← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 80

Sashe 9

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Garin Yaya yoghurt din yaje hannun dan naka ko dai yarinya ta gano akwai abinda kake so ka Mata shiyasa tak'i Sha karka manta ance karka nuna Mata komai"

"Ban nuna Mata komai ba bansan ya akayi yoghurt din yaje hannun sa ba dan Allah ka taimaka min kaga kafi kusa da shugaban Rabiu ko dai bani da saan yin kudin nan ne,duk wani Abu da akace nayi indai zanyi sai an samu matsala"

"Kana ina yanzu"?

"Ina k'ofar gidana"

Kazo mu had'u sai muje Allah yasa da abinda za'a iya yi.

Har suka isa wajen hankalin Kabiru a tashe yake.

Tunda suka isa wajen shugaban su yace ba abinda zai iya yi akai Kabiru ya dafe kansa Annur na daban ne a cikin yayan sa yana jin Annur a zuciyarsa,sai gashi Yana ji Yana gani zai kurmance bashi da yadda zai yi.

Wani irin Haushin Yesmeen yake ji dan da bata leko shi ba da bai yi abinda Annur zai kurmance ba.

Ya so da ita yayi amfani wajen yin kudin shugaba yace Masa aa ya bari itama lokacin amfanin nata na zuwa.

Koda ya sake tambayar shugaban ba abinda zai iya yiwa Yesmeen sabida gudun tonan asirin sa dan Yana tsoro ta fadawa Sajeeda"

Shugaban su ce masa yayi gudun Kar a Kara samun matsala zai bashi abu ya fesa mata zata manta da komai ko ta kara ganin shi ko da tayi yunkurin fadawa wani bazata tuna abinda ta gani ba balle har ta fada ya Kara kafa masa sababin sharruda.

Kabiru kuwa ya tuna yadda Sajeeda ke yawan mafarki take ya fadawa shugaban nasu Yana "Tana da wayo Sajeeda ba naso ta dago ni, ba abinda za'a iya mata ta daina mafarkin Kuma ya Zama tana tsorona duk abinda nace tayi ta ringayi ba musu?

"Ka je kawai zan yi aiki akan ta ba za ta sake maka musu ba"

"Shugaba idan har za'a iya mata abinda ba za ta na bijire wa umarni na ba dan Allah ayi Mata na nemeta ta Bayan yafi min sauki da wancan da aka ce nayi"

Kallon da shugaban ya watsa masa yasa yayi saurin kau da Kansa dan da alama ya fara Kai shugaban nasu bango

Haka suka taho Yana bakin cikin kurmancewar da Annur zai yi dan sai a gobe zai tashi yaga baya iya magana gashi da balain k'ok'ari.

Sajeeda

Har tsoro nake ji dare yayi na gama yanke wa a raina indai na sake mafarki da abokin Abban Nusrah wlh bazan zauna a gidan daya bamu ba sai dai Abban Nusrah yasan yadda zai yi dani na riga da nasan idon sa ya rufe da San kudi ya kasa gane abinda nake fada masa akwai mutane da yawa da ni nasan abokanan nasa ne duk bai taimaka musu ba sai Abban Nusrah ga uban kudi ga kyautar gida da mai cikakken hankali ma yasan hankali bazai d'auka ba kasa da sati biyu duk yayi wa Abban Nusrah irin wanan alherin har da aikin da zai na d'aukan miliyan daya duk wata bayan nasan Abban Nusrah iyakacin sa secondary ballantana nace sabida ilimin sa zai bashi aikin miliyan daya.

Bansan ya akayi Yan uwa da abokanan arziki suka san mun tashi ba sai bulbulowa suke suna ganin gidan da yawan su basa iya b'oye mamakin su sabida girman gidan da kana gani kasan ya lashe kudi Mai yawa an Kuma san ba wani aiki arziki Abban Nusrah ke dashi ba.

Toh wa Zan yiwa bayani abokin sa ne tashi daya ya bashi kyautar gidan da har duk zuriar sa ya wadata su da komai tsabar yawan da kudin suka Masa da gidaje shine ya bawa Abban Nusrah kyautar gida.

Bakin da muka yi ya d'auke min hankali ban Kara tambayar Yesmeen abinda taso fada min dazu ba,na Kuma ga ta ware ba kamar dazu ba.

Karfe tara na dare Abban Nusrah ya dawo fuskarsa a mugun hade rabon da na gan shi a b'acin rai haka tun lokacin da ya tsiri nemana ta baya Ina hana shi.

Ko kallon abincin da na jera masa a gabansa bai yi ba yace "Ina su Saifullahi da Annur?"

"Suna d'akin su dazu nan suka gama cin abinci suka shige d'akin su".

Bai ce komai ba ya mik'e ya nufi d'akin nasu na bi shi da ido na tab'e baki dan fa tunda Abban Nusrah ya fara samun Yan canji nake ganin abubuwa iri iri,ko Mai yaran zasu Masa oho na tashi na shige d'akina.

Kabiru

A hankali ya tura k'ofar d'akin su Saifullahi ya gansu a zaune gabadaya hankalin su na Kan game din da suke bugawa.

Ganin bai ga Annur a cikin su ba yasa ya waiga wajen gadon ya hango shi a kwance da sauri ya Shiga d'akin da sai a lokacin suka ankara dashi suka hau Masa sannu da zuwa ba ta su yake ba ta Annur yake hakane yasa Yana zuwa ya zauna a gefen gadon Yana

"Annur bacci kake ne"?

