← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 65

Sashe 46

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmnnn Abin nema ya samu Nan Hajiya Salma da Hadiza suka dingA gulmah,suna yiwa su lantana wani kallo,Hajiya Maryam(matar malami sambo) murmushi tayi saboda ita ta daban CE acikinsu,"Daman halinta na kirki daya da mijinta,,"

"Bayan dangin Innerie sun Gama duba kayan,cike da murna sai sa saka Albarka suke da fulatanci Dan ko Hausa basuyi," Sannan ne Hajiya Maryam, ta CE to KU Tashi mu tafi Hajiya Hadiza,Idan Kun Gama,"

"Kunya CE ta Kama su saboda sun gane Maryam ta fahimce su,Amma fuskewa sukayi sai wani hurar hanci suke, suna yiwa bayin Allah Yan uwan su,kallon hadarin kaji, saboda kawai suna talakawa ( _Sai kace arzikin nasu sune,ko su suka baiwa kansu,Hattara dai wulaqanci ba kyau!!Rana 1 Allah Zai amshe Daga gareka yaba Wanda yaga dama_)

"Hajiya Maryam da fara'ah tayi Sallama da sauran jama'ar gidan suna kokarin tafiya"

"Ay kuwa Hajiya lantana da Baba kiruwa (Yayar Innerie)kayan tukuici suka damkawa Hjia Maryam daidai karfinsu suna godiya da Allah Sanya Alheri."

"Baba Kiruwa Cikin hausarta da ba dai-dai ba ta fulani,Tace Hashiya Dan Allah kushi da Hakuri kinshan harkar talaka!"Sai ahankaki,mungode!kaya shunyi kyau Allah shanya albarka,"

"Ameen,Hajiya maryam tace tana dariya,tace ba komai suma sun gode," tayi musu sallama tare da karba kudin tukuicin dubu ashirin Wanda da kyar aka had'a aka Basu da Sauran Tarkace,Tayata kwasar kaya sukayi wasu daga cikin gidan sukayi ta fice,"Ko da Hajiya Maryam ta fito su Hajiya Hadiza da Salma sun shige Mota da makotan momy sai tsegumi suke,ganinta da Yan Kaya dariya suka kwashe da ita,suna fadin Allah ya raba kowa da harkar tsiya,''Nan suka wuce gidan momy ran Hajiya Maryam ba Dadi saboda Sam batason irin rayuwar ta su."

"Yanzu Kam aski ya kusa Kai gaban goshi Domin Nan da mako biyu za'a daura auren Muhammad Jawad Husamaddin da Nadiya Balarabe."Su Saudat da Mardiyya Yan matan amarya anyi anko Duk da WALIMA kawai za ayi na auren,Su Esha ma Nan da wani mako zasu dirou Argungu shagalin Aure."Naseer ma Tuni ya hakura da Nadiya yabarwa Allah komai Daman Yasan Nadiya tafi karfinsa,karambani NE irin na so,"

************A gefena ba laifi Mama lantana da mamana suna kula da Ni sosai tare da gyara min jikina,Duk mama tana Jin Kunya sosai Abu ga fulani....Amma tafara min gyara kafin Yan uwanta Suzi suci gaba daga inda ta tsaya.

A Cikin kwanaki uku fatata tafara sheki da haske,nayi kyau sosai harda jiki nayi saboda Yanzu hankalina ya kwanta,Jawad na bani kulawa sosai,"Haka komai nakeso agidan mu ina samu,"

"A BANGAREN mansura da Saddiq suma anyi baikoh har Ranar aure an saka,Idan akayi Auren Nadiya da sati Daya za'ayi nasu,"Mansura ta Sami kud'ade masu dama awurin Saddiq tuni tafara dilka da gyaran jiki,Ta kammala final exams dinta,Shiyasa ta koma gida Kebbi,suna Shirin aure,"suma dai Ranar aure kawai ake jira."Har yanzu Nadiya batasan waye matar yaya sadiq dinta ba,Saboda tuni ta manta da labarin mansura arayuwarta tun alokacin da sukayi fada,"Bata kara jin labarinta ko kuma ta ganta."

"Dukkan wasu shirye shirye da akeyi na aure Saif shi ke zuwa a matsayin babban abokin ango haka saudat abokiyar amarya da sauran yaran makota kawayen su.

