← Book details Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 62

Sashe 15

Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ta mayar da kallonta kan ushna tace I checked the portal ashe gaskiyaki ne system dinmu baya bada exceptions faga zarar application ya shigo sai ya rejectinh automatically

ushna ta sauke cup din tea in data kurba ahnkli tace yes maam nayita gwadawa ai baiyi ba

cikin kyabe baki rihanna tace but tell me something What exactly are you looking for in this internship opportunity?

ushna dake kallonta kai tsaye cikin nitsuwa tafara mata bayanin kan abun batare da ta boye mata komi ba..

cikin nuna gamsuwa rihanna ta amshi file da application letter din ta dubasu da kyau snn tace masha Allah.. ushna ke ta dabance,, you are beauty with brain hala shiyasa ranar kika sha wahala cos you knw misogyny is now everywher, ba maza ba har mata idan wani misogynist yakaga yarinya haka datake da gwazo da kuma dama bazasu bata kwarin giwa ko taimako ba, babban burinsu shine su kusheta ko suyita binta da maganganu marasa dadi. ina fatan abunda ya faru ranar a office ya wuce miki ko?

murmushi me sanyi ushna tay tace yawuce ma'am karki dmu how u treated me is what really define the day koda bansamu aikin nan ba bazan taba mantawa da kirkinki ba

sosai wann kalaman yay ma rihanna dadi tay murmushi can tace ina fatan dai bazaki damu da activities din da zamuyi yau anan wajen ba u knw girl to girl stuff lemme make it up to u properly.

ushna tana gyada kai rihanna ta ja hannunta suka wuce cikin wani luxurious office komi sai taga ana haba haba dasu tarasa wani irin kazamin kudine su rihanan nan suke dashi haka...

duk dama tsantsr kyau da wayewar da yabi jikin ta yasa taga ana mata kallon daraja da mutunci amma duk a tsarge take da kalar kwarjinin rihanna.

anan aka kaisu cikin seperate consultation room spa therapist ta tattauna da su aka san ma wani kalar abu zaa musu da wani irin oils da bath za'a yi amfani dashi. dake rihanna regular customer ce bata wani jima ba ta fito, ushna ne kawai aka tsaya mata kwaje kwaje. daga nan kai tsaye aka kaisu inda ake pressure massage dan acire any allergie da skin sensitivies...

tun ushna tana dar dar tana shan baqin ciki da mamakin yadda mace me kudi, mutunci da daraja ta auri mr abdul aranta harta hakura ta sake ranta dake kusan komi atare ake musu two treatment bed side by side.

rihanna tanata bata labarin kasashen data jejjje a duniyar nan hutu da yawon bude ido har da wanda bata taba jin sunansu ba ma. 90 minutes full body wash aka musu ga wasu kalar deep tissure nd swedish massage, sai aka musu facials da scrubs,full hair treat nd body wraps, detox snn aka cancade musu kafa da hannunsu

duk wannan anayi ana kawo musu abinci mostly fresh seafood, grilled chicked salads fruit flatters da mock tails kala kala sbda karamin ciki yasaka rihanna ba komi take iya ci awajen ba.

duk uban kyan ushna din nan yau bakaramin kara wankuwa takarayi ba dan har wani kyalli da sheqi takeyi daga nesa
gashi anwani irin gyara mata dogon gashinta yay wani irin sulƙi da laushi ya zubo mata har tsakiyar bayanta.

yau shi ne mata rana na farko databsan yes taji dadin rayuwarta takuma huta sosai a kasar nan tunda tazo dan har wani mantawa da damuwarta tayi for a moment musmn yadda rihanna take janta cikin hira masu abun nishadi da dariya

sosai rihanna tafarajin kamar jininta ne ya hadu dana ushna dan ita akwai ta da sanyin zuciya da son taimako kuma bata taba yin ƙawa ko kanwa ba

akalla ta girme ushna da kusan shekara Shida ko bakwai but she likes her alot already yadda taganta very innocent, duk da ta taso acikin turawa amma take da nitsuwa da kunya sosai, ga aji da iya daukar wanka me classz uwa uba kyaun jiki da fuska na ushna din yana daya daga cikin abunda yafi burgeta ta.

anan suka karashe ranarsu gaba daya har yamma iyakaci sudan yi ciye ciye suyi sallah da hira da games din masu kudi irinsu chess da browls dake wajen.

ata fannin farees kuwa abuja ya nufa wajen arisha sam bai damu dayasan dawa dawa rihannan take tare ba dan iyakan saninshi da ita yasan dai bata da kawaye ko yan uwa akusa snn bata kuma san kowa ba kuma tundacan ma haka take rayuwarta

contact dinta daga iyayenta ne da yayanta da mijinta sai family members dinsu kamr su leelah da marida da sauran close cousins dinsu maza da mata na abuja zamfara da tharim vale wanda ma babu sa'anta acikinsu kodaya dan wasu sun girmeta wasu kuma ta girmesu they just vibe as family in aka hadu amma bayan mijinta bata shaku da kowa sosai a duniyr nan ba.

wajajen 6:30pm na yamma kafin subar wajen spa din saida ta tula ma ushna tsaraba na abubuwan cime cime da tarin hair nd beauty products da turaruka masu shegen tsada da aji snn tasaka drivernta yakaita har inda ya daukota tareda mata alkwarin cewa zata kai application din office gobe dan haka ushna ta shirya snn ta tabbata ta kasance cikin shirin interview akowani lkci aka kira.

