← Book details Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 62

Sashe 18

Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

few private gurds ne agaba kafin nan Sultan Shamsan ya bayyana sanye cikin ash colour suit da long overcoat dinsa mai tsananin aji yabi ya toshe idonsa da wata smorking hot limited spy goggles me aji data masa mugun kyau kamr kasashi a kwano ka cinyeshi, as usual fuskarsan babu wani walwala yanayin nan nasa na tsananin nitsuwa da kasaita kawai ke tafe dashi

tun kafin ya karaso ya dan lura dasu yamusu kallo daya tun daga nesa snn ya dauke kansa calmly yayi kamr wanda tunda yazo duniya bai taba sanin wata me kama da leela arayuwarsa ba

Leelahr kuwa tana ganinsa cikin sakin murmushi ta daga red rose flowers din dake hannunta sama tana waving tanata sauri sauri shirin karasawa ta inda yaken saidai kafin tamotsa kafarta atake wasu daga cikin security suka matsa ta gabansu musmn ma da sukaga kawayenta sunata kokarin bude camerarsu zasu fara recording live stream

Leelah ta mugun hade rai tanajan tsaki ganin wani murjajjen security man da gurds sunwani tsaya agabanta..

cikin sharesu tasaka kai cikin izza da rigima tafara kokarin wucewa ta gefen daya security din tana cewa excuse me heyy move.

taga mutumin baiko motsa ba ya tsaya da bindiga yayi wani kyam acikin yanayin rashin fahimta ta dago girarta sama da gatsine tace did you just block me?

shiru securityn yayi

Nala dake gefenta ta karaso gaba da rawan kai tace kai malam ka bata hanya ta wuce mana kana bata mana lokci fa cos i don't even think you understand who you're trying to mess with.

Sanah ma ta karaso da sauri yadda takeji da wani irin Gen z energy na rawa akanta tana tauna cingam kas kas kas tace 'hellooo this is Leelah Wazeeri..are u guys aware of that?

security din ya kallesu nadan lokaci kadan kafin nan yace i am sorry ma'am nobody is allowed beyond this point.

Leelah ta saki wata yar dariyar raini ahnkli tace nobody fa kace?

saita nuna kanta da yatsa tana kif kifi da ido tace do you even know who i am?

kai tsaye yace mata "yes ma'am.

da dumbin mamaki Leelah ta dada gyara tsayuwarta tace okay

good. then moveeee

yace i'm sorry ma'am, i can't do that.

fuskar Nala daya cike da ruwan mamaki tace

are you serious right now?..

Sana tace ohh my god ure going to be sooo fired cos she's Sultan Shamsan's fiancée.

security din ya kallesu daga sama har kasa in calm professional tone yace my oders and instructions remain the same maam dolene fa kiyi hakuri

bakin Leelah abude ta dinga kallonsa cikin takaici da mamaki

can nala tace what instructions?waya saka dokan cewa bazamu wuce ba

yace 'no unauthorized access maam. as you all know this section is highly confidential.

atake leelah data gama harzuka ta nuna kanta cikin tsananin bacin rai tace me kake nufi kenan kai kasan da wakake magana kuwa ..havent u heard who i am..ko so kake na watsa maka mari

security din ya gyara tsayuwarsa yace..yes ma'am i know who u are but you cant go in am sorry..

nan take Nala da sana sukadan ja baya suna masu sakin baki, hmm this is insane.

Leelah da ranta ya riga yabaci da tsawa tace okay ni bazanyi cacar baki daku kananan kazamai jahilai ba just call your superiors

..right now.

daya gayen yace pleas there's no need for that maam bcoz the answr will still be no

bata kara jin takaici da zafin abun da ya furtan bama sai da tajuya can baya taga irin raini da gulmataccen kallon da kawayenta suke mata daga nesa

Da masifar haushi ta dauke kanta acikin ranta tace i can just believe this nonsense..

wayarta ta ciro ta fara danne danne zata kira gida koda zaa gwada kira mata ogan wajen asashi yazo

ta fara dialling lambar kakarta kenan dai-dai lokacin ne kuma taga tawagar private gurds din Shamsan suna kan kkrin karasowa tanan inda take tsaye.

tana jin motsinsu nan da nan tadada gyara tsayuwarta, Nala da Sana ma suka matso da rawan jiki suka fara gyara camera na iphon dinsu zasu fara daukar komi live.

Shamsan yana fitowa

sanyin qamshinsa da kasaitarsa ta mamaye wajen gaba daya duk suka saki baki suka tsaya a muce sunata kallonsa kamr mayu

Leelah data dauke numfashinta da kyar ta iya saukarwa atake ta manta cewa tana da aji, dan nan da nan ta fara daga masa hannu kmr irin football fans din nan sunga ronaldo a aiport yazo wucewa da rawan jiki da dan dan karfi ta fara kwala masa kira dan yaganta

..Shamsan...shamsan

baiso ya juyo ba amma daya tuna cewa inya sharetan hala zatayi tsammanin kodan baiganta bane sai ya fasa ya dago idanunsa yasauke su a kansu

for some seconds taga ya kare musu kallo, ya gansu sarai ya kuma ga tarukucen flowers da duka childish gifts din, da kawayenta data kwaso.

suna hade ido da Leelahn sai ya kau da kansa yy kamr baitaba ganinta ba ya cigaba da tafiyarsa kai tsaye

babu shiri Leelah ta tsaya cak walwalan dake kan fuskrta atake shima yamutu tay wal wal da idonta cikin rashin yarda da karfi tace wait....am u just dreaming?

ta sake kwalla masa kira taga ko kallon inda suke bai sake yi ba.

atake taji giwarta ya wani irin sacewa dan batasan cewa duk walakancin shamsan da ake fada a family yakai har ya kalleta ido da ido ayayinda wasu banzayen security men suke walakntata snn ya dauke kansa ya wuce yashareta ba

security din dake ta gabansu ya dan matsa gefenta kadan ya fara nuna musu hanyar fita waje tadayan sashen yana cewa...thank you for your cooperation ma'am.

