← Book details Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 62

Sashe 40

Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

batay kasa agiwa ba ta dauka tun batayi magana ba muryar Mr James ya katseta am i speaking to ms ushna murad?? da mamaki a muryanfa tace yes sir Good aftrnoon..bai amsa ba muryansa ciki ciki yace You need to come to the office ryt now..Ushna ta dan hade gira Sir is der any problem? yace yes Akwai mistake a file din da kika submiting jiya budan baki tay da kamar zata musa sai kuma tay shiru tace Okay sir. daga nan baice mata komi ba ya katse wayarsa.

zama tay na wasu dakiku tana tunani dan har acikin ranta tasan batay wani kuskure ba, dan kafin tay submiting file saita duba fiye da sau uku kafin nan ta ke kai masa kuma shima ya duba yagani

cikin basar da komi tare da kyabe baki ta mike ta jawo kimono ta daura akan gown inta ta sauya takalmi ta dauki jakarta da su ID cards dinta ta fito har waje neman abun hawa dan tasan idan ta tsaya neman uber xai iya ɓata mata lkci

tafi minti 30 a tsaye dakyar ta samu ride ya kaita har gaban prime real estate group aka sauketa, cikin sauri ta karasa gate masu gadi data saba gaishesu da mamaki suka fara tambyarta meya faru tace musu ai mr james ne ya kirata akan wani kuskure..kowa ya mata fatan alheri snn ta shige ciki.

karar takunta ne kawai yake tashi koina ya dau shiru dake wkends few wknds staff da contractors ne yawanci suke zuwa wkdns suyi abubuwa amma duk wani maaikaci yana gida yana hutawa

har takai floor in da mr james yake bataci karo da kowa ba iyaka masu aikin share share ne da sauran masu gadi suke shawagi ata wajen.

kai tsaye ta nufi office dinsa
tay kncking saida ya dau lokci kafin nan ya bata izini ta shigo ciki, tsikar jikinta atake ya tashi ganin yadda ya mata wani irin mugun kallo, gabanta tun anan ya fara bugawa she notices the bad energy shifts ta dauka kodan kuskuren datayin ne yake jin haushi

Bayan gaisuwa ta tambaye shi inda files me dauke da kuskure din yake saidai da mamakinta bai bata file din ba Ya jingina bayansa yana kallonta da izza yace mata Just go and start over..

baki bude tace Sir? you mean The entire report

buga desk dinsa yay saida ta tsorota a tsawace yace Did you not hear what I said?

kafin ta bude baki taji yafara mata masifa kmr hanjinsa ta cinye yanayi yana daga jijiyar wuya yana cewa tana da raini zai koya mata hankali.

ta yi shiru sai bata kara cewa komai ba ta koma office dinta aranta wani abu na gaya mata cewa da akwai matsala dan ba haka tasan halin mr james din ba

Amma dake bai barta da wani hujja ba haka ta bude laptop dinta ta fara komai daga farko tun daga kam valuations, calculation da observations har zuwa reports tayisu dalla dalla kuma ahankali tabi komi a tsanake. wanda kafin ta gama har sai karfe 4:30 na yamma ko abinci bata ci ba sallah ma acikin office din tayi dan ta samu ta gama ta tafi..

kusan biyar saura na yamma tagama lkcin ta balain gajiiya dan aiki kawai tay babu hutu cikin sauri ta tattara tana tunanin finally zata tafi gida sai intercom din yay kara tana dannawa taji ashe mr James ne yake nemanta, bata wani damu ba dan dama wajensan zata je, komi da kominta ta tattara ajaka ta fito tasake komawa office dinsan takai masa report din bayan ya karba sai ya kalleta yace u can leave, Ushna ta gyada kai tana shirin juyawa knan ya sake cewa.."One more thing. Gabanta ne ya sake faduwa ta juyo gani tayi ya hau nuna mata wasu filing cabinets dake can gefe yace ke tunda kina nan I want those rearranged

Na wasu dakiku bata ma gane cewa dagske yayi maganan ba sai da taji ya sake maimaitawa yana kuma cewa tay aikin yanxu

A hankali ta lumshe ido tanajin wani irin gajiya bata amsashi ba takai hannu wajen tafara gyara Files da Labels da Records da wasu Documents komi ta jerasa a Cabinets dinsa wanda kafin tagama saida yamma tayi sosai, Lokacin da ta kalli agogo karfe shida da minti biyar ne 6:05pm Office din ma kusan daukewa da shiru A hankali ta tattara kayanta bata jira cewarsa ba tay waje da sauri dan Wani irin gajiya take ji har cikin zuciyarta

ga haushi Saboda a ranta tana da yakinin cewa ba tayi kuskuren a file dinta na farko ba Amma duk da haka ta hadiye komai Ta fita daga building din tana jin kafafunta suna yi mata nauyi fiye da yadda suka saba dan saida taci taku sosai kafin ta samu abun hawa yakaita hotel.

