← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 65

Sashe 49

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta had'ou da Angonta, Saddiq sun sha fira,da tsare-tsaren su,A KARSHE inda ake pre-wedding pics,suka nufa,"Mansura trolley daya aka cika da kayan hoto,Wurin Deenee Mai hoto,sukaje akai Mata makeup,Daman ya kware sosai mai hoton,Nan ya dinga daukar su hotuna ita da Saddiq taso suyi banzan styles sai dai shi Saddiq Bai amince ba,"Amma sun canja tufafi Sunyi kyau matuka,"Bayan an Gama aka tura masu awaya tare da wanke na katin aka Basu,"Mansura jikinta har rawa Yake ta zAuna ta watsa pics din su a social media."Daga Wurin Mai hoton,gidan kawarta Lubna ya ajiyeta da zummar gobe zai mayarda ita Kebbi,"Tunda Saddiq ya ajiyeta ko ruwan da lubna ta kawo Mata Bata Sha ba, ta zAuna ta dinga turawa kawayenta pics dinsu,Nan ta aza adpnta na Instagram,facebuk,whasp,da sauran chat nata,"Status dinta ma duk pics din ne"Nan fa mutane kowa ya gani sai San barka,Wannan satin kam duka na Mansura da Saddiq NE,Domin Nan take media ta d'auka ko'ina sune ake azawa,"tamkar fashin kwai da Yake popular ce nan labarin Auren mansura lashe money ya bazu ko'ina. Ana ta masu fatan Alheri,"Mansura sai dad'i takeji tana masu godiya,"Domin ta samu miji Mai kyau ga kudi ba k'arya Sunyi kyau a hotunan fiyema da zahiri.

"Ali da matarsa Umaimah suma sun bi sai Shirin SHAGALIN Auren sukeyi. Domin sun ga Ango Saddiq ya riga yace sai Rabin ransa mansura Yar mutan Kebbi,"Shiyasa Suma suka shigo dumudumu Domin Taya shi murna,"Komai na Shirin bukin auren an shirya shi tsaf, Umaimah ce zatayi abinci da snacks din Abokan ango da duk wasu hidima,"Saddiq ya kammala katafaren Gidansa a Nan unguwar su Ali,"Amarya mansura kadai ake jira da Kayanta,Domin shi ya gyare sashensa da na Yara tsaf ya zuba furniture madu kyau da tsada sai San BARKAH."

**********"A falon muka samesu suna fira harda dariya da shewa...Ganin mu yasa sukayi shiru,Saif sunkuyar da kansa Yayi Yana sosar keya cike da kunya,"Jawad ko wani mugun kallo ya bini da shi, murmushi nayi Masa,"Nan muka zAuna Ni da Saudat,"

"Nace Abokin Ango saukar yaushe Ina gajiya,"

"Yake Yayi a Dan daburce yace"Amarya ya bakunci!?"

"Nace...Alhamdulillah saifullahi,tare da Kallonsa na Dan canja yanayin walwalata na Kawar da kaina gefe!"Nace" Ashe Daman Kaine na hannun Daman Ango sai akai min basaja!?" To ba damuwa hakan yayi kyau Wannan ma wani sabon salon tsarine Mai dauke da wata manufa! ,Amma a kiyaye Gaba Domin gudun matsala!"Idan anyiwa Mai *TARBIYYA* an kwashe lafiya za'a iya haduwa da b'ara gurbi maras *TARBIYYA* Kasan kuwa sai wani ikon Allah Domin komai ta fanjama fanjam!"na karashe zancen Ina murmushi,"

"Wani Abu Saif yaji kamar Yana cikin Ruwa Don kunya..."Saudat ma taji dadin yadda Nadiya ta dauki mataki acikin ruwan Sanyi ta mayarda martani!"

"Tashi nayi na dauko drinks na zuba Nace yallabai ga Ruwa saifullahi Bismillah Nan na zubawa Saudat da Ni muka Sha,"

"Jawad wani haushina ya kamashi mamaki Yake wato har Yanzu bakina da sauran magana,zaiyi maganin komai,"Yace azuciyarsa

"Bayan ya kurba lemon Mai Sanyi ajiye Glass cup din yayi Kan stool tare da sauke Numfashi,Yace Allah Nadiya kiyi hakuri Daman suprise ne mukayi maki,"Amma ki manta da Wannan Duk abinda Kika Gani plan din Jawad ne,"Dariya Saif yayi irin ta rashin gaskiya yace"Jawad yace zai gwada ki ya gani ko Zaki so shi ko da baki sanshi ba!"

