← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 80

Sashe 55

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fitowa daga d'akin Sajeeda ya haye sama Yana Jin Kamar ya fashe dan bakin ciki,bai san yadda zai yi ba idan bai kwanta da Sajeeda ta baya ba,yarinyar da yake nema ta baya,ya daina samun ta a waya, a
Yanzu gani yake bazai iya Neman mace ta gabanta ba dan ta bayan yafi Masa mugun dadi,so kawai yake ya samu yayi aikin da aka saka shi,ganin Sajeeda ba iya magana take ba Kuma ba kwarine da ita ba yasa yayi tunanin gwara kawai ya nemeta ta bayan in yaso ya toshe hancin sa sai dai Duk yadda yaso yayi
jikinsa ma yak'i bashi hadin kai dan kyankyamin Sajeeda kawai yake,wayarsa ya d'auko ya nemo lambar Rabiu dan shi ya bashi shawarar ya nemi Sajeedan dan arzikin sa hauhawa kawai zai tayi ,har garinsu yaje ya siyi katon fili dan so yake yayi wa mahaifiyar sa gini itama ta mori arzikinsa,dan tana tambayarsa ya akayi ya samu kudi,ya sharara mata karya take ta yarda ta hau zuba Masa albarka,daga gidansu ya tafi gidansu Sajeeda da alama
aikin da aka yiwa iyayen Sajeeda yayi dan Koda yaje basu Masa maganar daukota ba inda ya shirga musu karya akan nan da wata uku ma zasu fita wajen yanzu an dora Sajeeda akan magani,ya nuna musu tana samun sauki, Gwaggo ce ma kamar aikin bai wani Kamata ba sai cewa take ita dai zata d'auko Sajeedan,sai Babansu Sajeedan ne yace baza'a daukota ba tunda ance tana samun sauki,da yazo tafiya ya d'auko kyautar kudi ya Basu,duk sukayi turus suka kasa karba sai ya tuna zasu iya zargin ya akayi yayi kudi haka,sai ya saki murmushi ya hau sharoro musu karya ai yanzu harkar mai yake, Gwaggo kin karbar kudin tayi,dan haka kawai taji bata yarda da shi ba amma ta kasa zargin ko Yana aikata mumunan Abu wajen samun kudin dan gani take kamar bazai iya aikata mugun abu ba,bai Kuma yi Kama da mai aikatawa ba, kafin ya tafi ya sanar musu da zai Kara auren,babban su Sajeeda ya sa albarka dan gani yake kabirun ma yayi k'ok'ari da ya zauna da Sajeeda duk tsawon lokacin nan bai Kara Aure ba, da wani ne ma sakinta zaiyi yace bazai iya zama da ita ba, Gwaggo kuwa ji tayi kamar tayi ta yiwa Sajeeda kuka zuciyarta ta sosu da auren da yace zai yi tana tsoron ya Kara auren ya juyawa Sajeeda baya tunda Sajeeda ba moruwa take ba,sai da ta kasa dannewa ta hau rokonsa akan ya rike Amana ya kwatanta adalci a tsakanin su tana nan tana yiwa Sajeeda Addu'a in Sha Allah zata warke, Kabiru kuwa ya hau rantsuwar bazai tab'a juyawa Sajeeda baya ba,Babansu Sajeedan kuwa yace masa Yana auren yasa Abu ta dawo Dan Yana ciwon kafa ne da tuni yaje ya taho da ita da dan abin kunya ne ace taje ta tare a gidan kanwarta.

A haka suka yi sallama ya taho bayan Gwaggo ta bashi lodin maganguna akan ya kawowa Sajeeda tayi amfani dashi,Yana yin nisa da gidan ya wurgar da ledar.

