Sashe 1
Tarbiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*🌲🌲TARBIYYA🌲🌲🌲*
*©NABEELA DIKKO*
*PEN WRITERS ASSOCIAON✍🏻*
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._
*GABATARWA* _Dukkan yabou da godia sun tabbata ga Allah ubangijin tallikai,Salati maras adadi zuwa shugaban mu Annabi (SAW) da alayensa da sahabbansa ba ki daya,Allah yaqara mana rai da lafia da ikon fadakarwa akan turbar Manzon rahma Ameen._
*TSOKACHI* _Wannan littafi na TARBIYYA na rubuta shi ne domin ilimantarwa, fadakarwa, da tunatarwa,Bugu da kari na tsara salonsa domin nuni da halaye masu kyau da maras kyau,wadanda sukaci karou da addini musulunci,Banyi domin wani ko wata ba,Labari ne kirkirarre kuma kagagge,Duk wanda ya ga ya ci karou da halayensa ko dabi'un sa to ya sani Arashi ne kawai._
*GARGAD'I* _Ban yarda wani ko wata ya canja min Labari ta kowacce fuska!,Matsawar ba tare da izinina ba!Duk wanda ya aikata hakan to ya sani shi barawoun fasaha ne,kuma Mai aikata aiki maras kyau,Allah ne gatana kuma shine wanda zai sakamin._
*SADAUKARWA* _Ga Iyayenah Abin Sona,Abin Kaunata, Abin Alfaharina,Rabbil izzah yaqara masu rai da lafia tare da nisan kwana,Ya rahman ya sadasu da rahmarsa, fatana Aljanna ta zamou mazauninsu na har Abada Amin._
*SHAFI NA D'AYA*
*SHIMFID'A* Da farko Ita dai *TARBIYYA* Abi ce mai muhimmanci a rayuwar Al'umma,A wannan zamani da muke ciki, Hakika *TARBIYYA* Tayi karanchi a rayuwar mu,Idan mukayi la'akari da tsantsar so da kauna da iyaye ke nunawa yaran su Ayau,Hakan agefen yara suna yawan ajiye halaye da dabi'un gidan su agefe suna aikata abubuwa son ransu....Anan na kanyi nazari akan shin meye *TARBIYYA?* Lalacewar ta da tabarbarewarta laifin waye? iyaye ko yaran?ku biyoni...ni ce taku Mai kaunar ku *Nabeela Dikko* domin sanin yadda zata kaya,Shakka babu *TSANSAR SO* ne ya sanyani nake subourboudou maku littafai masu ma'ana....Banda zabi akan ku masoyana *MATAN AURE* da 'yan mata,na nesa da na kusa domin *MATA JIGON AL'UMMA* ne,Kuma su Abin girmamawa ne akoda yaushe,Ina baku shawara ku rike hakuri saboda halin *WATA RAYUWAR....* Domin *IDAN AN CIZA HURAWA AKE* Duba ga Ukuba irin ta wasu *DANGIN MIJI* Da sannu zata zo karshe,Kamar yadda *ALMAJIRANCHI KO AIKATAU* zai zamou labari nan ba da dadewa ba,Dama caan ita *BAK'AR AK'IDA* Abin gudu ce,Allah ya dauramu Abisa tafarkin gaskiya,Ya bamu ikon yiwa yaranmu *TARBIYYA* mai kyau Ameen.
______________________________________
"Sunana Nadiya Bello, Wanda akafi sani da suna Balarabe,saboda fari ne sol, kamar zubin larabawa."
"Mafi yawan kawayena na firamare da sakandare sunfi Kirana da (Naddy Balarabe),"
"Tun Ina karamata na Tashi da nutsuwa gashi ,Allah yayi min baiwar kyau da farin jinin jama'a,shiyasa bakin mutane yayi yawa akaina,saboda tsabar kyau na,Iyayena akullum cikin zuba min addu'a suke, Kasancewar ni kadai ce, Allah ya basu a duniya!"
