← Book details Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 62

Sashe 16

Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ahnkli yake tahowa kmr zaa karba masa tafiyar tsabar ruwan mulki da iko dake yawo ajinin sa duk dama kana ganinsa kasan Shekaru sun dan ja dan da Akwai farin furfura dariga ya fito masa akn sajensa da nauyin jiki tareda gajiyar shekaru a fuskarsa da idanunsa

saidai har yanzu yana dauke ne da wannan karfin izza da daraja da kuma tsarin addini da adalci da shiya sanya har yau mutanen su na tharim vale basu ji wani kewan marigayi shugaba khaleefa sosai ajikinsu ba

daga gefensa kuma matarsace wato hajiya Ummu Zulaiha duk da son gayunta Ita ma shekarun nata sun danja bakamar lokacin da suke mugun ji da kansu ba.

she look more calmer nd royal sbd tariga tasamu haihuwar ɗa namijin datake mugun muradi aranta duk dama ance bazata sake iya haihuwa ba har abada. babban yarta marida waxeeri datake kusan sa'a da shamsan tayi aure amma kuma dan autar ta suleiman waxeeri tuni suka turashi kasar waje shima dan yay karatu me nisa kafin nan shima yadawo cikin tharim vale tunda kujerar shugabanci da iko na hannunsu ne, har yanzu da akwai wannan sanyin izza da girman kai da kuma baqin cikin dake yawo ajininta

tsawon shekarun nan takasa ta tsare ko wani lungu da sako dake gidan tana lura da komi haryau kuma idanunta yanaga kan ummu bilqees ne da yanzu haka itama tanada yaranta maza har biyu Aliyu da kamal da mace guda daya me suna jannat kuma dukkanin yaran nasu sun girma duk dama anjima ba asake haihuwa a zuriar ba badon komi ba saidan hada kansu da nana atiqa dasukayi tana tayasu yaqar junansu da asiri.

kusan atare shugaba imran da matarsan suke karasowa

A nitse shamsan ya karasa gabansu snn yafara gaidasu cikin girmamawa

Shugaba Imran ya dafa kafadarsa ahnkli yana murmushi yace sultan ka girma fiye da yadda nake zato.

takaitaccen sakin fuska ya bayyana ayanayin shamsan din duk dama baice komi ba

Ummu Zulaiha dage gefe tana murmushi tafara saka masa albarka tana masa maraba tareda nuna farin cikinta naganin yadda yazama cikakkn namiji kmr kakan sa marigayi shugaba khaleefa

dakema yawanci maganarsa bamai tsayi bane dan haka suka jagorance shi cikin fadar iko inda akagama shirya masa kyakkwan tarba....

bayan kamar awa guda dagata dayan bangaren Nana Atiqa ne a tsaye cikin yanayin nutsuwa wanda haryau Itace mace mafi kusanci kuma amintaccyr yar uwa ga Uwarjini bazata ma iya irga yawn shekarun data dauka tana hidima a karkashinta ba

sanye take cikin manyan kaya masa mutunci ta lullume jikinta da lafaya me aji da tsada duk dama yawan Shekaru da nauyin jiki ya nuna akan fuskarta sosai daya nuna alaman ta tsufa.

Gashinta ya fara yin furfura
Amma har yanzu idan ta tsaya zaka ga karfin hali da tsantsar biyayya a tattare da ita

A hankali ta bude daya daga cikin manyan kofofin babban shashen Sannan ta sunkuyar da kai da ladabi tasanar da uwarjini isowar shamsan.

shiru uwarjini tay sai cahn muryarta mai sanyi dake da cike da iko yafito ahnkli tace "Na sani..Atiqa.. idan ya gama hutuwar a turominshi nan

Nana Atiqa takara sunkuyar da kanta snn ta amsa, daga nan bata sake cewa uffan ba domin tulin bayan shekarun nan Har yanzu akwai wani abu game da Uwarjini da yake saka wa mutane sukasa sabawa da wasu yanayinta musmn ma yadda take sanin abu kafin ma ya faru.

ko ita datake kusa da ita bata iya mata shishigi kuma Ba wai dan saboda matsayinta na uwarjinin zuriar kadai ba Saidan gani da sukayi kmar Lokaci ma baya aiki a kanta.

