← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 80

Sashe 10

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa. Bamu tsaya anan ba zamu koyar da ke yanda zaki haɗa kayan mata 'yan gaske da hannunki, kama daga dahuwar kazar amarya da uwagida, dahuwar 'yan shila, haɗin tsumi kala lala kai abin dai ba'a magana.
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM

*RUFAFFEN SIRRI*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Page 7*

Muryar Sajeeda da Kabiru yaji yasa yaji hankalinsa yayi mugun tashi, cikin zafin nama ya manne a bayan k'ofa ya zarowa Yesmeen ido da jikinta ke wani irin k'yarma wandon baccin dake jikinta a jike da fitsari a daidai lokacin da Sajeeda ta fara kwankwasa k'ofar tana "Yesmeen Yesmeen ke da waye a bandaki?

Alamar yankan wuya Kabiru yayi wa Yesmeen,

Yesmeen tayi sauri ta fara magana tana "Ni kadai ce Umma cikina ke murda min.

"Kina nufin ke kadai kike magana da Kan ki a bandakin Yesmeen"?

Alamar da Kabiru yayi wa Yesmeen yasa ta fara share hawayen fuskarta dan da hannun sa ya ringa nuna Mata alamar ta goge fuskarta ta kunna pampo saboda Sajeeda taji motsin ruwa.

Jiki na rawa Yesmeen ta kunna pampo ta hau goge fuskarta Kabiru kuwa sai zare ido yake a bayan k'ofa

Sajeeda kuwa ta Kara buga k'ofar tana "ki bud'e min k'ofar dan ni dai naji tashin magana shi yasa na yo d'akin ki idan ba tab'in hankali Kika sa mu ba karfe biyun da wani abu na dare ki shige bandaki ki ringa magana ke daya"

Kabiru karewa bandakin kallo kawai yake Yana tunanin Inda zai b'uya hankalin sa a mugun tashe Yana tsoron Sajeeda ta shigo bandakin ta gan shi,gashi bai sani ba ko shugaba yayi aiki akan Sajeeda ballantana ya mata borin kunya Kara mannewa yayi a bayan k'ofar yayi wa Yesmeen ido akan ta bud'e.

Yesmeen dake Jin kamar numfashin ta ya d'auke ganin ta da take yi da Kabiru a waje daya tayi sauri ta nufi wajen k'ofar tana Addu'a Allah yasa tana bud'ewa Sajeeda ta fado ciki asirin sa ya tonu ko da ta bud'e k'ofar da sauri Sajeeda da ta fara k'ok'arin zama a gefen gadon Yesmeen ta juyo tana kallon Yesmeen da ta hada gumi wandon jikin ta a jike idonta jajjur

"Yesmeen kalau kike kuwa"?

Yesmeen wajen gadon ta nufa ta zauna tare da dafe kanta da taji Yana Sara Mata sai sauke numfashi take.

Sajeeda kuwa ta nufi wajen bandakin Kabiru ya Kara matse jikinsa a bayan k'ofa a lokacin da Sajeeda ta dan leleka bandakin daga bakin k'ofa taga ba kowa ta rufo k'ofar Kabiru ya saki numfashin da ya rik'e.

Yesmeen taji kamar ta Mata nuni da hannu akan ta duba bayan k'ofar sai dai tana tsoron Kabiru ya kashe ta kamar yadda yayi kirari

Sajeeda ta dawo gefen gadon ta zauna ta kai hannun ta Kan Yesmeen tana "Mai kikaci daya b'ata miki ciki"?

"Ba abinda naci umma tun dana kwanta nake ta fama da ciwon ciki sai zaryar bandaki nake"

"Kin Sha magani"?

Gyada mata Kai Yesmeen tayi tana satar kallon k'ofar bandakin tana adduar Ina ma Sajeeda ta Shiga bandakin ta gan Shi.

Sajeeda kuwa ta fara magana tana
Na farka Zan yi fitsari ban ga Abban ku a daki ba shine na fito na duba ko Yana Palo sai naji kamar tashin magana a d'akin ki Ina Abban ku yaje daddaren nan naga Kuma k'ofar palon a kulle na Kuma duba bandakin baya nan,wai Mai ke faruwa ne Yesmeen na daina gane wa Abban ku,ya canza gabad'aya Kamar bashi ba tunda ya hadu da wanan abokin nasa na fara ganin sauyi a tare dashi,bansan Mai yasa nake ji a jikina tarayyar sa da Abban ku ba alheri bane,na rasa Wanda Zan samu na yiwa magana ya fahimceni Abban ku ya riga da yayi nisa taya haka kawai abokin sa zai d'auko gida sukutum guda ya bashi kyauta ba dangin iya babu na baba ga uban kudin da yake tula masa,hankalina bai kwanta da wanan alherin ba, bani da kwanciyar hankali wallahi dauriya kawai nake tunda muka je wajen mutumin nan godiya nake fama da mugayen mafarkai idan na gaya masa sai ya rufeni da fada dake da Nusrah kawai nake ganin zan iya fadawa damuwa na ku gane yanzu dan Allah Ina Abban ku yaje da tsakar daren nan sai da ya tabbatar da nayi bacci ya tashi ya fice Ina tsoron abokin nan nasa ya koya masa wani mugun halin.

