← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 80

Sashe 8

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Karfe biyu na tashi wlh motsi naji Wai dole a gida zan yi Abubuwan nan ba zan iya yi a wani wajen ba"?

"Aikuwa dole a gida zaka yi Kuma indai an gan ka wallahi da matsala ka samo jinin nata"?

"Eee gashi nan a Aljihu na"

"Tom bari mu karasa,tunda tak'i bamu hadin kai ayi ta baya kaga kuwa Dole a biyo mata ta bayan gida"

"Kasan me ke damuna wai tana yawan mafarki dakai abin na damuna dan har ta fara nuna min Kamar kudin da kake bani bana halal bane tana da saurin gano abu fa Ina tsoro asirina ya tonu da Wanan mafarkin da take"

"Ni mai hadina da ita da za ta yi mafarki dani ai da Kai ya Kamata tayi mafarki bani ba"

A haka suka cigaba da hira har Suka karasa wajen.

Ta baya Suka Shiga d'akin da shugaban nasu ke zaune kafin su karasa su zauna shugaban ya daka musu tsawa Yana "ku dakata!!

Cak suka tsaya

Cikin wani irin murya shugaban nasu ya taso da kana masa kallo daya sai gaban ka ya Fadi a d'akin da yake har da kwarangwal din kawunan mutane cikin wani irin murya yace "Rabiu abokin ka jiya ya bata min aiki dan ya bari an gan shi"

Ido Kabiru ya zaro ba dama yayi sallati cikin tashin hankali yace "Shugaba waye ya gani"

Akwai yarinyar da ta gan ka Kuma kasan ka'idan aikinmu indai wani ya ganmu sai mun d'au mataki dan bazamu so ta tonawa wani sirrin mu ba"

Gaban Kabiru ne ya yanke ya Fadi dan Yana tsoron matakin da zaa d'auka akan Yesmeen dan ya gano itace ta gan shi dan ita kadai ce mace a gidan.

"A cikin abu uku dole ayi daya

"Ko mu kasheta
"Ko mu makantar da ita

"Ko mu kurmantar da ita wane za'a mata a ciki"?

Kabiru shiru yayi Yana tunani bai so ayi mata ko daya daga ciki ba amma karambanin ta ya jawo mata a yanda ya fara dandana zakin arzikin nan duk abinda zai kawo masa cikas a cikar burin sa zai iya kau da koma waye tunda har ya yarda zai tab'a Sajeeda

Batare da ya wahalar da kan sa yin dogon tunani ba yace "A kurmantar da ita yadda ko da gani na ta sake yi nasan bata da bakin fadawa kowa"

Gyada kai shugaban nasu yayi ya koma ya zauna sai a lokacin Suka zauna ya fara kafawa kabiru sababin sharruda dan yace na baya duk ya ruguje dan Yesmeen ta b'ata musu aiki a cikin Abubuwan da shugaban nasu yace yayi daya ne yayi balain girgiza shi Kuma shine zai yi na karshe ya samu kudaden.

A haka ya taso bayan ya bashi abinda zai sawa Yesmeen din a abinda zata ci maganar ta ta d'auke.

Sajeeda

Na Rasa Wanda zan fadawa damuwata na rasa Wanda zai fahimtar da Abban Nusrah zuwa yanzu wani irin tsoro nake ji.

Ban yarda da abokin Abban Nusrah ba a yau da na sake mafarki dashi na Kara tabbatar wa kaina abinda nake ji a jikina da gaske ne.

Ko da na farka ban ga Abban Nusrah a d'akin ba hakane yasa nayi tunanin kila ya fita tunda na dan dade Ina baccin.

Fitsarin da ya matseni yasa na shiga bandaki sai da na gama fitsarin na maida wandona har zan fito na tuna pad din da na saka a leda hakane yasa na matsar da randar ruwan dan a bayan randar ruwan na ajiye ledar.

Ga mamakina sai naga ban ga ledar ba,ba inda ban duba a bandakin ba amma ba leda ba dalilin sa haka ne yasa na fito daga d'akina Ina mamakin waye zai d'auke min ledar pad dana cire a jikina.

Ina fitowa palo naga su Saifullahi a barbaje suna karyawa ganin ban ga Yesmeen ba yasa na nufi d'akin ta dan sai nake tunanin kila ita ta Shiga dakina Ina bacci ta shiga bandakin ta d'auke ledar a kwance na tarar da ita tayi rub da ciki.

"Yesmeen"

Da sauri ta dago tana kallo na sai na ganta kamar a firgice

Hakane yasa na zauna a gefen gadon ban amsa gaisuwar da take min ba nace "Yesmeen lafiyar ki kuwa"?

Yatsun hannun ta ta hau murzawa tana motsa bakin ta alamar akwai magana a bakin ta hakane yasa na Kara gyara zamana bana san naga Yesmeen a cikin damuwa ko kad'an

Na ruko hannun ta ina "Yesmeen menene wani abu ne"?

Yesmeen kasa magana tayi tana tunanin yadda zata fadawa Sajeeda abinda ta gani dan abun ya tsaya mata a rai dan har ta hada abincin karyawa ba'a nutse take ba,bata san taya zata fadawa Sajeeda abinda taga Abban yayi jiya daddaren ba,dan har ga Allah yanzu tsoron sa take ji.

"Ina jinki yesmeen menene"?

"Mafarki nayi umma Mara kyau akan Abba mafarkin ya tsaya min a rai"

Da sauri Sajeeda ta gyara zaman ta kirjinta na dukan tara tara Kar dai mugun mafarkin da take itama Yesmeen ke yi sai taji ta ma manta da batun pad.

"Wane irin mafarki Kika yi Yesmeen"?

