← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 65

Sashe 16

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hakane Baba yace cike da gamsuwa da bayanin su.''

"Innerie Tace Allah yasa MUDACE,Amma gaskiya munyi kewar Nadiya saboda yau kusan mako daya ba mujita ba!"Sai Idan Saddiq din Yana kusa da ita ne."muke jinta watarana sai dai yace Bata kusa da shi."Amma da ace tanada waya da munjita...."

"Tabbas Mana Fatty,Jawad yace cikin Jin Dadi."Abisa karfafa masu gwuiwa da tayi,"

"Saif yace ku kwantar da hankalinku Baba da mama. ba abinda zai faru...Mudai ku tufa Mana asirin mu awurin Nadiya idan ta dawo."

"Babu matsala saifullahi karku damu komai zai zo kamar yadda muka tsara Inji Baba."

"Innerie Tace "yadda kukazo Mana da manufar ku jawad itace ta sanyamu karfafa muku gwuiwa.."Domin Hakan shine Dai-dai."

"Dariya sukayi tare da inkiya da ido cike da kwarewa ta wayayyi..."Sannan sukace Mu zamu koma,Bayan sun wanke hannunsu, Jawad daurin kudi ya fito a aljihunsa ya ajiyewa Baba atabarma..."Yace"Baba ga wannan afara Shirin tarbon Nadiya."

"GODIYA!"su Innerie sukayi ma su tare da rakiyar su har zaure..."Tana Mika sakon gaisuwar ta awurin mommy da Mami."

"Ficewa sukayi Baba da Innerie suka dawo gida cike da murna da godewa yaran."Su Jawad ko suna fad'awa mota suka dinga murna...turare suka feshe jikinsu da shi,tare da jefa sweet Mai kamshi a bakinsu,Domin Kamshin daddawar ya fita jikinsu Sannan suka Kama hanya,"

"Baba Balarabe yace "wallahi Innerie Ina Jin so da kaunar yaran Nan Shiyasa bana iya Koda Girgiza masu..."Musamman Jawad Ina Sonsa har zuciya kamar d'ana gudan jinina!"Shine dalilin da yasa nakeson ganin na aura Masa Nadiya da zuciya D'AYA."Kudinsu basa rudani illa halin su na kirki na burgeni..."

"Innerie Tace"Nima dai na yaba halayensu da kirkinsu Allah ya nuna Mana mun saka masu da auren Nadiya ai duk Wanda yaso abinka dole kaima ka so shi, Musamman ta yadda suka bullowa lamarin Nan yasa naji Ina kaunar sa ALLAH dai yasa mudace."

"Ameen..."Mallam Balarabe yace tare da dibar kudin ya baiwa Innerie sauran yace ta ajiye masu da basu san ko nawa bane KAMAR yadda ko Wanda ya basu kudin bai kirgasu ba."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍*
🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA TARA*

_SADAUKARWA GA AMAREN 👰🏻DECEMBER🌙,DA KUMA NA SABUWAR SHEKARA📆 INA MAKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YASA AYI LAFIYA A WATSE TAROU LAFIYA_

_SANARWA!SANARWA!!SANARWA!!!IINA MASOYAN OFFICIAL NABEELA DIKKO,INA MAKARANTA NOVELS DINA...DUK INA GAYYATAR 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI DA KUMA MASOYANA ZUWA AUREN KANWATA TA KAINA ❤ PRINCESS YASEERA DIKKO👰🏻 WANDA ZA'AYI ON 28/DEC/2019 ,BAN DAUKEWA KOWA BA NA NESA DA NA KUSA AZO LAFIYA ALLAH YA KAI MANA RAI AMEEN._😍
______________________________________

"Tun ranar Yaya Saddiq Bai Kara min zancen komawata Hostel da Zama ba."Har nayi sati daya agidansa." domin na kula yaya Yana Jin dadin ganina agidan.Shakka babu Tabbas an samu canji agidan mussaman agefen girki,ina yiwa yaran abincin safe kullum suje da shi makaranta, kuma duk kalar Wanda su keso shi nake girka masu."Sannan idan na dawo da Wuri Ina daura sanwar dare,Ina tuwon semo,shinkafa da miyar taushe da kubewa."mufeed da Mufeeda Kuma yanzu suna jin dadi sosai sun sake da Ni kwarai, sun daina hayaniya,suna sallah yanzun,Kuma sun iya gaida Mutane idan sun gan su, har iyayen nasu yanzu suna gaidawa,Yanzu kowa agidan ya fahimci yaran sun samu canjin RAYUWA kuma Ina kokarin koyar da su karatun Islamiyya da na boko."Yaya Saddiq Yana jin dadin yadda nake kulawa da taimakon yaran, aransa sai fatan Alheri yake min,Yana son zamana gidan sosai Domin farin cikinsu ya karou ta kowanne fanni,Gashi Yana sakewa da Ni sosai tamkar kanwarsa ta jini,komai mukeso Ni da yaran Yana saya Mana,Haka kullum suke ganin kamar kada na tafi saboda canjin da akasamu agidaan Kuma kowa na nuna min kulawa cikin Yan kwanaki Anty Jalila ta sake min komai na gidan."

