← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 80

Sashe 50

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*INA BUDURWAR DA JARABAWA TA FAD'A MATA MUNTANADAR MINI WANI SET MAI SUNA BACK TO VIRGIN 08132506044*

*MAGANIN MATA MUNA SA KURMA KUWWA,SATA SHAKAF,GUMBA TSUMI ZUMA DA SAURAN SU HAJIYA INDAI MATSI KIKESO KISAI BACK TO VIRGIN*
*INA MATAR DA KE FAMA DA INFECTION MUN TABADAR MUKU MAGANI SADIDAN WANDA DA ZARAN KIN FARA AMFANI DASHI ZAKIJI YADDA ZAKI FITSARE WANNAN SANYIN INSHA ALLAH*

MUNADA TURARUKA MASU SIRRIKA NA MATAN AURE KAMAR SU

*HATSABIBIYAR TURARE*
*NI DA MIJINA*
*SAI KA BIYONI*
*SHU'UMAR HUMRA*
*BITA ZAIZAI*
*DARE DAYA WANKA GOMA*
Hmmm wadannan pls banda yan mata matan aure kadai zanbasu duk budurwar da ta siya ta shafa babu ruwana
08132506044

OTHER ROOM WANNAN TURARE MAI SUNA OTHER ROOM BA NORMAL TURARE BANE SIRRIKAN DA KE CIKINSA BAYANIN SAIDAI MU HADU TA PRIVATE

*INA BUDURWAR DA JARABAWA TA FAD'A MATA MUNTANADAR MIKI WANI SET MAI SUNA BACK TO VIRGIN WANNAN SET DIN ZAKISHA MAMAKIN YADDA ZAI HADE JIKINKI GAMGAM. 08132506044*

*MAGANIN MATA MUNA DA KURMA KUWWA,SATA SHAKAF,GUMBA TSUMI ZUMA DA SAURAN SU HAJIYA INDAI MATSI KIKESO KISAI BACK TO VIRGIN*

*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 40-45*

Yanzu ganin Yaya Abu tamkar ganin malaikan mutuwa ne a wajena ,jikina rawa ya d'auka na hau addua a zuciyata a daidai lokacin da ta zauna a gefen gadon ta hau juya taliya da mai da yajin tana "Kin dai san bazai yu ki zauna da yunwa ba tunda baki Sha kunun dazu ba ki daure kici taliyar sai ki Sha maganin ki"

Ta ajiye taliyar ta zaunar dani

Ta debo taliyar
Ta nufo bakina ba abinda nake iya motsawa a jikina sai kaina,hannuna ma a shanye yake ballantana na ture hannunta,sai hawaye ya fara zubo min dan nasan kila yau zan yi bankwana da duniya dan idan ta turamin taliyar ta k'arfi ta danne ni dole na hadiye,

Kau da kaina nayi kirjina na wani irin bugu dan wani irin kamshi ne ya bugi hancina Ina ma iya ganin birbidin magani a cikin masifa ta fara tana "Wai ke Sajeeda mai hakane ke fa ba yarinya bace,da Zan ringa wani lallaba ki dalla ni ki bude bakin ki kici ko na miki dure.

Ta fara k'ok'arin tura taliyar bakina ta k'arfi.

Na riga nasan kwanana ya Kare.

Ba mai kwatata a hannun Yaya Abu,Ina ma Yesmeen ta shigo, turo k'ofar d'akin da akayi yasa na waiga da sauri Kamar yadda naga Yaya Abu ta kalli bakin k'ofar itama da alama ta tsorata,wani irin ajiyar zuciya na sauke da naga Yesmeen ce ta shigo tana lalubar iska kanta a sama,sai dai taya zata taimaka min ita da ta nuna bata gani,

Yaya Abu kuwa taja wani dogon tsaki tana "ke Kuma uwarki Kika zo nema a d'akin nan da zaki wani shigo ba izini, bazaki tab'a samun waje daya ki zauna ba haka Zaki ishi mutane da sintiri da lalube uban me kike nema"?