Yesmeen na k'ok'arin magana Kabiru ya fado d'akin hankalin sa a balain tashe dan ya d'auka Yesmeen ta gama tona masa asiri.

Yesmeen kuwa cikin rawar baki ta hau gaishe shi ya hade rai ya kalli Sajeeda Yana "Mai kike yi anan"?

"Ban dade da tashi daga bacci ba ganin bata falon shine na biyota daki ashe bata Jin dadi Ina tambayarta me ke damun ta ka shigo"

A hankali ya sauke ajiyar zuciya dan ya d'auka ta tona masa asiri.

Ya Kara hade rai Yana "ki fito ki hadamin abincin karyawa"

Daga haka ya fice daga dakin Sajeeda tabi bayan sa.

Yesmeen ta dafe kirjinta da taji kamar zai fado yau sai taga Abban nata ya zama abun tsoro yadda ga gan shi daren jiya ya fado Mata.

Taso ta fadawa Sajeeda kamar mafarki tayi taji ko zata ce wani Abu da zai saka ta Gane maanar abinda yake yi jiya.

Haka ta zauna a daki bata Kara fitowa ba sai wajen daya da Sajeeda ta kwalla Mata kira ta fito daga dakin da sauri ta tarar da dukan su a zaune a palo suna kallo Sajeeda Kuma tana Kitchen hakane yasa ta nufi kitchen din ta hau tayata girkin.

A Palo suka ci abincin rana har da Kabirun ko a fuska bai nuna mata komai ba sai jan yaran yake da Hira.

Wajen karfe biyar yasa Faisal ya d'auko masa leda freezer ya hau fito da yoghurt Yana basu daya bayan daya.

Cikin murna suka hau karba Suna godiya ciki kuwa har da Yesmeen.

Take duk suka fara Shan yoghurt din.

Sajeeda ta aiketa kitchen akan ta d'auko mata kofi.

Yesmeen ta mik'e da yoghurt dinta ta nufi kitchen Annur ya tashi da sauri ya bi bayan ta dan har ya shanye nashi saboda zakin yoghurt din.

Yesmeen kuwa data bud'e yoghurt din ta ajiye akan kitchen cabinet ta sunkuya dan ta d'auko kofin.

Annur yayi sauri ya suri yoghurt din ta ya kafa baki sai da ya shanye rabi ya ajiye Mata ya fito daga kitchen din ta biyo shi a guje har suka dawo palon.

Kabiru kuwa ganin su a guje da robar yoghurt da alama Kuma ta Sha yasa yaji wani irin farin ciki ya rufe shi.

Maganar daya fito daga bakin yesmeen da "umma Kinga Annur ya shanye min yoghurt dina ko"

Kabiru sai yaji Kamar ta gwada Masa guduma akai..........

: Assalamu alaikum wa rahmatullah.

Na ce bara in tunasar daku cewar na shirya aji tsaf don ci gaban mata iyayen gida,A wannan lokacin da sanyi yayiwa mata yawa a matsayin ki na mace yaya kike kula da kanki don kariya daga ɗaukar cutar sanyi ko da mai gida ya na ɗauke da shi?
: Shin kinada labarin sai kin isa ake tafiya dake? Aure nawa ke suke mutuwa saboda mazaje sun gaji da rashin damun isashiyar gamsuwa awurin matayensu?
Da yawan mata basuda labari game da kansu ma bare su nemi maganin matsalar su abu ɗaya suka sani sanyi ko dryness
Kina zaune kinashan maganin da ba shine matsalar taki ba
Kiyi ƙoƙarin shiga wannan ajin da naira dubu ɗaya jal, inda zaki mallaki ilimin da babu mai ƙwace miki shi har abada; A wannan ajin namu zamu baki ilimi akan sanin wace kalar macece ke acikin mata, menene matsalar ki a ɓangaren jikinki, yanda zaki kula da kanki a lokacin saduea da bayan saduwa, dabarun samun gamsuwa yayin jima'a musamman da ragon namiji.
Hanyoyi inganta tukunyar gidan ki, zamu kawo daɗaɗan abubuwan da zasj taimakawa mai gida idan kin mishi ya dawo da ƙarfinsa. Bamu tsaya anan ba zamu koyar da ke yanda zaki haɗa kayan mata 'yan gaske da hannunki, kama daga dahuwar kazar amarya da uwagida, dahuwar 'yan shila, haɗin tsumi kala lala kai abin dai ba'a magana.
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin
Tallafawa tukunyar azuminki ta hanyar koyar dake ƙayatattun girke girke, shu'umar humrah da kuma kulacham ga turaren tsugono don zama tauraruwa👍🏻👍🏻👍🏻
Duk fa wannan akan kuɗi naira dubu ɗaya kacal!
To me kike jira? Maza hanzarta biyan kuɗinki ta wannan asusun akawunt ɗin Saiki tura shaidar biya ta nan👉🏻 07084161619.
Na gode.
2073065733
UBA BANK
SHA'AWA IBRAHIM
*RUFAFFEN SIRRI*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Page 6*

Hankali a tashe ya mik'e tsaye maganar Rabiu da ya tuna yasa ya koma ya zauna Yana zabga sallati a zuciyar sa dan dole ya iya takun sa sabida Kar Sajeeda ta dago shi.

Sajeeda kuwa ta d'auko yoghurt din ta tana "karbi nawa ki shanye Zan Kama shi ne"

Kabiru kuwa ya mik'e yayi waje da sauri Yana fita ya Kira Rabiu cikin tashin hankali kamar zai fasa ihu Yana dagawa ya fara magana cikin tashin hankali "Rabiu Autana na ne ya shanye yoghurt din na Shiga uku ka taimaka ka Kira min shugaba ko da akwai abinda zai iya yi dan Allah dan cikina ne ya Sha yoghurt d'in"
Chapter 8 · 0% Book details