Mutanen da suka san ta shekaru talatin da suka wuce har yanzu suna ganin ta da fuska daya zak da mutanen da suka san ta shekaru ashirin da suka wuce abaya. she look almost d same all the time.

gabaki daya kamanninta baya sauyawa snn bata tsufewa kamr su she is very very old but bata lalace ko ta yamushe ba kmr ace me shekaru 70 ne amma kagan sa atsaye kuma tsaf kamar me shekara 50.

Duk wanda suke lura da hakan sukan yi shirune su kame bakinsu domin anan Tharim Vale akwai wasu tambayoyi da mutane basa son yawan furtawa musm ma inya shafi uwarjini.

bayan ficewar nana Atiqa bada jimawa ba shugaba imran ya sako private gurds suka rufa ma shamsan baya har ixuwa sashen uwarjini.

Suna kaiwa kofar xauren iko dukansu suka tsaya daga bakin kofa ayayinda shamsan yakarasa ciki shikadai acikin nitsuwa.

wani irin shiri wajen ya dauka gefensa da gefensa manyan lanterns masu aji ne suke manne da jikin bango da wani kayataccen sanyin A.C daya dulmuya da qamshin wasu turarikan gargajiya mai hade da original frankinchence da aka jima sosai ana amfani dasu acikin daular.

dake ba kowa yake da ikon shigowa nan ba kai tsaye ya tsinci kansa acikin babbn zaurenta na iko

da sanyin sallama ya kutso kansa ciki ayayinda already uwarjini dake zaune akan kujera ta kure masa idanu tun bai gama karasowa ba

killatatun kaya masu daraja ne ajikinta flowing robe inta mai yelwa da tsayi koinanta yana rufe kirif face kan fuskrta, hannunta da kafafunta da sukasha kwlyr sarkan zinariya.

Har yanzu tana dauke da irin kallon nan nata da ke sanya mutum yaji kamar tana ganin abunda yake boyewa a cikin zuciyarsa

Shamsan bai tsaya kallonta ba Kai tsaye ya karaso gaba sann yasauka kasa bisa kan gwiwowinsa cikin tsananin girmamawa ya sunkuyar dakansa kasa muryansa na fita ahnkli yace.. ranki shi dade
..ina fatan na sameki lafiya...

Shiru tay na wasu sakanni Kwayar idanunta suna tsaye tsarr akansa tanadada kallon yadda ya zama cikakken namiji Mai sanyin iko, jinin mulki kuma kasaita mai tasiri Kuma duk da hakan da alaman ya san matsayinsa a gabanta.

Ahnkali ta amsa shi da gamsuwa da darajawa Daga nan ta daga hannu kadan da Alamar ya mike

A nitse ya mike tsaye Sai dai bai zauna ba har sai data nuna masa kujera snn ya zauna cikin nutsuwa ruwan Idanunsa suna kallon kasa

tadau lkci tana lura dashi badan komi ba sai dan wani irin nutsuwa da alfahari datakeji a ranta datagansa

sanin cewa shi din pure jininta ne na farko kuma jika ɗa namiji na farko ga babban danta shugaba Khaleefa wanda babu wanda zai kalleshi yakasa gane hkn ayanayinsa.

Ahnkali tace Na dade ina bibiyar rayuwarka..

atakaice tafara gaya masa abubuwa da yafaffaru a tharim vale din cikin tsari da kuma killace inda tasan bai kamata yaji ba

shiru ya yi yana saurarenta cikin nutsuwa ba tare da ya dora niyyar katseta ba.

Uwarjini ta dan jingina bayanta jikin kujerar da take kai sannan tace alhamdullh Na ga yadda ka fadada harkokin gidaje da filaye a yankuna da kasashe daban daban snn na ga yadda ka tsaya da kafafunka ba tare da ka dogara da sunanmu ko na iyayenka ba naga yadda kake tafiyar da dukiyarka cikin hikima...nasan duk inda khaleefa yake zaiyi alfahari dakai sosai..

batare da ya dago kansa ba yace.."Alhamdulillah...

