← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 80

Sashe 20

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata wani samu baccin kirki ba dan gani take tana kwanciya Kabiru zai iya shigowa d'akin,a duniya ba Wanda take tsoro sama da Kabiru,a jiya sau uku tana taka abu dan ta cire glass din fitilar d'akin ta tsoro na hanata tasan akwai abu a cikin fitilar, mafarkin da tayi da ta kunna wutar d'akin ta hau ihun idonta ya tsaya Mata a zuciya,sai ta tafi tunanin yadda Annur ya kurmance tasan ita Kabiru ya so ta kurmance Allah ya tsallakar da ita,shine ya Kara biyo wa ta wanan hanyar dan ya makantar da ita tunda tasan sirrinsa sau uku tana mafarki iri daya ta kunna fitilar ta makance,bata mafarki a banza dan Sajeeda ma hanata take ta Fadi mafarkin da tayi,dan Haka ma mahaifiyar ta take indai tayi mafarki sai ya tabbata saboda ance tana da Aljannu,shiyasa da aka gano itama in tayi mafarkin tabbata yake aka hanata fadar mafarki saboda Kar a fassarata.

Tasan da akwai matsala indai ta kunna fitilar d'akin

Koda ta iddar da Sallah asuba bata koma bacci ba azkar kawai ta ringa yi zuciyarta na wajen Sajeeda rabin adduata akan Sajeeda ne,

Karfe shidda ta fito daga daki dan ta fara aikace aikacen da ta saba dan su koma hutun makaranta tana ss2 a yanzu.

Yau gabadaya bata ji motsin Kabiru ba.

Koda ta Gama share ko'ina Dustin bin din kitchen daya cika da shara ta d'auka dan taje ta zubar a a katon Dustin din dake wajen hanyar fita.

Tana zuwa ta zubar da sharan muryar Kabiru da taji Yana magana a waje yasa ta tsaya cak kirjinta na bugawa da Jin ya ambaci sunanta.

Hakane yasa ta Kara gyara tsayuwarta tana Jin Mai yake cewa,abinda taji yasa ta zaro ido jikinta na d'aukar rawa sallati kawai take a zuciyarta hankali a tashe ta koma cikin gidan ya shige daki ta hau safa da marwa in ta zauna bata tsira ba in ta gudu ma bata tsira ba dole tasan nayi kafin Kabiru ya samu cikar burinsa a kanta tuni taji bama zata iya zuwa makarantar ba.

Tana Jin motsin Hamza da Annur Amma ta kasa fitowa.

Jikinta rawa kawai yake har taji Kabiru ya shigo Yana tambayar su Hamza inda take ya hau kwalla mata Kira ta fito a guje.

Ya daka mata tsawa akan ta hada wa su Hamza tea su Sha shayi su tafi makaranta.

Jiki na rawa ta shige kitchen ta hau hada breakfast.

Sajeeda

Ban farka ba sai wajen goma da rabi na safe Koda na farka ba kowa a d'akin,Ina k'ok'arin mik'ewa tsaye naji wani irin kaikaiyi a gabana tuni na saka hannu na fara susa da na tuna ruwan daya zubo min jiya mai wari sai naji hankalina ya Kara tashi Ina cikin susa Abban Nusrah ya shigo da faranti a hannun sa.

"Kin tashi"?

Ban iya bashi amsa ba har ya zauna Hannuna a cikin zani Ina susa,wai jikin naki ne har yanzu"

Tun dazu nake so na tashe ki ki karya na Kai ki asibiti a duba ki bansan Mai ya kawo Miki wanan ruwan ba"

Karbi shayi ki sha da magungunan ki idan kin gama sai mu tafi.

Bata abinci nake ba hakane yasa na girgiza Masa Kai akan bazan ci ba ya dage min akan sai na karya

Koda na karya na shirya dan muje asibitin yayata Abu ce ta kirani akan suna hanya ita da yar kanwar babarmu Asmau sun kusa isowa.

Hakane yasa na cire hijabina na koma na kwanta nace masa ya bari idan su Yaya Abu sun tafi sai muje asibitin a yanzu ma kaikayin ya ragu amma har yanzu hankalina a tashe yake da ruwan da ya zubo min mai wari jiya.

Zama yayi a gefena ya hau jana da hira Yana
"Saifullahi da Fahad sun samu Admission a kasar waje abokina Rabiu ya taimaka min an samo musu acan Ina tunanin karshen watan nan zasu tafi kinsan a duniya burina naga yarana sunyi makaranta Mai kyau,yadda zasu samu aiki mai kyau a baya dama dan bani dashi ne amma tunda yanzu Allah ya hore min zan tsaya musu har sai sun samu ingantaciyar rayuwa,Hamza Kuma da Annur zan canza musu makaranta"

Da ido nake bin sa har ya idda magana na fara Jin tsoron Abban Nusrah a kasa da wata hudu da sati yayi wanan kudin har zai kai su Saifullahi waje karatu.

"Kinyi shiru baki ce komai ba sai kallo na kike"?