Rabiu na d'aukar wayar ya fara magana Yana "kasan na kasa nemanta abinan kwanciya tayi,tak'i mik'ewa,Rabiuu Ina Shan wahalar yin ayyukan nan ni kadai nasan kalar wahalhalun da na sha daga lokacin da na fara harkar nan zuwa yanzu kai kuwa banga alamar kana Shan wata wahala ba"

"Taya Zan Sha wahala bayan Ina taka tsantsan da komai,wanan kame kamen da kake fa kana auren yarinya da zata maka biyayya fa an wuce wajen,baka da fargabar komai sai dan aikin da bazaa rasa ba"

"Toh idan na aureta bata bani hadin kai ba fa ta zama mai taurin kai irin na Sajeeda"?

"Sajeeda a mutanen da tazo ai,na yanzu suna da San kudi ga Ateeka nan Ina ta moreta Ina cikata da kudi,Kuma ko damuwa batayi ba Dan tana samun abinda take so,Kamar yadda nima nake samun abinda nake so,auren nan kawai zaka yi,ka samu ka ringa cika duk aikin da aka baka,itama nasan ka kasa nemanta ne Saboda halin da take ciki,Ina ta baka shawara ka kaita a cika aikin nan kak'i

Ido Kabiru ya zaro Yana "Bazan iya ba Rabiu iya wanan da nayi ya Isa ba sai na karasa ta ba har ga Allah baa san raina nayi harkar nan da ita ba taurin kanta ya jawo Mata"

"Toh ai gani nake idan baka karasa ta ba bazaka saki jiki ka mori kudinka ba duk tsawon lokacin nan Wai ka kasa Kara Aure wai Kar aga ka mata wulakanci,da nine da tuni nayi biyu ma,nasan banda an rufe mata baki da tana magana zaka iya zuwa kace min zaka fita a kungiya dan naga kamar tsoron ta kake"

"Bazaka Gane ba Rabiu Sajeeda tamun hallaci a rayuwa ta kaunaceni shi yasa nake jin ban kyauta mata ba amma zan tura gidansu Barakan sati biyu kawai zaa saka dan ko ba'a Sakani aiki ba yanzu ji nake idan banyi ta bayan nan ba Zan iya zaucewa na siye Iyayenta da kudi sosai,har sun kori saurayinta,duk da naga alamar ba Sona take ba Iyayenta ke tilasta Mata Ina sakar musu kudi nasan an wuce wajen.

"Kudi ai sunyi a rayuwa abokina kayi abinda ranka ke so ko jarirya ka nuna kana indai kana da kudi,da gudu zaa baka,yanzu abinda za'ayi sai ka nemi wata a titi kayi aikin kafin kayi auren"

Hira suka Kara tab'awa kad'an kafin suyi sallama Kabiru ya kwanta Yana tunanin yadda zai barje baraka idan har ya aureta,dan yarinya ce mai tarbiya dan ko gwada rike hannun ta bai tab'a ba dan babu ma fuska hakan ya Kara kwadaita masa da san ya aureta ya ringa yiwa Iyayenta ruwan kudi,da yake mabukata ne da hannu biyu Suka rike shi, mahaifin Barakan ma idan zai gaishe shi sai ya rusuna,ba Kuma komai ya jawo haka ba saboda Yana da kudine.

Sajeeda
Ba abinda na saka a gaba yanzu sama da Addu'a dan tunda bakina ya daina yankewa da addua nake Jin dadin jikina,babbar matsalata yanzu Yaya Abu ce da naga ta karfin tuwo take so ta kasheni,yanzu bata tilasta min naci abinci bama ta kawomin,dan sai dai naji muryarta daga Palo,sai dai idan Yesmeen ta faki idonta ta kawo min naci.

Bansani ba ko canza salo tayi ni dai addua kawai nake Allah ya kareni daga sharrrinta.

Ina nan a kwance wajen sha biyu na Rana sai ga Abban Nusrah ya shigo yana washe baki,hannunsa rik'e da waya,yana "Ma Sha Allah na shigo d'akin sai dai kasan ba magana take ba,bani Nusrah"?

