← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka gaisa da yaya Abu ya shige d'akinsa sai da yayi wanka ya fito yana jin sa a cikin nishadi,batun sallah kuwa babu,dan yanzu idan akwai abinda ke Masa wahala bai wuce sallah ba,dan ba kowane lokaci yake yi ba,yau ba karamin dadi yaji da Yan matan da Rabiu ya hada shi dasu ba,har ga Allah daya daga cikin su ta kwanta masa Husna ya samu yadda yake so,dan har lambarta ya karba dan ji yayi ma zai iya aurenta bata fi sa'ar Yesmeen ba.

Koda ya fito d'akin Sajeeda ya shige dan ya dubata.

Sajeeda

Mafarkin da nayi ya tsaya min a zuciya dan kasa ma samun nutsuwa nayi,sai da na saka Saifullahi ya ruko mun hannun Yesmeen ya kawota d'akina, daga mafarkin nan da nayi nasan cewar dagani har Yesmeen muna cikin mugun hatsari nama Shiga hatsarin tunda Kabiru ya gama dani, Yesmeen na ganin Saifullah ya bar d'akin tayi saurin Mai do da fuskarta kasa tana "Umma ya jikinki"?

Sai na cije lebbena dan ni kadai nasan mai nake ji a jikina dan yanzu kasana ma ji nayi Yana numfashi shi kadai,

"Umma dan Allah dan Annabi karki nunawa Abba kinsan komai wallahi dazu ma sai da ya zo har dakina ya shakeni ya Sha alwashin kasheni idan har sirrinsa ya fita Umma wallahi Abba zai iya kasheni ki taimaka min ki rufe sirrin nan, mu dage da Addu'a da saukar Qur'ani, in Sha Allah zaki warke idan guduwa ma zamu yi sai mu gudu"

Girgiza kaina nayi ina "Yesmeen ranki da nawa a hannun Allah yake yau ko mutuwa nayi,lokacina ne yayi,ji nake idan ban tona sirrinsa ba bazan samu kwanciyar hankali ba,dan ya fara tunani tura su Saifullahi kasar waje,idan har zai iya mun wanan cutar ya kurmantar da Annur dan ya siyar da su Saifullahi ba wahala zai Masa ba gwara na nuna masa nasan sirrin sa"

Yesmeen zubewa tayi a gabana ta hau magiya sai kuka take tana na rufa mata asiri Abban nusrah kasheta zaiyi idan na nuna masa nasani

Na ruko hannun ta Ina "Ki kwantar da hankalin ki bazan nuna Masa ke Kika fadamin ba,ba Kuma magana Zan Masa ba da kaina nake so na gano sirrin sa ya Kuma san cewar nagani din ba fada min aka yi ba da naso na fadawa su Saifullahi sirrin sa dan su san cewar zai iya yin kudin dasu suma amma na fasa fada musu zan dai hana tafiyar tasu"

Yesmeen magiya kawai take akan na rufa Mata asiri sai da na rantse mata akan bazan fada masa komai ba ta samu nutsuwa dan na yanke abinda zan yi bazai tab'a zargin Yesmeen ce ta fada min wani abu ba.

Bayan fitar Yesmeen daga d'akin Yaya Asmau ta shigo na fada mata ta bar Yesmeen ba sai ta tafi da ita ba Yaya Asmau tafi nuna kulawar ta a kaina akan wacce na Kira da yayata ni gani nake ma Kamar murna take da rashin lafiyata tunda duk zata yi abinda ranta ke so.

Ba Mai hanata.

Kafin Yaya Asmau ta koma dakinta na Kara rokonta akan ta saka mallamai suyi min Addu'a da sauka tamun alkawari da zata saka ayi min Addu'a.

Ba ta kuwa bar dakina ba sai da ta tabbatar da naci abinci Yaya Abu bata lekoni ba sai wajen goma ta shigo tana har yanzu bata ga Abban Nusrah ya dawo ba dama yana dadewa hakane"?

Kai kawai na gyada mata.

Ta sa Kai ta fita.

Tana fita na fara susa dan wani irin kaikaiyi naji kamar na cire gabana na Yar ga ruwan dake bulbulo min duk wanan masifar uban yayana ne ya jefani saboda abin duniya.

