← Book details Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 62

Sashe 4

Tales Of Wazeeris Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

buga saman table din yay saida ta tsorata tay shiru yace ya isheki haka. i dont care if this is all about ur pregnancy hormones, u need to have some respect. bazaki cigaba da maidani dan iska ba for god sake sau nawa zangaya miki cea na dena bibiyar yan mata wnda nayi abayan ma ai kuskure ne da yaranta yanxu kuma na tuba i knw ure a princess amma nifa bawanki bane..u cant talk to me or oder me around kinaji ko??? ni mijinki ne ba servant dinki ba.

hawayen da suka fara sauka mata ta share snn ta zauna akan chair batare da tace masa komi ba tay shiru..

shiru wajen ya dauka yafara kallonta da gefen idonsa dan wani bin har mamaki take bashi yadda tafara canzawa, da can she is a very soft nd kind girl amma koda suka sha zaman aure da juna ta tafara gane halinsa aynxu inta fara ayyana masa bori da zafin kai me tattare da ruwan izza da kasaita dake yawo ajininta har sai yaji kansa ya kulle ya rasa abunda zaiyi.

ganin duk maganan nan dayayin batace mai uffan ba tasharesa yasaka ya dan sassauto da fuskarsa ya dauki juice din ya miƙa mata da kamr ma bazata karba ba sai tabudi baki ya bata kadan da sanyin murya yace "i am sorry babe. yes i was not in d building amma ba abunda kike tunani bane wallhi na dan fita ne zuwa bakin titi to meet a mechanic

rolling idanunta kawai tay batace masa komi ba ya jawota cikinsa yafara rarrashinta har saida tay sanyi ahakanma da kyar yasakata ta yi magana tana kwance lazyly ajikinshi yana shafata tace "na dauka ai ka fasa deal dinmu ne ka tafi yawonka kaga nima saina aje kudina.

..yay karamin murmushi tuna cewa fitarsan ne yasaka har yasan inda ushna take zama sai yace no my love ai nace miki zanyi i will do anything for your sake. tun kan ta amsashi sai ya dago kanta casually yadan kalleta yace" so u met a new girl friend? cikin rashin fahimtarsa tace whattt?kai tsaye yace yarinyar da naganki da ita dazu mana kinsanta ne ?naga kin rakata har waje

tace ohhhhh itace fa yarinyar nan da yusuf suka walakanta awaje dazu nd you knw dat was not fair..yace hmm, ina fatan dai baki mata alkwarin samun komi anan ba.

dada kwantar da kanta tay akan kirjinshi da muryan shagwaba tace mmm, not yet amma kuma ina tunanin yin hakan cos i really want to help herm

cikin kyabe baki yace inda kinajin shawarata danace miki a'a...

da sauri ta dago kai ta kallesa tace amma meyasa?

batare da nuna kulawa sosai ba yace cmnn my love bakifa santa ba. zai iya yuwa irin yara yara karuwan nan ne da suke barin gidan iyayensu su fito bariki, trust me, i knw lagos girls more than u do they are desprate whores nd dangerous.

tamasa kallo sama da kasa da kishi ayanayinta tace hmm ai dole ne kuwa kasan su tunda kay harka dasu.

karamin dariya ya kwace masa yace dats not what i mean..kedai kawai kin fiye zargi da kishi ne amma ki kalle yarinyar da kyau basai angaya miki ba babu wani alheri atattare da ita inada yaqinin cewa tallan kanta kawai ta kawo a building innan shiyasa banga kaifin yusuf ba the guy is just doing his job...nd it seems u nd ur egoistic brother are too naive nd emotional to see.

kwace kanta tay ajikinshi ta zauna dakyau tana kallonsa da mamaki baki abude tace wai bangaren mr yusuf kake gani, are u fucking serious?

zai maganan cikin katsesa tace haba fareess ta ina ne walakanta dan adam ya taba zamowa abun burgewa...look nima fa inajin labarin yan matan lagos din nan amma u shudnt judge a book by its cover... yarinyar nan bafa ma yar lagos din bace daga kasar london tazo nd i have her documents here they all are legit.

cikin katseta yace hmmm toh meyasa bata nemi waje a london ba tazo nan nigeria...i mean spare me the horror ko makaho yasani ratar cigaba tsakanin london da nigeria yana dayawa in my opinion she is just a desperate chick.

cikin share abunda yace din ta kyabe baki tace toh nidai zan taimaketa kuma ina fatan Allah ya bata sa'a..

shiru yay a fuskarsa yana mai nuna kamar ba ya sonta ne da abun amma aransa kuma kawai shiryawa yakeyi dan muddin rihanna ta jawo ushna cikin kamfanin nan dolene shima yakasance a shirye sosai amma kafin nan sai yasan yadda zaiyi yau dinnan ya shawo kan ushna koda ta hanyar kulla mata sharri ne

ahaka suka cigaba da tattaunawa cikin sabanin raayoyi inda farees ya zaƙe yana kkrin kushe lamarin ushna rihanna kuma tace sam bata iya ji ba...

suna cikin wnn maganan ne aka kwankwasa musu kofa faress ya bada ixinin shigowa ciki, jim kadan sectariyar shamsan ta shigo cikin girmawa ta kalle rihanna kai tsaye tace excuse me ma'am my boss is expecting to see u now.

