← Book details Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 62

Sashe 27

Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dagata dayan bangaren kuwa sosai gidan nasu ya dau shiru dake tun safe leelah ta wuce kasar Ibiza da kawayenta akan zasuyi hutun sati biyu masu kyau acan kafin nan su dawo

har ta tafi kuwa bata iya gaya ma kakarta abunda shamsan ya mata ba badon komi ba saidai sabuwar feelings meyawa data faraji akansa.

rihanna tana dawowa gidan kusan babu irin kirar da batay ma layin ushna ba amma har yanxu jinshi take akashe har taxo ta rasa wani irin tunani ma zatayi

bacci kawai ta shara agidan bayan ta farka tay wanka tay sallah taci abnci tana jawo wayarta kuwa taga email ancire mata 20k dollars daga cikin acct dinta..

duba jakarta da zatay kuwa sai kawai taga babu card inta tun anan jikinta ya bata cewa farees ne ajiyr zuciya kawai ta sauke kasa tare da yin tgumi

tafi minti ashirin ahaka can kuma saiga ruwan hawaye masu tsanann sanyi sun fara zubo mata bakuma ɓarnan kudin dayake mata takewa hawaye ba

kawai tuna yadda ta aminta dashi ne tun suna yara da yadda ta so shi tsakani da Allah amma haryanxu bata samu kwatankwacin irin wann soyayya da darajawar daga wajen sa ba. ta tuna dacan har dena magana da yayanta tay for month sbd ya nuna baison auren akan wann dalili

gashi just few years with him amma yaki ya nemi kwararen aikin yi baya kuma mata komi genuinely da kudinsa a matsayinta na matarsa sai idan wani abu zaiy gaining daga wajenta.

sumtime she just feel like she is in this marriage mainly to sponsor his lifestyles tun daga kan kayan sawa, motoci, kudin kashewa, his travels, kai ko under wear bai iya sawa makansa face saida kudinta abun yana mugun ci mata rai bana wasa ba

when is he eva going to be a good husband to her kodan ma idon yayanta, da mutanen gidan kmrsu leelah da suke kan mata kallon shashasha.

da wannan tunanin ta share hawayenta dayaki tsayawa

kai tsaye ta mike tsaye ta isa gaban wani hadadden ottoman table snn tajawo kujera ta dan zauna ta bude p.c dinta tay wasu danne danne kafin nan ta jawo wayarta shima tahau kiran personal manager na acct dinta tace mishi tanada bukatar rage debit limit na acct inta sbida tasan inhar ta sauya password wani sabon tashin hanklin ne zai taso tsakaninsu and she doesnt want to loose her baby again..

atunaninta idan tay hakan hala zai saka shi yafara maida hanklinsa akan aikin datake kkrin sama mashi tunda har Allah yasaka shidin yayi intervw dinsa lafiya ba kamar ushna da bata da wani dama yanxu ba...

CONTINUE....

#SURAYYAHMS
TALES OF THE WAZEERIS

THIS STORY IS NOT FREE

PAY 700 NAIRA FOR WASAP

2K TELEGRAM VIP GROUP

INTO
ACCT:9132352275
MOHD SURAYYA SULE
OPAY

EVIDENCE 08060712446

*AREWAPEN @SURAYYAHMS*

#SURAYYAHMS

https://www.arewapen.com/u/surayyahms

*18:*
Haka ta wuni da abun aranta musmn ma da fareess ya xuxxuba mata karyan cewa da akwai lefin ushna ackn batun kayarda ita da akayi, if its true ushna bata yi yunkirin amsa koda question daya na tasan bazata kara iya tunkarar yayanta da wani batun neman alfarma akanta ba.

tsabar bataji dadin hakan ba kamr wacce bata da lafiya haka ta fito tazauna abakin ruwa awaje, sai can da yamma kafin nan ta sake gwada number ushna jinshi a kashe har yanxu yasaka sai ta hakura kawai da tunanin ko rabuwarsu kenan na har abada

abun dai bai mata dadi aranta ba amma haka tay kkri ta barshi.

dagata fannin ushna kuwa tunda tay bacci mai masifar nauyi ta farka taji zuciyarta fayau dan kota kan wayrtan batabi ba ta cire kayanta ta nufi bathrom tay wanka ta fito da alwala ajikinta tazo tay sallahn azhr tana idarwa tafara yan shafe shafenta tana bin koinanta tsilla tsilla saida ta tabbata komi ya mata snn ta kara gyara gashinta shima

tunda ta fahimce cewa baccin datay yasaka abun ya lafa mata sai sam taki tabari tinanin komi ya dawo mata

tana gama tsantsale jikinta da mayuka da ka turaruka masu sanyin qamshi nan ta gabatar da sallan asr snn ta shirya ta dauki card inta taje kasa taci abinci bata dawo dakin ba sai wajejen 5;30pm na yamma tana kunna wayarta kuwa saiga nan kirar oganta na dubai din ya shigo

sosai gabanta ya fadi cikin tattaro makanta nitsuwa tadaga wayar da sanyin murya tay sallama sann tace Good evening sir...

dagata dayan bangare yace good evening Mss Ushna How are you doing?

tace Alhamdulillah sir.

kai tsaye yace Good
So how far abt ur own placement kin samu wajen da xaki faran kuwa

zcyarta taji yakara tsinkewa saida ta gyara tsayuwarta kafin nan tace Sir...I'm still working on it.

da wani irin mamaki a muryansa yace what??
you are Still working on it please what exactly does that mean??

yanayin yadda yay mganan yasaka ta hadiye yawu da dar dar aranta tace sir Ban gama securing placement din bane sir.