Muryar mijin Nusrah da naji yasa na baza kunnena Ina jin Mai suke cewa,barka barka da naji Abban Nusrah nayi Yasa na gane Nusrah haihuwa tayi,tuni hawaye ya hau zubo min na faranciki dan ban taba kawowa Ina rayye zata haihu ba,tana yawan Kira ta layin Abban Nusrah da sai ya shigo zai fada min ta Kira wani zubin idan ta matsa Masa sai ya kawo wayar ya saka a handsfree,haka zatayi ta magana ita kadai tana min kuka da Addu'ar samun sauki,Ina Umman take Abba dan Allah kasa tayi motsi naji ana yin suna Zan taho"?

"Ai kema kinsan ba iya motsin za tayi ba amma bari naga ko zatayi"

Ya matso da wayar bakina "hawaye na zubo min na fara gurnani dan ta jini,bani da bakin magana Amma Addu'a nake akan Allah ya bata lafiyar shayarwa,cikin rawar murya ta fara magana tana "Umma Allah ya baki lafiya kina raina cikin nan ne dama ya hanani zuwa washegarin suna zanzo,in Sha Allah akwai wayanda na saka suke miki addua anan umma dan Kamar larurarki bata asibiti bace Unma Sunan ki zaa saka wa jaririya zaa ringa kiranta da ummi"

Rabon da nayi murmushi Ina ga tun kafin Abban Nusrah ya kashemin rayuwa,maganar Nusrah yasa na saki murmushi na fara gurnani,Abban Nusrah ya d'auke wayar daga wajen bakina yana "Yau kinsa Umman ki murmushi rabon da naga fuskarta haka har na manta"

"Allah Abba naji dadi, in Sha Allah umma zata samu lafiya kullum sai nayi mafarki ta warke"

"Zata warke ne ai Ina nan Ina nema mata magani,Gobe Zan saka mamanki ta taho ta zauna dake in yaso kwa dawo tare yanzu ki fadamin Abubuwan da kike bukata sai na turo Miki kudi ki siya,karki sake ki dorawa mijinki nauyin komai,a yanzu da nake dashi so nake na nuna Miki gatan da ban samu na yi miki ba a lokacin aurenki,Zan kashe abinda yayi daga Dubu dari zuwa miliyan daya in sha Allah"

"Abba miliyan daya fa kace"?

Murmushin ya saki Yana "Nusrah Abbanki yayi kudi,yanzu harkar Mai da nake na shigo min da kudi,Su Saifullahi ma zasu zo hutu wata mai kamawa Ina nan na siya musu mota iri daya"

Kallon Abban Nusrah kawai nake Ina mamakin yadda yake lissafa jin dadi da Haram,daga yadda Naga muryar Nusrah yayi kasa nasan itama mamakin arzikin nasa take,dan shi kadai ya cigaba da magana Yana zai tura mata Yaya Abu,zai Kira can Malumfashi yasa Yan uwansa suje Mata,Yana jira yanzu nan ta turo acct din ta zai saka Mata Dubu dari biyar ta Kuma turo na mijinta.

Nusrah kuwa sai cewa take ita bata bukatar komai ya bar shi,yadda take magana ma da alamar a rude take,sai da ya daka Mata tsawa akan ta turo masa acct dinta yanzu Nan kafin ransa ya b'aci ya kashe wayar Yana k'ok'arin magana aka turo k'ofar d'akin,kafin ma ta karasa shigowa kamshin turarenta ya fara iso Mana,nasan ba kowa bace sai Yaya Abu.

Ta saka Riga da skirt gotai gotai da ita ya matse ta ko kunya bata ji sai uban tumbinta da ta matse kamar mai ciki,daidai da tafiyar ma cikin rangwada take ta canza murya Abban Nusrah da a yanzu na lura ya fara rainata yace "aa hajiya Abu wanan kwalliya haka ko dai kinyi sabon bazawari ne"?

Sai tayi wani farr da Ido a daidai lokacin ta karaso gefen gadon ta zauna tana "Wane irin bazawari ana zaune kalau kawai dai nayi kwalliya ne dan naji dadin jikina Dan a rayuwata bana San kazanta"
Chapter 55 · 0% Book details