuwan da dama Kuma ya iyasu adalilin wayar Nan ta zamani."Shi NE nake Jin tsoron barin Nadiya ta rike waya domin kare mutuncinta da

"Gyaran murya yayi a kausashe!"Ya ce"Baba na tabbata hakan bazata faru ga Nadiya ba!"Saboda nasanta da mutunci da sanin ya kamata!"Bazata taba zubarda kimarta da mutuncinta tare da *TARBIYYAR TA* Ba,A sanadin waya!"Inji Jawad."

"Saif ya CE"Baba gobe zamu sayo waya mu kawo maka,Kaine zaka Bata da hannunka yadda bazata zargi wani Abu ba!"Kuma idan ka Bata da kanka zatabi umurninka da kashedinka akAn duk wani Jan kunne naka!"Da GARGAD'in da zakayi Mata."

"Hakane Baba yace cike da gamsuwa da bayanin su.''

"Innerie Tace Allah yasa MUDACE,Amma agaskiya munyi kewar Nadiya saboda muna mako ba mujita ba!"Sai Idan Saddiq din Yana kusa da ita ne."muke jinta watarana sai dai yace Bata kusa da shi."Amma da ace tanada waya da munjita...."

"Tabbas Mana Fatty,Jawad yace cikin Jin Dadi."

"Saif yace Duk KU kwantar da hankalinku...Mu dai KU tufa Mana asirin mu awurin Nadiya idan ta dawo."

"Babu matsala saifullahi karku damu komai zai zo kamar yadda muka tsara Inji Baba."

"Innerie Tace "yadda ku kazo Mana da manufar ku jawad itace ta sanyamu karfafa muku gwuiwa.."

"Dariya sukayi tare da inkiya da ido cike da kwarewar su ta Zama Yan duniya wayayyi..."Sannan sukace Mu zamu koma Jawad daurin kudi ya fito a aljihunsa ya ajiyewa Baba atabarma..."Yace"Baba ga wannan afara Shirin tarbon Nadiya."

"GODIYA!"su Innerie sukayi ma su tare da rakiyar su har zaure..."Tana Mika sakon gaisuwar ta awurin mommy da Mami."

"Ficewa sukayi Baba da Innerie suka dawo gida cike da murna da godewa yaran."

"Baba Balarabe yace "wallahi Innerie Ina Jin so da kaunar yaran Nan Shiyasa bana iya Koda Girgiza masu..."Musamman Jawad Ina Sonsa har ajinina kamar d'ana gudan jinina!"Shine dalilin son ganin Naga na aura Masa Nadiya da zuciya D'AYA."

"Innerie Tace"Nima dai na yaba halayensu da kirkinsu Allah ya nuna Mana mun saka masu da auren Nadiya ai duk Wanda yaso abinka dole kaima ka so shi...Hakan ta yadda suka bullowa lamarin Nan yasa naji Ina kaunar sa ALLAH dai yasa mudace."

"Ameen..."Mallam Balarabe yace tare da dibar kudin ya baiwa Innerie sauran yace ta ajiye masu da basu san ko nawa bane KAMAR yadda ko Wanda ya basu kudin bai kirgasu ba."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 14*

*Hakika Samun Masoya Babbar Nasara ce, Haka Zaman lafiya Babbar Sa'a ce, Bazaka San meye so bah sai ka samu masu sonka, Ina miqa Gaisuwa tare da jinjina ta musamman gareku MASOYANAAH, Masu kaunar Rubutu na, Tabbas Ina ALFAHARI da ku Bazanyi dana sanin Samun Ku rayuwata ba, Kun min komai bansan da me zan biyaku ba, Fa ce fatan Alheri gareku wa zuriyar ku, Wannan Shafin TUKUICHI ne na baku, Allah yabar Ni da ku Ameen, Ku chigaba da bibiyar littafai na, Ay comment, Share and post, A karshe Taskata abude take domin karbar korafi ko kuma kawo gyara a kundin alqalamina NAGODE😍*

_Nayi mamaki alokacin da nasamu kaina atsakiyar Masoya na,Alokacin da na tafi wani tarou ne,Naga yadda Masoya suka nufoni tare da min rumfah suna nuna farin cikin ganina awurin,Tabbas Abin ya burgeni sai naji Banda kamar ku,A duk Inda na ganku bazan barku bah, Alhamdulillah Alaa kulli yaumn...😊_
______________________________________

"Mansura ce zaune akan kujera da ke falon,ta daura kafa daya kan daya,Daurin Nan na ture kaga tsiya ne kwance akwaryar akanta,Wanda yaji kwalli har ya gaji,Daram yake yayi kyau... "Simple makeup ne Zane a fuskarta ba laifi tayi kyau da yake black beauty sai dai siririn jikinta da rama suka mata cikas..."Chewing gum take tauna kas..kas...kas tana Danna wayarta mayafinta da jikkarta gefe suke ajiye...Dinkinta A shape ne,ya matseta sosai tamkar idan ta motsa rigar zata yage..."

"Karasowa tayi jikinta asanyaye hannunta dauke da Dan ture ruwan pure water ne da lemun fanta sai glass cup..."Ajiyewa tayi akan stool dinda ke wurin tare da matso shi wurin mansura."

"Tace mansura Bismillah ga ruwa ki Sha tare da nuna ruwan da hannunta..."Ta ce,Ashe dai kinsha wuya kafin ki gano gidan..."

"Haba!zancen wuya ay baima taso ba!"A gaskiya Nady baki iya kwatance ba!"Mansura Tace tare da tsiyaya lemun ta Kai bakinta..."

"Nadiya tace"to kinsan nikam ban San gari ba!"Kuma Anty Jalila Bata Nan bare ta kwatanta min...."

"Hmnnnn. Mukam mun Zama kudajin sakkwato domin cike da wajenta ba Inda bamu sani ba!"Inji mansura tana dariya..."

"Nadiya tace"KU Manya ne mansura ba'a gasar ku....."

"Wai Ni Naddy Ina Yaya Saddiq ne,Naga gidAn shiru....Kuma fa akan nasan ranar weekend kowa Yana gida shiyasa na zabeta aranar da zan kawo muku ziyara na gaida Yayanmu..."

"Ayyah!Kinga ko yau gidan Ni kadai ce sunje bikin suna matar abokinsa ta haihu...Nima cewa nayi bazanje saboda karatu Kuma gashi tun jiya kin kirani Zaki zo....."Katseta tayi ta hanyar cewa kin San gidan!?

"Da mamaki Nadiya tace"A'ah bansani ba!"Meyafaru..."

"Murmushi mansura tayi tace''wai da munje na maki rakiya..."
Chapter 21 · 0% Book details