tunda ta shiga daki wayarta tafara kashewa snn ta fada agado tadan huta na minti biyar daga nan sallah ne kawai yake daga ta, arnd 10pm tay wanka batay wata wata ba sai bacci, bata kara tashi ba sai tsakar dare da ruwan sama me karfi ya tasheta jin ta kasa komawa baccin yasaka ta diro kasa kawai tay alwala taxo tafara sallan tahajjudi tare da neman sauki da mafi alherin duk wani irin sakamako arayuwarta

cos sumtimes intay tunanin yadda abubuwa suke mata wahala, take yawan cin karo da maqiya da kalubale da uwa uba komi tasaka agaba sai taga abun yana neman wahalar da ita sai taji kamar kodan mahaifnta bai taba saka mata albarka bane yasaka komi nata yake bata wuya, wani bin kuma inta tuna cewa she always try to do things ryt for him, sai taga kmr kawai jarabawa ne, dan kakanta marigaya sarki saleem imamu zamkora kafin ya mutu yasha gaya mata only ppl with great destinies will walk a rougher part koda sakamakon su ya zo musu a bayyane ko baizo musu a bayyane ba amma zaixo din akan lkci kuma ata hanyar da basuyi tsammani ba snn Allah baya daura ma bawa abunda yafi karfinsa..

ta duba rayuwarta sama da kasa gata dai kyakwyam gaske, ga ilimi ga kyan jiki kuma ubanta babban sarki ne ba talaka ba amma gaba daya har yau bata samu sukuni ko sakat acikin zuciyarta da rayuwarta ba.

ayayinda take tahajjud in she cried nd pour out her heart to Allah akan ya saukaka mata snn ya bata nasara ya kuma daurata akan maqiyanta na fili dana boye. bata idar da sallahn ba sai gabanin fajr bayan ta xauna kadan snn ta tashi tay ta rufe da azkr da addua ta nemi tea mai kauri tasha bata ko kula wayarta ba bare ta bude, jin ruwan saman ya dawo sabo tuni ta hau gadonta ta bararraje ta fara sheƙa bacci kmr ba gobe.

girman kai da nassircistic toxic mindset shi yahana farees iya budan bakinsa ya bawa rihanna hakuri itama haka ta daure ta daukr kai akansa duk da abun yakaita makura dan tana mutuwar son mijinta and she wish xai canja halinsa ya dawo namiji kamar kowa shiyasa ma ta cije take iya masa wnn hali wanda Allah nr kadai yasan zafin datakeji aranta datake daukar sati basu hada gado dashi ba gashi yanxu kwanansu uku kenan basuy magana da juna ba. she miss him alot ata kowani bangare amma harga Allah tagama gajiya da yanayin yadda rayuwar aurensu yake tafiya wai shi kenan ita mijinta bazai mata komi ba, itace zata providing komi???right frm mental,physical nd financial support? iya abunda yake matta kkri akai din fa shine sex nd fact that he wll alwys apologise after her cheats or abuse her...

bayan nan babu wani value dayake kawowa acikin auren shiyasa inta tuna haka sai taji kawai gara tadena kulashin gabaki daya.

haka suka cinye sartuday gashi baida ko asi baije koina ba, idonta kuma bata barshi yagani akasa ba bare har wani magana ya hadasu washe gari yau sunday kuma aka tashi da ruwa its almost the worst day of his life inbadan daxu dayaci saa arisha ta turo masa text a wasap ma cewa she need his prayers monday result din test inta zai fito zaa mata surgry within the week tareda masa tuni akan kudin da zata saya kayan jinya dasu kafin nan ta dawo

wannan text sosai ya kara daga masa hankli she dint even try to apologise for ditching him and ignoring his endless text messges yarasa meyene arisha ta dauke kanta amma kuma dake son jaraba yake mata sai yabasar ya fara tunanin dolene ma kawai gobe yaje yay sulhu da matarsa rihannna dan bazai iya cewa arisha baida kudi ba

ranar sundayn bacci maiji da lafya ushna ta sha but sbd ruwa bata samu damar zuwa kasuwa sayan sbbin kaya ba, dake daf sallan azhr ta farka tayi wanka tay sallah taci abinci tazauna ta shirya kayan da gobe zataje office dashi.

sama taki ta bude wayarta saida tagama kimtsa komi nata tay sallahn asr snn ta jawo system dinta tarage wutar dakin fara kallon
adventure series, chan dare kuma ta shirya akan zata kalli mad max fury road movie daga na dayansa har karshe. tasan duk tsiya by 10pm na dare kawai xatay baccinta dan ta samu taje office gobe da wuri kuma akan lkci

dagata bangaren shamsan haka kawai yau shima ya farka da tunaninta altho he seem busy and absent minded amma tun da asubhin Allah yafara jin kamr hanklinsa ya fara komawa lagos din kuma. da can ya so ya basar da abun amma dayaji tana yawan fado masa aransa,

atake sai yayi requesting new reports daga security head office dinsu aka turo masa ya bude file din yaga records tun daga ranar da tafara zuwa aiki ya jima yana observing komi da kwayar idanunsa sai baiga alaman wani reports na harassment ko bully aciki ba. tunda yaga hakan yaji dama dama aransa sai bai kara bi takansu ba.

farar magensa husna dayazo da ita har abujan itace kawai take debe masa kewa dan ynxu sosai da sosai magen ta shaku dashi da kuma qamshinsa
Chapter 40 · 0% Book details