Sashe 51
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda na so danne kukan dake neman kwace min a gabansu sai na kasa sai da na fashe da kukan,bani da bakin bashi Amsa,bani da bambanci da hoto Nima kaina Allah zan kaiwa karar Yaya Abu.
Hamza shima ya fara magana muryar sa na rawa "umma bana san wanan rayuwar da muke rayuwar mu a zango ta fimin dadi, umma tunda Abban ya zama Mai kudi kike rashin lafiya Annur ya kurmance aunty Yesmeen ta makance,su Yaya Saifullahi Suka tafi suka barmu mama bana san gidanan,nafi san gidanmu na zango nafison yadda muke ada"
Ya karshe hawaye na gudu a fuskarsa shekarar Hamza Sha hudu amma yasan yayi wanan tunanin,Amma jahilar yayata bata tab'a zama tayi tunanin ta Ina Abban Nusrah ya samu kudin sa dare daya ba,sai ta fara tunanin hanyar da zata bi ta kasheni.
Ina kuka yarana na sharar kwala sai da Yaya Abu da ta Zama matar gidan ta shigo dakina taci kwalliya cikin doguwar rigar shadda har da su kamshin turare,ashe duk kawaliya nan da take yi saboda Abban Nusrah ne,tsawa ta dakawa su Hamza tana "ku wuce kuje ku cire uniform kun zo Kun sakata a gaba Kuna kuka,kuna nufin baa isa a muku fada ba toh Baku Isa ba wallahi dole na muku fada idan kunyi ba daidai ba"
Da gudu suka fice daga d'akin.
Sai a lokacin ta juyo tana "Nasan ko an kawo Miki abinci ba ci zakiyi ba sai kiyi ta Abu Kamar wata yarinya ko wa zakiyi wa shagwaba oho"
Daga haka ta fice daga dakin.
Ni kuwa na fara Jan hasbunallahu wa neemal wakeel dan yanzu bakina bazai yanke wajen addua ba kuka da tunani a yanzu ba nawa bane taimakon Allah nake nema.
Ina Jin karar tv nasan itace,Ina daka dai bansan wainar da ake toyawa ba nasan yarana basu isa su fito Palo ba.
Wajen Sha daya naji muryar Abban Nusrah a Palo suna magana da Yaya Abu,na kasa kunne na Ina Jin Mai suke cewa,bayan ta Masa sannu da zuwa tace masa "Ina ka tsaya haka tunda zu Ina ta jiran dawowarka"?
Dariya naji yasa ya fara magana Yana "Yaya Abu ya zaki tsaya jiran dawowa na ai da kinje kinyi kwanciyar ki"
"Ta ina zan kwanta ai bazan samu kwanciyar hankali ba har sai ka dawo yanzu dai ga abincin ka can na Kai ma sama ko kasa zan sauko ma dashi"?
"Aa a koshe nake wallahi Ina su Annur sun yi Bacci ne"?
"Ee sunyi bacci tundazu"
"Allah sarki yau ma ban ga fitarsu ba dan kafin na sauko har sun tafi"
"Wai yanzu kana nufin bazaka ci abincin nan da na kwashi awani Ina girkawa ba"?
"Yaya Abu wallahi a koshe nake da yake naje gidansu Baraka wacce nake ce Miki zan aura a gidansu naci abinci a satin nan ma nake so na tura gidan su in Sha Allah"
Kirjina ji nayi yayi wani irin dokawa da k'arfi da naji abinda yace wa Yaya abu da naji tana ta maimaita "yanzu auren dai zaka yi Kabiru"
"Toh zan ta zama hakane Yaya Abu kinsan hakan bazai yu ba dole na Kara Aure tunda Kinga Sajeeda ba lafiya ne da ita ba ni so nake ki taimaka min ma wajen shawo hankalin ta gobe da safe zan Gaya mata idan Allah ya kaimu bari na hau sama dan a gajiye nake"
Jikina wani irin rawa ya d'auka da naji abinda Abban Nusrah yace wato aure zai Kara tunda ya riga da ya gama dani, a yanzu zai auro wata yazo ya fara sabuwar rayuwa da ita ni Kuma Ina nan na gama Masa amfani,kuka kawai nake Ina Kiran Sunan Allah.
A ranar bacci bai ga idona ba haka na kwana Ina kuka da Addu'a ba kishin auren da zaiyi nake ba,cutar da yamin kawai nake wa kuka,har wani sabon zazzabi ne ya rufeni.
Akan idona aka Kira sallah Asuba
Ba iya sallah zan yi ba amma haka na rufe idona na daura niyyar alwala da zuciyata,nayi Sallah raka biyu,Ina daga kwancen ta hanyar ayyana komai a zuciyata kamar dai sallah nake, Ina iddar wa na fara istigifari.
Tuni naji zuciyata ta rage nauyi.
Karfe bakwai da rabi su Annur Suka shigo Suka gaisheni na musu addua a zuciyata suka tafi.
Wajen karfe tara na fara Jin bacci na neman daukata kamar a mafarki naji muryar Gwaggo na kwada sallama a Palo.
Tamkar wacce aka yiwa bushara da gidan Aljanna haka naji na zubawa k'ofar dakina ido.
Yaya Abu....
