← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 80

Sashe 76

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jiki na rawa ya Shiga motarsa Yana mamakin yadda Rabiu ya Zama Mai kudi,dan kayan jikinsa da motar sa kawai ya nuna kudi sun zauna,a ranar Rabiu ya danka Masa kyautar dubu dari,ya bashi lambar wayarsa,akan ya kirashi,yayi nadamar haduwa da Rabiu,dan daga kiransa akan ya Masa hanya yayi kudi,ya dorasa akan mumunan hanya Wanda da fari sai da ya bijire yace bazai iya ba, Rabiu ya hau wanke shi da kudade da har sai da ya kwadaita masa yaji zai iya komai dan ya samu kudin,yau ribar mai yaci a Shiga kungiyar matarsa Mai kaunarsa mai rufa Masa asiri,ya butulce mata yayi amfani da ita ya kassara mata rayuwa,tunda yake bai tab'a aikata zina ba sai gashi da girmansa da yayansa ya hau neman Mata,ya kwanta da Kare yaje makabarta yasa layya a bakin gawa,ya daina sallah gabadaya duk a Kan kudin da zai iya mutuwa ya bari Kamar yadda Rabiu ya tafi cikin kiftawar Ido,Allah ya dauki ransa,mai ya Kai shi jefa kansa a cikin wanan masifa yanzu ya ma Zama kafiri tunda baya sallah,taya zai nemi yafiyar Allah daga Ina zai fara.

Kuka kawai yake har Yana Jin zazzabi na neman rufe shi.

A haka mahaifiyarsa ta shigo ta sameshi.

Hankali a tashe tayi kansa tana "Kabiru Wai Mai yake damunka Mai kake boye min Kabiru yanzu da na fita akace Sajeeda ta dawo gida ni bangane mai ke faruwa ba, Kabiru kana da sama dani ne Mai ke faruwa ne ka fadamin ni mahaifiyar ka ce zan iya maka addua ko na taimaka ma da shawara"

Kabiru kuka kawai yake dan bazai tab'a iya bude baki ya fada mata abinda ke faruwa ba,ya faro kuruciyarsa da kyau,tsakiyar rayuwarsa da kyau wai sai da yaje matakin karshe ya kauce ha ya saboda san zuciya da san abun duniya ko da asirinsa bai taba tonuwa ba ace duk abinda yake so Yana samu dole watarana ya mutu ya bar duk abinda ya tara dan baza'a bine shi da komai ba sai kyawawan ayyukan sa.

Mahaifiyar sa kuka ta saka masa tana ya fada mata damuwarsa dan bata san Mai yasa gabanta ke faduwa Kamar akwai abinda zai same shi ba ya fada Mata koma menene ita mai rufa masa asirine"

Kabiru da ya fara Jin Kamar ana cire Masa Abu a jikinsa ya bud'e bakinsa dak'yar Yana "Kiyimin addua kawai Hajiya adduar ki nake bukata"

Hajiya na k'ok'arin magana sai ga wasu sun shigo aguje suna motarsa ta Kama da wuta.

Hajiya ta mike hankali a tashe Kabiru kuwa ya rufe idonsa dan yasan duk sai sun karbe abinda Suka bashi.

Kiran da ya shigo wayarsa yasa ya dauka makocinsa ne yace gidansa ya Kama da wuta.

Bai ce komai ba ya kashe wayar.

Tuna gidan da ya ginawa mahaifiyar sa ma da kudin kungiya ne yasa ya mik'e a zabure Yana "Hajiya mu bar gidanan yanzu Nan kizo mu fita karki d'auki komai"

Hajiyarsa na k'ok'arin magana yaja hannunta da sauri suka fita.

Suna fita gidan ya Kama da wuta kamar an jefa bomb

Hajiyarsa ta fara ihun sallati tana neman fita a hayyacinta.

Kabiru kuwa ya hau Jan hannunta dan mutane sun fara k'ok'arin kawo agaji Wai zasu kashe motar dake taci da wuta da gidan.

A takaice Kabiru tsohon gidan da mahaifinsa ya gina Suka koma gabad'aya ji yake kamar ya yanke Jiki ya Fadi,mahaifiyarsa kuwa sai tambayarsa take akan ya fada mata mai ke faruwa.

Amma Kabiru yaki magana Dan yanzu yasan zasu iya kashe shi a kowane lokaci so yake ya nemi Sajeeda ya nemi yafiyarta so yake ya sake saka yaransa a idonsa amma ji yake bazai iya ba dan jikinsa ba kwari haka ya kwanta idonsa a rufe Yana Jin zuciyarsa kamar ana hura masa wuta saboda zafi,a karshe dai yasan kashe shi zasuyi Mai zai cewa Allah,yasan tun a kabarinsa zai fara girbar abinda ya shuka.

Mahaifiyarsa haka ta saka shi agaba sai kuka take,duk abincin da ta kawo masa baici ba Yana kwance idonsa a rufe kwmar matace ya kira Saifullahi Yana Jin muryar sa ya kashe waayar duk yaran ba Wanda bai Kira ba amma ba Wanda ya d'auki wayarsa,ya Kira lambar Sajeeda a kashe,Ina ma da yadda zasu yafe masa.

A Haka mahaifiyar sa ta kwanta a gefensa tun tana zaune har sai da ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita.

Wajen karfe uku yaji wani irin iska ya shigo d'akin kafin ya gane Mai ke faruwa sai yaji ana ta Kiran sunan sa Kamar daga nesa,kamar Wanda ake bawa umarni ya mike Yana jin jikinsa na d'aukar wani irin zafi,gabansa ya mik'e Yana harbawa.

