Sashe 71
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana ji tana gani ya sabata a kafadarta ya fita da ita ya kaita cikin mota, Addu'oi ta cigaba da yi tana Daga bayan mota tana Jin Yana magana shi kadai, ji take kamar ta tashi ta Kai mishi shaka ko ta Kama steering din motar, dan bata tab'a sanin Kabiru zai iya rufe ido akan neman duniya ya kauce hanya har haka ba,Ashe duk kudin Nan da yake facaka dashi ba na Allah da Annabi bane,Ashe Kabiru kungiya ya shiga,tuni taji tausayin Sajeeda ya cike Mata zuciya,Ashe duk halin Nan da take ciki, Kabiru ne sila,ina ma tana da yadda zata tonawa Kabiru asiri,so take ta mik'e daga bayan motar ta hau danna ihu amma jikinta da zuciyarta sunki bata had'in Kai,tana ji tana gani zaa kaita Wai wani kungiya.
Addua kawai take dan tasan Allah maji rokon bawansa ne Allah kadai ne zai tsallakar da ita.
Tana Jin lokacin da suka iso ya kinkimeta daga bayan motar idonta a rufe yake, amma tana Jin lokacin da ya kwantar da ita Yana magana da wani,,addua kawai take a zuciyarta maganganun da taji suna yi akan Yesmeen ya matukar girgiza ta,ba iya fyade ma yake so yayi wa Yesmeen ba kasheta suke so suyi,mai Yesmeen ta musu da zafi haka, ko dai itama sirrinsa ta gano shi yasa suke so su kasheta,sai da taji maganar da suke ta gane Ashe Yesmeen ba makancewa tayi ba tana gani,ashe Yesmeen sirrin Kabiru tasani shi yasa tayi karyar makanta, haka ta kwanta Kamar mataciya har taji an taba kanta da Abu sau uku da kafin a tabata addua kawai take a ranta.
Jin a watsa mata ruwa yasa ta ja dogon ajiyar zuciya ta dan bud'e idonta.
Taji shugaban na yanzu ta samu tabin hankali suje su kaita wajen Tasha bazata tab'a iya tona musu asiri ba idan sun ajiyeta yaje yasan yadda zai nemi Yesmeen ya kawota su kasheta.
Haka suka tayar da ita Suka jata mota,ta ringa yiwa Allah godiya da ba abinda ya sameta.
Dan tasan ita dai a hayyacinta take,tana Jin yadda Kabiru ke tsalla gudu wai dan ya ajiyeta yaje wajen Yesmeen.
Suna ajiyeta Suka ja motar aguje,sai da ta daina hango motarsu ta mik'e a hankali tana Jin jiri na daukarta,dan ji take kanta Kamar baa jikinta ba,bata san yadda akayi ta zub'e a kasa ba,sai muryar wasu maza taji a kanta rashin kwari da k'arfi ya hana ta motsawa,a haka suka kinkimeta sukayi chemist da ita,yadda bayan keyarta ya kumbure yasa suka dauka hatsari tayi ta buge a kai,tuni aka mata treatment wayanda suka kaita dayake masu mutuncine Suka biya kudin magani har abinci suka siya mata, da maltina tana ci kuwa ta dan ji kwari kwari,ta roke su akan tana so tayi sallah tafiya tayi gidan da tazo Bata same su ba ba Kuma Wanda tasani a garin,tuni mai chemist yace ta Shiga cikin gidansa dan chemist din nasa a jikin gidansa yake.
Sai da ta rama duk sallolin dake kanta tana ta godewa Allah daya kareta daga sharrin Kabiru,ganin matar nada sakin fuska yasa ta nemi arzikin aron wayarta.
Ta kuwa bata aron wayar ta saka lambar mijinta ta Masa flashing.
