Sashe 80
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Kirjina wani irin bugawa yayi naja da baya tare da sakin sallati jikina ya dauki rawa,Taya wanan tsohuwar zata zama Yaya Abu, sallati kawai nake Saifullahi ya hau bani labarin yadda ya ganta da ya d'auko hanyar tahowa motarsa ta lalace,a garin Nemo mai gyara motar ya dan shiga bayan gari shine ya ganta a kwance kudaje nata binta ya dauka ma mutuwa tayi Saboda warin da take sai da ya tambayi mai gyaran motar ya hau bashi labarin ta akan almajira ce da suka kasa gane wane irin cuta ne da ita mutane ma kyankyamin ta suke dan har yanzu ma mamaki suke da bata mutu ba,cikin tausayawa Saifullahi ya matsa kusa da ita dan ya bata kyautar kudi,a daidai lokacin da ta bud'e idonta tana numfarfashi duk da tsufan da yaga tayi da yadda koma kamar kwarangwal sai da ya ganeta,jiki na rawa ya roki Mai gyaran mota akan ya taimaka masa zai biya ko nawa ne,a samu wasu su wanke ta a canza mata Kaya,yayar mahaifiyar sa ce da ake ta nema,abinka da kudi,tuni ya samo wasu mata suka kaita gidansu Suka wanketa suka Nemo Kaya suka saka Mata Saifullahi ya Basu kyautar kudi,ana gama gyara Masa mota suka dau hanya yasan Sajeeda zata ji dadi, dan daidaikun rana ne bata maganar Yaya Abun
Sajeeda
Kuka na fashe dashi,dan ba Wanda zai yarda Yaya Abu ce ta dawo haka,itama kallona kawai take tana hawaye ba mai imanin da zai kalli Yaya Abu bai tausaya mata ba,jiki na rawa na kaita bandaki dan wari kawai take,banji kyankyaminta ba na wanketa na bata abinci na Kira Gwaggo a waya na sanar mata da anga Yaya Abu yanzu haka tana gidana,yarana ma sosai suka tayani murna dan ban basu fuskar da zasu tsani yayata ba,tuni na hau hidima da ita,dan har ga Allah na yafe mata,ita kuwa kuka kawai take tana gurnani,Wanda halin da take ciki ya tuna min da Nima halin da na Shiga a baya, washegari da sassafe gwaggo ta duro ita da Yaya Asmau da Yar Yaya abu shemau suma sun girgiza da yadda ta dawo,shemau sai kuka take dan ta dade bata ganta ba,ita kanta batasan Mai yasa bata nemi Yaya Abu ba duk tsawon lokacin nan
Kuka muka ci muka koshi muka hau Taya Yaya Abu da Addu'a dan nasan ba maganin da zai warkar da ita sai karfin Addu'a.
A.ranar da ta cika kwana shidda a gidana muna d'akin a zaune ciki kuwa har da Gwaggo dan baba bai dade da tafiya ba shi ma yazo ya dubata ba Wanda ma zai rike yaya Abu a ransa da idan ya ganta Bai ji tausayin ta ba,
Ganin kamar tana so a tayarta zaune yasa na mikar da ita na jingina bayanta da jikin gadon hawaye na zubo mata naga ta fara motsa baki kamar mai koyon maganar ta fara "Sssaaj jj ee da ki yafe min Gwaggo dan Allah ki yafemin,kice baba ya yafemin, Yesmeen ki yafemin dan Allah ku yafemin na yafewa Kabiru dan inaso nima Allah ya yafemin.
A rude muka hada baki wajen cewa mun yafe mata Gwaggo kuwa sai saka Mata albarka take,a hankali muka ga ta fara shakuwa muka yi kanta gabad'aya cikin kiftawar ido ta daina motsi Yaya Abu ta amsa Kiran Allah
Munyi kuka Kamar ranmu zai fita,Muna ji muna gani aka yi Mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya duniya zancen banza,duk San mu da duniya dole mu tafi watarana tunda mutuwa dole ce,a kwana a tashi sai gashi mun tafi wata biyar da rasuwar Yaya Abu da muke ta binta da Addu'a dacewa da Rahamar Allah
Kabiru kuwa da ya dawo hayyacinsa kad'an tilastawa yayansa yayi suka kirani Yana kuka ya hau Neman yafiyata nace Masa na yafe Masa yayansa suma suka ringa tayashi kukan,da Addu'a ya bimu gabad'aya sai da muka zo tafiya ya bawa Annur wani farin takarda akan ya bani, muna fita daga asibitin ya bani Ina dubawa naga takarda saki ne ya sakeni saki daya Wanda har ga Allah Dadi naji dan ko ya warke ba koma Masa zanyi ba.
Cikin sauki ya bani takarda ta a haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin rufin asiri, Saifullahi kuwa budi yake samu ko ta Ina Fahad shi ma ya samu aiki,Nusrah kuwa mallaminta daya dage mata sai da ya turo magabatansa aka sa musu rana, ni kuwa ganin Yesmeen na tsalle tsalle da Saifullahi na Kira Saifullahi har daki na fada masa Ina so ya auri Yesmeen dan babban burina kenan a rayuwata na dade da burin nan a zuciyata amma idan Yana ganin bazai iya aurenta ba shikenan.
Ga mamakina Saifullahi take ya amince da auren Yesmeen
Toh mai ya ragemin a rayuwa babu,Kamar a mafarki sai gashi na aurar da yayana uku Rana daya, Saifullahi a gidan da ya gina ya ware bangarensa da na Yesmeen Nusrahh kuwa itama bata da nisa dani,ba abinda yayi farko da bashi da karshe wuyanta kayi hakuri, Kabiru har gobe Yana asibiti dan idan ciwon nasa ya tashi Yana dan tab'a hauka.
Shekara biyu a tsakani Saifullahi ya biya Mana muka je muka sauke faralli ni dashi da Yesmeen da ke hidima dani kamar a baya.
Yanzu zan iya cewa Alhamdulillah rabbil alameen dan yarana gabad'aya ba Wanda bashida abin yi ta hanyar halal har rububin kyautata min suke,duk da ba tsufa nayi ba bana kawowa kaina aure Wai kusa bansani ba ko nan gaba.......
Alhamdulillah rabbil ala meen anan na kawo karshen littafin RUFAFFEN SIRRI kuskuren da nayi a ciki rabbi ya gafarta min nagode da fatan alheri da hakurin da akayi wajen bibiyar littafin sai mun sake haduwa a sabon novel da zai zo muku nan da bayan sallah idan muna da tsawon rayuwa
Taku Mai kaunar ku sadnaf Dan darajar Allah Kar a hadamin document ngd🙏🙏🙏🙏