Waje ya fita yana jin magana a kunensa,kamar zai haukace ya hau fara gurnani shi kadai Yana dube dube,nesa da gidan ya hango wani katon karya bai yi wata wata ba yayi Kan Karyar,Yana zuwa ya damketa Karyar na cizonsa jikins na jini,haka ya hau saduwa da karyar,Yana gurnani,Yana Jin jikinsa na d'aukar wani irin zafi.

Ji yake jikinsa Kamar ya Kama da wuta a jikin karyar ya fara k'ok'arin zare jikinsa daga jikin karyar da ta daina motsi,sai yaji Kamar an like jikinsa da Gam,ya kasa zarewa,idan yaja da k'arfi sai yaji Kamar numfashinsa ake zarewa, tuni ya fara ihu,a wanan halin aka fara kiraye kirayen sallah asuba.

Mutane suka fara fitowa dan su tafi massallaci,Suka ga Kabiru a durkushe jikinsa a jikin karya,sai gurnani yake Yana ihu Kamar ta karyar.

Tuni wasu Suka kasa zuwa massallacin Suka zagaye shi suna sallati,kad'an daga ciki Suka gano ai Kabiru ne, sallatin da ake ta zubawa yasa mahaifiyar sa fitowa da gudu,tana zuwa taga halin da Kabiru ke ciki ta yanke Jiki ta fadi,tuni mutane Suka taru suna kallon Kabiru dake Haushin Kare da Kuma alama jikinsa ya manne da na Karyar da bata motsi,abinka da karamin gari,tuni labari ya Kai ko Ina,a wayanda suka zo ganinsa har da mahaifin Sajeeda da hankalinsa ya yi matukar tashi,dak'yar ya koma gida dan tunda yake bai tab'a ganin abinda ya girgiza shi haka ba.

Sai manya a cikin garin ne Suka d'auke Kabiru da karyar dan har yara sun fara jifansa.

A takaice sai da mallamai Suka zo da karfin Addu'a aka iya raba Kabiru da jikin karyar, Kabiru kuwa sai haushin kare yake,jikinsa ya fara komawa na Karyar,sai susa yake Yana ihu,yana k'ok'arin cizge gabansa dake ta jini, tuni aka yanke a daure shi dan jiwa kansa ciwo yake,sai dai suna k'ok'arin Kama shi ya ture su ya diba a guje a tsirara Yana Haushin Kare.

Allah ya tsare Mana imaninmu ya hanemu da kauce hanya alfarmar Annabi Muhammad sallalahu alaihi wa salam.

Mahaifiyarsa kuwa jininta wani irin Hawa yayi Wanda sai da aka kaita asibiti aka bata gado.

Sajeeda...........

2nd to the last page in Sha Allah munzo gangara ko?

*AYYIRIRIRI AHAYYE CHAS 💃🏼💃🏼💃🏼 sunan wata waƙa wai ita LUWAI*
_Ana tayi muna tayi manyan mata dai da gaske sun dage sai sun zama kalar gaban mota kalar camera tare da gudummawar Mg's skin care Hajia ta kina ina ake ta wannan harkar arziƙin mata nata glowing suna faranta zuciyar mazajensu da laushi da santsin fatar su ke kina nan kina fama jiki duk kirci😱😱?_
Ah haba madam yunƙuro ayi tafiyar nan dake ki shiga ki wataya acikin shahararrun matan nan da ko'ina ake fatan gani dan an daɗe ana jin su watau *team glow by Mg's*
Macen da ta isa itace mace karki bari ki zama cikin irin muna matan nan da suka rako mata duniya kuna tafe da mijinki yana kallon wata har miyau na zuba tsabar haɗuwarta da kyan fatarta
Mg's skin care sune sirrin duk wata macen da ta isa a ɗaga kai a kira da suna mace wacce ba'a jin kunyar shiga taro da ita daga nan har villah kizo/kuzo mu haɗe a wannan ƙasaitacciyar tafiyar ta Mg's skin care domin sune na gaban gaba sune suka ciri tuta indai a harkar gyaran skin ce hajiata kiyi wani fresh kiyi smooth wow🥰🥰🥰kina tafe kina walwali idan fa kina amfani da *Mg's skin care* ba kya buƙatar ko wanne irin mai product ɗinmu katt ne duk matsalar fatarki muna da maganinta uhmm inata miki labari nace ba sister shin meye matsalarki ta gaban goshin ƴallaɓai?
Acne?, pimples? spot?, strech marks?, sunburn?.
to hutas bi'izinilLah muna da maganin matsalarki kina ganin mata a tiktok fuska luwai lumus kice dama ni ko? to in dai kina tare da *Mg's* matsalarki tazo ƙarshe bama cika baki gaskiya itace takenmu haka nan kuma siyen nagari mai da kuɗi gida *MG's skin care gagarabadau*
Price ɗinmu daidaitacce ne sannan kuma dai dai da aljihunku

*Soap price:4k*
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare

Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki
Small 14k
Babba 16k

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Sanan Kuma akwai kit
Karami 12k Abubuwa 6 ne aciki😱😱😱 wannan garaɓasa har ina?
Soap
Body cream
Face cream
Scrub
Cleanser
Oil
*BE PART OF THE GLOW TEAM KARKU BARI A BAKU LABARI

**WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*

*PAGE 96-*

Sajeeda

Nayi kuka Kamar raina zai fita a lokacin da labari ya iskemu akan halin da Kabiru ke ciki,na kasa yarda wai uban yayana ne ya haukace yake Haushin kare

Babana ma kuwa har da zazzabin sa dan da alama abinda ya gani ya tayar Mai da hankali,jikinsa sai rawa yake Yana zuba sallati,yana "Akan neman duniya akan kudi Kabiru ya cutar da kansa haka"??
Chapter 76 · 0% Book details