← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 65

Sashe 43

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yace"Kamar yadda Kika sani suna MUHD Jawad Husamaddin,Nayi karatu har bautar k'asa na kammala,yanzu hakan Ina kula da kamfanin mahaifina na fata,"Na ganeki tun ba Yanzu ba,Shiyasa na nemi iyayenki mukayi magana da su har Allah ya bani nasara,kiyi Hakuri na boye Miki Kaina da nayi,saboda bana son in Zama sanadiyar lalacewar karatunki,na sameki kina karatu Kinga gwara na Bari har ki kammala,"Sai Gashi na ci Karo da sakonki Wanda yayi sanadin zubar hawayena!"Amma albishirinki my Nadiya in shaa Allah zakiyi karatu Bayan auren mu."

"Ajiyar zuciya nayi,tare da Jin wani sanyi arayuwata,nace bakomai Nagode Allah yasa hakan NE alheri."

"Ameen,yace Yana murmushi akasan zuciyarta tausayinta NE aransa,Amma in shaa Allah zaiyi iya kokarinsa Kar Jawad ya cutar da Nadiya sosai."

"Ledoji ya fitou da su amota,yace kinga Wannan,"Sannan Ina son kiyi min texts abubuwan da kike buqata,"

"Sunne Kaina nayi,nace nagode,tare da amsar ledar."

"To Ni Zan koma Duk abinda kike buqata ki turou min text ko Kuma sai munyi waya Nagode ki gaida su mama."

"Murmushi nayi nace to,Amma ya zancen hoton...."

"Shiru Yayi....yace to ba damuwa zanzou na tura maki, format wayata tayi Shiyasa,Duk hotunan sun goge,Amma later Zan turo but Nadiya Meyasa Baki chat," ya tambaya

"Baba ya hanani saboda karatu,Kuma yace Ana daukan halaye marasa kyau. nace Cikin sanyin murya,"

"Dariya Yayi yace,okay ba damuwa niKam da munyi aure zan barki ki sada zumunci,"Da abokanki ay sai kaso halinka zai lalace,"Domin shi hali zanen dutsi.

"Hakane Kam.

"To ni Zan wuce,"Rabin Raina Haske Mai Haskaka zuciyata

"Nace,Yayi nagode."Allah ya tsare ka da tsarewarsa.

"Sallama nayi da na koma gida shi Kuma ya wuce abinsa."

"Wani Sanyi naji araina da kwanciya hankali,ganin Jawad dina Mutumen kirki ne Mai Sona da nuna kulawar sa akaina,ba irin Jawad din da na tab'a Samun matsala da shi ba...Tsaki nayi nace wancan Kam marar mutunci ne"

Allah nayiwa godiya da ya bani miji nagari Domin Yanzu kam hankalina ya kwanta na Sami nutsuwa,"

"Saif Duk Jikinsa Yayi Sanyi Alokacin da ya samu Jawad inda ya ajiye shi,daukarsa Yayi suka nufi gida,Nan Saif ya labartawa Jawad Duk abinda ya faru tsakanin sa da Nadiya.

"Yace,A gaskiya na tausayawa mata,irin yadda zakayi Mata kamar abin Yayi yawa,Duk sai naji ban kyauta Mata ba!"

"Dariya Jawad Yayi tare da kaima saif dukan wasa,yace"Kai Dan iska ne,meye to!?"Sai ta dauki matakin da take ganin zata iya,banzar yarinya nifa manage ma Zanyi mu zAuna gida daya da ita,"Inji Jawad

"Numfash ya saukei yace Nidai Dan aike nake ko da takanje ta dawo,saboda mommy da iyayen Nadiya Basu cancanci mu yaudare su ba!"Muyi masu karya da wasa da hankali,"Ada ban dauki abin komai sai da Naga zancen auren yazo da gaske Kuma manya sun shigo cikin lamarin Sai Naga kamar bamu kyauta ba!"Kayi nazari Mana Jawad,

"Ba wani nazari da Zanyi Dole na auri yarinyar Nan na Rama iskanci da wulaqanci da tayi min,"Shine kawai Zan huce haushinta,Auren ma na Dan lokaci NE sakinta Zanyi nasamu wacce ta Dace da ajina ba irin Wannan kwaila kucaka ba,"Jawad yace."

"Saif Yana driving yace "Hmnnnn....Jawad kenan baka gane ko abinda na hango ba''

"Ba abinda ka hango Baaba,sai Alheri."ya Kai Masa dukan Wasa.