" Anty Jalila sai dadi take ji aranta tasamu ma'aikaciya agida,Iyakacin tayi bacci,ko Kuma Kallo sai ta wanke goma ta tsoma biyar"KOMAI ni nakeyi agidan idan dai banje makaranta ba da Wuri ba,ko Kuma kafin na tafi tun Wuri sai na kammala aikin duka Sannan na wuce saboda wataran da karfe goman safe ko Rana ko Kuma karfe hudu na yamma nake fita."Daga Baya ne kawarta Subbyh ta shiga atsakanin mu,saboda ta zugaa Anty Jalila,akan na bar gidan kada na aure Mata miji."Duk da Ina Mata biyayya Ina kula da yaranta,Bai hanata daukar shawarar aminiyarta ba,saboda tana da tsananin kishi!"Akan Yaya komai zata iya aikatawa."Hakan akayi domin kuwa Anty Jalila ta takewa Yaya Saddiq burki dole saina bar gidan na koma Inda yace Mata tun farko Zan zauna!"Ba domin sun so ba shi da su Mufeeda."Yace na tattara kayana zan koma makaranta, ya Kara min sayayya na koma hostel da kwana.."Sai dai kullum mu kanje ofishinsa Ni da Abokina Naseer mu gaida shi."Wataran ya bamu kudin abinci Wataran Kuma bama samu saboda yau da gobe sai lillahi."

"Na kwantar da hankalina sosai Ina karatuna yadda ya kamata Kuma Ina ganewa sosai."Dan kuwa muna group discussion da Naseer da abokinsana Deeni."

"A hakan na Cigaba da tafiyar da rayuwata akwalejin shehu shagari.."Sai dai Banyi sa'ar abokan kwana ba, wato Yan Dakin mu da yake mu hudu NE adaki daya."Hali na ya babbanta da nasu."Hakan Rayuwata ta fita daban acikin tasu."

"Su uku ne Esha Hayat wato (Aisha Hayatu)sai Kuma Deejah Yak(Khadija Yakubu) sannan Deeyarh Bas(Badiya Basiru) sai Ni Nadiya BB da yake ko Nan ma hakan suke Kirana wato Nadiya Balarabe Bello."

"Kullum Yan Dakin mu ganina suke ban waye ba!"Sune suka waye suka San duniya da Abin da duniya take ciki."Saboda kawai bana shigar banza irin tasu Kuma bana watsewa da maza kamar yadda sukeyi."Sam basuda kamun Kai da yake na lura mafi yawa hakan yam matan suke na kwarai kamun Kai"Kalilan ne acikinsu abin mamaki har matan auren ba'a barsu Abaya ba!"Shiyasa na Kara yarda da kuma gasgata Maganar Mallam yunus Dina,Da ya CE"Jami'a gidan kowa da kowa ne."Nako gani saboda akwai shege akwai Dan banza Sannan akwai nagari aciki,kowacce kalar rayuwa akwai Kuma ko da me kazo amfika."Na tabbata hakan."

"Ina ganin SU Esha Kullum cikin Kudi suke da sayen sutura masu kyau da tsada,Har gasar wanka da saka manyan Kaya masu tsada suke." ga su duk sun San manyan mutane da malammai suna shiri da su sosai,da duk wani Mai fad'a aji acikin makarantar." Iyakacin su,Fashion da budawa amakarantar ga yan jaan wanka cikin fita ta rashin mutunci,su fita yawon su,sucii mai kyau su Sha Mai kyau,Ina ji Ina gani nazama doluwa Yar Kallo acikinsu." ko sun ce min in zo ci abinsu banaci Kuma bana nuna bukatar komai Daga garesu."Ba yadda basuyi ba domin su ga na shiga acikin harkar tasu Ayta sha'ani tare,Amma naki!"Sun nuna min sutura saboda sun fahimci banida ita da yawa Mai kyau."sun nuna min kud'i sun bani abubuwan kwadayin duniya duk nayi banza da duk abinda suka bani."Nace da su nagode banaso Domin nafison abinda nasamu ta dalilin iyayena!!"Hakan Na Cigaba da karatun da ya kawoni makaranta." saboda su na gane basu damu da karatu ba Kuma basu da niyyar yinsa." sharholiyar su kawai suke ta duniya."A kullum fatan shiriya nake masu."Su kuma suna min kallon lusara Wacce batasan komai ba bagidajiya Yar kauye."

