← Book details Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 62

Sashe 13

Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lokacin shamsan har ya fito ya sauko kasa Yana zaune daf hajiya ummu salma dake kan kallonsa cikin so da kaunar datake ma jininta suna tattauna tafyarsa tharim vale din sama sama

she just can't get enough of him sabida yadda yake mugun kama da babban yayanta wato shugaba khaleefa waxeri msmn ma a hali da nagarta shiyasa duk tulin jan aji da miskilancin sa tana iya daga masa kafa duk da uban masifa da da iya takurin da Allah ya zuba mata.

suna zaunen leelah da kitchen servants suka fara kawo abinci, sai wani irin basu directions take wanda tun dataga shamsan anan azaune a falon komi na jikin ta yarasa nitsuwarsa dan butterflies kawai takeji all over her head nd stomach duk dama bata iya kallonshi cikin ido ba.

daurewa tay takama ajinta ta dan tsime sbd gani take kamar darajar mace kenan musmn ma agabn sultan taja ajinta sosai...

with him in the palor atmosphern wajen tuni ya sauya gabaki daya kusan kowa ahnkli yake bi da kansa

kowa kuma yaxo sai ya gaisheshi amma bai amsa uban kowa ba.

tsabar jan aji haka taki ta gaishesa ta karaso kusa dashi ta zauna like she have already crown herself as his life partner already.

duk yadda grandma inta tamata ido bata lura ba har dai suka je kan dinning domin cin abinci..

sai yaba leelahn takey tana cewa ai itace ta shiga kitchen ta tsata masa abinci specially for him lkcin kusan kowa ya fito an zauna rihanna ne kawai bata sauko kasa ba hjy ummu salma tayi tambaya akan hakan amma cikinsu babu wanda ya amsata dan kowa yana ji dakansa

leelah ta mike tsaye sai kuma tarasa ta ina ake fara serving abinci tana fara debawa da spoon kuwa ta zubar da rabin abincin akasa gata da son jan tsaki da mita, ganin yadda ta zubar da komi ajikin ta da kasan floor yasaka shamsan ya daure ya debi abincin dake ta gabansa dan kadan kamr wanda jariri ne xaici tunma kafin tazo kansa ta watsa masa abinci tasakashi ya bata lokaci.

farees baice uffan ba face hade furkansa dayay kamar hadarin kaji, hjy ummu salma dake kallon shirmen da leelah takey atake tabi tahade rai duk dama shamsan din bawani kallonsu yakeyi ba.

da takaici leelah ta haura sama da sauri dantaje ta sauya kaya

after few min wajen ya dau shiru shamsan yanakai abincin cikin bakinsa ya dauki table towel ya tofar dashi quietly aciki snn ya dauki ruwan sanyi ya sha ya miƙe tsaye yace "zai tafi..takaici ya cika kwayar idanun hajiya ummu salman amma ta daure tana kakalo murmushi...

"har ka koshi kenan? da rashin jin dadi a muryanta tace but u havent even eaten much ranka shi dade kasan dai koya takeyi sai anyi hakuri da ita..

baice komi ba ya gama gyara zaman hadaden deep blue suit dinsa data masa mayen kyau servant din dake tsaye awajen yay ma alaman takira masa rihanna..

da sauri ta haura can sama after like 3 mint sai ga ta tadawo tace mishi rihannan tana zuwa ynx.

nan take farees ya aje spoon dinsa ya naɗe hannu a kirji yanakan jira yaga ko rihannan dagske zata sauko tsabar bata da zucya

dan dazu yana waya a dakinsa da Arisha hajya umma salma ta kirashi tana tambayar sa koyasan dalilin dayasa rihanna ta sauko daga sashen shamsan tana rusa kuka, dan dole ya katse wayar yaje ya sameta anan ne take gaya masa abunda ya faru sosai yasha mamakin abunda shamsan yay mata kwarai dagaske

ransa ya harzuka ya balain baci har yakasa boyuwa yana jin wani irin tsananin haushi da takaicin girman kai irin na shamsan..

wato irin shi yafi karfin yaje sama innan ya rarrashe yar uwarsa gara yasaka akira masa ita ta fito upon all the pain nd humiliation he causes for her harda kira mata security ashashensa

after few min kuwa sai gata ta fito tanakan saukowa ahnkli ta dan yafa karamin mayafi daya kusan rufe jan da idonta yay tsabar taci kuka..

tana karasowa ta taho da sanyin jiki har zata rusuna ya saka hannu yadagata sama tareda sauke mata kallo daya atakaice, dan kumburin da idonta suka yin ya isa ya gaya masa cewa tay kuka sosai.

jawota yay kurkusa da shi cikin wuyarshi yace meya sameki,why is ur eyes red?

dago kai tay zata amsa yace "ya isa..i will always give u a reason to cry if u dont quit being silly.

farees dake jin kansa na tafasa ya dan karkatar da kansa gefe kadan koda zaiji me suke cewa hjiy ummu salma kuwa Allah Allah take leelah ta sauko kafin shamsan ya gama mgna da rihanna dan so take su fice agidan atare

rihanna ta dan marairace fuskarta da shagbwa ahnkli tace.."i am soryy..

baice komi ba Sai ya kai hannu yagyara mata xmn mayafin da ya dan zame daga kanta Kafin nan ya dan sunkuyo kadan ya sumbaci goshinta lovingly

lokacin ne idanunsa suka hade dana farees wanda tsabr ya kumbura da fushi saida fuskrsa yay wani irin jaa shikansa baisan sanda yasoma sakin wani zazfr huci daga cikin kirjinsa ba.