"Da haka suka Cigaba da fira,har suka karasa gida,Saif sauke Jawad yayi Sannan ya wuce nasu gidan."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍

*SHARE, & COMMENTS*👍🏼
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*

_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

*SHAFI NA 28

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

_INA GWANI WANI....,GA NAWAN, 'YAN MAGANA KANCE GASKIYA DOKIN KARFE, HAKA BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE,INA MASOYANAH...? KU FITOU K'WANKU, DA K'WARK'WATAR KU, KU NEMI LITTAFAN MAYAN MATA, MAGANIN K'ANANAN MATA, WAD'ANDA ALLAH YAYIWA BAIWAR RUBUTU KU NEMI NAKU KADA KI/KA, BARI ABAKU LABARI,DA YARDAR ALLAH ZAKUJI DAD'I LABARAN MASU ILIMANTARWA, DA KUMA FAD'AKARWA,SU NA DAUKE DA DARASI MAI D'IMBIN YAWA, BUGU DA K'ARI ZAKU NISHAD'ANTU SOSAI,ALLAH YASA MU DACE AMIN._

_LITTAFAN SUN HAD'A DA_

_HASSANA DA HUSAINA_
_(NA HASSANA DAN LARABAWA,Qawar Aminchi)_

_GIRMA YA FAD'I...(NA NABILANCY LUV, Abokiyar Aiki Kuma ta hannun damana, Takwarata,)_

_GUDAI....(NA NABEEHA AMEENU, Tawan sonki daban ne, Aminiyar Nabeela Ameenu,)_
_____________________________________

Bayan mako D'aya

"Abu kamar wasa karamar magana ta zamou Babba,Domin alaka mai karfin gaske ta dinke atsakanin saddiq da Mansura."

"A yanzu babu abinda saddiq ya Sanya agaba face,Aurensa da abar Sonsa da qauna wato mansura."

"Haka gefen mansura abin nema ya samu,Har ta gayawa mamanta cewa tayi sabon kamu,Wanda takeso ta aura kwanan nan zai shigo gida Domin zancen aure ne da gaske."Mamanta tayi murna matuka musamman da taji akwai kaya a Aljihunsa."

"Duk Bayan kwana biyu saddiq sai ya hadou da Mansura sun Sha Fira aje shopping da sauransu,Ko da yaushe suna waya idan dai ba Aiki ya fita ba."

"Hankalinta ya kwanta ta sameshi yanzu atafin hannunta sai yadda taga dama da shi,"Shiyasa ta dauke nauyin abincinsa Sarai,Duk abinda yake son ci ko sha Naseer kawai zai Aiko da cefane,Nan mansura zata baje basirarta ta hada masa girki naji nagani na fad'a,''Saddiq Yana Jin dadin hakan domin wasu kalolin girkin da Mansura ke masa baima Saba ganinsu ba,wasun ko Yana ci agidan Abokinsa Ali."Tabbas burinsa zai cika yayi Dace da macce wadda ta iya girki ga tsafta,ko yaushe Yana alfahari da Mansura idan ya tuna Wannan."

"Itama dai mansura acikin abincin da take dafawa tana bashi,ta nan take samun nasara zuba Dan kulle-kullenta a abincin ko abin Sha."
( _Oh ni yar mutan Dikkawa, Mansura dai,hmnnn ke kam kakarki ta yanke saqa,tsuntsu ya fadou maki Daga sama gasasshe,To Allah ya fidda A'i ga rogo_)

"Tun dawowarta har zuwa yanzun suna da labarinta, tunanin mafita suke Domin jiya sunyi waya da jawad din har Nadiya take nuna masa tana son ta ganinsa azahiri da kuma ahoto dan kawai tasan Waye shi."

"Tirkashi to Yanzu jawad kana nufin bazata game ka ba!?Inji saif da mamaki

"Jawad yace "Yadda bazan manta da ita ba,Saif Ina da tabbacin itama bazata manta da Ni ba!"Ko a hoto zata shaidani,"A Murya ne bazata saurin daukowa ba Dan Ina canja maganata kamar ta ustazai.

"To,ya zamuyi Yanzu, Kuma wace Amsa kabata?"

"Neman mafitar nazo awurinka,sai dai na Gaya mata yau zamuyi Tafiya Abuja tun da safe,Shiyasa na cire layin da nake amfani da shi a dayan awayana,Wanda nasaya kawai saboda ita,"Amma na gaya mata da zarar mun sauka na huta zan turo Mata pics din,"

Kuma nayi nazari akai

"Kennan hotonka zaka tura mata!?Meyasa zaka watse mana lamari!?"Saif yace da Dan hasala

"Dariya yayi tare da tafawa da Shi yace"Ba abinda zai faru mutume na ba nawan Zan tura ba,Hotonka zan tura mata amatsayin Ni, sannan Bayan kwana biyu Kaine zakaje gidansu,Sannan Ina son ka daukota ka kawowa momy ita ta ganta,"

"Tayaya hakan zata faru Jawad!?"karyar da yaudarar tayi yawa!?"Saif yace cike da damuwa."