ana kirar isha ushna ta dawo hotel da tsaraba niki niki ahannunta ko kula wancan gaye mai saka mata idon yau batay ba dan da alama shima baiwani ganeta ba tsabar wankuwa da tayi dan jikinta irin me daukar gyara innan ne already dama yana da kyansa amma yau da aka lailayeshi aka sake dirjeta bakaramin fidda fitinannen kyanta spa treats din nan yayi ba.

tana kaiwa dakin sallahn isha ta farayi kafin nan ta rage kayan jikinta tazo ta zauna ta ciro dukkan abubuwn da mrs rihannan ta siya matasu tana dada kalla tana murmushi me sanyi she tots the world out of her dan ta jima arayuwarta bata ci karo da mutum mei kirki da mutunci kmr rihanna ba, sun saba a kasar waje kowa yana minding business dnsa ne dan ko taro aka gayyace ka birthday ko wedings ders usually no free foods kaine dakazo din zaka biya kudin cin abinci..

abun da rihanna tay mata ya bata mamaki da nishadi saidai inta tuna wai cewa mr abdul ne take aura saitaji baqin ciki da takaici ya mamaye mata zuciyarta sosai.

tajima ahaka sai can wani tunani yazo mata cikin kwakwarlta atake tafarajin kamar fa zata iya samun wani clean hanya da zata tonawa mr abdul asiri inhar ta sake jiki ta shaku da matarsan nan sosai.

nannauyar ajiyan zuciya ne ya kwace mata ta jawo wani joter daga cikin troly inta tabude dede inda take rubuta to do list inta yake

acan ta kasa inda ta rubuta Abubuwan data lissafasu dayawa wnd zatay achieving a wata shidan nan a nigeria tarubuta wani sabon secret plan dinta na ceto rayuwar rihanna daga hannun mugu mayaudarin nan.

dagata dayan bangaren wajajen karfe 11 da rabi na safiya dede ayarin motocin sultan shamsan suka fara ratsawa acikin shararrun hanyoyin da suke shimfide agarin sokoto har zuwa yankinsu na tharim Vale.

CONTINUE....

#SURAYYAHMS
TALES OF THE WAZEERIS

THIS STORY IS NOT FREE

PAY 700 NAIRA FOR WASAP

2K TELEGRAM VIP GROUP

INTO
ACCT:9132352275
MOHD SURAYYA SULE
OPAY

EVIDENCE 08060712446

*AREWAPEN @SURAYYAHMS*

#SURAYYAHMS

https://www.arewapen.com/u/surayyahms

*11:*
wanda tun kafin akaiga isa cikin killataccen daular tasu zaka fahimci cewa wannan ba irin wajen da ake shigansa haka kawai bane Akwai wani irin nutsuwa da tsaruka da ke lullube da wurin har ila yau da shekaru aru aru suka ja

Manyan bishiyoyi da suka ja shekaru da dama ne sukai layi a gefen hanya. sai tsoffin katangunsu na dutse daya zagaye daular gabaki daya da aka ginashi tun tun zamanin kakanninsu na farko wato wazeeri tharim vale The first..

cikin nitsuwa shamsan yake zaune a bayan black armored suv din da ake jansa aciki wannan kyawawan kwayar Idanun san suna kallon waje ta cikin tinted glass din motar babu alamar komi atattre da yanayinsa dan ko kadan bai batama kansa lkci wjn tunanin mezaije gidan ya tarar ba.

Huge steel Gate har sau hudu aka bude musu kafin nan suka karaso ainihin harabar gidan nasu wanda tsawon shekarun daya dauka baizo nan ba ya lura wasu abubuwan sun canza amma wasu abubuwa na al'ada da tsafin uwarjinin ko kadan basu sauya ba.

ankara kawata daular tasu yay wani irin kyau gwanin ban sha'awa..

motocinsa suna tsayawa nan take guards din wajen suka mike tsaye cikin ynyin tsananin girmamawa bayi da domestic servant suka sunkuyar da kansu can kasa wasu kuma suka rusuna domin ko anan daular tharim Vale din ma sunriga sunsan matsayinsa na Sultan Shamsan Wazeeri

tabbatacen Jinin Uwarjini daya fito daga tsatson danta khaleefa na farko magajin daya fi kowani magaji tasiri da daraja a wnn zamanin.

koda motocin suka tsaya wani irin shiru wajen ya dauka har sai bayan kamr mintina 5 kafin nan shamsan ya sauko acikin yanayin kasaitacen nitsuwarsa dayariga ya bimishi jiki

Sanye yake cikin limited dark navy suit dinsa mai tsananin aji data masa wani irin kyau wanda ko yaushe babu wani hayaniya attatare dashi Sai dai duk inda yatsaya da akwai wani irin kasaitaccen izza da royal presence da yake mamaye wajen.

tunda ya fito ya tsaya gurds suka rufa masa baya sai tarukucen gaishe gaishe da ya fara cike wajen saidai ko kallo daya bai musu ba bare ya amsasu

ko karasowa gaban main mansion baiyi ba sukaji motsin takun private qurds da ga saman matattakala

nan ma kowa ya ja baya baya aka akara tsayawa wajen yasake daukar shiru kmr babu mai numfashi.

shugaba Imran waxeri ne dakansa ya bayyana cikin kayataccen sutura Wanda har yanzu shine kawai yake shugabantar kujerar iko na daular Tharim Vale.

Tun kafin ya karaso kasa wasu hadimai suka fito cikin sauri suna masu rufa masa baya

kallo daya dayay ma shamsan daga nesa saida yasaki wani kalar raunataccen murmushin bazata kuma me sanyi tare da tunowa da kyakwan hali da kuma fuskar babban yayansa marigayi shugaba khaleefa.
Chapter 15 · 0% Book details