← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 80

Sashe 78

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata Kara sanin inda take ba,bata San tsawon lokacin da ta dauka a sume ba,sai muryar mutane taji a kanta,Inda ta bud'e idonta a hankali tana kallon sama sai da ta dau tsawon lokaci ta tuna abinda ya faru da ita,ta fara k'ok'arin mik'ewa zaune dan taga Inda take,sai dai sam jikinta yak'i bata had'in kai,dan ji take jikin nata ya mata wani irin salaf kamar an kwashe komai na jikinta ga Abu da taji Yana zubo mata da ko daga kwancen da take tana shako warin,sai ta hau hararo yadda take kyankyamin Sajeeda take fesa turare idan zata Shiga dakinta,ta hararo yadda take yiwa Sajeeda idan ta b'ata waje,idan ma taimaka mata za tayi haka zata ta mata da mugunta,Ashe itama watarana zata wayi gari ta zama tamkar Sajeedan zata iya cewa ma tafi Sajeedan dan ita kadai tasan mai take ji,bata San Mai ya hau kanta ta bawa Kabiru kanta ba,batasan Ina kunya da tunanin ta ya tafi ta bar Kabiru ya nemeta ba,duk ba wani abu ya jawo mata haka ba sai San kudinta,yau da ace ta ji maganar Nusrah da kila bata tsinci kanta a wanan halin ba, gashi dai tana ganin yadda Kabirun ke wadaka da kudi,amma rufewar da idonta yayi yasa ta kasa yarda kudinsa bana halal bane, rufewar da idonta yayi yasa ta so kashe Sajeeda duk saboda ta samu abin duniyar da yau a garin kwadayinta gata a kwance bama tasan Inda take ba,da yanzu tuni an yanke mata kai,yau da ta samu taci galaba a kashe Sajeeda da ya zata yi Ina zata Kai wanan nauyin,ta tuna yadda Babansu yace Kar ta sake tazo Masa gida,ta tuna yadda tayiwa babba yalwa rashin kunya akan tace tazo su tafi gida bai dace ta zauna a gidan Sajeeda ba,Ina ma lokacin tabi su babba yalwan ta tafi da kila duk bata tsinci kanta a wanan halin ba kuka ta fashe dashi,tana tuno yadda Sajeeda bata iya magana,da yadda take buga kanta a bango idan tana san tayi magana,yanzu ma batasan Inda take ba,kuka kawai take a daidai lokacin da taga wata mata ta tsaya a kanta tana "Mama kizo kiga ta farka"

Sai a lokacin ta kalli Yar budurwa yarinya da ke sanye da daurin kirji, ta toshe hancinta da hannu biyu ga wani tsagu a fuskarta hausar ma da tayi Kamar ba bahaushiya ba,yadda ta toshe hancinta yasa taji wani irin kuka ya taho mata Ashe haka Sajeeda ke Jin ciwo idan ta toshe hancinta, isowar wata dattijuwar Mata da itama ta toshe hancinta tana gurgurarren hausa da "Ai kuwa ta farka bari babanku ya dawo a gaskiya gwara ya maidata Inda ya d'auko ta dan bazai yu mu zauna da ita tana wanan warin ba,na gaji da kwashe kashin dake zubo mata,ni kamar har tsutsa take fitarwa tunda nake ban taba ganin mai irin larurarta ba"

"Wallahi mama warin fa har daki tunda ta farka a tambayeta Ina ne gidansu sai a kaita dan gaskiya da cutarwa zamanta a gidanan.

Yaya abu da ido kawia take binsu hawaye na zubo mata daga maganarsu ta gane tsinto ta mai gidan yayi,so take ta bud'e baki tayi magana amma ta kasa so take tace su taimaka mata su kaita garinsu amma ta kasa magana numfashin da take ma dakyar takeyi,yanzu shikenan bazata iya magana ba,da ido ta ringa bin su tana Jin datijuwar na rokon Yar budurwa akan ta kaita bandaki a dan wanke mata jiki,yarinyar ta hade rai,a haife ma ta haifi yarinya,haka ta figeta ba ko tausayi,ta ajiyeta a bandakin ta debo ruwa ta hau watsa mata daga nesa tana toshe hanci,tuni taji wani irin radadi da azabar kaikaiyi ta fara girgiza Kai tana tuno yadda itama ta tab'a figar Sajeeda tayi mata yadda yar budurwar yarinya nan ta Mata,lailai ta yarda sharri dan aikene,Sajeeda bata da hakkinta gashi tun a gidan duniya an samu mai rama Mata,ta hau gurnani tana "Sajeeda ki yafemin na samu sauki a rayuwata nayi nadamar Abubuwan da na Miki,baba ka yafemin Gwaggo kimin addua kaicona"

Kuka kawai take Yar budurwa na daka mata tsawa tana cudata da tsintsiya daga nesa,dan bazata iya ma matsowa kusa da ita ba.

Koda ta gama wani wajen ta maida ta,ta dauko wani.kaya ta zura mata, duk rai a hade take.masifar babanta ya jawo musu balai ya rasa wa zai kawo gida sai Mai larura,abincin ma a wulakance ta bata tana tura mata cokalin bakinta Kamar zatayi amai,tana gama bata ta bar d'akin a fusace tana bazata yarda ta kwana ba indai kuwa babanta bai maidata ba a yau wallahi guba zata saka mata taci ta mutu.

Wani irin tsoron Allah ne ya shigeta,da taji abinda yarinyar tace,duk wani mugunta da tayiwa Sajeeda yau gashi Yar cikinta na Mata har tana kirarin zata kasheta,Ashe duk abinda take Allah Yana kallonta lokaci ya bata ta gama duk abinda za tayi,Allah kadai yasan irin kararta da Sajeeda ta kaiwa Allah da har ta fara ganin irin wanan sakayya.