Take kuwa ya kirata Yana Jin muryarta ya saki ajiyar zuciya yana "kin bi kin daga mana hankali Mai ya samu wayarki a kashe"
Yaya Asmau kuwa tace Masa kalau take ta Yar da wayar ne ya taimaka ya saka mata kati ta layin nan yanzu ya Kuma turo Mata lambar Gwaggo,dan tasan idan har ta fada Masa abinda ke faruwa zai iya cewa zai taho a daren,ya Kuma dagawa kansa hankali,a yanzu fadawa Gwaggo halin da ake ciki kawai take so tayi,a samu aje a taimakawa Sajeeda da Yesmeen dan addua kawai take akan Allah ya Kare Yesmeen daga sharrin sa,sosai tausayin Yesmeen ke daiwaniya da ita,Ina ma tana da yadda zata je ta taimaka mata,duk tambaya da ya mata bata iya bashi amsa ba haka ya kashe wayar ya saka Mata katin dari biyar ya turo lambar Gwaggo ta layin
Tana Kiran Gwaggo ta dauka tana Jin muryarta itama ta hau godewa Allah tana Mai ya samu wayarta Mai ya sameta?
Yaya Asmau da ta fita can waje ta hau labartawa Gwaggo duk halin da ake ciki,ba abinda ta rage har yadda ya kaita kungiya dan ya haukatata, Gwaggo ihun sallati kawai take har sai da taji mahaifunsu Sajeeda ya karbi wayar shi ma ta labarta masa tana a taimaka a ceto Sajeeda daga hannunsa a taimaka a ceto Yesmeen.
Hankalin Abban su Sajeeda a tashe ya hau cewa ta taimaka ta kirawa Kabiru Yan sanda
Yaya Asmau kuwa tace bazai yu ba tunda Yana da kudi,zai iya Basu cin hanci,anan baban Sajeeda yace zaiyo shatar mota gobe da safe suzo shi da Gwaggo su dirar masa idan sun iso zasu kirata ta layin su hadu su je gidan.
Da haka sukayi sallama washegari kuwa suna isowa Suka kamo hanyar gidan Kabiru kowane bakinsa d'auke da Addu'a Allah yasa Kabiru bai cutar da Sajeeda da Yesmeen ba, Gwaggo kuwa sai kuka take
Kabiru
Ihu ya fasa da "Shikenan asirina ya tonu"
Yaja da baya jikinsa na wani irin rawa ya zubawa Asmau ido da take kallonsa.
Yaya Asmau kuwa ta saki murmushi tana "Kana mamakin ganina ko?ka dauka na haukace ko ka dauka zaka cigaba da samun nassara a duk abinda ka saka a gabanka na zalinci ko? Kabiru da Allah na dogara ban hada bautarsa da kowa ba,shi yasa ya tsareni ya kareni daga mugun nufinka,Duk abinda kayi jiya Ina kallonka ba Suma nayi ba har kungiyar da ka kaini da kake tunanin an taba kaina saboda na samu tabin hankali Ina cikin hayyacina, Kabiru,na gano sirrinka a yau asirinka ya tonu,dan su Gwaggo ma sun san Kaine ka cutar da Sajeeda
Kabiru da jikinsa ke balain rawa da kafafu zubewa yayi akan gwiwarsa ya sunkuyar da kansa Yana Jin Kamar numfashinsa ya d'auke saboda tashin hankali kukan Sajeeda kawai ke tashi da na Gwaggo da ta rungimeta,Sajeeda kuwa cewa take "Gwaggo mijina uban yayana shi ya nakastamin rayuwa saboda ya samu kudi, Gwaggo ko a mafarki ban taba tunanin Kabiru zai tab'a min haka ba,umma yayata da muke uwa daya uba daya wai ita take so ta kasheni saboda ta samu ta aure shi,Yaya Abu haka ta ringa saka min guba a abinci wai dan naci na mutu Allah na kareni,Yesmeen na kareni,a yanzu saboda san kudi ta sallamawa Kabiru kanta ya nemeta Wanda nasan dan biyan bukatarsa ya nemeta,mai na musu haka da na cancanci haka daga wajensu,cikin kuka Sajeeda ta hau labarta musu yadda Kabiru ya kwanta da Kare yazo ya kwanta da ita Wanda daga lokacin ta kwanta rashin lafiya,tana Basu labari tana kuka,
Su Gwaggo kuwa Suka kaure da sallati, Kabiru kuwa da ke ji dama kasa ta bud'e ya shige ya Kara sunkuyar da kansa Yana Jin kirjinsa na bugu fiye da misali,mai ya rage masa Kuma Babu asirinsa ya riga da ya tonu fakar idonsu yayi,duk da ba riga a jikinsa yayi waje da balain gudu dan bazai iya kallon su ba,Yanzu dama duk tsawon lokacin nan Yesmeen ta fadawa Sajeeda sirrinsa Ashe duk tsawon lokacin nan Yesmeen ta San komai a kansa,Ashe lokacin da ya kwanta da Kare Yesmeen ta ganshi, motarsa ya fada ya samu wani riga a bayan motar ya saka ya tadda motarsa dan bai fiye zare mukullin mota ba a jiki yake bari.
