Sashe 77
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yarana kuwa daki suke shige suna ta rizgar kuka,Hamza da Annur da suke je Suka ganewa idonsu halin da yake ciki akan bola,dak'yar aka dawo dasu suma suna ta kuka, tuni aka cika gidanmu wanda rabinsu gulma ne ya kawo su,daga ni har yarana haka muka kulle kanmu a daki, a ranar sai da jinina ya hau,dan sai da aka Kai ga Kaini asibiti shekara ashirn da hudu ba wasa ba hankalina ya tashi da halin da Kabiru ke ciki, bansan Mai ya kawo shi garin nan ba,bansan ya akayi asirinsa ya tonu a bainar jamaa a garin da aka haife shi kowa ya san shi ba.
Nusrah ma sai da aka bata gado wai ana ta kiranta a waya wai an samu wasu sun masa video sun yada a duniya a tsirara yana Haushin Kare,da zuciya na bugawa da na nida yarana ya buga,wai bamu muka aikata ba Amma muke Jin wanan kunyar,wai iya kunyar duniya kenan Ina ga anje lahira,da zaka tsaya agaban Allah,mai yasa Kabiru yazo garin nan yazo ya tona min asiri,dan tamkar ni ya tonawa asiri tunda ya shafa min bakin fenti da yarana.
Daidai su Saifullahi haka suka ringa Kira a waya,bazan iya jure wanan tashin hankali da abin kunyar da Kabiru ya jawo mana akan neman duniya ba,hakan ne yasa na nemi iznin mahaifina akan zan koma garin kano nida yarana dan mutane da gangan suke zuwa su zauna a gidan suna so sugani ko suga yarana,ni kaina abin kallo na zame musu,yaya Asmau ce ta ringa tausa ta,ba abinda ya rage kowa yasan halin da muke ciki, mahaifina Kuma yace nayi zamana anan din bai yarda naje ko'ina ba,tuni na mika lamarina wajen Allah,duk da ba wai gama warkewa nayi ba,haka na daure na ringa kwantarwa da yarana hankali,dan a karshe unguwar muka bari muka koma wani unguwar wajen dangin mahaifina,Nusrah tayi wani irin rama gata da danyen jego a jiki,tashin hankalinta nasan bai Wuce mijinta da bai tab'a kiranta a waya tunda tazo garin ba idan itace ta kirashi kuwa baya dauka,tun tana boye min sai da na gano,na hau kwantar mata da hankali wanan Yana cikin kaddararmu bamu isa mu kauce masa ba,nasan abinda Kabiru ya aikata sai yayi balain shafar yarana,kila Mijin Nusrah sai ya rabu da ita,tunda bazai kasa samun labari ba tunda har a gidan radio an bada labarin Wanda jikinsa ya makale a jikin Kare yake Kuma kukan karen,dan a yadda naji har daga wani wajen ake zuwa ganinsa, gashi an kasa Kama shi balle a killace shi,mahaifina balain tausayin shi yake ji,kamar yadda nima naji Ina tausayinsa,a da na dauka bazan tab'a iya yafe Masa ba,a da na dauka da zan ga abinda zai cutar dashi kau da kaina zanyi sai gashi na tsinci Kaina da tausayin halin da yake ciki,Wanda ni nasan Allah ne ya tona Masa asiri,da asirin nasa ma ya tashi tonuwa sai ya tonu a bainar jamaa,duk wanan masifar da ya jefa kansa akan neman duniya ne,ga Inda Neman duniyar yayi dashi,mun gina rayuwar mu cikin kwanciya hankali da soyayya san zuciyarsa ya Kai shi neman kudin haram ya jefa kansa a masifa ya saka mu a tashin hankali duk abinan ko shekara uku baiyi ba.
kwana biyu da komawar mu gidan kanin mahaifina Saifullahi da Fahad suka zo daddare,rabona dasu shekara daya kenan da watani,yarana sun zama Samari sosai,haka muka rungume juna muna kuka.
Sai tambayoyi suke min da banida amsar tambayar su,akan abinda ya samu Kabiru har ya haukace,a takaice a daren Suka bi dare da rakiyar su Annur Suka gano Kabiru da ke saman bola Yana tsince tsince,sai da suka dawo cikin kuka Suka hau bani labarin yadda jikinsa ya koma kamar na Karen, fuskarsa ce kawai bata canza ba,wai Yana ganinsu ya daina haushi ya zubo musu Ido yana kallon su.
A ranar dagani har yarana sai da muka ci kuka muka gode Allah.
Annur sai cewa yake a dauko shi a Kai shi asibiti yarana ma balain tausayin shi suke, Saifullahi sai cewa suke Ina ma ace sun gano da kila basu bari yayi nisa ba,anan suke bani labarin yadda komai nasu ya kone,har da na Yaran abokin Kabiru Rabiu sai a wajensu nake Jin wai ya rasu,yayansa kamar su haukace da suka ji rasuwarsa,Suma sun gano kudin nasa bana halal bane.
Saifullahi cikin kuka ya ringa bani labarin yadda ya ringa kawo zargin mahaifunsu daga baya sai ya watsar dan gani yake bazai taba kauce hanya dan ya samu kudi ba.