"Hakika iyayena sun inganta rayuwata, tun yarinta ta har kawowa girmana, suna bani TARBIYYA Mai kyau tare da bani cikakkiyar kulawa,"Shiyasa akullum nake alfahrin Samun su arayuwata,"
"Sunan mahaifina Mallam Bello, asalin sa fulanin Sudan ne, fari ne tatas Mai kyaun gaske gashi da kwarjini Duk inda ake neman dattako to idan aka sameshi ansamu,dalilin shi farine tas shine kowa ke kiransa da Balarabe,Amma sunan iya Nigeria ne, sanadin hakan sunansa na ainihi ya bace bat,
" Assultaan shine mahaifinsa ya mutu da dad'ewa bayan yayi wafati ne ya dawo Nigeria da Zama...,kasuwanci ne ya kawo mahaifina Nigeria,Har ya gidadan ce anan,duk yan uwan mahaifina suna caan kasar Sudan,Dalilin kasuwancin da yakeyi na sayar da gwanjou,''
"Watarana gurin tafiye-tafiyensa yaje cin babbar kasuwar nan ta garin kalgo da ke jihar kebbi,
"To anan ya hadou da Ard'ou dakin gari,daga nan suka kulla abota, Mai karfi da inganci tare da amanar juna atsakanin su,Balarabe ya zamewa Ard'ou aminin gaske,bayan wani lokaci Ard'ou yayi masa tsaye batare da binciken sanin Ahlinsa ba, ya baiwa Balarabe auren kanwarsa da ya ke riqou bayan rasuwar iyayensu wato fad'imatou(Innarei)wato mahaifiyata kenan."Itama kyakkyawar gaske ce."Shiyasa agefen uwa da uba na gado fari da kyau bana wasa ba."Mamana da Babana suna zaune lafiya babu Mai jin kansu,Domin halayensu sun zou d'aya mutanen kirki ne sosai."Shiyasa da suka sameni suke inganta rayuwata da TARBIYYA, Bayan tsawon lokacin da suka d'auka basu samu haihuwa ba,Duk da soyayyar da suke nunawa agareni bai Hana su kula Dani ba tare da hukunta Ni idan na aikata laifi,"
" Har yanzu mahaifina bai daina sana'ar sa ba wacce da ita muke ci da sha kuma acikin ta na kammala karatuna firamare na sakandare, Wanda Halin yanzu babana yana kokarin yaga na d'ane gurbin jami'a."A kwalejin shehu shagari da ke garin sakkwato."
"Dukkan mu muna rayuwa a jihar kabi,A garin argungu cikin unguwar tudun wada."Na samu kulawa da Mai kyau awurin iyayena, ilimin islama da na zamani sunyi kokarin bani."Haka suna saka min ido akan dukkan al'amurrana,da duk wani motsi na musamman Mamana,wacce komai nawa akan idon ta yake har alakata da abokaina duk mamana tana sane.Bana Komai sai da saninta ko Kuma izinin su, Domin akwai yarda da aminci atsakani na da su"
"Shiyasa na kasance abin so ga kowa, da kuma alfahari awurin iyayena da malammai nah,har ma da mutan unguwa Duka Kowa Nadiya."Domin na zamou daga cikin Yan matan unguwa,",masu nutsuwa ladabi da biyayya zan zamou ta daya, da zarar ka zAuna Dani na dakika zaka fahimciina da kirki da mutunci duka sun yalwatu arayuwata,"
"Nadiya..!Nadiya..!Kiran da Mama ke mani NE ya fargar da ni daga tunanin wacece Ni.."
"Da hanzari na amsa da na'am mama,gani nan."
"Da sauri na fitou daga dakina zuwa Dan yalwataccen filin gidan mu, inda mama take zaune a tabarma,dake shimfide karkashin bishiya,rediyo ne ajiye gefenta tana sauraren gidan rediyon nan Mai farinjini wato Equity fm birnin KEBBI inda suke Shirin Nan na IN DA RANKA."
"Fuskata mama ta duba, tana murmushi tare da rage karar rediyon..."ta ce ''yooo ni...Nadiya wai sai yaushe zaki daina kumshewa acikin daki kamar kunshin kaya ne!?..."
"Mama kiyi hakuri zan daina zaman d'akin..nace da alamun damuwa!"
"Ni kinga,idan ma kin cigaba ke zakita rub'a!"yanzu kije gidan lantana ki amso min sako."Kice mata Ina gaidata, Nace ta baki sakon, ki kawo min,kuma karki Jima nasan dai mutuniyar taki na makaranta"inji mama
"To,mamana, an gama,nace Ina dariya domin idan da sabo na saba da sauraren fadan, yawan zaman da nake daki,,Wanda ya zame mani jiki..Nan dai na dauko hijab Dina,na fita zuwa makotan mu domin amso mata sakonta."
Muje zuwa fans wasa farin girki🤙🏼
*Yar mutan Dikkawa ce*
*SHAFI NA BIYU*
______________________________________
Gidan su Hajiya Lantana(Kawar mamana) na nufa,da sallama na shiga gidan, hanyar da zata sadani da kofarta na nufa, da yake su biyu ne, A gidan ita da Abokiyar zamanta Laraba, sai dai ba wani zaman lafiya suke ba,zaman su irin zaman nan ne, na doya da manja,kuma laraba ce Mai matsala,"A tsakar gidan ko nasami laraba, tana daka a turmi tana wakokin ta na habaici,,duk da ta ji sallamata Amma sai tayi banza dani ta Cigaba da aikinta,Da sanyi na gaidata da girmamawa,sai dai wata uwar harara ta zabga min, Domin tasan inda wacce nazou wato lantana, shine bazata amsa min sllamata ba,"Sai ma Kawar da kanta da tayi gefe cike da masifa,"
"Shiyasa ma taki ta amsa min sallama ta da gaisuwa,Sum sum na wuce nikam,Harara ta bini da shi tana cewa munafuncin banza irin cuta da babu asali!"An kullo bala'i an kawowa oniga!"Komai nisan jifa dai kasa zai dawo.."
