← Book details Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 65

Sashe 37

Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shiru Saddiq yayi,tare da sauke Numfashi yace"Ali ka fahimce Ni, rike Yara hudu ga lalurar ciki ba abune Mai sauki ba.."Awurin Umaimah

"Umaima ta katse shi,Tare da cewa Saddiq kada ka damu Ni Banda damuwa na Saba da kula da Yara tun agidan mu,Ciki Kuma ay Kasan na daban ne!Bare ma jibi Suhaila kanwata zata zo hutu daga Kano,Anan zata zAuna har sai na haihu,kaga kafin nan ma ka mayar da Jalila."

"Tana Dariya Tace"Kasan Ni da mijina ba yinmu Jalila take ba tun da muna fad'in gaskiya. naso na kirata na Bata shawara!Amma Ina da Tabbas ba dauka zatayi ba!"Sai dai Ina rokon ka kayi Hakuri ko domin yaran Nan!"

"Wallahi Jiya Saddiq da kukana da hawayena! alokacin da nake jin Labarin nan awurin Abban Salim."Banso ka saketa ba!"

"Shiyasa ma ba'a so gaya min ba!Dan kawai na matsa NE, da tambaya saboda Naga yaran wujiga wujiga afirgice!"kuma da dare!"Shine fa ya bani Labari Kuma su ma sun fad'a min duk kuskuren da Kuka Aikata a Gaban idon su."

"Ali yace"yanzu dai koma meye ki tashi ki kawo Masa breakfast kinsan ya koma gwauro..sai da taimako Yana Dariya

"To Bari mu taimakesa Tace cike da zolaya tana Dariya."

"Saddiq ma dariyar yayi yace ba komai,amaryata na nan zuwa kwanan Nan."Zolayar zata zo karshe!"

"Ba wata amarya shiryawa za'ayi da tawan,Ai Fadan masoya hutu ne Inji('Yar mutan Dikkawa)Umaima Tace tana dariya tare da kokarin Tashi."

"Bayan ta wuce Ali yace"Karka damu Saddiq zamu kula da yaran ai abin ya zo da sauki Tunda a school daya suke karatu, ka hadou kayansu har uniform,ka kawo Mana,zamu rike yaran mu kafin kusan ciwon kanku.."

"To ba damuwa,Zasu zauna anan idan anyi hutu Argungu Zan kaisu hutu,Ina son na shiga weekend din nan naje nayi masu bayanin komai,Saboda nikam aure zanyi ba Zan dawo da Jalila ba!"Yanzu ina son muje makaranta nasa anemo min Nadiya saina ci mutuncinta,Dan Nasan tana can!"

"Kamar ya!?"Saddiq

"To Tayaya Ali, zance kada ta fita sai bayan bana nan ta fita!?"In Banda rainin wayo!"

"Karfa ka manta ka gaya min yadda kukayi da ita Kaine ka hanata Kuma taga Jalila tadawo inaga ta firgita da ganinta ne ta wuce Abinta!"Sam nikam Banga laifinta ba!"Kada ma ka soma ganin laifinta."Inji Ali

"Nan Umaima ta dawo d'auke da kayan Kari,Amsa yayi ya dawo kasan kafet din hau ci harda su Santi sai da ya koshi."

"Umaimah da Ali,sai dariya suke Masa tare k'ara zolayarsa."

"Saddiq Yace"Sai kuyi ai ba abin kunya nayi ba!Domin agidana bana samun abincin yadda yadda dace,Zuwan Nadiya ne ma nasamu sararin yunwa."

"Ali Yace"To Allah yasa MUDACE."

"Amin,sukace dukkan su

"Saddiq ya kammala cin abincin ya tashi suka fita,zuwa makaranta."

"Umaimah ko kayan ta kwashe tare da gyara falonta, Saboda macece Mai tsafta,ga kirki da mutunci bugu da kari ta samu kulawa Mai kyau awurin iyayenta musamman mahaifiyarsa macece Mai kula da dagewa Akan yaranta" Shiyasa har yanzu Umaima ta kasance tauraruwa Mai haskakawa agidan Aliyu suna zaune lafiya da kuma yaranta masu matukar nutsuwa da tarbiyya.

********* "Zaune nake sun sani tsakiyar a faculty mu,suna min ya jiki da fatan samun lafiya, Nan ne suke bani Labarin gwajin(tests) da akeyi bana nan GSE 214,EDU 212,da Kuma ENG 222,."Duk sai naji banji Dadi ba!"