A takaice Saifullahi shi ya nemo Mana gida a Kano ya roki mahaifina akan Yana so mu koma can,dan idan muka bar garin zamu dan samu nutsuwa,idan an kwana biyu zai san yadda zai yi yasa azo a dauki Kabiru,dan yana da kudin da ake biyansa na zanne da yake tarawa, dan kaf makarantar su ba Wanda ya Kai shi iya zanne wanda har masu kudi nemansa suke dan ya musu zannen da ya ringa shigo Masa da kudi.
Mahaifina albarka ya sawa Saifullahi dan da Kabiru baiyi gaggawa ba da ya samu kudin ta hanyar Saifullahi dan da dukan alamu Saifullahi shi zai zama silar da zasu yi kudin.
Yaya Abu
Tunda Kabiru ya fita ya barta a d'akin da aka kaita ta ringa rusa ihu,tana nadamar biyo kabirun da tayi,sai a yanzu ta fara nadamar zuwa ma gidansa,yau gashi garin kwadayin ta bayan nemanta da yayi ta gaba da baya,da a yanzu ruwa zubo mata kawai yake Yana bin kafarta mai balain wari,duk haka bai ishe sa ba sai ya kawo ta an yankata,sai a yanzu take nadamar duk Abubuwan da ta aikata,kila hakkin Sajeeda ne ma ya Kamata,kila muguntar da tayi ne duk yake dawo mata, Ina ma tana da yadda zata tsira da ranta wani irin sanyi take ji dan zazzabi ne ya rufeta tana Jin kamar karfin Jikinta na raguwa,kaikaiyi da zugi kawai take ji tun tana iya kuka da k'arfi har sai da ta koma kukan zuci,shigowar shugaban a tsirara da wani tukunyar kasa dake ci da wuta yasa ta mik'ewa a zabure tana ya mata rai,Kar ya kasheta,bai ko saurareta ba ya ajiye tukunyar kasar,ya Ciro wani abu.kamar fifiken kaza daga tukunyar kasar ya nufo wajen da ta manne da bango ya hau shafa goshinta Yana gwarancin da bata gane ba, ihu kawai take tana sallati,idan tayi sallati sai ya buge bakinta,a haka ya Kara ficewa daga d'akin,Yaya Abu kuwa ta zub'e a kasa ta hau Kiran sunayen Allah dan da iliminta sarai,kawai shagala yasa bata wani maida hankali,zata so ta nemi yafiyar Iyayenta kafin ta mutu,zata so taga Sajeeda ta nemi yafiyar ta zata so taga Yarta kafin ta mutu, tun tana iya Addu'a da k'arfi har sai da taji numfashinta na neman d'aukewa.
Haka ta kwanta tana Jin azabar radadi a jikinta,ga zazzabi mai zafi,da ace bata biyo Kabiru ba da kila ta samu ta tsira Koda babu kudin.
Tana nan a kwance taga shugaban ya dawo da wasu maza uku da ido ta ringa binsu dan bata da karfin motsawa sai hawaye dake zubo Mata,umarni ya bawa daya daga cikinsu akan ya dagata ayi mata aski a fita da ita dan karfe biyar zai yanka ta.
Mik'ewa tayi cikin tashin hankali da taji yankata zaiyi tuni ta nemi rashin lafiya da take ciki ta rasa ta hau ihu tana Kiran sunayen Allah akan yazo ya taimaka mata,tana ji tana gani suka ririketa Suka Mata kwal kwabo,suka daga ta sama suka fita da ita waje bayan sun bade kanta da wani abu da take tunanin Hoda ne.
Kashi da fitsari haka ta ringa saki saboda akwai tashin hankali Wai kaga mutuwa da idonka,wayanda zasu kashekan ma basu San Allah ba balle suyi imani, a wani karamin daki suka ajiyeta dake d'auke da kwarangwal din kawunan mutane,suna ajiyeta suka fice daga d'akin.
Yaya Abu da take Jin Kamar ta mutu ma tun kafin a kasheta ta fara sallati tana neman hanyar da zata gudu,kamar ance ta kalli bakin k'ofar ta hango abu kamar mukulli jiki na rawa ta karasa bakin kofa tana zuwa ta dauki mukullin Kamar Wasa ta zura a k'ofar taga ya bud'u.
Ta bud'e k'ofar a hankali ta fito, batasan ma wajen da suka ajiyeta ba dan kamar bayan gidan ne, ga karnuka nan sunfi hamsin da aka daure,tuni ta fara neman hanyar da zata bi ta gudu,sai dai duk Inda taso ta samu hanya bata samu ba,waige waige ta hau yi ta hango wani drum a kife a wajen katangar,da balain sauri ta danne drum din har tana kurjewa a kafa ta daka tsalle ta hau katangar ta dira,tana dira ta sa gudu,duk da batasan Ina ta nufa ba haka ta ringa tikar gudu,kayoyi na soke Mata kafa ko damuwa batayi da ta tsaya ba,sai da ta fara Jin jiri,da rashin k'arfi tun tana daurewa har sai da duhu ya gifta mata ta yanke Jiki ta Fadi .....
Kuyi hakuri,wallahi wayata ta samu matsala sai da ya goge gabadaya wajen tara na sake typin gobe dai zan gama in Sha Allah naso a yau na gama
*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*
*PAGE* *97-100*