← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 80

Sashe 34

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 16*

"Kina gani Yesmeen?kina gani fa kika ce"?

Hawaye ne ya hau zubowa Yesmeen ta hau gyadawa Sajeeda Kai,Sajeeda kuwa cikin mamaki ta tashi tsaye tana so taga ko zata bita da Ido, sai taga Yesmeen din ta daga kai tana kallon ta alamar dai tana ganin ta

Sajeeda cikin mamaki da bacin rai ta Kara nuna kanta tana "Yesmeen kina nufin kina ganina yanzu?dama ganin da kika ce ba Kya yi karyane"?

Yesmeen Kai ta Kara gyada mata tana danne kukan da ke Neman kwace mata, ta nunawa Sajeeda tana gani ne saboda ta samu kwanciyar hankali,dan damuwar da ta Shiga akan makantar karyar da tayi yayi yawa tunda har sumewa tayi aka Kai ta asibiti,ganin sun dawo ta Kuma kasa bacci sai kukan da take yasa taji bazata iya jure ganin Sajeeda a damuwa ba,tana da hawan jini bata San jinin ta ya hau,sai Kuma da ta nuna mata tana gani,ta gano kuskuren da tayi dan dole sai ta fada wa Sajeeda dalilin daya saka tayi karyar makanta, Marin da Sajeeda ta watsa mata ya katse mata tunanin da ta tafi Sajeeda da ranta yayi mugun b'aci ta fara k'ok'arin magana Yesmeen cikin zafin nama ta mike tsaye ta daka tsalle tana neman rufe mata baki dan bata so tayi magana Kabiru ya jiyota idan har Kabiru ya gano tana gani tasan kashinta ya bushe,

Sajeeda kuwa hannun ta ta buge da ta kai bakinta dan ranta yayi mugun b'aci taya Yesmeen zata musu karyar makanta duk tashin hankalin nan da ta Shiga har tana Jin bugun zuciyarta na wuce misali ashe duk karya Yesmeen take.

"Wane irin rashin hankali ne wanan Yesmeen akan me zaki mana karyar makanta?

Yesmeen zubewa tayi akan gwiwarta ta daga hannu alamar roko tana "Ki daina daga murya umma dan Allah ki Rufa min asiri bana so Abba ya jiyoki idan har ya gano Ina gani kasheni zai yi"

Yesmeen tace tana rufe bakinta dan a yanzu tana tsaka Mai wuya,tasan a yau dole ta tona sirrin Kabiru ga Sajeeda dan tasan dole ta fada mata mai yasa Kabiru ke San kasheta.

Idan har ta Kuma fadawa Sajeeda tasan dole Kabiru yasan ta tona sirrin sa a sani,Mai ya kai ta nuna wa Sajeeda ta na gani,da ta sani ba ta bude idon ta ba,tasan damuwar bazai wuce na yan kwanaki ba har ya zame wa Sajeeda jiki, Amma sai taji ta kasa jure ganin ta cikin damuwa ita Kuma haka tata kaddarar tazo mata a tsaka mai wuya.

Sajeeda kuwa cikin daurewar Kai da mamaki ta zubawa Yesmeen ido,da jikinta ke rawa tana danne kukan dake neman kubce mata,shayar da Yesmeen ne kawai bata yi ba amma daga wanan kukan da take tasan akwai wani gaggarumin abun da Yesmeen ke b'oyewa da Kuma dukan alamu Yesmeen na cikin tsananin damuwa ya aka yi duk tsawon lokacin nan bata tab'a ganowa ba.

Gefen gado ta samu ta zauna tana "Yesmeen wane Abban ne zai kashe ki idan ya gane kina gani"?mai yasa Kika yi karyar kin makance"?Mai ke faruwane Yesmeen"?

Yesmeen bakin kofa ta kalla tayi kasa da murya tana "Umma zan fada miki gobe dan Allah a yanzu bana so a jiyo muna magana dan Allah umma ki Rufa min asiri karki nuna kinsan Ina gani"

"Bangane ba yesmeen ai kin Kara Sakani a cikin duhu ki fito ki fada min abinda ke faruwa kin manta ni mahaifiyar ki ce taya kike tunanin Zan samu kwanciyar hankali idan baki fada min ba?Yesmeen mai yake faruwa ne Abban ki akan me zai kashe ki idan ya gane kina gani,kin daure min Kai Yesmeen ki fada min ba Wanda zai jiyo mu yanzu karfe biyu kowa bacci yake Yi"

"Yesmeen hannu ta dora akai dan bata san taya zata fadawa Sajeeda sirrin Kabiru ba,bata san ya akayi Kabiru ya gane ta leka shi ba kwanaki sai gashi har daki ya biyo ta ya kusa kasheta,yanzu idan ta fadawa Sajeeda dole Kabiru ya gano,ta tuna yadda ya Sha alwashin sai ya kasheta idan ta tona masa asiri,Allah ne yayi da tsawon rayuwarta da karfin adduar da take yi tasan da tuni Kabiru yaci galaba a kanta,idan har zata bawa Sajeeda labarin abinda ke faruwa tamkar ta saka wa kanta tafiya lahira ne,idan Kuma tak'i fada Sajeeda bazata tab'a barin ta ba har sai ta fada Mata,idan Kuma ta fada Mata,tasan Sajeeda bazata tab'a shiru ba Koda Kabiru Bai sani ba sai Sajeeda ta tare shi da maganar

"Yesmeen daga kukan nan da kike na Kara tabbatar wa da kaina akwai wani gaggarumin abun da kike boye min har mai zai saka ki mana karyar kin makance Yesmeen idan har baki fito kin fada min abinda ke faruwa ba wallahi yanzu ba sai gari ya waye ba Zan taso kowa na fada musu kina gani,taya Zan daukeki a matsayin 'Ya ni baki daukeni a matsayin uwa ba saboda me zaki ringa min b'oye b'oye"

Yesmeen hannuwa ta fara yarfawa tana k'ok'arin magana suka ji bugun k'ofa.

