Sashe 44
Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kullum falon Hajiya cike Yake da manyan mata, da matasan unguwa sa'an su Rasheeda sai Fadi banza Fadi wofi,ake Wanda dama al'adarta gidan ne, Gidan Mama Atika ko gidan uwar Daba shine sunan gidan."Tun Bayan rasuwar mijinta ta mayarda gidan dandalin gulmar unguwa."Shiyasa su Jalila ada Zama sukeyi ayi dasu bare Rasheeda da ta kware ta fannin."A gidan ake ci asha har sai an tushe."Ba ruwan Hajiya ita har ma Dadi takeji gidan ya fita daban a unguwa kowa MAAMAH,har wasu banzayen mata,ke dafa abincin mazajen su agidan,Da kayan Aikin abincin suke zuwa tun safe sai yamma,Domin maza na wurin Aiki,Idan sun gama girki su zuba akuloli idan sun Tashi,awuce gida saboda tsabar rashin sanin ciwon Kai."
"A hankali su Jalila suka gane hanya sanadin Islamiyya da suke zuwa Ana FAD'AKAR da su,Shiyasa suka dingA canjawa matan fuska,haka Tahir yace"ya daina ci da matan banza da kudinsa,ya daina ba Hajiya kudin abinci."Ayko Hajiya Ba Dan Taso ba!Itama ta canjawa matan fuska har suka daina shigowa gidan su Jima."Sai dai idan Sunji gulma da zafi!suzo su gayawa Hajiya su fita."
"Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, Jalila tayi nasarar sayarda yan Kayanta masu wuyar ajiya,ta dauko zannan atamfa,takalmi da hijab,tana zuwa da su Islamiyya tana sayarwa,bashi karshen wata abiyata kudinta,"Cikin ikon Allah jarinta yayi Albarka ta ko'ina kudade na fitou Mata,tana lalurorin ta,Sannan tana taimakawa Anty Talatu,da Mahmud da ke imo state wurin service."Nan fa Hajiya aka dawo gefenta ba laifi tana tsakurawa Hajiya,Jalila ta dukufa ga zuwa Islamiyya,,ta mayar da hankakinta ga ibada da rokon Allah tare da tuba,Sauran watan ta daya ta cika iddarta,Ta shirya zuwa ta dauko yaranta mako Mai zuwa saboda yafiye zamansu gidan Umaimah Duk da tana da Tabbas akan zasu samu kulawa Mai kyau Amma ayanzu batada wani buri illah tasa yaranta ajiki,ta kula da Duk wani motsinsu da kula su kamar Yadda malamin su ya ja hankalin su."
"Yanzu dai gidan yayi dama Kasancewar Jalila da Anty Talatu suna da ilimi ga halin kirki da suke samowa a makaranta,Tahir ma ba laifi ya Zama kamili har ya fara neman aure."Hajiya ma ta rage fita saboda ayanzu gidan in Banda cin Dadi ba abinda suke Tahir ya tsaya masu,Asiri ya qara tufowa."Anty Talatu ma Tahir yayi Mata alqawarin kudin da zata ja jari albashin watan Nan idan anyi,tayi murna sosai, ta gama shiryar kalar sana'ar da zatayi,"Rasheeda Kam tun Ranar da tayi wani munafunci akazo har cikin makaranta agaban dalibanta akai Mata dukan kawo wuqa,Tun Ranar ta sanyawa bakinta D'an mukulli ta rage gulma sai dai can ba'a rasa ba,tazamo Jinin jiki."
*****************
"Na shiga Islamiyya,Lafiya qlaw mukayi karatu har aka Tashi,Daman tun agida na kaiwa Saudat nata kayan,na yan ajin mu Kuma da Mallaman mu Duk na damka mata,Ana Tashi ta rabawa kowa,Naso ace yau Badi'atu tana ajin abata,sai dai Bata zo ba,kawarta munira, Saudat taba Tace ta ajiye Mata,murna da Allah Sanya Alheri yan ajinmu sukayi min tare da godiya."nima Godiya nayi musu.
Muna fita saudat ta wuceni taje ta Sami Mallam Bilya da yunus tabasu tare masu bayani,har da iyayi,Daman tayi da biyu,Ay ko nan malam yunus ya hade Rai!"Ko meye dalili oho!"Mallam Bilya Allah Sanya Alheri yayi mana,har inda nake tsaye nesa da su, yazo Yana min murna godiya nayi Masa muka wuce ajin Dalibai na muka raba masu alewa,sai murna suke suna cewa malama Nadiya AMARYA."Saudat Dadi kamar ya kasheta saboda yau dai mun Rama abinda Malam yunus yayi Mana agaban Badi'atu."