dan shiru yay kafin nan yace i hope you realize yo have only 3 days left kina da kwana uku ne kacal fa kafin deadline nd to be honest with you you're the only one delaying the inevitable. Dukkan students din da suke karkashin wnn batch din sunkusa kmmala komai nasu kowa nan da kwana uku zai fara aiki nd u still don't have a placement?

cikin lumshe ido da budewa tay tsamm jin wani irin fargaba da dumbin rauni yana neman ya rufeta atake

muryanta kasa kasa tace sir in sha Allah zan...

cikin katseta da rashin jin dadi a muryansa yace I'll give you a maximum of 48hours kawai.

idanunta ta gwalo waje da sauri kamar zatay kuka tace "48 hours sir?

bai kulata ba cikin muryarsa da bata dauke da wasa ko kadan yace idan har baki samu placement ba gaskiya ni zan fara processing withdrawal dinki ne ma daga wannan program din cos it seem like ure not ready kuma baki daraja damar da Allah ya baki ba u have 48rs nd dat it.

wani irin bugawa da karfi zuciyarta yayi tana jin kmr andanne mata wani abu a kirji, murynta asanyaye sosai tace apologise sir,..in sha Allah i will get back to u within 48hrs i promise

baice mata komi ya katse wayar abunshi

tsayuwar cak tay awajen kmr andasata harna wasu yan dakiku can kafin nan ta zauna akan gadonta tanata kallon screen din wayar babu ko kiftawa jin dakin da duniyan gaba daya ya mata fadi.

sanin cewa bata da wani sauran lokacin batawa nan take ta hadiye duk wani abu mai daci dataji ya mugun tsaya mata a makoshi

cikin sauri tabude laptop dinta takoma kan search engine nan take ta fara shiga real estate websites daban daban tana dubawa

wani bin bata ma tsayawa duba kalar companyn sai kaga ta tura application

abunda tajima tanayi kenan har saida aka kira sallahn magrib tay ta jira isha shima tayishi atsanake

bayan mintuna awa daya zuwa awa biyu bata samu ko amsa daya ba dan wasu ma requirements dinsu daban ne wasu kuma internship dinsu ya cika tun watannim baya.

har wajejen karfe daya na dare idanunta suna bude duk sun fara ja saboda tsabar kallon screen amma ji take kamar bataci ka zama ba dan duk lokacin da ta tuna 48 hours din nan sai taji gabanta ya fadi.

tsabar hankalinta ya tashi har tunanin kirar rihana awaya tayi amma kuma tsoron yadda shamsan yace tabar wajen batare da ta tsaya ta mata bayani ba yasaka taji wahalar kirarta dan ko ta kira batasan wani bayani zata mata ynxu ba

akarona farko tun zuwan ta lagos data kasa iya samun bacci kenan dan ba rasa gurbin aikin bane ma babban damuwatta yadda zata je gidansu ta fayyace maganr ne babban matsala sbd yadda ta nuna musu cewa already aikin takeyi anan

dan tasan dai dolene ta saka mahaifyarta jin kunya snn mahaifinta kuma dama abunda yake nema kenan yayi mata auren dole tun ba ace yaji cewa wai karya tay musu tazo lagos din nan kuma ta zauna a hotel da sunan cewa tasamu wajen aiki bayan bata samu ba.

sosai kanta ya rikirkice baqin ciki da damuwa duk sai ta rasa wanne ne ma zata faraji aranta guda daya dan bayan uban rashin sa'a da karin damuwa bataga wani abunda tazo taci karo dashi a nigeriar nan ba.

gashi bisa ga dukkan Alamu zata iya rasa wann program din datake ganin shine kawai zai iya sauya mata rayuwarta na har abada.

dagata bangaren shamsan kuwa bayan komi ya lafa schedules dinsa na ranar kawai yay attending sbd yaune aka kawo masa replacement na mr jafar daga U.S yazo aka masa interview snn yafara musu professional sketches da wasu primary roles da aka bashi za'ayi biyasa kudi me yawan dayaci uban wanda client din mr jafar din ya rubuta.

ranar haka gulman abun ya dinga zagaye acikin office din musmmn ma a bakin senior officers da directors da suke mugun shiri da mr yusuf, wasu sosai suka ji masa baqin ciki da har sultan shamsan dakansa yasauke dan uwansa jafar akan wannan babban harka snn ya kuma dora wani wanda yafishi akan lokaci

wasu tuni sukayi waya dashi sukahau gaya masa duk ababen dake faruwa mr tijjani was oll over the place sai dada tonawa kansa asiri yake da vain talks acikin mutane yana cewa ai dagangan yayi failing din ushna sbida itace ta asalin jawowa yan uwansa yarbawa asara har suka rasa wnn babban damar.

kai har wanda basu san meyafaru awajen intevw din ushna ba saida sukaji asalin dalilinsa a rade rade.

Dakyar maganan yay shiru kowa ya cigaba da abunda ke gabansa sultan shamsan bai sake kiran kowa ba iya abunda ke gabansa kawai yayi ana tashi a aiki can da yamma yawuce pent house dinsa dan ya huta tare da yar magensa husna sai baixo gidansun ba.

daga ta fannin farees ma bai dawo gidan ba sai can can tsakiyar dare saboda yasan yariga ya cire kudaden rihanna in few millions ya tura a acct dinsa baima son yazo dakin yasamu idonta a bude bare suyi wata yar hayaniya.

yana dawowa shima dakinsa ya nufa da asubh kuma yasake zillewa ya fice agidan abunsa..
Chapter 27 · 0% Book details