rihanna ta dan gyara zamanta a jikin farees idonta ya motsa daga kan secretary din zuwa kan kyakkwan fuskar mijinta farees kamar wacce take neman approval dinsa ba tare da ta ce komi ba

farees da bai ko daga kansa ba fuskarshi was soo rigid dan har ga Allah daga yaji an ambace sunan sultan shamsan ransa baci yakeyo sosai taciki

duk dama ransa ba'a bace yake a fili ba saidai cikin kwayar idonsa akwai wani subtle irritation da bai iya bayyanawa a fili.

ganin rihanna ta tsare da da ido tana neman yardanshi yasauke ajiyan zuciya murynsa ciki ciki yace lets go..

da murmushi rihanna ta dan ja numfashi tana mikewa daga jikinshi snn ta dauki handbag dinta farees yana bin ta da ido har tagama kimtsawa a hankali ba tare da ya kalli secretary din kai tsaye ba she is on her way.

kai tsaye secretary din ta gyada kai ta juya tabar wajen da sauri

tana ficewa farees ya mike a hankali shima ya gyara zaman suit dinsa dan baison raini fuskarsa kamar bai wani damu da komai ba saidai hankalinsa gaba daya baya nan.

his heart is deeply consume by pride nd hatred irin girman kai da dagawan innan na dan talaka, gashi nan dai ahalinsa sun hada jini da asalin familyn waxeeris amma kuma ko kadan subasu da irin dumbin daraja da arxikin da waxeeris din suke dashi, shiyasa tun basu wani gama girma ba soyayyarsa da rihanna shine ya fara sakawa har yasan waye shamsan kuma wani irin arxiki gayen yake dashi, tun anan kuma yaji kamr duk duniya baida wanda yake jin mugun kishi da haushin dukiyarsa kmr shamsan wazeeri

tunma kafin axo ya gane cewa yarinyar dayake mutuwarso ya mallaka a rayuwarsa wato sarauniya arisha itama shamsan din takeso everything abt shamsan haushi yake bashi badon ya matsu da rihanna ta bashi kudaden nan ba da har abada yanaji kmr bazai iya taka kafarsa anan kamfanin ba

yana cikin wnn zullumin rihanna ta sauke idonta akansa ganin wani irin silent frustration da yake kokarin boyewa duk dama duk wanda yake kallonsa ahaka bazai iya gane komi ba

ganin ta zuba masa ido sai yamike mata hannunsa a hankali ta kama suka fara tafiya takunta cikin natsuwa da kame kai sukabar nan farees yana biye private lifter yakaisu har 18th floor wanda shine floor na karshe a building din gabaki daya after few min suka iso floor din

wajen gabaki daya ya dauki shiru ga wani irin sanyi raɓa da qamshin scented candles nd freshner masu axabn qamshi me tsada.

security da assistants da suke aiki a floor din ma ksan unifom dinsu daban ne dan anan wajen zallan office din shamsan yake da extra rooms na international meetings da safe na kudi da wasu ire iren confidential locker rooms da bakowa yake da ikon shiga ciki ba.

harsuka wuce gaba receptionist din dake wajen baice musu uffan ba face few assistant da suke kai kawo suke miko musu gaisuwan girmamawa ganin rihanna saboda sun san me take wakilta.

tunda suka sauko nan floor din idon farees yake famar scanning din wajen danjin kansa yake kamr wanda ya shigo filin yaki..

sunakan takawa atare tunbai gama dawowa cikin hayyacinsa ba yaga wai har sun iso gaban desk in sctariyar shamsan dake zaune cikin nitsuwa

suna karasawo ta dago kai a hankali tana bin su da kallo yanayin ta a nitse with strick professional calmness

batare dawani gaggawa ba rihanna ta tsaya gabanta cikin kame kai farees kuma yana baya baya kadan yanata kallon haduwar wajen kamar wanda yake kkrin absorbing filthy rich atmospher dake wani irin zagawa.

sectariyar tana gama gaishe su tamike tsaye daga kujerarta ahankli cikin kwarewa tanamai gyara files din da ke gabanta rihanna kawai takalla direct tace i will lead the way ma'am..

gaba tay suka fara binta abaya har suka kai gaban wani irin hadadden cathedral length door irin kofofin zamani masu kyau da fadi da shegen tsayi innan tsawonsa daga can sama har kasa

suna kaiwa nan ta fito da security key card tana swiping a jiki ta juyo tadan kallesu da murmushi tace..."only ma’am is allowed in sir u may have to wait over there.

rihanna ta juyo kadan takalli farees ganin ya mugun hade rai bai motsa ba yasaka tace u okay? kai kawai ya gyada mata yace yeah i wll be fine here. kyabe baki tay batace komi ba ta dauke idonta a hankali sannan ta juya ta bi ms lara charles zuwa cikin office din

suna bace ma ganinsa cikin jan tsaki ya koma yatsaya daga wajen reception jikinshi har rawa rawa yake taciki da bacin rai dan yasan dagangan shamsan ya bada oda akan kar abarsa ya shigo ciki.

baice ma kowa komi ba yagama karewa wajen kallo ganin kamar duk nan babu wanda zai kulashi sai kawai yanemi waje ya zauna yay odering tea nd snacks duk dama zuciyarsa tafasa take yi takiyi tay sanyi ko kadan...
Chapter 4 · 0% Book details