Kuka kawai take dan har ta sake Bata kayanta wari ya dume d'akin.

Har ga Allah da ace tasan idan ta mutu Aljanna zata tafi da ta roki Allah akan ya dauki ranta da wanan rayuwar kwanci tayar din,ashe baka yiwa bawa gori da halin da ya Shiga ciki,idan har kayiwa bawa gori da jarrabtar da Allah ya Masa,zaka iya wayar gari kaima a jarrabce ka kamar yadda itama kwadayinta ya kaita ga Shiga halin Sajeedan,kafin ta mutu tana bukatar Neman yafiyar Sajeeda da Iyayenta,kafin ta mutu tana bukatar ta nemi yafiyar Yesmeen, Yesmeen da bata Mata komai ba ta Dora Mata Karan tsana.

Tana daki ta ringa jiyo muryar dattijuwar na yiwa wani Wanda take kyautata zaton shi ne maigidan akan ayau take so a fitar da ita daga gidan tunda ta farka, yadda taji muryarsa na rawa yasa ta tuna nata mijin da take juyawa da tana tunanin har da bakin cikinta ya Kashe shi.

Ido ta zubawa k'ofar a lokacin da ta ji sun nufo d'akin mutumin na zuwa ya rike hannunta matarsa ta Taya shi Suka yi waje da ita.

Suna zuwa k'ofar gidan matar ta saketa tana "Yayi maza ya kaita bakin titi"

Ta rufo k'ofar.

Mutumin da alama.yana tausayin ta.

Haka ya nade rigarss duk da warin da take haka ya kinkimeta dan tuni ta dawo sirriya Kamar Mai cutar kanjamau.

Da alama gidan nasa a wajen gari yake dan sai da suka yi tafiya Mai nisa Yana yi yana ajiyeta yana sosa hanci da wari ya saka ya ringa haka,karar motocin da take ji yasa ta gane sun kusa titi.

Hawaye ne ya hau zubo mata dan idan ya ajiyeta bata san waye zai taimaka mata ba,Yana kuwa zuwa bakin titi ya ajiyeta yana "da ace kina iya magana da kin fadamin wani naki na neme shi na Kai ki,a yashe na tsince ki a daji da naje saro itace,nan wajen gari kike hanyar barin garin Abuja bansan Mai ya kawo ki Nan ba,har ga Allah naso na taimaka miki,amma naga hakan na Neman haddasa min matsala da mai d'akina Allah ya baki lafiya ya kawo Mai taimaka miki"

Girgiza Kai Yaya Abu ta hau tana gurnanin Kar ya tafi ya barta ta taimaka Mata.

Sai dai tana ji tana gani ya juya ya fara tafiya haka ta kwanta a titi tana sharbar kuka,ta dauka zata ma iya daga hannunta sai dai ta kasa,haka ta kwanta a kasan tana Kiran sunayen Allah dan yanzu bata da mataimaki sai Allah.

Sajeeda

Tunda muka dawo garin kano muka dan samu nutsuwa, Saifullahi shi ya ringa Kai kawo,bansan yadda yayi ya d'auko mahaifinsa a Kai shi asibitin mahaukata ba,sai da ya dawo yake fadamin,hawaye cike a idonsa ya hau rokona akan na yafewa Babansu iya halin nan da yake ciki kawai ya isa yasa a yafe masa dan tun a gidan duniya Allah ya ke hisabi,wani zai iya dadewa Yana sabawa Allah bai samu ya tuba ba har Allah ya dau ransa kamar yadda Allah ya dauki ran Rabiu a lokacin da bai tab'a tunanin ba,Wanda sai da ya mutu wasu da yawa Suka san halin da ya jefa kansa da arzikin sa ya fara konewa, Wanda ya na da tabbacin shi ne ya jawo mahaifunsu ya Shiga wanan kungiya,kila Allah Yana san mahaifin su da rahama shi yasa ya tona Masa asiri a gidan duniya kowa yasan halin da jefa kansa a ciki,na tuna baya da ba haka yake ba, mahaifunsu nagartacen mutum ne,haduwa da mugun aboki da San zuciya ya Kai shi ya baro"

Hawaye kawai ke zubo min dan duk maganar da yayi ba karya tun kafin ma ya rokeni akan na yafewa Kabiru na yafe Masa dan Allah Yana San masu yafiya,nima zanso ya yafemin kura kuraina,ko iya warkar dani da yayi a lokacin da na fid da rai da rayuwa na fara kawowa kaina mutuwa Allah ya mikar dani, cikin ikonsa ya nuna min tsafi karya ne,raina a hannunsa yake ba a hannun kowa ba shi yake azurta Wanda yaso ya Kuma talauta Wanda ya so Allah shi buwayi ne gaggara misali,yayi min niimar da zan dawwama ina gode masa dan bana Jin ko duk kudin duniya zaa hada dan a nema min magani zan iya samun sauki,cikin ikonsa ba tare da an sha wahalar komai ba ya warkar dani,iya wanan kawai ya Isa yasa na yafewa Kabiru da Yaya Abu da naji kwana biyu ta tsaya min arai,bansan inda take ba dan bata je gida ba

Nasan duk Inda take tana nan tana Shan wahala har ga Allah balain tausayinta nake ji,dan ko makiyina bana Masa fata ya Shiga halin da na Shiga balle jinina da muke uwa daya uba daya,cikin sheshekar kuka nacewa Saifullahi na yafewa Kabiru duniya da lahira yamin godiya ya kalli kanensa ya musu nasiha yace su ringa yiwa abbansu Addu'a,yayi wa Yesmeen godiya irin daiwaniyar da tayi dani.
Chapter 78 · 0% Book details