← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 65

Sashe 22

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yake Nadiya tayi tare da kallon mansura, tace''nikam bazanje ba!"yanzun ko da nasan gidan,saboda tun farko ya kamata naje tare da su,Kinga nifa Ina da abin yi karatu NE nasa agaba!..."A zuciyarta ta k'osa mansura ta fice saboda Lokacin dawowar su yayan ya kusa."

"Mansura ta katse Mata tunani ta hanyar dafata tana cewa"Nadiya Ina damuwa azuciyata sai dai ban san ko da wace fuska Zaki dubeta ba!"Amma Ina son ki min uzuri...."Sannan ki taimake Ni!"

"Dubanta nayi cikin yanayin rashin fahimta nace"Na taimake ki!Kuma mansura!?"Ni Ina da abinda zan iya taimaka maki ne!?"

"Kina da shi Nadiya...!"Ay taimakon iri iri ne qawata..."Mansura Tace

"To Ina jinki....sai ki fad'a min naji...."

"Yawwa...Naddy...Daman tun ranar da na daura idona mukayi ido HUD'U da yayanki Saddiq!"Sai naji duk duniya ba Wanda nakeso kamar shi..."Nasha kiransa Ina gaida shi...Ina Nina Masa afakaice..Sai dai Banda wulakanci ba abinda yake biyo baya...Nayi iya kokarina Naddy domin Abbakar ya fahimce Ni Amma Sam yaki ya kulani..."A ranar da kaddara ta farmin nakira shi na gaya Masa....Tatas yayi min na Sanya lambata ablack list!!!"Naje makarantar ku office dinsa ya korou Ni yanzu gani Gidansa Shakka bana yi ko yanzu ya sameni zai koreni....."Ajiyar zuciya tayi tare da Kama hannayen Nadiya ta rike gam, da wacce Tuni tayi mutuwar zaune ba abinda take sai kallon mansura..."

"Wannan dalili ne yasa nazo domin ki taimake Ni ko Dan uwanki zai so ni!"Duk abubuwan da suka faru Abaya na boye maki ne domin Naga ke kina tsoronsa na dauka zan iya saye zuciyarsa da kalamai da Kuma irin salon nawa kissar...."Amma yanzu tura ta Kai bango"Saboda na kasa...."

"Sanyin Hawayen mansura NE suka digo min a hannu Wanda yayi sanadin Dawowata hayyacina...Tabbas yau na shaida mansura tafi karfina kuma ta wuce sanina...."

"Da kyar na motsa bakina da ya hade gum....Nace nikam Wannan al'amarin yafi karfina mansura saboda bazan iya tunkarar Yaya Saddiq da Wannan zancen ba!"Kiyi Hakuri kawaai...."

"DakAta Nadiya karki sa Nayi Dana sanin tunkarar ki a mutum ta FARKO kamar ya!Nayi Hakuri ya kamata ki gane shi so kaddara CE Kuma baisan Hakuri Wallahi!Bazan hakura da Saddiq Dina ba!"Sai Inda karfina da iyawata ya kare...."

"A firgice na kalleta tare da zame hannuwa na daga natan nace Mansura Tabbas giyar so ta bugar da ke!kinsan me kike fad'a kuwa!?"To Bari kiji Yaya Saddiq ba Yayana bane na jini Dan gidan abokin Babana ne..."Kin ga bazan taba shige Masa domin alaqarmu Bata Kai ga Nayi Masa shishshigi arayuwa ba!"

"Hmñnnnn....Bari yayi Kama da mutum Naddy kice akwai aure atsakanin KU watakila kema Sonsa kike!"

"So Kuma Mansura!?"

"Eh!Mana idan ba Sonsa kike ba ko Kuna tare me zai Hana ki taimakeni....Shiyasa ma Kika tare agidansa...yanzu na fahimce ki."

"Da mamakin na kalleta nace ka da ki min sharri Ni Babu abinda ke tsakanina da shi fa CE zumunci...Tayaya zan daurawa Kaina dala ba ganwo...Ay ruwa ba sa'an kwandou bane!"Na tsaya a Inda Allah ya ajiyeni bana kankamba bare shiga hurumin da ba nawa ba!"

"Ni Kuma kin ganni Nan Naddy Ina shiga hurumin da ba nawa ba!"Kuma Ina kokarin har ya zama mallakina...kedai ki zuba ido ki gani!"Domin duk abinda nasa agabana sai na same shi....

"Tuni idona sukayi jajur cike da kunar rai!"Ina Allah wadai da mutane irin su mansura da basa son azauna lafiya...."Kayanta ta dauka Tace Ni zan tafi Naddy NAGODE..."