Yesmeen ta mik'e a gigice tana kallon bakin k'ofar a daidai lokacin da aka Kara buga k'ofar da k'arfi Yesmeen ta fada jikin Sajeeda da ta zuba mata ido tana mamakin yadda Yesmeen ke neman shidewa cikin rada Yesmeen ta hau magana tana "Ummana na miki alkawari Zan fada Miki dan girman Allah Karki nunawa Abba Ina gani ki Rufa min asiri"

"Sajeedaa"

Kabiru ya kwalowa Sajeeda Kira

Sajeeda da Yesmeen ta Kara daga mata hankali ta kwantar da Yesmeen tare da gyada Mata Kai,kasan zuciyarta rawa kawai take ta rasa tunanin da ya Kamata tayi kanta ya kulle da lamarin Yesmeen duk yadda akayi abinda Yesmeen ke b'oyewa Yana da nasaba da Kabiru tuni taji hankalin ta ya Kara tashi taji tana neman Rasa nutsuwarta ji take idan Yesmeen bata fada Mata Mai take b'oyewa ba bazata tab'a samun kwanciyar hankali ba"

Kiran da Kabiru ya Kara kwalla mata yasa ta nufi k'ofar yesmeen kuwa ta rufe idonta gam tana Addu'a Allah yasa ba jiyosu Kabiru yayi ba.

Sajeeda kuwa yamutsa fuska ta ringa yi kamar wacce ta tashi daga baccin a lokacin da ta bud'e k'ofar

Kabiru kuwa ya fara k'ok'arin shigewa dakin dan ya fito zai je baya yayi wankan da akace ya ringa yi kullum idan biyu d tayi,ya jiyo muryar Sajeeda hakane yasa ya nufi k'ofar ya fara kwankwasawa Yana mamakin da wa take magana daddaren nan.

Yesmeen daya hango a kwance yasa gabansa mugun faduwa ya kalli Sajeeda da ta zuba masa ido tana nazartar sa

Ya hade rai Yana "Mai yarinya nan takeyi a d'akin nan Sajeeda"?

"kasan larurar da ta sameta,ba gani take ba,shiyasa naji na kasa barinta a can d'akin ta dan idan tana bukatar wani Abu ba lailai su Yaya Abu su iya mata ba ko bandaki zata je ba lailai su Mata jagora ba shi yasa na kawota dakina ta kwanta"

"Da Kika kawota ta kwanta ni Ina kike so na kwana"?

"Abban Nusrah naga dakinka ka wuce ka kwanta kayi hakuri Yesmeen ta ringa kwana a d'akin nan dan Allah saboda na ringa kula da ita"

"Ban yarda ba Sajeeda wanan wane irin rashin hankali ne kina nufin Saboda Yesmeen Zan daina kwana a d'akin nan ko a yanzu da Kika ga na wuce dakina kema kinsan b'ata min rai kika yi Yesmeen din nono take sha da Zaki kawota dakinan kina nufin idan ta kwana a dakinta tana so tayi fitsarin su Yaya abu bazasu iya taimaka mata ba kenan Mai yasa baki da lissafi ne ni mijinki kikeso ki kora daga dakinki saboda Yesmeen toh baki isa ba yanzu nan zata koma d'akin ta"

Daga haka Kabiru ya nufi wajen gadon a fusace ya bubuga kafar Yesmeen da jikinta ke balain rawa,yana "Ke tashi ki tafi dakinki ki kwanta"

"Da wane idon zata tafi d'akin ta Abban Nusrah ka barta ta kwana daga gobe sai ta cigaba da kwana a d'akin ta"

"Yadda Kika kawota haka zaki maida ta Sajeeda ke tashi tashi"

Yesmeen bud'e idon ta tayi tana kallon sama ta fara lalube Sajeeda ta karasa wajen ta ta mik'ar da ita sukayi hanyar waje.

Kabiru Yana ganin sun fita ya zauna a gefen gadon taya da hankalin sa zai bar Yesmeen ta ringa kwana da Sajeeda a daki daya,har a yanzu da Yesmeen ta makance bai ji ya samu kwanciyar hankali ba tunda zata iya magana kila watarana zata iya tona masa asiri,shi yasa tun farko yaso ma ace b'atar da ita yayi,har gwara ace kurmancewa ma tayi da makancewar dan yasan duk masifarta bata isa magana ba sai dai ta ringa bin mutane da ido, barin Yesmeen ma a raye ya zame masa barazana dole yasan nayi tunda a yanzu ba gani take ba.

Sajeeda
Chapter 34 · 0% Book details