"Saifullahi Aminin Jawad ne sosai Kuma Abokin shawarar sa."Sun shaku da JUNA sosai sai dai shi Saif yafi Jawad dama Amma dai dukkan su Maras *TARBIYYA* ne."Sun taso acikin so da kauna, ga gata da ake basu." Saifullahi shine karami agidansu,Saboda duk yayyensa Mata ne su biyar shi kadai ne namiji Kuma auta agidansu,saboda iyayensa manyan Mutane ne,Kuma yayyansa suna auren mazaje masu kudi.shiyasa ta ko ina,yake damawa da kudade son ransa Dan gata ne Dan auta Kuma autalele Sha leleh awurin iyayen sa da yayyensa ."

"Yanzu kimanin sati biyu da zuwan su wurin Mallam Balarabe wato mahaifin Nadiya Tabbas sun Sami karbuwa kwarai da gaske agurin Baban nata Haka kawai yaji jininsa ya hadou da Jawad kaunarsu na ratsa jini da jijiyarsa,Duk ya kula yaron sai ahankali Amma dai ya karbe su hannu biyu kuma ya gamsu da kudurinsu."Aykuwa sunji Dadi sosai sai dai sun fahimci Baban bayada kwadiyin Abin duniya."saboda sun nuna masa kudade yaki ya karba."

"Shiyasa suka canja dabara ta hanyar Sayayyar kayan masarufi sukayi yau,Saboda sun Kwana biyu basuje gaida shi ba!"Kuma wannan Yana Daga cikin shirinsu...Shiryawa sukayi tsaf acikin jallabiyoyi da huluna farare tas sunyi kyau kamar larabawan Sudan da yake dukkan baqaqe ne masu Dan haske."Da misalin karfe hudu na yamma hanyar tudun wada suka nufa kamar yadda suka Saba, Bayan duk kwanaki uku sukanje da sunan kawo gaisuwa ta mussamman agurin mahaifin Nadiya ko Yanzu hakan CE ta kasance."

"Tun Malam Balarabe na sanyi sanyi da su har ya sake masu saboda ya lura yaran na da kirki,Kuma sanin girman na gaba ne yasa suke girmama shi Kuma suka dauke shi da muhimmanci tun Baya amsar abubuwan da suke kawo masu har ya fara amsa har cikin gidan suke shiga su gaida mama fad'imatou(Inneirei) suyi fira sosai da zancen kewar Nadiyar Haka sukeyi har aka Saba da JUNA."Kamar kullum yau ma zaune suke rashe rashe agidan Bayan an kammala shigo da kayan da suka kawowa su Mallam Balarabe." Sannan suka cigaba da firar su daga bisani suka fito."Mama Da Baba sai albarka suke saka masu da dimbin GODIYA."

"Dariya sukayi alokacin da suka fad'a Mota,suna tafawa Jawad yace"Wallahi da farko sai Naga kamar bazan iya ba!"Saif

"Hakuri ne bakada shi Jawad Shiyasa.. Saif yace Yana Dariya."

"Yanzu nafara koyon ahakurin adalilin daukar fansa!"

"To Jawad yanzu dai kaga Shirin mu Yana tafiya dai-dai."

"Haka NE faa...Wai kasan da kyaar na tsara momy ta daina zancen zuwa ganin mutumen Nan.."Sai da nagaya Mata yaji sauki munje dubashi Baya gari yayi tafiya kauyen su..sannan NE fa ta hakura Tace sai yadawo ta tafi."Nace Mata to da kanmu zamu kaita har gidan."

"Kace munyi arziki da mummy ta Batamana shiri,Inji Saif."

"Wallahi kuwa narasa Ko Meyasa mom ta damu da taje, ai idan ta dage sai taje sai ta wargaza Mana shiri."Jawad yace."

"Tafiya suke suna Hira da shewa,Saboda a yadda suka kaga Shirin nasu na tafiya kamar yadda suka tsara."Daa kamar wuya Nadiya ta kubuta Daga tarkonsu."Sai dai ta zama Abin tausayi, Domin Bata sani ba, ta tafi makaranta tabar Baya da kura."
Chapter 16 · 0% Book details