"Murmushin keta yayi,Karfa ka manta da sunan da ta kirani yarinyar ta Gama dani dole na nuna Mata nidin cikakken marar *TARBIYYA* ne,"Babu tausayinta acikin raina ko kad'an,saboda hakan Ni ba ruwana da Duk halin da zata samu kanta aciki,"Ina son ka shirya saboda Duk wata hidimar aure Kaine Ango,sai Ranar auren mu idan an kawota nake son tagane Waye Angonta na gaskiya!?"Sai na gabatar Mata da kaina na kuma tabbatar Mata da *MUHAMMAD JAWAD HUSAMADDIN* shine mijinta.

Nayi tunanin idan ta ganni yanzu na sani bazata aureni ba,zata fad'a iyayenta gaskiya Bata Sona,ka ga Burina na daukar fansa ba zai tabbata ba kenan.

"Saif,yace"A gaskiya bakada dama jawad,Amma Kuma........To shi kenan dai ba damuwa hakan za'ayi."

"Rungume shi yayi cike da murna yace Nagode Saifullahi Tabbas Kai wani B'ari ne na rayuwata."Jawad yace Yana Dariya,shima saif din dariya yakeyi yace Kai Dan uwana ne,ka wuce Amininah."

********""Tun Ranar da iyayena suka zaunar da Ni,sukayi min nasiha akan mijin da zasu aura min na hakura da komai Kuma nayi biyayya akan zabinsu."

"Kwantarda hankalina nayi na cigaba da sha'ani nah,Tare da neman mafita awurin ubangiji."

Washe gari

"Tun da wayewar safiyar yau mama,tabani katuwar leda cike da kayan alawa,"

"Tace"Kayana ne na shiga gida wanda Zan rabawa abokaina."

"Nace,To nikam mama Wannan yayi yawa wama zanba tunda ba wasu qawaye NE da Ni ba,Anan garin Kuma danginta suna Bagudo,Baba ba Yan uwane da shi ba!"Bare ace dangina Zan rabawa su Saudat NE kawai Zan debewa."

"Mama Tace Dan kawai bakida dangi shi zai Hana kibawa yaran makota tsaranki,Sannan abokanki na Islamiyya da can sokoton bazaki Basu ba!"Meyasa kinka cika wauta Nadiya!?"Ta karashe maganar tana faman yimin mita"

"Bata fuska nayi da sangarta,Nace to kiyi Hakuri Amma idan kina buqata ki ragemin su."Sai na debewa kowa yau ma sai naje Dana Islamiyya nabasu."

"Mama Tace"Nadiya duk mu rabawa mokota da abokai,Mallam goro ya sayo da alawa masu yawa, kowa an ba, ya shaida ay shalli ne,ko dangina mutanen Bagudo da dakingari da yawa Mallam ya aika masu,"

"Amma ki tabbata kin debewa su Saddiq da yaransa,Sannan ki debewa su Mallam yunusa ko!?"

"To mama Haka za'ayi Nace Ina murmushin karfin hali Amma niKam bazan iya baiwa Mallam yunusa alewata ba!Mutumen da ya wulaqanta ni agaban budurwarsa na Riga na rufe shafinsa."

"Ina Cikin tunanin sai ga mama da Ledoji farare a hannunta Tace"karbi Wannan sai ki kullawa kowa nashi aleda ga Kuma manya baqaqe."

"Amsa nayi tare da yin yadda Tace "Har na kammala."Ajiye su nayi har zuwa lokacin da zan fita, makaranta."Nasu Esha da yaya Saddiq ajiyewa nayi har na tashi."Sai dai na Kira Duka kawayena na shaida masu da anyi min baikoh,fatan Alheri sukayi min."Naseer Kam kasa Gaya Masa nayi Sak'o na tura Masa wanda nasan zai Sanya shi acikin wani Hali,"Sai dai yayi Hakuri Domin kaddara ta riga fata."( _Inji''yar mutan Dikkawa_)

************* "Zaman gidan Hajiya zama ne Wanda ya koma tamkar dandalin 'yan siyasa saboda ita fa Hajiya Duk inda taga maikou acan take,yau tana nan,jibi tana can,"canza sheqa awurinta kamar kiftawar gira NE,'

"Abin Gwanin mamaki,saboda Tunda Tahir ya samu Karin girma,Hajiya ta daina yin Rasheeda ta koma gefen Tahir kullum Cikin yabonsa da saka Masa Albarka take."Duk wasu lalurorin gidan shine,Ga gini yanayi ba da wasa ba,saboda Yanzu hankali yafara shigo shi."Mahmud ma ya dawo gida,sai Shirin zuwa bautar kasa."Jalila da Anty Talatu sun dawo Yan kallo agidan."
Chapter 43 · 0% Book details