← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 65

Sashe 26

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jawad wasu kudi ya zarou ya mikawa sahabi..da Tuni ya Kai kasa Yana GODIYA...Nan sukayi Sallama da m.Bala suka fito sahabi baimasu doguwar rakiya ba ya KOMA office din Amna Ina Tuni M Bala ya kargame kofarsa da makuli...Sahabi cike da haushi yabar wurin saboda yayi ta bugawa malam Bai bude ba!"Sai CE Masa yayi ai anbiya shi kudin aikinsa sai dai ahadou wani aiki idan yasamu... hakan ya hakura yabar wurin Yana ma M.Bala Allah ta Isa!"

"Su Jawad na fita suka dinga zaga harabar school din ko da kadara zata hadasu da Nadiya Amma Ina...Har yamma Basu ganta ba!"Hakan suka hakura suka Kama hanyar Argungu cike da farinciki aransu."

_Share and comments my fans_

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍
[2/18, 7:25 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

*SHAFI NA 19*

_DAN TSOKACHI"GAISUWAR BAN GIRMA GAREKU ABOKAN TAFIYA, WATOU MASOYANA,DAN ALLAH KUI HARURIE MASU NEMAN BUKS D'INA, ZAKU IYA SAMUN SU, A NABILA'S FANS GROUP KAI TSAYE" KO KUMA KU BINCIKI SHAFUKA NA, FCBUK, INSTAGRAM,DA KUMA WHTSP NAGODE."👍🏼👍🏼👍🏼😍_

_Masu comments ina ganie kuma ina jin dadi musamman masoyan Nadiya naga kamar kun damu da yawa,Yoo nie ita mansura banji ana tabou chapter ba,Masoyan jawad yana godia,Wasun ku kuma na bar maku jalilah domin nikam tafi karfina sai ku fans🤣🤣🤣_

_*LITTAFAN MARUBUCIYA*_

_*WATA RAYUWAR..._

_*TSAN-TSAR SO_

_*MATAN AURE_

_*BAK'AR AK'IDA_

_*ALMAJIRACHI KO AIKATAU?_

_*DANGIN MIJI_

_*IDAN AN CIZA..._

_*MATA JIGON AL'UMMAH_

_*AUREN DOLE!_

_*SAI KUMA TARBIYYA.....✍🏼_

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

______________________________________

"Mansura kam tana kare chashewarta gidan su kawarta Safna, saurayinta Bimboy ta Kira awaya yazou ya kwasheta sai mabera."Bayan tulin kayan birthday din da safna ta hadata su tare da godia"...karya tayiwa Bimboy da cewa Zata biya ta gidan kawarta Suhaila da ke unguwar ta amso sakou..."Nan ya tsaya gefen titi Yana jiranta amota har ta dawo, ita kuma tana fita wani lungu ta shige Mai hanyoyi daban2 ahankali ta shiga wani Babban zaure..."

"Da hanzari ta zube gabansa tana kwasar gaisuwa...Da fara'a malam ya taryeta domin sun Saba da ita SOSAI."

"Gyaran murya yayi tare da kallonta "yace mansura yau kece a zauran namu...To meke tafe da ke."Matsalar jarrabawar ce to taso?ko malaman ku ne!?Ko Kuma iyayenki nasan Tuni muka Gama da zancen su....Ko samarin ki ne ko Kuma Abokai!?"Ajere Mallam zakiru ya tambayarta..."yana cigaba da Jan carbinsa."

"Gyara zamanta tayi tare da cewa"Ay malam yanzu sai abinda nace iyayena keyi, aiki yayi kyau domin tsorona ma sukeyi yanzu Tuni nayi watsi da *TARBIYYAR* da suke kokarin yimin...Haka exams sun fitou Duk sunyi kyau na lashe...samarin ma biye suke abayana..."Sai dai malam yanzu mijin aure nagani Ina so,Ina ga lokacin aurena yazo Ina son kaimin aiki..."Mai kyau akansa Mallam Nike Sonsa shi Kuma ya tsaneni!..."Ina bukatar agaji da taimakon ka!"Gobe zanxou da matarsa wato uwargidan sa inason ka had'a min kullin da zan mallake shi duka Amma fa da sunana sai dai ita kabata amatsayin Yar aiken mu..."Ina son ka janyo min hankalinsa ya aureni Kuma Sai abinda nace da shi zaiyi da matarsa Jalila harma yaransu su kasance kamar bayina...."Ita zaka baiwa maganin tayi amfani da su Amma aiki yazamou nawa..."Da fatan ka fahimta Babban goro."