A hankali Annur ya bud'e idon sa yana yamutsa fuskarsa ya Kai hannun sa wuyansa Yana "Abba sannu da zuwa wuyana ne yake min zafi tunda zu ko magana nake sai naji Yana min zafi"

Kabiru ba karamin daurewa yayi ba ya boye tashin hankalin da yake ciki ya hau masa sannu yana nadamar karbo ma maganin,dama Shugaban yasan Yana da abinda zai yi Ma sa Yesmeen ta manta abinda ta gani shi ne ya bar shi ya karbo maganin kurmancewa gashi nan Yana ji Yana gani Annur zai kurmance.

Sannu kawai yake jerawa Annur Yana Jin dama da yadda zaiyi dama ya iya maida hannun agogo baya.

A ba yadda zai yi ya tashi ya fito daga d'akin.

Ya nufi d'akin su Yana zuwa ya tarar da Sajeeda a kwance bai ko kalleta ba yayi shirin kwanciyar shima ya kwanta a gefen ta burin sa kawai bacci ya d'auketa yayi waje.

Sai dai a madadin tayi baccin sai ta hau bashi labarin wayanda suka zo ganin gidan.

Baccin bai d'auketa ba sai biyu na dare.

Sai da ya tabbatar da tayi nisa a bacci ya mik'e ya fito daga d'akin bai zarce ko Ina ba sai d'akin Yesmeen,ya d'auko mukulin dakin ta da ya zura a Aljihu ya fara k'ok'arin bud'ewa

Yesmeen da ta samu bacci dak'yar saboda tsoron da ta ringa ji tun ganin da tayi wa Kabiru jiya kamar a mafarki taji ana k'ok'arin bud'e k'ofar d'akin ta.

A mugun tsorace ta mik'e zaune ta fara k'ok'arin kwalla ihu cikin zafin nama Kabiru ya Kai wa bakinta cafka ya matse bakin ta.

Yesmeen ta zazzaro ido kirjinta na dukan tara tara wani irin tsoron Kabiru ne ya rufeta kamar ta shidde ya fusgota daga Kan gadon ya fara janta bai zame da ita ko Ina ba sai bandakin dake cikin d'akin ya rufo k'ofar

Kamar mai Athsma ta hau sauke numfashi dan Kabiru ma tamkar dodo ya zame mata Yana cire hannun sa daga bakinta ta d'auke ta da Mari kafin ta dawo daidai ya Kara dauketa da mari dan wani irin haushi da tsanar ta yake ji daya tuna ta sanadinta dan cikinsa zai daina magana kila na har abada.

"Idan Kika sake ki ka yi ihu aka jiki wallahi kashe ki zan yi rufe bakin ki da hannu bibiyu"

Da sauri ta rufe bakin ta da hannu biyu ta saki fitsarin tsoron kabirun dan ji take Kamar ta sume dan azabar tsoron sa.

Kabiru ji yake Kamar ya shaketa har sai ya rabata da numfashin ta ko a yanzu da yake tsaye bakin cikin sa bai Wuce da shugaba yak'i yarda yayi kudin da ita ba,

Cikin wani irin murya ya fara magana yana "Uban me ya sa Kika lekani jiya"?

Kasa magana tayi ta ringa zare ido

Ya daka mata wani mugun tsawa dan idon sa ya rufe Yama manta da a sace yazo d'akin ta

"Ba tambayar ki nake ba nace Mai yasa Kika lekani jiya"?

"Ban leka ka ba Abba wlh ban leka ka ba"

Wani irin Mari ya Kara d'auke ta dashi da har sai da gefen bakin ta ya fashe ya Kai Mata shak'a Yana "Jiya daddare Kika lekani a tsirara dayake Yar iska ce ke Kika makale a Window kina Kare min kallo Kika jawo min asara tsabar masifa kowa na bacci ke idon ki biyu kina munafirci gashi a garin haka kinsa nayi abinda har na mutu Ina Jin ciwon sa a zuciyata Yesmeen daga yau duk ranar da Kika Kara lekoni wallahi sai na aika ki lahira,duk ranar da Kika bud'u bakin ki da zumar ki fadawa wani Abinda Kika gani wallahi a ranar sai na kashe ki,ki nisance ni Yesmeen duk abinda zanyi duk motsin da zakiji Koda a saman kwanan d'akin nan ne Babu ruwan ki karki sake ki yarda ki leko idan har Kika leko a ranar Zan aika ki lahira"

Ya Kara shaketa Yana "kinji Mai nace ko baki ji ba"?

Da sauri Yesmeen ta fara gyada kanta cikin azabar tsoron sa

Yana k'ok'arin magana suka ji ana

"Yesmeen ke da waye a bandaki daddaren nan"?????

Kuyi maneji biki muke yi bana typing weekends Amma nayi Dan na faranta muku

Karku manta mun kusa Gama free pages in Sha Allah ga Mai bukata zai iya payment 500 ta wanan account din 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko katin mtn ta wanan layin 0803371070 sai a turo da shaidar biya ta Wanan layin 08033719070 ko ta wanan layin 08068484400.

: Assalamu alaikum wa rahmatullah.
Chapter 9 · 0% Book details