Haka na kwanta Ina zubar hawaye idan ya lafa na daina idan ya motsa na cigaba da susa,Ina Jin lokacin da Abban Nusrah ya dawo na dauka zai lekoni sai naji shiru Wanda hakan na nufin dakinsa ya wuce sai da ya dau tsawon lokaci naga ya turo k'ofar d'akin ya shigo sanye da jallabiya kudin haram sun zauna masa dan har wani kiba yayi Yana sheki.

Ya zauna a gefen gadon Yana "Sannu Sajeeda ya jikin naki"?

Mik'ewa nayi na zauna Ina "Abban Nusrah dare daya na wayi gari da wanan masifar a jikina,a ranar da na fara Jin canji a jikina a ranar da ka kusanceni ne na karshe Abban Nusrah shekara ashirin da doriya muna tare Kai ma kasan ban taba cuta makamancin wanan ba,Mai zai jawo min wanan masifar"?

Wani irin kallo ya fara min cikin hade rai ya fara magana Yana "Toh mai kike nufi da tunda na kusance ki na karshe kika ji jikinki ya canza kina nufin ni na saka Miki cuta ko me?idan a jikina kika kwashi wanan cutar ni zaki gani haka ne,wanan cutar kila a bandaki Kika kwaso ko a wani wajen dan haka ki cigaba kawai da Shan magungunan da aka Rubuto miki Zaki warke a hankali kinci abinci"?

Ba karamin daurewa nayi na danne abinda nake ji ba,na gyada masa Kai da naci abincin ya fara magana Yana "Ina ganin ya Kamata Yaya Abu tazo ta ringa tayaki kwana ni sai na ringa kwana a dakina har zuwa lokacin da zaki warke"

"Tun baaje koina ba Abban Nusrah ka fara guduna kenan bazaka iya kwana da ni waje daya ba"?

"Aaa Sajeeda akan me Zan gujeki,kawai Ina ganin a yanzu kina bukatar kulawa sosai,shi yasa nace tazo ta ringa kwana anan ai na dan lokacine"

"Abban Nusrah bana so Yaya Abu tazo ta kwana Kai nake so ka kwana din idan Kuma dan larurata zaka ki kwana dani shikenan ba komai"

Nace Ina Jin kamar na shako shi har sai ya daina numfashi so nake na Kama Abban Nusrah da kaina shiyasa nake so mu ringa kwana waje daya.

Kabiru kuwa ganin Sajeeda ta dage yasa yace zai kwana din zuciyar sa fal da tunanin yadda zai gudanar da abunsa ba tare da su Yaya Abu sun gan shi ba.

Haka ya ringa sintiri daga dakinsa zuwa na Sajeeda Yana tunanin yadda zai yi,bai san mai yasa wankan sai a bayan gidan zai yi ba ji yake Kamar ya taso su Yaya Abun yace su koma dakinsa su kwanta.

Haka yayi ta juye juye har Sha biyun na dare Yana Jin saukar numfashin Sajeeda dake nuni tayi nisa a bacci,a hankali ya lekata ya ga baccin dai take cikin sand'a ya mik'e ya fito daga d'akin.

Ya nufi bakin k'ofar d'akin Yesmeen ya Kara kunnensa Dan yaji ko zai jiyo motsin su ba abinda yake ji sai karar fanka.

Cikin sand'a ya koma dakinsa ya jawo tukunyar kasar da ke d'auke da ruwan maganin ya tube Zigidir Yana jira daya ta karasa yayi waje yayi wankan.

Sajeeda
Duk abinda yake yi Ina kallon sa rufe idona kawai nayi Kamar Mai baccin Yana fita na bud'e idona kila wani abun zai aikata tunda Yesmeen tace na ringa fitowa karfe biyu na dare Zan ganewa idona.

Gabana faduwa kawai yake a lokacin da na mik'e tsaye Ina Jin kamar na Fadi saboda rashin kwarin jiki cikin sand'a na isa bakin k'ofar Ina lek'e ta ramin mukulin k'ofar.

A Kan idona yazo ya fito daga d'akin sa tsirara da wani bakin tukunyar kasa a hannun sa,tuni naji jikina ya dauki wani irin rawa dan duk abinan labari Yesmeen ta bani ban taba gani da idona ba a yau zan gan shi da idona.