"Dariya yayi irin ta shaidanu wacce tayi sanadin fesou goron da ke kimshe a wangalelen bakinsa..."Sai da ya watsawa mansura afuska..."Ya ce bakida matsala yau aikinki zanyi na tsawon dare!" Amma Zaki bada kudin aikinki tun yanzu kinsan yankan wuqa alokaci daya..."

"Murmushi tayi Tace bakada matsala mallam zip din Jakarta ta zuge tare da doubou kudade tace ga Wannan Ta mika masa Nan yasa hannu ya karba tare da zuba su a aljihunsa Yana washe baki..."yace yanzu sai kunzou da Yar rakiyarki zan shirya komai."

"Yawwa malamin mallaimmai GODIYA nake Allah YABAR ZUMUNCHI ya qarou sani..."

"Ameen, mansura,Ay bakya da matsala tunda kinka rikemu tamau..."Mallam zakiru yace Yana munna."

"Inda Bimboy yayi parking ta nufa kai tsaye,motar ta fada suka nufi makaranta."

"Tsaye nake ina knocking kusan yafi akirga amma shiru ba motsin komai...."Gajiya nayi da tsayi na zauna abakin kofar falon tare da ajiye ledojin da jikata...Wayata na fitou da ita domin na kira layin Anty jalila sai dai kiran baya zuwa..."Nan na cigaba da buga kofar....Motsin keys na jiya alamar za'a bude...."

"Da karfi aka bude kofar...Wanda sai da na dan tsorata!"Rasheeda ce kanwar Anty jalila na gani...ta bude min kofar ko kallona batayi ta juya daga ciki...Su mufeeda ne a sanyaye sukayo kaina suna Oyo yo Anty Naddyh....Da taimakon su na shigo da kayan..."sai dai turus naja na tsaya ganin irin yadda Anty jalila ke harare na!"Ita da kanwarta da kuma yayarta Anty talatu...."

"Duk da naji wata irin fargaba da tsoro araina!"Bai hanani zubewa agaban su ina gaishe su cike da ladabi..."

"Dakata munafuka!!!"Ki ajiye gaisuwarki nan gaba idan da sauran rayuwa zatayi maki amfani...Anty talatu tace tare da daga min hannu..."

"Rasheeda da bazata wuce sa'a ta ba!"Sai hararena take tare da daure gyalenta a kugunta ta hade hannayenta akirji!!!"

"Rasss gabana ya fadi!na rasa me zance!"saboda naga Anty jalila ko kallona batayi ba!kuma tamkar tasha kukan wahala!"kamar ba ita ba!"

"Ban motsa da inda nake ba ban kuma tashi ba!"jikina sai rawa yake ga cikina sai qara kugi yake!!!"A karshe tashi nayi tsaye da nufin shiga dakin mu...."

"Karaf rasheeda ta cab'e min kafafuwa sai kasa tif....Dagowar da zanyi a firgice naji saukar zafafan maruka uku ajere wanda sai dai Anty jalila ta daddage ta watsa min su..."Cike da zafyn!nama...."

"Durkushewa nayi ina fadin Innalillahi!Wa inna ilaihir raju un!!!"

"Oh!!!Bakinki ma da sauran magana nan ta hayeni ta dinga dukana ita 'yan uwanta wanda tuni suka rufe min baki bana ko iya magana bare kuka!!!"

"Su mufeed sai kuka!!!suke suna cewa momy Anty kuyi hakuri!!"Amma ina dukana suke ta ko'ina!tun ina jin me suke fada har na fita hayyacina...''

"Ta ko'ina jibgata suke...kamar daga sama sai ga shi ya shigo falon sai dai yayi mutuwar tsaye ganin ana kokarin kisa agidansa!"

"Da hanzari ya isa wurin su inda yayi wurgi da rasheeda wacce sai da ta dan bugu da kujera...nan ya hankade jalila tare da watsa mata mari!!!"

"Anty talatu ko tuni ta daburce ta sauya kamar mai kokarin hana fadan...."

"A firgice ta dago kai ta kalle shi!"Ni zaka mara!"?"Saddiq akan wannan yar iska!?"

"Bai ko dubeta ba!"Tallafota yayi tare da jijjigata amma ina bata numfashi...Da gudu ya nufi fridge ya dauko ruwa ya dinga zuba mata duk bakinta da fashe!"fuska ta kumbura...."A hankali na bude idona gajimare kemin yawo!"Bansan inda nake ba!"A hankali naga yaya sadiq kamkame shi nayi nace yaya ka taimakeni!"Zasu kasheni!!"Yaya zasu kasheni Anty jalila da yan gidan su!"Ka mayarda ni inda Mamana..."

