← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 80

Sashe 69

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da tayi addua ta samu nutsuwa ta tadda sallah tare da ayyanawa tana gaban A Rahman a Raheem yasan me a zuciyarta,yasan mai tazo nema a wajensa tana da yaqinin zai amsa mata dan shi Mai amsa adduar bayinsa ne,mai taimaka wa bayinsa ne a lokacin da suke cikin tsanani,sallah raka'a shidda tayi,ta sallame ta dauki carbin da ta gani ta hau Jan istigifari sai da tayi dubu,ta hau yiwa Annabi sallati tana Jan majina dan har lokacin hawaye bai yanke a fuskarta ba,sai da taji yatsunta na ciwo ta ajiye carbin ta d'auko Qur'ani ta fara karatu,sai da ta karanta iya yadda zata iya ta ajiye Qur'anin,ta koma tayi Sujadda tayiwa Annabi sallati goshinta a kasa ta karanto sunayen Allah 99 kafin ta dago da hawaye Shabe shabe ta daga hannunta ta fara Addu'a "Ya samiu dua ya rabbi Maliki ya quddusu ka bawa ummana lafiya ka tashi kafadunta, Alhamdulillah ya rabbi mungode maka da tarin niimomin ka a garemu wanan halin da muke ciki Kai ka jarrabcemu ya Allah ka yanke Mana ka sausauta ma na ba dan halinmu ba,ka tausayawa umma ka tashi kafadunta kai kake da iko akan kowa da komai,ya Rahimu ka gwada ikonka akan Abba ka bawa Umma lafiya ka bata ikon tashi akan kafafunta ka bude mata bakinta ta iya magana dan ta wanke zargin da Nusrah ke min,ya Allah ka kadai ne shaidata ba yadda za'ayi na cutar da umma ko na bari a cuceta Allah a yanzu banida yadda zan taimaka Mata ya Allah ka taimaka mata ka ara Mata tsawon rayuwa Allah ka nuna min ranar da zata warke kafin na koma gareka"

Kuka kawai take rusawa jikinta na rawa sai da ta dade kafin ta cigaba da Addu'a mai tsayi,rawar da taga jikinta nayi har tana Jin jiri yasa ta rufe Addu'ar da amanar rasulu ta shafa ta kwanta akan sallayar ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkin Sajeeda.

3am

Sajeeda

A hankali na bud'e idona sai na Kara maida idona na rufe,a rufewar da nayi bana so na yaudari kaina nayi tunanin Ina rayye,duk da ban tab'a mutuwa ba nasan duk Wanda ya mutu binne shi akeyi a Kai shi makwancinsa wato Kabari Wanda a yadda ake bamu labari ana dawo maka da ranka,sai dai banjini a Matse ba,banjini a dadaure ba,ba dai bayan na cire rai da rayuwa na jiyo kamshin mutuwa ba mutuwar nayi ba,a hankali na Kara bud'e idona sai na kurawa saman rufin d'akin ido na mintuna kafin na juya kaina na kalli gefena na Kara juyawa na kalli daya gefen,tuni tunanina ya bani inda nake wato asibti,daga b'arina na hagu nurse ce a kwance a daya gadon da ba kowa.

A hankali na daga hannuna na dora akan kirjina naji Yana bugawa na mitsini kaina a daidai wajen da nake Jin bugun zuciyata sai naji tabbas ba mafarki nake ba Allah ya barni a raye bayan na fidda rai da rayuwa,Allah ya barni a raye bayan ciwon da naji a kirjina da na kwatanta shi da ciwon ajali,Ashe Ina da sauran kwana a gaba, Ashe cuta ba mutuwa bace ba,tuni hawaye ya hau zubo min Ina daga kwance wallahi ban taba tunanin Zan rayu ba,kuka na fara yi kasa kasa na fara motsa bakina dan nace Alhamdulillah.