Mg's skincare
Kunji takennan kunsake jinshi shin yar'uwa nace wai haryanzu baki jaraba products dinsu ba😵💫yar'uwa mace fa yar ado da kwalliyace koda kina dakyau akace kikara da wanka😍sufa kayan mg's basa bleaching duka kayansu 💯 natural ne sannan organic zasu gyara sukuma goge Miki jikine kawai yakara bayya ar da ainihin zallar Madarar kyawun halittar da Allah yayimiki🥰
Wai kinafama da pimples da spot afuska amma haryau baki nemi mg's ba🤔duk Mai tantama akan kayan gyaranjiki yacire mg's domin babu shakka sudin na dabanne indai problem dinki matsalan fatane yar'uwa kijaraba koda soap dinsu bi'iznillah zaki godemin👯♀️kayansu ga kamshi inkinjaraba kinga yanda suke na tabbatar bazakiso su Yanke Miki ba🤩08062991549 anatayi Baku sisters kusamu kugwada koda b duka kit din na gyaranjiki ba zakuga sauyin da fatarku zata samu cikin lokaci kalilan🥳jikin yazama so fresh ko Ina kikashiga kita glowing fatarki na walwali kamar madubi😘keda kanki zakina burge kanki balle wasu🤗08062991549
Adade anayi sai gaskiya sannan siyan nagari Maida kudi gida ❤️
Duk Mai bukatar products din mg's kutuntubi wadannan numbers din domin tasune kawai zaku samesu🙏
Chat 08062991549
07046881166,07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Team glow🧖♀️
*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*
*PAGE 50*
Yaya Abu
Jiya ko kad'an bata samu ta runtsa ba saboda hankalinta yayi mugun tashi da Kabiru yace mata zai tura kudin aure gidan yarinya da yake so ya aura,taya tana zaune zata bari yayi aure,indai ya Kara auren nan ba abinda zai sa ya tab'a aurenta,dan haka dole tasan yadda zata kau da Sajeeda da wuri saboda ta samu cikar burinta,dan indai ta samu Sajeeda ta tafi,tasan mutuwarta zai d'auke Masa hankali daga zancen Karin auren,zuwa lokacin da zai fara tunanin auren zata san yadda zata yi wajen shigar da kanta wajen sa.
Da wuri ta tashi taci kwalliya ta shige Kitchen dan ta dora musu abin karyawa,so take kafin Kabiru ya sauko daga sama ta samu Sajeeda taci abincin,tana ta d'aukar kwalliya dan ta fara d'aukar hankalin sa,amma ta lura bazai tab'a lura da kwalliyar ba saboda Yana tunanin ita yayar Sajeeda ce.
Sauri sauri ta ringayi wajen hada abincin karyawar
Tana gama hada shayi da dankalin ta d'auko maganin da ta boye a a zanin ta ta barbada a shayi ta jujjuya ko Sajeeda yau tak'i Shan shayin sai ta dura mata ta k'arfi
Tana fitowa daga kitchen taci Karo da Gwaggo dake kwada sallama a bakin palo, Bayan ta kuma babba yalwa ce da take Kamar kaka a wajen su.
Turus tayi ta zuba musu ido tana kallon su tama kasa amsa sallamar itama Gwaggo kallon ta take cikin mamaki yadda taci kwalliya dan har da dan Jan baki ta shafa,babba yalwa kuwa tace "Abu ce ta Zama matar gidan ne ko dai idona ke nuna min Abu ce"?
"Itace babba Kamar fa itace matar gidan wai da Sunan tana kula da Mara lafiya take zuba wanan kib'ar ta samu waje, ya Kika tsaya kina kallon mu ko gane mu ne bakiyi ba"?
Gwaggo tace tana cigaba da karewa Yaya Abu kallo tana mamakin yadda tayi fari tayi kib'a Kamar ma rashin lafiyar Sajeeda bai dameta ba,ita ta haifi Yaya Abu tasan halinta tun tana karama, tun jiya da suka yi waya da Kabiru taji Sam ta kasa samun nutsuwa burinta kawai taga tazo taga Sajeeda,ba yau tayi niyyar zuwa ba,sai dai mafarkin da tayi akan Sajeeda yasa taji idan bata zo ba bazata tab'a samun kwanciyar hankali ba,dama babba yalwa ta dade tana so tazo ta duba Sajeedan,tana Jin tace zata zo,tace itama zata biyota za Kuma ta zauna ta kula da Sajeeda,dan babba yalwa kanwar mahaifiyar Gwaggo ce tana balain kaunar Sajeeda dan duk sallah sai Sajeeda ta Mata Aiken turmin zani ko kudi,hakane yasa tunda taji ance Sajeeda na rashin lafiya tabi ta damu,yanayin da aka ce Mata Sajeeda na ciki yasa ta yanke zuwa ta zauna ta ringa kula da Sajeedan tunda har Kabiru ya kafe akan baza'a maida ta can ba, Gwaggo kuwa ba karamin dadi ta ji ba dan Sam Bata san zaman da Yaya Abu tayi a gidan Sajeeda da take kanwarta abun ya mata wani iri,ta Kuma san Yaya Abu ba hankali ta cika ba zata iya zuwa tayi ta zubarwa da kanta mutunci a gaban Kabirun, tun a jiya take Kiran Yaya Abu dan ta tambayi jikin Sajeeda ta Kuma yi mata kwatance taki dauka,ba Kuma tasan taga ta Kira Kabiru hakane yasa ta Kira Nusrah a waya ta fada mata unguwar da suka koma a Abuja dan dama tasan sun tashi.
Yaya Abu da ke ji kamar ta fashe da kukan bakin cikin ganin Gwaggo da babba yalwa dake neman hanata samun cikar burinta cikin yak'e ta fara magana tana
"Gwaggo sannun ku da zuwa ai mamaki zuwanku nayi da sassafe haka Kamar dama a garin nan kuka kwana"?
"Ai jiya da na ringa kiranki dan naji lafiyar Sajeeda baki dauka ba na Kuma sake kiranki daddare baki dauka ba Kuma baki Isa kice baki ga kirana ba ganin damar dauka ne kawai baki yi,dan nazo da sassafe duba ta ba wani abu bane ba da zaki tsaya kina kallon mu Kamar wasu bakin da baki sani ba"