"A hankali ya jinginar da ni ajikin kujera saboda duk sun halakani,sun min rauni a fuska,hannu da kafa..saboda harda cizo na sukai!!!"Da inda Anty jalila take tsaye sai kawai tayo kukan kura kaina ta shakeni sai dai naga wuta..."Nan take kuka ya kufce min...Yaya saddiq kam iya karfi nai!"Ya hankadeta sai kasa! tare da watsa mata lafiyayyen mari!"Nan Anty talatu itama ta kashe shi da mari!"cike da takaici da zuciya!!"Rasheeda da gudu tayo kaina ta hayeni tana duka!...A kufule yaya saddiq yayi wurgi da Rasheeda! harda kwallo da ita!!"Nikam da kyar na rarrafa na tashi na koma bayansa ina rusa kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro...."Saboda naga manyan namun daji sunyo kaina suna batun cinyeni...sam ba imani da tausayi azuciyarsu...."

"Anty Talatu tace tabbas saddiq ka canja!"yanzu akan bare zaki nemi halaka min kannai!!""

"Karfa ka manta jalila uwar yayanka ce kuma matarka tafi wannan banza munafukar yarinya!!!"

"Anty kibar shi wallahi zaiyi da nasani ke kuma kibar min gidaana ko kuwa tsoffin da kike ambata su zo su dauki gawarki!!"Wato bakinki ma da sauran magana baki kasu ba!!!"

"Ransa abace Ya ce" haka kawai zaku daketa!me tayi muku!"Anty talatu wannan haukar ba girmanki bane!"Ay saiku sanar da ni idan ma wani abin ta aikata!"Domin nine jigonta ba ku dauki mataki ba!"Na hauka da zalunci!!!"Irin hakan!!

"Ka kirani da mahaukaciya saddiq!Me ya rage!ko kuma kazo ka dakeni sai ka rage zafi saboda an daki Dadironka..!!"Anty talatu ta fada cike da rashin mutunci!"

"Dadirona na Kuma jalila.....Saddiq ya nanata tare da dafe kai!!"

"Nikam tuni na daura hannu akai ina ambaton sunan Allah ina hawaye!!"Saboda jin wannan mummunan zarafin..."

"Eh...ko karya ake maku wato ni zakuci amana acikin gidan nan saddiq wallahi ban yafe ba!kuma sai Allah ya saka min...sannan sai dai ka zaba ko ni ko yarinyar nan babu ni ba ita na tsaneta ko Lahira kada Allah ya hadani da shegia irinta banza mayya yar talakawa...."Allah ya tona asirin ku duk abinda kukeyi an gaya min maci amana kawai!ke kuma da bakisan halacci ba!"Ashe Sam bakiyi kama da wadanda za'a baiwa amana ba.....!!!"

"Ya isa Hakan jalila bana son rainin wayo.....yanzu kuma abin ya kai ga aymin sharri kuma har da ita Nadiya!?...ya kamata kisan waye ni ba sai wani yabaki labarina ba!"Kawai an shirya karya an gaya maki saiki dauka batare da bincike ba!!?"Yanzu kina nufin akan Wannan dalili maras kan gado zaku daketa!!!"

"An daketa din Ay horata ne akayi domin tasan cewa ba a shiga hurumin mu akwashe lafiya...Wallahi sai kinyi dana sani Nadiya...Rasheeda tace cike da tsiwa tana hararana..."

"Baice da su komai ba!"Ya kalleni..."

"Nadiya tashi muje asibiti aduba lafiyarki.."A hankali na tashi ina dingishi...yaran rikeni sukayi suna kukan tausaya min...Anty talatu fizgo su tayi sai da na kusan faduwa akan mangajeni da tayi...yaya saddiq ne ya tareni..tare da rike hannuna...."Tafiya nake sannu ahankali saboda zafi!"Dai dai bakin kofa Anty jalila ta cimma mana tare da sha gaban yaya saddiq hannu tasa afusace ta yage masa riga tun daga sama har kasa tace"Wallahi ba inda zaka!"Ta kira ubanta ya kaita asibitin mana!"

"Kallon jikinsa yayi tare da mamaki!" kuma ta kame rigar tamau taki sakinsa....yace Sakeni!!"kinji ko!yace da mutukar bacin rai!"

"Sai dai ka kasheni bazan saki ba!"Anty jalila tace afusace tana zubda hawayen bakin ciki!!"Da girgiza jiki!Da hurar hanci."

"Nikam bayansa na koma na labe jikina sai rawa yake tuni na nemi zawayi na rasa!!"Saboda tashin hankali..."
Chapter 26 · 0% Book details