Domin a cikin kallon da shamsan din yake masa akwai wani kalar silent hatred,warning da wani iriin Cold Direct disgust.

Farees ya ji kamar ana kan danne masa kirji da dutse da aka cirosu daga wuta..

bai iya numfashi dakyau ba face saida Shamsan din ya janye idanunsa anasa ahnki yana kallonsu yadan taba kumatunta kadan da wani irin dark humour yace Be a good gurl mmm i will see u when i am back. tagyada mishi kai da shagwaba tace Yes your highness..

daga nan ya juya gaba daya yakama hanyar ficewa waje rihanna ta rakashi har kofa yana wucewa qamshin turarensa mai sanyi yana binshi a baya.

Cikin mintuna kalilan aka bude masa mota nan take convoy dinsa na black armored suka fice daga cikin harabar mansion din

tana juyawa ta hade ido caraf da farees daga bayanta suka tsaya suna kallon juna ganin yadda ransa yake a mugun bace yasaka batace masa uffan ba ta janye jiki ta shige cikin gidan lkcin babu kowa a dinning da alaman takaicin leelah yasaka hajy ummu salma ta haura can sama masifa danga nan abinci ko tabawar kirki ba ayi ba

dakinta direct ta wuce ko zama batay ba taji anbude kofartan da karfi da wani irin fushi farees yashigo suna hade ido yace ashe dama ke babbn munafuka ce bansani ba?

bata kulashi ba ta nemi waje ta zauna ya hargitso kanta azuciye yace keeee magana nake miki i said what was the meaning of that.

tace.. meaning of what? cant u see i am stress out ni dan Allah karka min ihu akaina nide

muryansa harna rawa rawa yace ohh nine ma nake miki ihu akai, ko nine nake saka miki stress din ryt? anan kikazo kika zauna kina kuka kamr ranki zai fita sabida gayen nan ya walaknt ki amma daga ya kiraki yuu kin debi jiki kinje waya baki izinin saukowa??

cikin katsesa tace excuse me, dama me kakeso nayi

da tsawa yace i expect u to stand on yr ground nd stop worshiping him like a GOD
..ke baki da zuciyane..dama can nasha gaya miki irin abunda kike yi akaina agabansa kenan yasaka har yake rainani..ke kika bashi fuske yake min duk abunda yake min dan haka dont u dare act like you care about me or make me feel like taimakona kikeyi dan banga alaman haka ba..shi wayene da bazaki iya nuna masa fushinki ba ehhh, he call security on u, irin shi yafi karfin yazo inda kike ya baki hakuri kece wawiya marar zuciya zakije nd what the hell was he telling you down der??...

idanunta sosai ya ciko da ruwan hawaye ta mike tsaye tace dont talk abt my brother like dis, wanda ya kawo ka gidan nan ma wallh bai isa ta rainashi ba snn abunda yagaya min ba matsalar ka bane u just need to focus on being a real man. ai ba karya yake fada akanka ba, idan mutunci da darajarka kakeso agani agidan nan step up nd be a man go get a real job nd start paying my bills.

wani irin tasss ya dauketa da mari muryansa har na karkaryewa yace ohh haka kikace? mani kike gaya ma wannan maganan? kamar zai kuka yace fine rihanna
..naji bani da kudin da zan kula dake but you knw what kudi dana baki jiya akan kije spa ki dawomin dashi yanxun nan shi yayan naki daya fini arziki da daraja ya baki..

hawayenta na zuba taja tsaki da bacin rai ta daga wayarta tay dialing numbr shamsan for few min aka dauka ta share hawayenta ahnkli cikin sanyin murya tace yaya na..na manta ban gaya maka ba i wanted to go for a spa date day with a friend kaina yana dan min ciwo zanje na huta..

okay kawai yace mata snn ta katse wayar tana direwa daga kunnenta ko scnds biyar mai kyau basuyi ba taga ya tura mata isashen kudi.

farees dake tsaye da jajeyen idonsa ya fara ɓari kar kar kar cos what d fuck just happen.

tamasa kallo sama da kasa tace you seee a real man just send me the money i needed, nd am returning urs..

a zuciye ta juya zata fita yay sauri yafara binta kamr me ciwon hauka rihannaaaa rihanna..come back here wallh karki sake ki dawo min da kudin nan..ke kenan ba a isa miki fada ba saiki hau dokin zuciya rihanna

bata ko kulashi ba taje dayan sashen ta turo masa kudinsa da ya bata jiyan wanda baifi milliyan biyar ba amma duk minti daya sai ya sako batun kudinsa a cikin magana dama kuma abunda yasaka bata fiye son tambayarsa kudi ba kenan tunda sukayi aure ita takeyin komi makanta da kudinta bako asinshi aciki

ranar gabaki daya bakaramin drama sukayi dashi ba kafin nan suka dawo daidai dakyar

saidai sosai hanklinsa ya fara tashi dayaga rihanna tafara kawo masa batun bori da gori acikin lamarin rayuwarsa.
Chapter 13 · 0% Book details