Ga mamakina sai naji sautin maganata a kunnena,sai na zaro idona na hau wuwurga idona naga ko dai wata ce a gefena take hamdala na dauka nice,sai dai banga kowa ba nurse ce dai dake bacci a daya gadon.

Kirjina na dan bugawa da Kar na yaudari kaina na Kara cewa "Alhamdulillah ya rabbi"

Sai na Kara Jin sautin muryata a kunnena.

Sai na saki murmushi Ina tunanin yadda nake neman saka rai da magana bayan nasan da wuya.

Sai na Kara gwada magana Ina "Yesmeen Kinga Zan yaudari kaina Ina Jin maganata a kunnena"

Sautin maganar ya Kara tafiya kunnena daya saka jikina d'aukar rawa nasan abune da bazai yu nayi magana ba taya kunnena ke yaudarar kaina da Ina magana har maganar tawa na fitowa.

Sai naja tsaki a zuciyata na fi minti goma a haka kafin na waiga wajen nurse ina bari na sake yaudarar kaina sai nace "Nurse ki bani ruwa in Sha"

Sai naga ta bud'e idonta tana kallona,sai na zaro idona Ina Jin bugun kirjina da ido na bita naga ta sauko daga gadon ta nufo wajen da nake tana "Yanzu nan fa bacci ya daukeni ruwa zaki Sha"

Jikina wani irin rawa yake hannuna da nake iya motsawa na Kai na damki hannunta Ina "Kina nufin kinji Mai nace"?

Sai naga ta yamutsa fuska sai ta kawo hannunta ta tab'a kaina tana "Ko dai zazzabi ne a jikinki bangane naji mai ki ka ce ba ba ruwa kikace Zaki Sha ba"?

A hankali na saki hannunta na maida idona na rufe bazan iya fassara halin da nake ciki ba,hakane kawai yasa na rushe da kuka na hau yiwa Allah godiya,Ina addua Allah yasa ba mafarkan da na Saba yi bane nayi akan Ina magana,Allah buwayi gaggara misali,Allah maji rokon bawansa,Allah mai amsa adduar bayinsa a lokacin da ya fidda rai,dan wallahi na fidda rai da rayuwa ko iya maganar Allah ya bani ikon yi alhamdulillah bani da bakin gode masa,Ina ma zan ga Yesmeen Ina ma tana kusa dani,Ina ma itace ta fara jin muryata,nasan bazan iya fassalta farinciki da zata yi ba ,ta Sha cewa tayi kewar murya ta,ganin nurse din ta fice waje yasa na fara magana a fili dan na tabbatar "Alhamdulillah ya Allah Alhamdulillah Allah da ka nuna min Wanan ranar da zan iya magana, Kabiru asirinka ya tonu"

Wallahi naji sautin maganata ta tafi kunnena dan da k'arfi nayi,

Kukan farinciki kawai nake,tunanin da ya fado min yasa na gwada daga daya hannun nawa sai naga na daga sai na zaro idona, bana iya tashi,bana so na zura jiki,amma sai na gwada mik'ewa daga kwancen da nake sai naga na mik'e a haukace na fara kabbara Ina "Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar na shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah na shaida Annabi Muhammad sallalahu alaihi wa salam manzonka ne laillaha illallahu Muhammad rasulillahi Sallalahu alaihi wa salam"

Sai na gwada sauke kafafuna kasa sai na Mik'e tsaye duk da bani da kwari,dan kafafuna sirarane sosai tamkar kwarangwal haka na dawo.

Sai naga na tsaya a Kan kafafuna sai naji wani irin farinciki na dibana na mitsini kaina da k'arfi sai na tabbatar ba fa mafarki nake ba Allah shi yake ikonsa a duk lokacin da yaso,Allah Mai yine a yanzu Allah mai yine a cikin Sakani,sai nayi taku biyu wai na gwada tafiya na gani, farinciki ya Sakani zubewa akan gwiwata na tafi sujadda Ina Kara kabbara sai na rasa mai zancewa Allah,sai na tsinci Kaina da cewar "Ina kaunarka Allahna Ina sanka Allah na bani da tamkar ka ka gama min komai" na dago Ina "Yesmeen kina Ina zoki ga sarkin sarakuna ya mikar dani,sarkin da bai Haifa ba,ba a haife shi ba ya warkar dani laillaha illallahu Muhammadu rasulillahi sallalahu alaihi wa salam.