A gefe kuma saif ya nunawa su saudat Jawad har gaisawa sunyi da shi a matsayin ango,"Kuma ta yaba da hankalinsa da kuma kyaunsa azuciyarta,"

"Saudat ta baiwa Nadiya labarin jawad,kuma ta yaba da shi sosai cike da jin dadi,"Nadiya ma tayi murna da hakan,"Saboda ita baifi sau biyu ko uku ba haduwarta da angon nata ba,kuma har yanzu batada hoton shi shima bayada nata hoton,"

"An kammala komai na shirin aure nan da mako mai zuwa za'a sha shagalin bukin auren jawad da Nadiya,Yan uwa da abokan arziki har sun fara zuwa taron taya murna."Mussaman dangin innerie fulanin Dakin gari da Bagudo."

********"Umaima da mijinta Ali suna zaune lafiya da yaranta tare da kanwarta suhaila,"Bayan sunyi nasarar samun amincewar ummah akan ta hakura suhaila tayi karatunta a nan sokoto,"Da kyar umma ta amincewa su umaima Akan zata bar suhailat ta zauna a gurinsu,Saboda tafi son suhaila tayi karatunta a kano(BUK),"a inda take ganin 'yarta yadda zata sa mata ido akan duk wani motsinta da kyau.

"A karshe dai umma ta amince amma sai da umaima da Ali suka daukar mata Alqawarin kula da suhaila."Sannan ta yarda."

"Umaima taji dadi sosai,saboda bata san kowa ba a sokoto aure ne ya kawota,Tana neman dan uwanta agefenta,Fatan ta Allah ya baiwa Suhaila miji a sokota sai tasamu 'yar uwa a gari."

"Ali yayi kokarin samawa suhaila gurbin karatu a state university sokoto, tafara zuwa daukar karatu hankalinta akwance,"Umaima na kula da duk wani yanayin na kanwarta,da shigarta da kuma irin kawayenta,"Tasa ta ajiki sosai ta zame mata abokiyar karatu da shawara ta hakan ne zata fahimci duk wani motsinta,"

*******"Tahir do kansa ya samu dangin mahaifinsa har garin gwaranyo,Ya shaida masu cewa yasamu matar aure,yana son suje su nema masa aurenta a garin Cikin unguwar Bado,Haka kannan mahaifinsa suka shirya suka shigo sokoto domin nema masa aure,Anyi nasara kuma an bashi yarinyar har baiko sai da akayi."Tahir yayi masu Godiya tare da masu Sha Tara na Arziki,Daman Yanzu Yana zuwa Kuma yana masu aike duk da Hajiya bataso Amma ya Gane duk Dan kwarai yafi kadari da daraja agidan ubansa.

***************
"Hajiya jiki yayi laushi saboda tayi neman magani har ta gaji,Har yanzu Tala,jalila da rashida babu labarin maza kamar anyi ruwa an dauke,"

"Mahmud anyi service an gama,Yanxu hakan ya samu wani karamin aiki,A kamfanin robobi da ke cikin garin"

"Jalila kam ta samu lafiya yanzu a hankali ta debe komai aranta,tayi jiki da haske tana cigaba da sana'ointa,"Amma tana jin so da kaunar sadiq aranta agefe kewar yaranta na damunta,"Tun ranar da ta fito gidan sadiq rabonta da yaran,"Wannan shi ke sata kuka!"Idan ta tuna,Tabbas Anty Talatu tayi juriyar rashin ganin yaranta shekara da shekaru!"Allah sarki wai abinda ka mallaka yake kokarin maka nisa,"

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍
_"Kuyi hakuri da wannan fans rashin caji ya sanyani gaba saboda muna fama da rashin wutar kantarki,Kawai ayi manage🙈"_

[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

*SHAFI NA 31*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*SADAUKARWA GA MAI GIRMA KUNGIYATA MAI ALBARKA✍🏼 PEN WRITERS ASSOCIATION ALLAH YA QARA HAD'A KAN MU YA SANYA MANA HASKE DA CIGABA MAI ALBARKA ACIKIN AL'AMURAN MU YA QARA KAIFIN BASIRA DA ZAKIN HANNU AMEEN, ANATARE🤝🏼ABOKAN ARZIKI ALLAH YABAR ZUMUNCHI,INA MAKU FATAN ALHERI DA SAMUN NASARA MAI D'AUREWA A RAYUWA😍UP UP UP PEWA*
_Only the exquisite and whizkid writers are opportune to be PEN writer_