"Tunda muka fito ajin idon Mallam yunus akan mu yake, Yana nan INDA muka barshi dazu ko dagau,Shi Mallam Bilya ya wuce abinsa."Ko kallon shi bamu yiba nida Saudat muka wuce,Muna kokarin fita get din sai gashi gaban mu yace''Nadiya Ina son magana da ke!"
"Shiru nayi bance komai ba ita Kuma Saudat kokarin bamu Wuri take."
"Yace Saudat ki tsaya agabanki Zanyi magana,Nadiya bazan boye maki ba!Wannan Rana da Naga baikon ki,bazan manta da ita ba a tarihin ranakun bakinciki na!"Kiyi Hakuri nayi miki hukunci ba tare da hakkinki ba!sai yanzu nasan cewa nayi sakacin barinki!"Wallahi Nadiya Ina sonki Kuma Banga wacce zanso kamarki ba!Ko da kika tafi makaranta kin barni da ciwon sonki,Ina kokarin da kin dawo na fada maki."Sai Gashi wasu matasa sun sameni sun gayamin cewa samarinki NE,Ba abinda Basu Gaya min game da ke ba na b'atanci!"Da Duk halayenki da Kika sauya a Dalilin zuwanki makaranta."Ni Kuma bacin rai da Kashin ki ya tunzurani har naji haushinki,Ina maki kallon Mai kirki Ashe kin samu kawayen banza kinyi watsi da tarbiyyar ki,da duk nasiha da jawabin da nayi maki,haka tasa naji na tsaneki! Bana sonki! harna huce haushi akan BADI'ATU Ido rufe na amshi tayin soyayyarta."Sai Bayan komai ya faru,kinzo hutu kin koma,A Yan kwanakin nan nayi tunanin ban Miki Adalci ba!"Saboda Banda Tabbas akan abinda akazo min da shi akanki!daga lokacin na shiga damuwa"Saudat kuyi min uzuri Amma na Yadda da kaddara."niKam nasan nayi asarar mace wacce zata iya Gina rayuwar yarana da gaskiya,yanzu shi kenan na rasaki a lokacin da nake kokarin gyara kuskurena! malam ya idar da zancen yana Hawaye!"
"Ni Kaina kukan nakeyi Kai duniya!su Kuma su waye!?me na tare masu!?"sune tambayoyin da nake ma Kaina Azuciyata har suka bayyana,
"Mallam yunusa yace da rawar murya,Nima ban sansu ba!"saboda Bayan isha NE suka zo wurina!"Amma samari NE su biyu Kuma acikin shigar banza na gansu Shiyasa abin ya bani takaichi, ace samarinki NE!,
"Saudat ta Share hawayenta tare da rika hannuna Tace"Mallam ka yadda da Wannan itace kaddarar rabuwarku Domin ta Zama sila!Amma Sam ba halin Nadiya bane!"Duk wanda yayi mata Wannan sharrin Allah ya isar Mata!Sunyi NE domin su b'ata mata suna ,Kuma su shiga tsakanin ka da ita sai gashi Sunyi Nasara, in Sha Allah zasu Gani ko ma su waye da yardar Allah.
Saboda Duk karya NE sukeyi babu gaskiya acikin zantukan su,Nadiya batada samari hasalima Bata kula kowa,mallam kamar ka manta Wacece ita!? Da halayenta da Kuma dabiunta ,Numfashi Saudat ta sauke da Tace mu zamu wuce Allah yasa MUDACE,sai da safe."
"Dan Allah Nadiya kiyi Hakuri Ina maki fatan Alheri,mallam yunus yace fuskarsa dauke da dinbim nadama Mai dauke da damuwa!"
"Bakomai mallam Nagode Nace da shi,muka wuce Yana kallon mu har muka bace Masa!"Jiki a sanyaye ya nufi hanyar gida yana tunanin abubuwa da dama!"Mallam yunus kenan."
"A hanya Raina ba Dadi Nace Saudat me nayiwa mutane da suka tsaneni!mutane sun sakani gaba,mutane sun hanani sukuni nikam dai kaddarar rayuwa ta da mutane acikinta Wai me nayi masu ne?"
"Saudat su waye?sukai min Wannan aikin!?Me na tare masu!?Meyasa ZASUYI min kazafi!?"Sun cutar da Ni sun Bata min suna a INDA ake ganin mutuncina da cikar kirki na,Yanzu fa su Mallam Bilya kilan ma da wasu malamai na sun san da Wannan maganar!?"Kuka ne ya ci karfina!?'nayi shiru Ina gunjin bakin ciki!"