"Saboda Yaya Saddiq ne ya gaya min cewa zaiyiwa malamman bayanin bana da lafiya, ya Kuma rokar min Alfarma agurinsu suyi min.."To Gashi yanzu na Masa laifi!"Yanzu ban San ya zanyi."

"Naseer ne yayi Sallama wurin Amsa Masa mukayi Nan muka gaisa Daga bisani Wuri muka kebe muna tattaunawa tare da min ya jiki,Naseer yace a gaskiya Naddy Baki kyauta ba!ko Baki da lafiya ai sai ki bude wayarki Mana!Amma ayi ta neman ki akashe!"A gaskiya na shiga damuwa da tashin hankali!"Gashi Mallam Saddiq din ma ba shigowa Yake ba!sai da na Kira Yake sanar min bakijin Dadi."

"Kayi Hakuri Naseer ba gani ba!?"Nasamu sauki."

"Amma meyasa Bai sanarda Ni Kuna asibiti ba!?"

"To Kasan kana karatu Kuma lokacin gwaji ne inaga Shiyasa baya so ya D'aga maka hankali!"

"Allah yaqara sauki."Yace

"Amin My Nass Nagode da kulawa."Nace Ina murmushi

"Abubuwan da akayi bana Nan ya dinga koya min har su Esha suka zo suka samemu Nan Suma suka zAuna aka Cigaba da koya mana,saboda yanzu sai San barka sun fara hankali Zama tare da Ni wasu halaye nasu da dabi'u maras kyau duk sun ajiye su,A hankali fadakarwar da nake masu ta fara shiga jikin su."Hankalin mu kwance muke karatun mu"Malamin mu Naseer Kuma sai kokarin fahimtar da mu komai Yake daki-daki."

"Yau Kam bakin mumy har kunne,Ta Sanya Mai aiki ta girka abinci kala-kala,Ta Sanya Saif da Jawad agaba aci Wannan aci wancan cike da nishadi."Lafiya kalau Jawad an warke kamar bashi ba!"Hankalinsa kwance ya cire duk wata damuwa,da tunani aransa ya sake sai fira da tsare-tsaren buki suke."

"A yanzu kam ba abinda ya Sanya agaba sai auren Nadiya Balarabe."Haka mommy tana nan sai shirin yadda bukin zai kasance takeyi."Saif Kam shine atsakiya ko'ina shine gefen mom da Jawad,Domin ya zamou wani bangare na rayuwar su."

"Malam kana jina!?"
"Eh,Ina jinki."

"Yawwa malam yanzu dai kaji duk yadda ake ciki."

"Dariya yayi yace"Tabbas mansura kina da kwakwalwa Mai kyau,Ai kamar yadda Kika gayawa sakaryar,To shi ne mafita."

"Kenan ba matsala!?"Inji mansura

"Babu Nidai ya kasance shi Saddiq din ya shaki turaren na jiki da na gidan."Inji malam Zakiru Yana Dariya."

"Malam nifa duk hankalina atashe yake Dan Naga ba'ayi turaren ba!Kuma dai naso ace Ina gidan zai saketa,nafiso Yama bani sakon sakin abaki ko a hannu na Gaya Mata!"Amma sai Gashi wawuyar tayi Masa iskanchi ya korata!"

"Sheqewa yayi da wata dariya yace"Mansura kenan kina da Ni hankalinki ke Tashi!"Yanzu da yadda Kika Gaya Mata hakane!"Da zarar tayi turaren zaiji ya tsaneta Daga ita har Nadiya bazai Kara kula su ba!''Ke zaiji fa da ya gansu da Idonsa gwara yaga mutuwarsa Ido biyu."

"Shewa tayi har tumami...Tace Nagode Mallam akwai goro na musamman sai na kayo maka."

"Allah yasa Albarka sai kin zo mansuratu."

"Tana ajiye wayar ta dinga tikar zawa har da su shoyki,Tana fadin _Idan babu kai Nima ba'a ganni ba!Yaya Saddiq mansura baby_

"Har bakin get din hostel din suke shi da abokinsa Ali,Maman Hostel wato Mai kula da Yan matan, Saddiq ya gaisa da ita kana ya bata cigiyar Nadiya."Amsa Masa tayi da yabari ta shiga ta bincikota."

"Tsaye sukayi tsawon mintoci suna jiran fitowar mama,Amma shiru tsaki yayi yace"Ali mu koma Mota mu jirata,nifa cika son tsayi anan ba!"Kasan mata ba hankali ne da su ba!"