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! INA MASOYAN MU...INA MA'ABOTA KARATUN LITTAFAN MU....MUNA KIRAN KU DA BABBAR MURYA,MUNA SHAIDA MAKU CEWA KUNGIYRMU MAI ALBARKA PEWA TA SHIGA GAGARUMAR GASAR NAN TA WOMEN24 TV WHATSAAP GROUP(AWARD),MUNA SON KU FITOU K'WANKU DA K'WARK'WATAR KU,DOMIN KU ZAB'EMU PEWA,DOMIN SHIGA SAHUN GANI GA IDO A RANAR VOTING, SAI KU TUNTUB'I WANNAN LAMBAR,INA MASU SON MU DA K'AUNAR MU KUFITOU KU ZAB'E MU GA LAMBAR.KARKU MANTA DA SUNAN PEN WRITER'S ASSOCIATION MUNGODE👍🏼*
______________________________________

"Rana bata karya..."Yau Allah Yayi dubban jama'a na birni da karkara sun shaida da daurin Auren Muhammad Jawad Husamaddin da Amaryarsa Nadiyatu Bello (Balarabe)A Kan sadaki naira dubu Hamsin kacal,"

"Yau Rana CE ta farin ciki awurin Yan uwa da Abokan arziki musamman iyaye,Haka Kuma Rana ce ta bakin ciki da tashin hankali!"A wurin Jawad da Nadiya,"

"Tun Alokacin da aka Gama d'aurin Aurensa abokansa da Aminan marigayi mahaifinsa sukayo Masa caa aka,suna taya shi murna da nasiha,Sai yaji wani bacin Rai!"Ya ziyarci Rayuwar shi,"Danasani ne fal aransa,Saboda Yanzu Shi kenan an fara kiransa da mijin Nadiya Kuma an damka Masa Amanarta! yarinyar da ya tsana Aduniya!"

"Suna barin masallaci da akayi d'aurin Auren,Gida suka koma,nan jawad ya samu ya kebe acikin jama'a da Abokan sa,Kuka!ya ke tamkar karamin yaro,ya rasa meke damunsa,Da kyar abokinsa Saif,ya lallaba shi yayi Hakuri suka shiga Cikin abokai,"

"Hajiya khaltumi Kam Baki har kunne duk Wanda ya ganta zai hangin farinciki kwance a fuskarta,Burinta da na mijinta ya cika Ina ma ace Yana duniya ya ga Wannan RANAR alokacin da aka dawo d'aurin Auren momy har Kukan Dadi sai da tayi"

"sashen Jawad ta shigo tana dariya da shewa tare da ma'aikatan ta,Kayan abinci da Abin Sha aka jerawa Abokan ango,kala-kala,"Sannan momy ta kira Ango domin yazo ya gaisa da abokanta da sauran bakinta,Jiki ba kwari saif da jawad suka bi Bayan momy,tana ta Jan su da Fira har suka shiga Babban falon ta da ke cike timjin da manyan Mata masu shiga ta Alfarma,Cikin ladabi ya dinga gaisawa da su,Albarka da fatan Alheri suke Masa,Harda hotuna da shi,"Momy an canja wani kayataccen wanka,Cikin ado na Gani na fad'a,"Tayi kyau matuk'a kamar wata yarinya Nan itama ta jone aka dinga daukarsu hotuna,harda Maman saif da yayyensa Mata,Gwanin burgewa,"Murmushin dole NE jawad keyi Ana daukar pics Amma akasan zuciyarsa kamar mad'aci,"

"Anci an sha anyi hani'an komai akwai naci da Sha agidan Hajiya khaltumi Husamaddin,Tayi rabon Kaya kamar hauka,"Tabbas ta barwa mutane abin fad'a Domin bukine akayi na kece raini da ban mamaki, Wanda yasamu halartar Wannan bukin kawai zai iya bayar da shaidar irin yadda tsaruwarsa da haduwarsa Yake, sai sam BARKAH."

"Tun da Naga Yan uwa da Abokan arziki na shigowa Taya Mamana Fatima(Innerie)murna na dinga rusa Kuka!"Haka kawai naji fargaba da faduwar Gaba!ya d'arsu azuciyata!komai ya tsaya min a rayuwa,wani k'unci nakeji azuciyata,Na rasa meye dalili?

Saudat CE tayi tsaye akaina har na hakura na daina Kuka!"
Chapter 46 · 0% Book details