"Dafani saudat tayi tace"kiyi Hakuri! Nadiya a hanya muke bai kamata kina Tafiya kina Kuka ba! Duk Wanda yayi Miki sharri Allah ya saka maki, Domin shi sharri Dan aikene wataran zai dawowa Mai shi. Gashi anyi walkiya gari ya haska,Allah ya wankeki!"Yazo ya sanar maki abinda baki san da shi ba!"Kuma Duk Wanda yaji Wannan maganar Yasan ba halinki bane,ko shi malam zafin so da kishinki yasa ya yarda Amma Allah Yana nan...Saudat ta ida zancen cikin sigar rarrashi da tausayin kanwarta!"
"Ajiyar zuciya,nayi tare da goge hawayena Nace bakomai ko su waye Allah zai saka min Saudat!"
"Hakane,ki Cigaba da Addu'a Nima Zan tayaki Allah yayi Mana mafita ta Alheri,kowa baya wuce jarrabawarsa a rayuwa,Kinga Nima rashin mijin Nan da banida shi Yana damuna Nadiyatu,kullum sai abokiyar zaman mamana! tayiwa maman mu fade! Wai anje boko an dawo Babu Miji,ba kalar kazafin da batayi min,Wallahi Nadiya da Ana sayarda Miji a kasuwanni da mamana Lantana ta zuba dukiyarta ko nawa ne ta saya min ko Domin gorin Yan gidan mu."Inji Saudat tana zubda Hawaye!,
"Na dubeta da tausayi Nace"Allah yasa MUDACE kiyi Hakuri komai Yana da lokaci da karshe! mutane NE suka jahilci hakan,Amma Idan Allah yace ka zamou ai ko Ana mazuru Ana shaho sai ka zamou."Da aure da haihuwa da mutuwa duk hukuncin Allah ne.
"Kwarai da gaske to su mutane basuda gadonka Amma suna da na zancenka Allah ya iya Mana kedai Nadiya."
"Ameen,Dai-dai Nan muka karaso kofar gidan mu, Sallama nayiwa Saudat tare da Bata SAK'ON gaisuwa ta zuwa ga mama lantana,hakan Itama Tace na gaida Mata da Innata,Tare da shaida min zata shigo da yamma,mu rabawa yam matan layinmu alawa,To nace da ita tare da godiya, Sannan na shiga gida, ita kuma saudat ta karasa gidan su, Daga gaba kadan domin makotanmu NE."
*********** "Mansura Anci kwalliya taji ta Gani ta fad'a acikin wani Swiss less kalar omo da Baki,dinkin A sharp ne,yayi kyau sosai takalmi da jika,ta saka tare da mayafi,A hankali take Tafiya har ta isa inda motar Saddiq take,Jikinta tamkar anyi barin turare,"
"Da Sallama ta karasa bakin motar Wanda tun Daga nesa yake kallonta ta glass,ta burgeshi sosai."Bata Kara gamawa da shi ba sai da ta karaso wurinsa yaji kamshinta."
"Lumshe Ido yayi da kyar ya Amsa Mata sallamar Yana murmushi,shima dai ba laifi yayi kyau sosai acikin gizna kalar kasa."
"Bayan sun gaisa motar ta shiga,ya tada injin mota suka Kama hanya,A wata plaza suka tsaya ta sayi kayan kwalam suka fito suka wuce."
"Bayan mintoci suka Isa sama road,inda gidan Ali yake,A Layi na uku suka tsaya gaban wani gida Mai kyau da tsari suka tsaya da Yake unguwar ba laifi ta masu shi CE,"Horn yayi Nan take Mai gadin gidan ya bude tare da dagawa Saddiq hannu,Kan motarsa ya kunno acikin gidan parking place ya nufa ya ajiye motarsa,kana suka fito, mansura sai rabon Ido ake Ana kallon gidan,Bata Kara tsinkewa ba,sai da suka shiga gidan, Saddiq Yana gaba tana binsa, har da canja Tafiya Ana wani kaudi da iyayi,"Falon suka shiga,da fara'ah Ali ya tarbe su tare da ba mansura wurin Zama Yana zolayarta."
"Mansura Kam tayi nisa duniyar tunani Domin Wannan gidan shine irin gidan da takewa kanta mafarki,Wai aljannar duniya..."kalaman Ali suka dawo da ita hayyacinta inda Yake cewa shin ko amaryar kurma CE!?"
"Murmushi Mansura tayi Tace"Hmnnnn...Da Ni kurma CE da bakuce Kuna so ba!"