"Murmushi nayi tare da cewa,Ay Yanzu yaga zAhiri saboda Ina amfani da umurnin iyayenah,Kasan su Baba sun tsaya maku dole ne nabi idan har na kasance Mai biyayya

"Ajiye kofin yayi da karfi ya kalli Saif yace" mu wuce gidan Momy, tana jirana tun d'azu fa Nace Mata zamu zo Kai nake jira"

"Daman saif ya kosa su bar gidan Dan Haka Tashi yayi suka wuce, jiki ba kwari,"

"Suna fita na fashe da wani irin Kuka Mai tsuma zuciyar Mai sauraro!"Saudat gefena ta dawo tana rarrashi na,da bani Baki!"Da sanyin muryata da ta disashe!"Nace Bari kawai Saudat kuka shine zaisa na rage zafin abinda Jawad da Abokinsa su Kai min!sun yaudareni da Iyayena,sun zo masu da sigar kirki da Kamala.

Saudat nifa har na manta da shi tuni na shafe babinsa a rayuwata Ashe shi Kam ya kullaceni har ya yi nasarar aurena. Ba komai inda rabbana ba wahala komi zai wuce.Nan na k'ara bata labarin abinda ya hadani da shi daga farko har karshe.

"Saudat ta Jinjinawa lamarin!Amma Hakuri da nasiha ta Cigaba da yimin tare da fad'a min irin dabarun da zanbi Kar jawad yaci galaba akaina!" naji sauki sosai Azuciata da Jin kalaman kawata,Nan itama Saudat ta sanarda Ni Duk abinda tasani da Kuma abinda ke tsakaninta da saifullahi."Da irin Shirin da su ke son kawowa a tsakanin mu.

"Da FARKO na nuna Mata rashin amincewata aganina Jawad da saif halinsu Daya,Kuma Duk sune marasa *TARBIYYA* wataqil yaudararta zaiyi,sai dai tuni na fahimci Saudat tayi nisa aduniyar son sa Shiyasa na barta tare da Masu fatan Alheri,"Amma Ina jiye Mata auren kaddara!kamar nawa,"

Bayan Kwana Biyar

"AURENA da Jawad Zan iya misalta shi da auren daukar fansa!"Domin tun lokacin da mutane suka D'aga Mana k'afa nake Shan wuya da azaba a hannun Jawad!"

"Bugu da k'ari Duk yawan gidan Nike share shi nayi mopping nayi abinci ga gyaran Kichen,kaf ayyukan gidan nice!"Zagi da Mari kullum Cikin shansu nake awurin Jawad,Ya mayar da Ni kamar wata baiwarsa,Banda tsimi Banda dabara dole na hakura na Cigaba da Masa biyayya. saboda na dauki Alqawari araina ko da Jawad zai kasheni!"Bazan fadawa kowa ba!"Face mahallicina!"A kullum wurinsa nake Kai karar Jawad ba dare ba Rana!"

"Kasancewar kusan kwanaki hudu Babu nepa a unguwar, Transformer din layin nasu ta lalace sai yau aka gyara,Murna sukeyi Domin an samu karamcin Ruwa da cajin wayoyi a Dan kwanakin Nan,"Sai yanzu da aka gyara wutar suka ji sanyi,"

"Nan kowa ya saka cajin SA da Yake kowannen su Yana da Yar k'aramar waya,shiyasa abin yazo masu da sauki!"

"Zaune suke afalon suna kallon Arewa 24,Hajiya An hakimce a kujera Ana cin Naman kaza,Ana Kora fanta,"

"Anty Talatu itama Naman takeci tana kallon Gidan Badamasi da akeyi,"Sai Dariya suke,"

"Mahmud system dinsa Yake operating shima dai Rabin hankalinsa na Kan t.v."

"Rasheeda gaban t.v take wayarta na caji tana dannawa Domin tayi missing din chat kwana biyu,"Hankalin kowa a falon Yana gurin abinda yakeyi!"

"Tunda ta bude data sakonni ke Shigowa wayarta Babu Adadi da status a WHATSAAP dinta, Danna wayarta take tana murmushi sai dai Abinda idonta suka gane mata NE ya yo bala'in firgita ta!"A zabure ta mike tare da cewa jabbala'i! Me Zan gani!"Cin Amana ko Kuma meye!?"

"Tsaki mahmud yayi tare da cewa Wallahi kin kusa haukacewa Rasheeda!"Waya na neman haukata ki!"Ke Kam kullum chat Zama online kamar ibada Allah yasa battery dinki ya buga,waya ba caji Kuma kina chat..mtwssss yayi Tsaki.

"Tashi Rasheeda tayi Tace"Anty Talatu duba min shin mansura din nan ce ko kuwa!?"