"Bance da ita komai ba nidai!Duk da naji zafi araina sai dai ba sa'an yina bace ina girmamata Kuma Abokiyar zaman qawar mahaifiyata ce, ita ce uwargida agidan tana da yara har jikoki,Bazan mayar mata da martani ba,Amma na lura Sam batasan ciwon kanta ba irin ballagazayen matan Nan ce Domin Bata daukar girman ta."gashi dai ko yanzu ta nuna(Gaskiya ne akwai Mata masu halayen laraba basa Amsa Sallama muddin ba wurin su ajazou ba,A kiyaye Wannan dabi',un jahilai ne)
"Daga cikin dakinta ta jiyo Ina jera sallama,Da fara'arta ta tarbeni sai da na hango haurenta na makka dake walkiya kamar zinare abakinta ya bayyana,da ladabi na gaidata, amsa min tayi, tana cewa Yawwa Nadiya,Ya Innarei!"Shigo daga ciki,kujera ta nuna min afalon na zauna."Duk dai kuna lafiya Nadiya!?."
"Lafiya qlaw,Hajiya da yake hakan yaran gidan ke kiranta."
"Nace daman mama ce ta aikoni tace agaishe ki sannan kibata saqon.."
"Allah sarki,Dan Allah Nadiya ki ce mata tayi hakuri daman Ina jiran dawowar yaran nan, ne daga makaranta,Sai na basu sukai mata,Amma Ina zuwa..."Tashi tayi ta fice uwar dakinta....Dan madaidaicin falonta dake kallon Daman falon ta shiga,Wanda ke zuba kamshi komai atsare kamar wacce bata da yara,A raina Ina jinjinawa tsaftarta..."Dawowarta ne ya dawo da ni hankali na."Murmushi nayi Ina sadda kaina k'asa."
"Ta ce Karbi Nadiya kirga ki gani nawa ne!?"
"Amsa nayi a nutse na kirga su yan dari biyar_biyar ne,kimanin naira dubu goma."Daga kaina nayi na dubeta nace Hajiya dubu goma ne cip."
"Yawwa,Nadiya ki kaimata,ki gayamata wasu ne suka kawo mana tsaiko! basuyi zubin adashin su ba,ko yanzu ma ajikina ne na cika mata kudinta tunda lokacin kwasar adashenta yayi, kafin sukawo nasu zubin!"Kinsan Mutane basa da Alkawari!"Sai dai Hakuri kawai!"
"Murmushi nayi nace to Hajiya zan gaya mata,Allah ya sauwaqa ya taimaka, su Saudat ba'a dawo ba ko!"Na tambaya."
"Ameen nadiya....Eh saudatu Bata dawo ba Abokiyar yawonki, ana can makaranta,jiya fa take kirana awaya waai anfara koya masu yadda zasuyi allura,nace lalle sai anyi malamar asibiti sarkin kaudi, sai ku shirya Nadiya afara koyo gareku mukam mun yafe...Hajiya tace tana dariya..alokacin da ta bude katou firijin din ta na kwance,wanda yake cike da kayan sanyi..kunun aya,da zobou da kunun zaki ta dauko min roba uku 'yan talatin tasa a leda,ta miko min."Tace Gashi Nadiyatu NAGODE ki gaida Innerie
"Da murna na amsa Ina godiya cike da ladabi saboda Hajiya akwai mutunci ga kyauta,Abinta na kowa ne,Shiyasa yan uwan miji,da makota duk ta amshewa laraba su wacce ke ganin maganin mallakar miji da Mutane ne tayiwa kowa ita yakeso da yaranta."Batasan cewa kyautatawa nasa Komai arayuwa,"
"Har kofar gidan Hajiya ta rakani tana bani sakon gaisuwa wurin mamana."Ni Kuma Ina kara gode mata tare da Bata sakon gaisuwana zuwa ga Saudat idan sunyi waya, saboda Ni ban ma taba rika wayar kaina ba asalima duk gidan mu Babana kadai ke amfani da waya."Bare na Kira kawayena,"
"Gida na dawo Ina munna na mikawa Mama sakonta tare da nuna Mata alheran da Hajiya tayi min."