Yaya Abu ta daka mata wani irin tsawa!!

Yesmen kuwa ta cigaba da nufo wajen gadon cikin lalube tana "Kaina ke ciwo mama shine nazo duba paracetamol"

Ta Ina zaki ga paracetamol ke da ba ido ne dake ba,Sajeeda Kuma a kwance sai dai a kwantar a tayar,ita kike nufi zata tashi ta d'auko miki naganin?ke dai yarinya nan anyi munafika wallahi Allah, mai ya hana ni kizo wajena neman maganin dan uwarki bazaki tsaya ba sai kin hau kaina"?

Daidai lokacin da Yesmeen ta ringa baza hannu kamar tana laluben ta tunkuda farantin hannun Yaya Abun.

Yaya Abu ta saki ihun sallati tana "ta zubar da abincin tsinanniya"

Bata yi wata wata ba ta ta jawo Yesmeen cikin mugun b'acin rai ta hau kilar ta"

Girgiza kaina kawai nake Ina gurnani,tamkar ni take bugu haka na ringa ji,Yesmeen saboda ta taimaka min tayi karyar makanta ta daina zuwa makaranta saboda ta taimaka min take shan wuya a hannun Abban Nusrah Yanzu Kuma Yaya Abu ce sako Yesmeen din a gaba,na Dade da sanin ta tsani Yesmeen ba Kuma Wai iya Yesmeen ta tsana ba,har yarana ba kaunar su take ba tana nuna musu so ne na ganin ido, wani zubin idan taga Abban Nusrah na nan,Amma indai baya nan haka zan ji tana dakawa su Annur tsawa har ihun Hamza sai da najiyo kwanaki tana ta dimarsa tana surfa masa Ashar, tun ma ban mutu ba tana cin zalin yayana Ina ga ta samu nassarar kasheni.

Gajiya tayi dan kanta ta saki Yesmeen cikin masifa ta hau magana tana "wallahi sai kin bar gidanan bazan d'auki wanan iskanci ba,Allah ma kadai yasan Mai yasa ya makantar dake,haka kawai sai ki shigo ki zubar min da abinci,Ina ma zan ga laifinki ai duk laifin Sajeeda ne,bari Kabirun ya dawo, wallahi sai na fada Masa a maidaki wajen dangin uban ki Yar iska yarinya Mara mutunci, yarinya sai kace mayya,kin makance bazaki samu waje ki zauna ba kin ta yawo kenan kina bin bango,yadda kika shigo da lalube maza tashi kifita da lalube gwara ma da kika makance din dan da kina gani da Allah kadai yasan barnar da zaki yi

Yesmeen mik'ewa tayi cikin kuka ta hau lalubar iska tayi hanyar wajen tana Jin jikinta na zugin dukan da ta Sha dan ma ta Kare fuskarta,Yaya Abu ta wuce tunanin ta,Yaya Abu a yanzu ma tafi Kabirun hatsari,tunda da alama iya kudi yayi da Sajeeda ba kasheta yake so yayi ba,amma ita Yaya abu fa so take taga bayan Sajeedan,dan dazu tana fitowa daga d'akin Sajeedan ta shige d'akin ta cikin sand'a ta rufe kofarta dan Bata so tayi motsin da Yaya Abu zata jiyota,tana kwance tana karanta wani littafin addu'oi da ta kusan haddace wa saboda nacin da ta ringayi wajen Addu'ar motsin bud'e k'ofar da ta jiyo yasa tayi saurin boye littafin a kasan pilo ta rufe idon ta kamar mai bacci,tana Jin lokacin da Yaya Abun ta shigo d'akin tayi dube dubenta ta fita,dan kusan haka take Mata kullum,sai ta leko d'akinta.

Tana fita ta mik'e da sauri ta fara lekata,sai taga ta fita can waje,hakane yasa ta fito daga dakinta ta makale a jikin window tana leka Yaya Abun da ta karasa wajen maigadin.