Yesmeen kuwa zare ido kawai take ta kasa kwakwaran motsi dan tasan kunnen Kabiru na wajen su.

Ganin Sajeeda ta damu tana cigaba da magana yasa ta daure murya can kasa tace "Umma in Sha Allah ba wani matsala ki kwantar da hankalinki addua kawai zamu ta yi masa mu Kuma mu ringa dage wa da Addu'a tunda kince ki na mugun mafarki Ki ringa dan tashi daddare kina addu'oi"

Mik'ewa Sajeeda tayi tana "In sha Allah kuwa zan fara Addu'ar bari na duba su Saifullahi idan har ban ga dawowar Abban ku ba sai na dawo dakin ki na kwanta dan bazan iya kwana ni kadai ba.

Mik'ewa Sajeeda tayi da sauri tana "kiyi kwanciyar ki umma bari na dubo su Saifullahi"

Tayi waje da sauri dan so take ta kwana a d'akin nata ko wani uzurin zai saka ta Shiga bandaki ta ga kabirun duk da zuciyar ta cike take fal da tsoro da fargaba amma daga ganin da tayi wa Kabiru jiya tasan dole akwai wani mumunan abun da yake aikatawa idan ba tsafi ba taya zai yi tsirara Yana zagaya wuta daddare.

Ita kanta ta fara tunanin kudin nan da yake cewa abokinsa ya bashi har da kyautar gida ba na Allah da Annabi bane.

Kabiru kuwa iska ya kai wa Naushi a lokacin da ya ji Yesmeen nace wa Sajeeda ta koma ta kwanta wato Yesmeen so take ta tona masa asiri idan kuwa Sajeeda ta shigo bandakin ta gan shi ba abinda zai hana ya kashe Yesmeen.

Sajeeda kuwa koma wa tayi ta kwanta tana ta tunanin Inda Kabiru yayi daddaren nan ta daga kai ta duba agogo taga karfe uku har da minti goma sha biyar.

Tunanin Kiran wayar sa ne ya fado Mata hakane yasa ta mik'e daga kwancen da take ta fito daga d'akin a daidai lokacin da Yesmeen ta fito daga d'akin su Saifullahi.

Da sauri tabi bayan Sajeeda tana "umma kin fasa kwanciya a d'akin nawa"?

"Zan Kira Abban ku a waya ne naji Inda yaje"

Yesmeen bin bayan ta tayi dan ba abinda zai Kai ta komawa d'akin ta.

Kabiru kuwa Yana Jin motsin fitar Sajeeda yayi sauri ya fito daga bandakin Yana leka su Yana ganin sun shige d'aki yayi sauri ya fito daga d'akin ya bud'e k'ofar Palo a hankali ya fice Yana sharce gumi.

Takaicin sa bai samu ya fesawa Yesmeen turaren mantuwar da aka bashi ba tsoron sa Kar ta fadawa Sajeeda wani abu.

Sajeeda kuwa tana shiga d'akin ta,taga wayar Kabiru a gefen gadon.

Haka ta zauna a gefen gado ta buga tagumi.

Yesmeen kuwa ta zauna a kasa tana ta tauna harshen ta bakin ta kaikai kawai yake Kamar ta fadawa Sajeeda abinda ke faruwa bata san Mai yasa take ganin kamar Kabiru zai iya cutar da ita ba amma idan ta tuna kashedi da rantsuwar da Kabiru yayi akan zai kasheta sai taji gwara ta rufe bakin ta gam sai dai za tayi ta addua Allah ya tona masa asiri Sajeeda ta san halin da yake ciki.

Basu jima da Shiga d'akin ba suka ji motsin bud'e k'ofa

Sajeeda ta mik'e tsaye da sauri tayi hanyar waje taci Karo da Kabiru da ya hade rai,

Tuni taji ta kasa Masa ma magana balle ta Masa tambayar inda yaje daddaren nan,Yesmeen kuwa da sauri ta mik'e

Kabiru da ke Jin kamar ya harbeta ya bi ta da kallo Yana "Ke Mai kike yi a d'akin nan"?

"Abban Nusrah farkawa nayi ban gan ka ba shine na kirata tazo ta kwanta anan dan tsoro nake ji yau ma nayi mugun mafarki"

"Daga yau Kar ta Kara shigowa d'akin nan, ke yarinya ce daga na dan fita asibiti na dawo shine har sai kin wani kirata ta tayaki kwana ke Mai yasa baki da lissafi ne"

Fadan borin kunya Kabiru ya rufe Sajeeda dashi ta Inda yake shiga bata nan yake fita ba,Yesmeen kuwa da gudu tayi waje tana Kara Jin tsananin tsoron kabirun.

Sajeeda kuwa tsabar bakin ciki da takaici kuka ta fashe dashi dan bata san Mai tayi da har zai rufeta da fada haka ba.

Ko kallonta bai yi ba ya kwanciyarsa Yana girgiza kafa.
Chapter 10 · 0% Book details