Nala da Sana atake suka kalli juna da wani irin mamaki ita kuma Leelah ta tsaya rike da red flowers din tana jin kamar kasa ta tsage ta shige ciki.

lokaci guda kuma wasu security din suka matsa wajen su Nala da Sanah kamr da wasa sukaga an fara security stalk checking insu da questions kan kace wani abu har ankarbe wayoyinsu da suka fara recording din fitowar shamsan din daga hannunsu kai tsaye aka goge komi da suka fara dauka

dukansu suka rude sunata masifa kowa tanaji dakanta daga me ihu tana cewa hey dont touch my phone, did u knw who my father is, my mum will surely sue you , sai me cewa what are you doing? ihunsu kawai ke tashi awajen. gaba daya ran nepo babies din nan ya balain baci ganin duk da kudi da aji da matsayin iyayen su kasar nan wai anzo nan an walakntsu

Leelah ta dago kai tanata kallon bayan Shamsan da dumbin mamakin yadda yayi kamr bai taɓa ganin wata me kama da ita ma arayuwarsa ba

agefenta kuma ganan kawayenta suna debar walakanci kanta taji ya dau zafi yana shirin kamawa da wuta

jikinta rawa yafarayi tsabar bacin rai bata ma san sanda dukkan flower bouquet da gift din dake hannunta ya karkata ya xube akasa ba

gabaki daya fuskarta sauya yay jaaaaa kmr zai kama da wuta

Nala da Sana suka tsaya sunata kallon wayoyinsu a hannun security har saida aka tabbata babu wano footage din shamsan waxeeri ko na javeed mufasa aciki kafin nan aka maido musu dashi

a masifar zuciye suka bar wajen sunata mita daga bisani leelah tabi bayansu suka fito waje dukansu suna huciiii sunyi zuru zuru da ido kmr fararen kajin agric da sukayi flying sama snn suka fado

worst ma shine kafin su karaso harabar wajen haka suka samu wai har shamsan din ma yashiga tawagar convoy na motocinsa sunbar filin airport din gaba daya.

Leelah da kawayenta suka tsaya turus awaje fuskrsu kmr na wanda zasu fashe da kuka ga kuma tsananin jin kunya da takaicin yadda security suke ta satar kallonsu da wani irin ido kamr anga yan maula.

dagata bangaren Shamsan kuwa tun daya xauna acikin motar baiwani huta ba yafara amsa wayoyi acikin nutsuwa ko sau daya bai tuna abunda ya faru a airport din ba dan awajensa shirmen da leelah takeyi aknsa wani abune da bai ma cancanci ya fara ɓata lokacinsa akai ba

kai tsaye kyafaffun convoy na motocinsa suka karasa dashi har izuwa cikin katafaren penthouse dinsa na VI extension.

suna isa kuwa bai tsaya ko'ina ba yawuce sama can sashensa bayan dan lokaci sai ya sake fitowa acikin wani sabon dressing daga ash blazer suit din daya dawo dashi zuwa wani irin elegant cooperate charcoal suit mai tsananin aji da tsada.

daga nan home office dinsa ya nufa acikin mintuna kadan aka sada shi da video conference meeting dinsa mai matukar muhimmanci tareda wasu international partners dinsa daga kasashe daban daban.

meeting din ya dauki tsawon lokaci ko ma ince awanni masu tsawo dan anan suka tattauna akan foreign investement da files da

wasu new reports da kuma babban project din dake gabansu.

muryarsa mai cike da sanyin authority da nitsuwa ne kawai ya cike dakin, sai da har yagama meeting din snn yafito magensa husna datay fresh taji madara tay bulbul tana jiyo qamshinsa taxo da gudu ta wani mannu da kafarsa sosai.

acikin kyabe baki yasaka hannunsa anitse ya dauketa cak sann yasata ajikinshi suka fito waje atare har cikin motarsa ya ajeta snn suka nufi masjid dan yay sallar axahr dan daga nan ma wani meeting din zaije yayi a eko atlantic kafin nan ya koma gida dan yau acan yakeso ya kwana.

ata bangaren Leelah kuwa tun bayan fitar Shamsan daga airport din yanayinta dana kawayenta ya sauya gaba daya but bcos they are so shallow minded and superficial sai basu wani damu da emotional state inta ba

bacin ran da shamsan ya kumtsu musu na gushewa kawai nala tafara ma leelah dariya tana tsokanatarta like girl..i wasnt expecting that, ace duk ajinkin nan kike ma namiji rawan jiki kuma harma ya share ki

sana dake danne nata dariyar tace yooo but that was embarrassing i mean...he literally turn nd saw us and then he ignored all of us, not even a hi awwww leela kin tabbata gayen nan yasan da ke kuwa ba karya kawai kike kan sharara mana ba

tana fadin haka suka sake dariya.
Chapter 18 · 0% Book details