"Komai bance da ita ba!"Kuma ban motsa ba!"Jin tsayuwar motarsu Yaya Saddiq ne yasa naji wani fargaba!Kenan sun dawo na shiga uku na!!!"

"Mansura ko murmushi tayi Tace madallah turare ta dauko Jakarta ta fesa tare da gyara fuskarta..."Glass dinta ta manna afuska mayafinta ta rike a hannu tare da turo kallabinta gaba...Ta kalle Ni muje ki rakani kada ki mayarda agogo Bayan hannu...kinsan yaba kyauta TUKUICHI...Haka bako rahama ne..."

"Jikina ba kwari na tashi nabi bayanta Tafiya take kamar zata karye...Azuciya ta na k'osa ta tafi....Dai dai kofar falo Mika ci karou da Anty Jalila da yaran sun bode kofa!!!"Ledoji a hannunsa..."Wani Kallo tayi ma mansura..hakan mansura ta mayar Mata da martani..."Kallona tayi cike da tuhuma yayinda nake Mata sannu da zuwa..."

"Nan da Bata CE Mana komai ba ta wuce mu Kuma muka fita...Yaya Saddiq muka samu Yana kokarin rufe motarsa...Da hanzari na gaida shi.."

"Hakan mansura cike da yanga da kwarkwasa ta gaida shi..."

"Ko kallonta baiyi ba!"ya CE Nadiya Wannan fa!?"Daga Ina!?"Ina Kuma Zaki tafi Bayan ke kadai CE agidan...."

"Cike da razana nace Yaya,"Mansura CE,Daman anan zan ajiyeta ba ko Ina zamu tafi ba!"

"Ok,shige gida mu tafi..."Da sauri na koma gidan..."kallonta yayi yace Kar nakara ganin kafarki agidana!"Bana son iskanci!"

"Mansura Tace"Have Yaya Saddiq meye illar so!?"Kodai tare da Nadiya kake!?"Saboda Naga kwaryar sonta a mazaunin idonka!"

"Mari ya watsa mata...Sannan ya Kira Mai gadi cike da fushi yace ka dubeta da kyau...Kar na Kara ganinta gidan Nan ka fita da ita waje!!!"Sannan ya shige gida!"

"Angama yallabi mudi Mai gadi yace"tare da CE ma Mansura to Malama kina iya fita ko!?"

"Anki afita Kai acikin kayan Miya wa kake!?"Dan Abi yarima asha kid'a kawai...."

"Mudi maigadi ya zarou ido da Yake ko shi kansa matashin kauye ne...yace ke Ni zakima rashin kunya to kinzo gidan kisani tun a 1960 nike rashin mutunci akauyen mu har yanxu ba'a haifo kamata ba!"Wallahi ko ki fita da kafar ki ko na tallabeki Nayi waje da ke ko wajenma ajuji zan jefar da ke!"Kinganki ba nama ne da ke ba!"kamar an fige figaggiyar kaza Mai Dan hoda..."
"Mansura ta saduda Dan taga sai fama gyara rigarsa yake da wondo zai kinkimeta!"At da gudu rabar get din gidan Takalmi da mayafi ahannu.. "

"Dariya yayi yace da kitsaya kiga aiki da cikawa ayke karamar Yar iskace kina acikin Dalibai na yarinya..."komawa yayi kan aikinsa Yana Waka Yana Shan rake..."

"Nadiya Ina Kika samo Wannan yarinyar!?"Inji Anty Jalila

"Wallahi Anty Daga shiga mota ne da zAnzo shine ta laqabe min..."

"Mtwsssss...to ki kiyaye saboda bana son kwashe kwashen kawayen banza agidana...!"

"To,Anty in shaa Allah zan kiyaye..."

"Mufeeda KU kawowa Antynku kayan bukin ma kun wani zauna kunaci KU kadai..."

"Dawowar Yaya Saddiq afalon ne yasa naji..dif Ina jiran yace wani Abu sai dai baiko nuna damuwa...ba"Da yake ko da ya shigo Ina Kichen Duba girkin da nakeyi..."Shiyasa bangan shi ba sai da shiga bedrum ya fito yanzu."

"Kayan bukin nakeci ahankali duk na tsorata... Yaran ko sai fira suke min Sam hankalina baya kansu...tunanin ta'asar da mansura ke son yi nikeyi da Kuma hukuncin Yaya Saddiq gareni...

"Mansura da sassarfa ta karasa bakin titin estate din..."Lalle yau ta hadou da gamonta!!"Sai haki take saboda gudun da tayi alokacin da mudi ya biyota!"Napep tasamu Dan fodio Tace ya kaita!"Sai alokacin tasamu sarari ahankali wulaqancin Saddiq ya dawo Mata Hawaye ke zuba afuskarta!!"Lalle Dole ta dauki mataki akan Saddiq da kawarta Nadiya!"Wacce ta fahimci suna kaunar JUNA atsakanin su!!!"