Jikinsa rawa kawai yake ya figi motar dan horn din fitar hankali ya ringa dannawa Mai gadi.
Yana kallon lokacin da Yaya Asmau ta biyo shi a baya tana magana baisan Mai take cewa ba,ta tabbata shugaba bai iya komai ba, tunda gashi Yaya Asmau bata haukace ba gashi ta tona Masa asiri.
Babansu Sajeeda da Gwaggo sallati kawai suke,dan ko a mafarki basu tab'a kawowa Kabiru arzikinsa bana halal bane,
Da ido Suka bi shi a lokacin da ya kwasa da gudu yayi waje,sai Yaya Asmau ce ta bi bayansa tana yazo ya fada mata Inda ya Kai Yesmeen ya bawa Sajeeda takarda ta,
Tana komawa ciki ta nufi d'akin Sajeeda dan ta ga Yaya Abu da itama ta matukar bata mamaki,tana Shiga ta hango ta buya a wajen wadrobe dan tana jiyo muryarsu,da kunya Gwaggo da Babansu su san mai ta aikata,da kunya,wani irin radadi take ji a jikinta,da azabar kaikaiyi,tuni taji hankalinta yayi matukar tashi ta fara tsoron Kar dai ya nemi Sajeeda ne yazo ya kwanta da ita,da kuwa ya cuceta,idonta ya rufe da san kudin shi yasa ma bata nemi ya saka roba ba.
Shigowar Yaya Asmau da ta tsaya tana kallonta yasa tayi saurin sunkuyar dakai
Yaya Asmau kuwa ta fara magana tana "tirrr da ke Abu tirrr yanzu akan kudi Kika Bari mijin kanwarki ya kwanta dake?yanzu akan kudi kike so ki kashe Sajeeda ?dama haka kike Abu"?wallahi kinyi asarar rayuwarki ban taba zaton zakiyi haka ba,Ina tausaya miki dan kin cutar da kanki,akan kudin da ba na halak ba Kika kassara rayuwarki Abu,akan kudin da bana halak ba kikaci amanar kanwarki,Ashe ba dan Allah Kika zauna ba,kina da wani nufi a Zuciyarki"?kaiconki Abu dan kin kashe kanki da kanki, Kabiru dan yankan kai ne,Kabiru kudinsa na jini ne, Kabiru kudinsa ba na halal bane,dan biyan bukatarsa ya nemeki dan kema ya kassara rayuwarki kamar yadda ya kassara na Sajeeda dan ya samu kudi,
Yaya Abu wani irin ihu ta saki cikin tashin hankali tana "Na Shiga uku na lalace innalillahi wa Inna ilaihi rajiun wayyo Allah na dama dagaske Nusrah take ya akayi Kika sani Asmau"
Tsaki Yaya Asmau tayi ta bar d'akin Yaya Abu kuwa ta ringa zunduma ihu tana ta shiga uku taya zata koma kamar Sajeeda Kabiru ya cuceta.
Sajeeda.
Kuka kawai nake bayan na bawa su Gwaggo labari, mahaifina ma ya kasa motsi saboda mamaki, Gwaggo kuwa sai kuka take tana godewa Allah da na warke Kabiru Kuma baiyi nassarar kasheni ba,Yaya Abu kuwa abinda take nema ta riga da ta samu.