Kallonsa tayi na wasu sakanni kafin nan tace,Mutane daga yankin dala suna maganarka, Marayu Mata da matasa daka taimaka hakama talakawan da suka samu mafaka, dik Kada ka dauka bana jin komai..

...tabbas...Dukiyar da bata anfani mutane ba bata da amfani. Mulkin da bai anfani mutane ba shima baida anfani. nagode ma ruhi me tsarki dayasaka ka fahimci wannan sosai.

jin tafara kawo masa batun wai ruhi ne yabashi saa yasaka yay shiru baice mata uffan ba.

daga bisani cikin sauke ajiyan xuciya tace Sai dai ba wannan kadai yasa aka kirawo ka nan ba da akwai batun Zamkora dan yarjejeniyarmu yana nan yadda yake, nasan kasauke duk wani nauyin da aka dora maka Amma hakan baya nufin zamu zuba ido bane aja lokci har jinin zuria yakai matsayin da zai fara zubewa ata dalilin wani kaskantacen yarjejeniya.

Anitse ya amsata da Na fahimta...

muryanta kasa kasa tace Zamkora bayine da suka fito daga jinin mu Hakan kuma ba zai canza ba. Ina so kafara shirin cika mana wannan yarjejeniyar tunda yanxu ka girma.. Siyasa tana iya canzawa, hakama Dukiya tana iya canzawa amma jininmu me daraja bazai taba sauyawa ba.
.ina gargadinka da ka fara sanin cewa aure baya sauya matsayin jini hakama bazai daukaka jinin bawa sama da jini me daraja ba, ruhi me tsarki yacemin zai sanar dani dede lokacin da za'a kaiwa zamkora ziyarar amsho maka matar aure.

dan haka ka xama cikin shiri dan nasan hukuncin sa bazai jima daga yanxu ba kuma nasan kaima bazaka bamu kunya ba

shiru tay kadan snn tace

yaron nan murad zamkora yana da yara yan mata guda biyu.. dan haka idan lokacin cika yarjejniya yay zamu baka cikakken dama na gudanar da zabi dakan ka snn duk wacce ka nuna acikin yaransa kaga ta dace ta zauna dakai toh itace kawai zamu karba.

Kai ya gyada mata snn
ahnkli yace godiya nake...

cikin takaitacen yanayi ta gama wann bayanin ganin baiy objecting akan duk abinda tace ba yasaka taji dadi aranta sosai tareda saka masa albarka kan Shamsan dake sunkuye cikin girmamawa ya amsata da kalma guda

Daga nan kuma ta karkatar da maganar zuwa harkokin kasuwanci wanda duk yadda take boyewa tareda kamewa da akwai wani irin alfahari da take ji a ranta game dashi

Tsawon shekaru da dama kenan tana kallon jinin yayanta da jikokinta suna tasowa amma kuma da akwai wani abu game da Shamsan da ya bambanta da kowa duk dama ba iya hayaniya ko yawan magana yayi ba Sai dai qduk inda ya tsaya mutane suna sonsa kuma suna jin nauyinsa

tattaunawa me tsayi da sukayi kenan kafin nan ta sallamesa yakoma can sashensa na asali domin ya karasa hutawa acan dan gobe yakeso ya koma lagos da sassafe.

dan duk inda ya juya anan memories ne kawai na childhood dinsa tare da iyayensa da kuma kaknsa marigayi shugaba khaleefa

komi cikin karammawa da gata ake masa kamar dan gwal haka ake kallonsa wanda a fuska zakaga kmr kowane yake zumudi da kaunar hakan amma harga Allah ummu zulaiha bawani kaunarsa can can takeyi ba dan gani take kamar yayanta na cikinta harsu mutu bazasu samu farin jini da daukakar da shamsn yake dashi a idon uwarjini ba.
Chapter 16 · 0% Book details