Bata san mai take cewa mai gadin ba taga dai ta d'auko kudi ta bashi,tana ganin ta nufo palon ta koma dakinta da sauri,haka tayi ta leka Yaya Abun har taga mai gadi ya kwada sallama bakin palon ya kawo mata wani abu a bakin leda,tuni taji jikinta ya bata da kila wani maganin ta Kara samowa tunda dazu Sajeeda bata Sha kunun ba,motsinta kawai take ji a kitchen,ba Kuma ta hanyar da zata iya lekata sai da ta bata Yan mintuna ta fito daga d'akin ta ta hau lalube ta nufi Kitchen din kanta a sama,tana Shiga Yaya Abu ta dago da sauri tana kallon ta ta fara k'ok'arin tusa leda a cikin zanin jikinta, ita kuwa Yesmeen ta cigaba da lalube tana kallon ta,Yaya Abu wani irin tsawa ta daka mata tana tambayar ta uban me take nema a kitchen tace mata kishi ruwa take ji, masifa ta ringayi tana kiranta da munafika ita kuwa ta lalubo ruwan tayi kamar Sha take,Yaya Abu tazo ta wuce ta gabanta da plate din taliyar,tuni taji hankalin ta ya tashi ta fara tunanin hanyar da zata bi wajen hana Sajeeda cin taliyar dabarar da ta Fado Mata yasa ta fito daga kitchen din ta shige d'akin Sajeeda,bata Jin zata iya cigaba da karyar makantar nan, dan idan har batayi Wasa ba Yaya Abu na iya cutar da Sajeeda ya zama dole tasan hanyar da zata bi wajen hana yaya Abu samun cikar burinta kasan ranta kuwa mamaki kawai take tana tunanin mai yasa har Yaya Abu ke San kashe Sajeeda Mai tayi Mata haka.?

Sajeeda

Haka Yaya Abu ta ringa tsinewa Yesmeen tana kwashe taliyar daya zub'e,ni kuwa hamdala kawai nake a raina da Yesmeen tazo ya ceceni,Ina ma Ina da kafar da Zan tashi da na gudu na bar gidanan,Ina ma Yesmeen zata gane ta Kira mahaifiyata a waya ta kawo min agaji tazo ta d'auke ni daga gidanan,idan yau Allah ya kareni, gobe fa idan Yaya Abu ta faki idon yesmeen ta zo ta dura min maganin na sha fa.

Rai a bace ta gama kwashe taliyar ta fice waje ko kallona bata Kara yi ba.

Hawaye ya hau zubo min da na tuna wai yayata ke san kasheni saboda abin duniya,sallati kawai nake da istigari Ina daga kwancen,wani ikon Allah Kuma sai naji zuciyata tana min sanyi.

Ana kiraye kirayen sallah magriba naji sallamar su hamza a palon,dan makarantar boko mai hade da islamiya Abban Nusrah ya saka su,idan suka fita tun safe sai magriba suke dawowa,Ina Jin suna gaida Yaya Abu da bata amsa ba ta hau masifar su koma su cire takalmansu ita bata san rashin tarbiya shegu, ta hau auna musu zagi,sai na cije lebbena,Ina Jin wani irin nauyi a zuciyata,yanzu idan na mutu Yaya Abu haka zatayi ta cin zalin yarana.

Uwa daya uba daya fa, shigowar su Annur d'akina yasa na bud'e idona,dan indai suka dawo haka zasu shigo dakina su zauna sosai nake Jin tausayin yarana da basuyi dace da uba nagari ba, muna zaune cikin rufin asiri da sutura ya zabi ya ciyar damu da haram.

Hamza duk da yasan bazan iya magana ba sai da ya gaisheni,na lumshe idona na bud'e alamar amsa,Annur kuwa dama ba baki,da Ido kawai ya ringa bina idonsa ya Kada yayi jajjur da alama ransa a bace yake,jakar bayansa ya kunto ya d'auko biro da takarda ya fara rubutu dagani har Hamza kallon sa kawai muke Yana gamawa ya dago min takardar "Umma yaushe Mama zata tafi,umma kullum sai ta rankwasheni ta dokeni"
Chapter 50 · 0% Book details