"Da misalin karfe 7:30am na safe na shirya tsaf nida yaran Tuni na kammala abincin Karin mu Dana yaran."Mun zauna munci mun koshi su Yaya Saddiq harda kari.."Nan da muja kammala muka fita domin zuwa makaranta..."Ita Kam Anty Jalila tana can tana sharar baccinta batasan ma me ake ba!"Da yake yanzu Yaya Saddiq yama daina tashinta da zarar mun shirya wucewa muke sai dai ya kulle gidan ta waje idan ta tashi ta bude ta ciki..."Hakan ya fiye Mata komai Dadi arayuwa domin itakam tafi so kullum yazan tana hutawa..."

"Bayan an sauke yaran...Titin makarantar mu Yaya Saddiq ya hau ta gudunsa..."kallona yayi kana ya kauda kai..Nikuma kamar munafuka..sai sadda Kai nake saboda nasan fassarar kallon sa..."

"Nadiya..ya Kira sunana."

"Na'am Yaya na Amsa

"Ina son naja maki kunne Kar naqara ganin Wannan Kawar Taki agidana...tunda Nayi kokarin rabaki da Yan iskan makaranta!"Yanzu Kuma kin samu wata banzar!!!"

"Cike da bugun zuciya nace Yaya Dan Allah Kai Hakuri hakan bazata koma faruwa ba!"

"Daga yanzu na daina tilasta ki Kiyi abinda ranki keso Nadiya tunda Ni ba jininki bane ban Isa da ke ba!"

"Kukan da nake hadiyewane ya balle min...nace ka isa da Ni Yaya na dauke tamkar Yayana najini kayi Hakuri na daina Daman ta dameni da tazo mu gaisa ne,Shiyasa Nayi Mata kwatance tazo Amma Wallahi bazan Kulata Yaya!"

"Kallona yayi akarou na biyu Sannan ya CE "Shi Kenan...share hawayenki ya wuce!"

"NAGODE nace muryata adisashe idona sun kumbura ga kukan da Nayi ga Kuma kumburar rashin baccin da bansamu ba adaren jiya saboda karatun jarrabawar da zamu fara yau."

"Faculty dinmu ya ajiye Ni tare da yimin Addu'oin Samun nasarar jarrabawar."

"GODIYA Nayi Masa ya wuce..."Ni Kuma Inda muke Zama da Naseer na nufa kafin lokaci yayi..."Sai dai su Esha, Deejart da Deeja nasamu zaune suna jiran karasowata..."Da murna na fad'a kansu cike da kewar juna..."

*Toufaah wasa farin girki Inji"YAR MUTAN DIKKAWA*
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 15*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

_Kui min uzuri fans Ina ganin sakonku,A whtap,Text mssg da Kuma masu Kirana,Ina godia, sai dai tun farko na Gaya maku Ina busy a watan nan, Ina iya kokarina domin ganin na maku post akan lokaci,Daga SHAFI na 12,13,zuwa 14 har zuwa na gaban duk nt Edit ne sai kunyi hakura da MESONKU😍_
______________________________________
"Rana akace Bata bar komai ba!"Yau dai Allah yayi na kammala dukkan jarrabawar mu lafiya..."Na k'osa na koma gida Duk da yamma tayi Amma Ina ji ajikina kamar bazan Kara ko AWA daya agarin sakkwato..."Ban kwana mukeyi da Yan department din mu."Su Esha ma fatan Alheri mukayi musaya da su."Naseer abokina kamar ka da mu rabu saboda munyi sabou da JUNA..."Sai da Nayi Hawayen rabuwa da kawayena da Kuma Abokin karatuna!!!"

"Hakan dai kowa ya watse da Yake akwai wadanda basu kammala ba!"Suma sai jibi zasu wuce gida.. "Na amshi lambobin su Deeja da zummar zan dinga kiransu da wayar Baba."

"A hanya ne Yaya Saddiq ke Gaya min sai gobe zamu tafi *ARGUNGU* saboda Shima ya kwana biyu baije duban su Baba Musa."Tare zamu tafi Zaije har ma da yaran, da Yake sunyi hutu.. saboda Daman ita Anty Jalila ba zuwa take ba."

"Sai da yanayin fuskata ya canja da naji maganar kamar saukar guduma akahon zuciyata!!"domin na k'osa banje Naga Innata da Babana ba.."Da Kuma malamina Yunus."
Chapter 22 · 0% Book details