Kuka kawai nake motsin da naji yasa na tashi iska na d'aukana na koma Kan gadon na kwanta na rufe idona hawaye na cigaba da zubo min,wallahi ji nake mafarki nake bazan nunawa kowa na warke ba nurse dinan na iya fadawa Kabiru shi Kuma ya Kara kwantar dani.

Addua na tsinci Kaina da yiwa Annur akan yadda ya warkar dani Allah yasa shi ma bakinsa ya bud'e.

Nurse din da ta shigo ruwa ta bani dan Ashe ruwa taje daukowa na girgiza Mata kai ba abinda zai Shiga bakina Allah kawai Zan tayiwa godiya.

Wani irin farin ciki ya rufeni da na tuna yanzu Nima Zan iya tsayawa nayi Sallah nayi rukuu nayi sujadda na zauna nayi tafiya kamar kowa.

Akan idona aka Kira sallah Asuba nurse na fita na Mike iska na d'aukana Kamar Mai koyon tafiya na nufi bandaki,Ina alwala Ina hawaye rabona da alwala da kaina har na manta,ba hijabin da Zan iya sawa kayan jikina ba lailai yayi sallah ba dan har yanzu Ina dan Jin dumi da zuvar ruwa a kasana.

Watakila jikina ne bazai warke kamar yadda nake ada ba amma Zan ta rokon Allah in Sha Allah zan warke na daina zubar ruwan

Kan gadon na koma na zauna.

Tuni naji zuciyata ta rabu gida biyu wajen tunanin abin yi nasan Kabiru zai iya zuwa asibti ya tafi dani,ko dai na roki nurse ta kaini Tasha na tafi garinmu,ko dai na bi shi na bari sai ya saki jiki zaiyi wani abun na bashi mamaki.

Tuni naji zuciyata ta bani da nayi hakan.

Wajen karfe goma sai ga Kabirun ya diro yaci doguwar Riga ta maza

Kallon da nake Masa na yadda Zan fallasa sirirnsa kowa yasani ne, wani irin wutar tsanarsa ke ruruwa a kirjina amma haka na daure,ya zauna a gefen gadon Yana "Sannu Sajeedata kin warke Kai naji dadi yanzu likita yace zamu iya tafiya ya bani ma takarda sallama yace ki rage tunani Zaki ji saukine kinji"

Gyada masa Kai na nayi

Ya saki murmushi

Yana bari na sa a kawo keke a doraki a kaiki mota.

Yayi hanyar waje.

Ba jimawa ya dawo da nurse biyu Suka kinkimeni Suka dorani akan keken suka jani har wajen motarsa ya bud'e gidan gaba ya kinkimeni ya Sakani a seat din daya kwantar dan ba iya zama nake ba a wajensa Ina kallo ya zura hannu a Aljihu ya d'auko kudi ya basu Suka karba Suna zuba Masa godiya basu San kudin haram bane.

Shi kadai ya ringa surutunsa Yana cemin Kar na damu Zan warke fa zai siyamin mota zai kaini saudiya.

A garin kallonsa na naga wajen jikinsa a kumbure sai naji gabana yayi wani irin faduwar tashin hankali Kar nayi b'atar basiran bin shi yaje ya kwanta dani, sai naji zuciyata na "Ba abinda zai iya Sajeeda idan har yace zai gwada ki shamece shi ki kai Masa duka"

Duk da haka sai naji jikina na rawa dan a kumbure yake har Ina iya hango shi ta cikin rigarsa.
Chapter 69 · 0% Book details