"Ali yace hakane musamman Yan matan yanzu basu San darajar suturta jiki ba!"Ay ko iya su matan ne Ana son su rufe tsiraicin su."Amma aganin su sakin jiki agani burgewa ne sai kaga Mata na fitowa ba Kaya a jikinsu Wai hotel ne duk sune da hakan sure Lalacewar Suna bibiyar Yan uwansu mata."

"To Ali abin sai dai Addu'a Inji Saddiq."

"Hira suka Cigaba da yi Akan Abubuwan da ke gaban su."Can dabara ta fadowa Saddiq yace Ali Bari nakira yarinyar nan na manta tana da waya,Bari mu ga ko zan sameta, may be mama bata gane a inda take ba!"Wayar sa ya fito da ita iPhone 11 fara sol

"Dialing...No *NADIYA* yayi Wanda Tuni ta shiga.........."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*😍

*2020*
_Share nd Comments_
[2/18, 7:28 PM] Nabeela Dikko: 🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲🌲

*NA*

*NABEELA DIKKO*
_________________________________

® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_________________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

*SHAFI NA 26*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

_An karb'ou daga Abdullahi d'an Anas(R.A)Yace"Manzon Allah(S.A.W)"Ya ce"Zagin musulmi fasik'anchi ne,Yakarsa kuma kafirchi ne,(Bukhari da Muslim)_

______________________________________
"Bayan wata d'aya, abubuwa da dama sun faru, Musamman agefen Saddiq, Wanda a halin Yanzu ba abinda yafi tsana! irin Jalila ko ganinta baya son a rayuwarsa bare ayi Masa zancenta."

"Haka idan ya shiga makaranta, Nadiya ta same shi a Office dinsa domin ta gaida shi, duk sai yaji ya kosa Bata fita ba!"Saboda wani Abu da yakeji idan ya ganta kamar an daura masa dutsi aka,Duk sai ya damu,Shiyasa ko kallonta baya so saboda fargaba da Yake!."

"Haka kawai ya rasa meke Masa Dadi a duniyar nan,Gaba d'aya jinsa Yake tamkar an canja shi,Tun Ranar da Jalila ta bar Gidansa ya shaki turaren gidan ya kasa samun nutsuwa da sukuni.."yaji Kuma ya tsaneta da Nadiya baya son ganinsu bare su zo kusa da shi.

"A Hakan yake rayuwa Yana fita Aiki,Idan yadawo ya tafi restaurant ya ci abinci,sannan ya koma Gidansa,In Banda Tunani ba abinda Yake,Amma Yana ji azuciyarsa akwai wani Abu da take so na daban Wanda ya kasa gane ko meye."

"Tsaye tana nazari magana ale Mata, Amma Ina Bata jin komai Dan tuni ta nutse duniyar Tunani..."

"Jalila!ta sake Kiranta akarou na biyu"Da karfi!

"Tagumin da tayi, ta cire da sauri tare da kallonta,A zabure...da sanyin murya Tace Na'am Anty!

"Murmushi tayi sannan ta dafata,Zama tayi kusa da ita,Tace"Kullum fa Ina ji Hajiya na maki fad'a Akan tunanin Nan!Ki dubeki Dan Allah...Har kin wani canja wata daya kacal!"Duk kinyi bak'i kin rame Jalila!"kamar kanki aka fara fita gidan miji!karki manta Nima nan Daga can na fito kuma yarana Duka na Bari,kin sani har yanzu ban Kara ganin su ba!"Kiyi Hakuri Haka Allah ya nufa da mu!Daman abinda nayi Miki gudu kenan!"Inji Anty Talatu cike da damuwa da tausayin kanwarta,

"Jalila Ta sauke ajiyar zuciya!Tace"Anty kina fa ganin yadda su Rasheeda ke mana cin Kashi agidan Nan,Amma Hajiya Bata Gani!Shi kenan Dan muna zaman gida sai adinga wulaqanta mu!''Nikam kowa ban daukarwa!Duk wanda yayi min zan rama!"Haba!Da me zamuji!?Da takaichi ko da Danasani!?"Wallahi Anty nayi nadamar zaman gida,ki duba fa duk abinda kake so gidan Nan Kai zaka saye da kanka Ni Yanzu ma kudina ya Kare ko naira bani da ita, Ban san ya zanyi ba!!!"Hawaye ne suka zubou afuskar ta, Tace Anty kina Gani Kayana kaf sunyi datti Banda sabulu! Kuma Ni rabona da nayi wankin da kaina har na manta."
Chapter 37 · 0% Book details