"Wayar Anty Talatu ta amsa,sai dai azabure ta Tashi ganin Saddiq da Mansura ne sun Sha kyau!"

"Innalillahi Wa'Inna ilaihir Raju'un!!"Anty Talatu Tace tare da cewa yanzu Ashe daman mansura batada kirki!?"Hajiya duba kigani!"

"Hajiya na dubawa ta auna ashar Wanda yayi sanadiyar fitowar Jalila Daga dakinsu a sukwane!"Mah'mud yace shin meke faruwa!"

"Rasheeda ta ce"Anty Jalila duba ki Gani Mansura da Saddiq dinki NE maciya Amana Wai aure zasuyi Ranar jumma'a!"Kinga harda i.v da pre-wedding pics dinsu Yanzu nagani awani group,ko status Dina Duk sune mutane su ka aza daga Yar k'arya ce Dan duk Yan gayu Naga sun azasu!"

"Kallon hotunan tayi Sarai!ko'ina mansura ta washe baki!wani Wuri harda kallon soyyaya, styles iri-iri na masoyana!"Dafe kanta tayi Nan Hawaye suka sauko mata fuska!"Zama tayi kusa ga Hajiya tana gunjin Kuka!"

"Duk Wanda ke falon ya tausayawa Jalila irin yadda ta amince da Mansura!"

"Hajiya Tace"Kibar Kuka Jalila!Allah zai saka maki!"

"Anty Talatu Tace"nayi mamakin yadda hakan tafaru,Duk da Ni dama can ban yadda da ladabin Mansura ba!"saboda ta iya bakinta sosai,"Da ganin Idonta na fahimci Yar duniyace Kuma gogaggiyar Yar bariki..."

"Rasheeda ta amshe Nima haka Anty Talatu,Sam batayi min ba!"lalle mutim abin tsoro ne, ya shigo jikinka ya san sirrinka yayi amfani da shi wurin kashe ka!"Anty Jalila kibar su ga Allah shi zai saka maki amma Sadiq ya cuceki!"Ya rasa wacce zai aura sai wadda tasan sirrinki!Ni na d'auka Nadiya zai aura!"Sai Labari ya canja kuma mafi munin canji!"

''Jalila ajiyar zuciya tayi tare da share hawayenta,Daga Nan komai ya dawo Mata sabou!"

"Muryarta na rawa Tace"Hakika na aikata kuskure arayuwata na yadda da Mansura Kai tsaye!Batare da na karanceta ba!"Na Bata amanar sirrina!"Na mallaka Mata Amanata!"Sai yanzu na fahimci makamin kashe rayuwata da ta gidana na Bata!"Domin Gashi tayi Silar mutuwar AURENA,da rabani da yarana!"Nan Jalila ta zayyanewa Yan uwanta komai tun haduwarta da Mansura har kawowa yanzu,Kuka take Mai ciwo Tace Nadiya ki yafeni,Ina Zan ganeki na rokeki na ci amanarki bada alhakinki ba!"Wallahi sai yanzu na Gane k'arya mansura keyi Kuma tana haushinki da na Nadiya shi ne ta huce,bazan manta ba tayi fad'a da Nadiya ko da na ganta,Amma iya makircinta yasa na yadda da ita a lokacin kishi ya rufe min Ido....

"Mah'mud ajiye system dinsa yayi gefen kujera yace"Anty Jalila kinyi kuskure babba Amma Alhamdulillah Tunda Allah yasa kin gane Daga baya kenan,Bayan komai ya faru,"Wallahi Mata Kuna bani mamaki da kuke saurin yadda da mutane har Kuna basu amanar ku!"Kun manta cewa makashinka Yana tare da Kai!"Duk Wanda zai cuceka toufa sai ya kusantoka!"Yanzu Gashi ta fidda ke zata aure mijinki,"Allah ya saka maki sai Hakuri kawai,yana Gama zancensa ya wuce abinsa Dakinsa!"

"Zaune sukayi zugum suna Jimami,Anty Talatu da Hajiya har zubda kwallah!"Rasheeda ma taga bala'in da yafi nata,"Shiru ma magana CE"

"Jalila hawayenta ta goge!Da hannun..tare da sharce majina idonta yayi jajur!"Tashi tayi Daga falon daki ta nufa,ruf tayi da ciki tana kukan takaici! Da nadama! da Kuma Danasani!"Tunanin mafita takeyi domin kuwa Tabbas sai ta dauki wani mataki saboda mansura bazata cuceta abanza ba!Sai ta nuna Mata bataci bulus ba!"Duk da aski ya kusa kawowa Gaban goshi bazatayi k'asa a gwuiwa ba.
Chapter 49 · 0% Book details