Sashe 57
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kiran da Rabiu ya Masa ya tuna Masa aikin da ke gabansa, kwana biyu kacal ya rage Masa,sai yaji dama Yaya Abu ba yayar Sajeeda bace da ba abinda zai hana ya nemeta,Sajeeda kuma da zai nema asirin sa a rufe da sai yadda yayi da ita jikinsa Kuma yak'i bashi hadin kai, wanka ya sake Yi ya fice dan ya nemo wacce zata biya Masa bukatar sa
Yaya Abu kuwa karfe shidda na yamma ta fito daga daki,ta dora girki,dan bata da burin daya wuce yau dinan ta samu cikar burinta,idan har ta sake bawa Sajeeda abinci bata ci ba ba abinda zai hana ta danne Kan Sajeeda da pillo.
Tana gama girkin ta zuba na Sajeeda ta saka maganin ta ajiye a gefe,ta fito daga kitchen din tayi wanka ta caba ado dan so take ta karfin tuwo ta jawo hankalin Kabiru kanta,sai da aka iddar da Sallah isha ta fito daga d'akin tasan Kabiru tunda ya sake fita bai dawo ba,gwara kawai yanzu tayi abinda za tayi kafin ya dawo din,tana Shiga kitchen ta hau kwallawa Hamza Kira da take jiyo maganar su a d'akin Sajeeda,dan so take su bar d'akin ta samu ta bawa Sajeeda abincin.
Hamza na zuwa ta bashi abincinsa tana su wuce suje suci abincin su.
Hamza na karba ya koma d'akin Sajeeda.
Ita Kuma Yaya Abu ta fito da abincin Yesmeen dan ta tsani taga ta fito daga dakinta tana bin bango,ba karamin Haushin Yesmeen take ji ba dan wani zubin sai taga kamar ma tana gani,a yau ne kawai ta gama girkin bata shigo kitchen neman wani Abu ba,amma indai tana girki sai ta shigo,a hankali ta turo k'ofar sai taga Yesmeen ta saki littafin hannun ta da sauri ta mai da idonta sama,Yaya Abu ta saki baki tana kallon ta dan sai taga kamar karatu ta shigo taga tana yi"
Ba dai Yesmeen tana gani ta musu karyar bata gani ba,ta nufi wajen da Yesmeen din da kanta ke sama tana kalle kalle tana zuwa gabanta ta d'auki littafin taga littafin addu'oi ne daga dukkan alamu Yesmeen karya take yi musu tana gani idan bata gani taya zata dauki littafi tana karantawa,yesmen kuwa da jikinta ke rawa tana zuba Addu'a a zuciyarta Wayance wa tayi tana waye nan"?
"Nice nan ke da bakya gani ya akayi kike karatu"?
"Kafin na daina gani na Saba da karanta addu'oi mama shi yasa duk da bana gani,nakan d'auko na ringa shafa kowane shafi,sai naji kamar Ina gani"
Gyada Kai Yaya Abu tayi tana ba shakka toh ga abincin ki nan sai kici"
"Nagode mama"
Yaya Abu wani irin kallo ta zuba mata kafin tayi hanyar waje,ta bar k'ofar d'akin Yesmeen din a bud'e tana ayyana irin dukan da za tayiwa Yesmeen idan ta gano tana gani kitchen ta koma ta d'auko ragowar maganin da ta zubawa Sajeeda ta fito ta koma d'akin Yesmeen cikin sand'a ta zubawa Yesmeen ido da idonta ke kallon sama har lokacin tana zaune a yadda ta barta abincin ta na nan a gabanta,sai shafa littafin addu'oi take tana miis mis da baki.