"Abban Nusrah abokin nan naka kai kadai kawai yake taimakawa bashi da Yan uwa ko wasu abokanan a gaskiya Abban Nusrah na fara tsoro ta da lamarin ku biyu idan ba dan fashi bane ko dan yankan kai Ina zai samu kudin da zai ringa kashe maka haka,Abban Nusrah na roke ka da girman Allah ka rufamin asiri kar ka biye wa abokin ka ya saka ka a hanyar da bata dace ba, arzikin nan idan muna da rabo za muyi shi cikin kwanciyar hankali indai Yana rubuce a kaddarar mu jikina bai bani kudin nan ta hanyar halal ake samun sa ba,dan Allah ka maida masa gidansa da kudadensa daga tarewar mu a gidanan Annur ya kurmance,banda mugayen mafarkai da nake fama dashi Abban Nusrah bazan yarda a Kai min Yara kasar waje ba kila ma yaudarar ka yake so yake ya sace min Yaya yayi kudi dasu

Kabiru ya matukar girgiza da maganar Sajeeda ya d'auka aikin da yace a Mata bazai tab'a sawa ta iya Masa magana ko musu ba,da alama sai ya Kara sabunta aiki akanta dan ba yaso tunanin ta ma ya Kai sai da ya kwanta da ita jikinta ya fara canjawa,ko shi ya grigiza da ganin ruwan jiya,dan basu fada masa wani abu zai same ta ba idan ya kwanta da ita bayan ya sadu da kare.

Murmushi ya saki Yana "Ba matsala tunda bakya so a kai yaran nan waje karatu amma inaso kisani da hankalina da ilimina ba yadda za'ayi na ringa karbar kudin da ba na halal ba,ki bari idan kin warke ki nemi wani ya miki bincike a kan Alhaji Rabiu,kudin halal ne ki kwantar da hankalin ki ki mori arziki tunda ke ma da bakin ki kince idan Allah ya rubuta zamu Yi arzikin nan sai munyi toh lokacin arzikin namu ne yayi"

Nidai bance komai ba,dan Sam magnarsa bata shigeni ba ban yarda da kudin nan na halal ne ba.

Ganin ban magana ba yasa yace min zai fita ai yasan su Yaya Abu kwana za suyi in ya dawo zasu gaisa.

Yaje bakin kofa kenan muka jiyo ihun Yesmeen tana "Wayyo idona"

Kabiru ya bud'e k'ofar ya fita da gudu,na take masa baya Ina Jin kamar na Fadi saboda iskar dake neman kayar dani....

Rufaffen sirri na kudine biya 500 zuwa acct dinan 2029764071 first bank nafisa Nuhu ko Katin mtn a lambar Nan 08033719070 ko wanan lambar 08068484400 sai a turo da shaidar biya ta wanan layin 08033719070 ko wanan 08068484400. Mutanen Niger ku nemi layin Nan. +227 96 82 89 84

Labarin rufaffen sirri labarine da ya faru a gaske wacce take a matsayin Yesmeen ta bani labarin nan, bazan iya canja rubutun dan na faranta muku ba is already past Sajeeda bata Isa ta canza kaddarar ta ba ku cigaba da bibiyar labarin kawai...

ALJALAL HALAWA(TAHANIYYA)
Gumbar ridi tasamo asali daga kasashen Larabawa, tana da matukar amfani ga jikin dan Adam especially mace, tana Kara ni'ima ga mata, tana taimakawa mata masu shayarwa su samu ruwan nono, haka ma maza tana taka muhimmiyar rawa ajikinsu s0sai.

Tana da amfani ga yara sbd tana kunshe da sinadaran Zinc da Calcium, tana gyara Kashi da Fata, anasawa a bread in za'ayi breakfast aci, ana damawa da Madara ana damawa da nono ko da yoghurt asha, batasan zafi ana ajeta gu Mai sanyi, anaci hakannan gidajen Larabawa basa rabuwa da ita ko yaushe tana cikin tsarin abincinsu sbd ingancinta da amfaninta; Yar'uwa/dan'uwa me kike Jira ko kake Jira. Siyawa iyalanki/iyalanka sbd amfaninta ga jikinku. Domin siyan Daya ko sari??????08062991549

Maibukata yayi magana zakusamu agun mg's skincare kamfanin da kukasan sun shahara indai afannin gyaran jikine 08062991549 😍
.ALJALAL HALAWA(TAHANIYYA)
Gumbar ridi tasamo asali daga kasashen Larabawa, tana da matukar amfani ga jikin dan Adam especially mace, tana Kara ni'ima ga mata, tana taimakawa mata masu shayarwa su samu ruwan nono, haka ma maza tana taka muhimmiyar rawa ajikinsu s0sai.

Tana da amfani ga yara sbd tana kunshe da sinadaran Zinc da Calcium, tana gyara Kashi da Fata, anasawa a bread in za'ayi breakfast aci, ana damawa da Madara ana damawa da nono ko da yoghurt asha, batasan zafi ana ajeta gu Mai sanyi, anaci hakannan gidajen Larabawa basa rabuwa da ita ko yaushe tana cikin tsarin abincinsu sbd ingancinta da amfaninta; Yar'uwa/dan'uwa me kike Jira ko kake Jira. Siyawa iyalanki/iyalanka sbd amfaninta ga jikinku. Domin siyan Daya ko sari??????08062991549

Maibukata yayi magana zakusamu agun mg's skincare kamfanin da kukasan sun shahara indai afannin gyaran jikine 08062991549 😍

*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 13*

A wajen makunin d'akin ta ta tsaya tana ta tsalle da hannuwanta biyu a idonta tana murzawa sai ihu take tana "Umma ku taimaka min idona Abba idona"

Hankali a tashe na ruko ta Ina duba glass din fitilar d'akin dake watse a kasa,Ina "Mai ya samu idon naki Yesmeen innalillahi wa Inna ilaihi rajiun muga idon naki"

Na Kara rukota Ina k'ok'arin raba hannun ta da fuskarta amma fir tak'i sakin fuskarta sai tsalle take tana ihun idonta.
Chapter 20 · 0% Book details