Numfashina kamar ya d'auke haka na rik'e kirjina har sai da ya fice na bud'e k'ofar dakina a hankali na fito Ina Jin kafafuna kamar bazasu iya d'aukana ba.

A haka nayi waje na labe Ina sauke numfashi Kamar Mai cutar Asma,yadda naga Abban Nusrah a tsirara ya matukar daga min hankali

Sai da nayi minti goma a labe kafin nayi bayan gidan a hankali Ina Jin jiri na neman zubar Dani.

A tsaye yake a bayan gidan tsirara Ya daga tukunyar kasar sama ruwa na zuba a jikinsa can gefe Kuma wani tukunyar kasa ne da wutar kyandir.

Kallon Abban Nusrah kawai nake Ina k'ok'awa da numfashina a lokacin da kowa ke bacci shi ya fito Yana tsafi duk akan duniya.

A haka Zan tsaya har sai ya gama nafi so ya gani da idonsa ya tabbatar da idona na ganshi ba Yesmeen ce ta fadamin ba.

Dafanin da naji anyi ta baya yasa na bud'e baki dan na saki ihu.....

*Karku manta da saka yar uwata a adduar ku Allah ya kubuto ita ya tsare mata mutuncinta ameen*
*ZAN KOYA MIKI YADDA ZAKI HADA TURAREN WUTA KYAUTA SBD KISAMU ABINDA ZAKI DOGARA DA KANKI KIYIMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 08144679009*

*HUMKAM INCENSE GIDAN KAMSHI DA GYARAN JIKI*

MATAR DA HAIHU MUNTANADAR WANI PACKAGE MAI TAKEN TUNA BAYA RANAR FARKO DARE DAYA MAI DUMBIN TARIHI

*MUNA GYARAN JIKIN AMARE SOSAI MUNA SAIDA TURARUKA DA MAGANIN MATA MASU KYAU DA INGANCI*

KANAWA KUZO HUMKAM TA *ZAN KOYA MIKI YADDA ZAKI HADA TURAREN WUTA KYAUTA SBD KISAMU ABINDA ZAKI DOGARA DA KANKI KIYIMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 08144679009*

*HUMKAM INCENSE GIDAN KAMSHI DA GYARAN JIKI*

MATAR DA HAIHU MUNTANADAR WANI PACKAGE MAI TAKEN TUNA BAYA RANAR FARKO DARE DAYA MAI DUMBIN TARIHI

*MUNA GYARAN JIKIN AMARE SOSAI MUNA SAIDA TURARUKA DA MAGANIN MATA MASU KYAU DA INGANCI*

*INA MATAR DA KE FAMA DA INFECTION MUN TABADAR MUKU MAGANI SADIDAN WANDA DA ZARAN KIN FARA AMFANI DASHI ZAKIJI YADDA ZAKI FITSARE WANNAN SANYIN INSHA ALLAH*

MUNADA TURARUKA MASU SIRRIKA NA MATAN AURE KAMAR SU

*HATSABIBIYAR TURARE*
*NI DA MIJINA*
*SAI KABIYONI*
*SHU'UMAR HUMRA*
*BITA ZAIZAI*
*DARE DAYA WANKA GOMA*
Hmmm wadannan pls banda yan mata matan aure kadai zanbasu duk budurwar da ta siya ta shafa babu ruwana
08132506044

OTHER ROOM WANNAN TURARE MAI SUNA OTHER ROOM BA NORMAL TURARE BANE SIRRIKAN DA KE CIKINSA BAYANIN SAIDAI MU HADU TA PRIVATE

*INA BUDURWAR DA JARABAWA TA FAD'A MATA MUNTANADAR MINI WANI SET MAI SUNA BACK TO VIRGIN 08132506044*

*MAGANIN MATA MUNA SA KURMA KUWWA,SATA SHAKAF,GUMBA TSUMI ZUMA DA SAURAN SU HAJIYA INDAI MATSI KIKESO KISAI BACK TO VIRGIN*
*INA MATAR DA KE FAMA DA INFECTION MUN TABADAR MUKU MAGANI SADIDAN WANDA DA ZARAN KIN FARA AMFANI DASHI ZAKIJI YADDA ZAKI FITSARE WANNAN SANYIN INSHA ALLAH*
Chapter 45 · 0% Book details