A hankali ta tsugunna a gaban Yesmeen ta barbada maganin a cikin abincin,tana cigaba da kallon Yesmeen idan har Yesmeen tak'i cin abincin nan tasan tana gani idan kuwa taci tasan dagaske bata gani,dan ko kad'an bata yi motsin da Yesmeen zata san ta shigo ba ta koma gefe daya tana kallon yesmeen da har lokacin take ta shafa littafin,Yaya Abu kuwa tuni ta fara tunanin karya Yesmeen take tana gani,tayi gyaran murya tana "Kici abincin ki Mana sai ya hucce"
Yesmeen duk abinda Yaya Abu take yi tana kallonta da ace Yaya Abu zata Mata kallon tsaf zata ga yadda jikinta ke balain rawa har tana hada gumi,da dukan alamu Yaya Abu so take ta kasheta itama dan tana kallon sama ne kawai amma tana kallon sadda ta zuba mata abu a cikin abinci,da kulle k'ofar d'akinta take Yi,Yaya Abu ya kafa Mata dokan ta daina kullewa dan ta tsani tazo ta ringa kwankwasawa, ta riga tasan Yaya Abu so take ta gano ko tana gani ko bata gani,a yanzu indai tak'i cin abincin nan zata gano tana gani,karshen ta idan Kabiru ya dawo aka fada Masa tana gani,a yau ya aikata lahira ba Mai iya kwaceta dan itama Yaya Abu ba karamin tsanarta tayi ba,da hankalin ta ba yadda zata ci abinda zai cutar da ita,a yau dai asirinta zai tonu dan bazata ci abincin ba, zata nunawa Yaya Abu tana gani,maganar Yaya Abu ya katse mata tunanin da take da tace taci abincin Mana Kar ya sallamce,duk Shirin da take yi na su gudu da Sajeeda idan har Yaya Abu ta tafi wajen Yesmeen gobe ya tashi a banza tsawan da ta daka Mata da "Kici abincn nan nace kuut a lailai yarinya nan ta dauka dunkulallen kai ne dani, har na shigo d'akin nan naganki da littafi kice min bakya gani,ci abincin nan nace"
Yesmeen so take ta saukar da kanta ta kalli Yaya Abu tace tana gani,ta fada Mata dalilin da yasa tayi karyar makanta,indai da zuciya a kirjinta ai dole ta tausayawa Sajeeda da ita kanta,sai dai a madadin ta saukar da kanta sai ta hau lalubar abincin ta d'auko cokalin ta debo abincin duk bisa umarnin zuciyarta dan Yaya Abu na gabanta a tsaye ta kame kugu da alama kiris take jira ta rufeta da duka,tana bude bakinta Yaya Abu ta tunkude hannunta ta d'auke abincin dan tasan indai tana gani tasan bazata tab'a yarda taci ba,tana ficewa Yesmeen ta kifa tayi sujada tana godewa Allah Dan Allah ne ya rufa Mata asiri ya kareta,yanzu ba iya Kabiru ne abin tsoro ba har Yaya Abun bata tab'a tunanin zata tunkuda hannun ta ba ta dauka zata barta taci abincin ba abinda zai zaunar da ita a gidanan da Sajeeda Yaya Abu na tafiya gobe taga Kabiru ma ya fita zata Nemo Mai taimaka Mata su gudu,ta koma ta zauna tana Jin yadda kirjinta ke bugun uku uku,yau dai ta tsallake rijiya da baya.
Tana dagowa daga sujada ta koma ta zauna a daidai lokacin da Yaya Abu ta sake dawowa da wani plate din ta dire a gabanta tana "Ga wani abincin kici wancan da na d'auke abu ne ya fada a ciki.
Daga haka ta kullo rufo dakin Yesmeen ta koma kitchen ta d'auko abincin Sajeeda,a yanzu ta tabbatar wa kanta da yesmen bata gani,ba yadda zaayi ta kashe Yesmeen,dan bata ga amfanin kau da ita ba za Kuma a gano idan suka tafi lokaci guda da Sajeeda dama gwaji take so tayi ta Kuma ga Yesmeen din ba gani take ba.
Sajeeda
Hawaye kawai ke zubo min da naga Hamza Wai shi ya kaini bandaki ya gyarani,ya canza zanin gadon da na b'ata ko kyankyamina banga yayi ba ballantana ya toshe hancinsa.
A fadar sa ma a d'akina zai kwana dan sunyi hutun makaranta,ina Jin lokacin da Yaya Abu ta kwalla masa Kira ya fita ba jimawa ya dawo da farantin abinci a hannun sa dama tare suke ci da Annur,shinkafa da taliya ne da miya,ya hau tsakiyar gadon ya juya abincin ya kalli Annur Yana yazo suci,haka Hamza ya ringa ci Yana bani a baki, Kamar yasan wani zubin da yunwa nake kwana dan Yaya Abu yanzu ba bani abincin take ba, Yesmeen Kuma ba ta iya zuwa ta bani dan Yaya Abu sai ta Kai Sha biyu a zaune a Palo tana kallo,a haka yayi ta bani har sai da na d'auke kaina ya bani ruwa na sha,yaje gaban mudubi ya kwaso magunguna na da ni nasan ba aikin da suke min amma ba bakin da zan hana a ringa bani,haka na Sha ya maida ledar gaban mudubi ya dawo ya zauna,Annur kuwa suna Gama cin abinci ya ringa buga game a tab din da Abban Nusrah ya siya musu,shi kadai ne banga Abban Nusrah ya siyawa waya ba,wayar Yesmeen ma da ya kwace Ina ganin dan Yasan tasan sirrinsa ne Amma sai cewa yayi wayar bata da amfani a wajenta tunda ba gani take ba,Hamza Kuma ya d'auko wayarsa ya ringa daddanawa,duk da ido nake bin su iya su da nake gani wallahi Dadi nake ji a raina,haka nake kwana ni daya Kamar mayya ba Mai kula dani,dama su barmin su su ringa kwana a d'akina nasan ko Yaya nayi gurnani Hamza zai tashi kila ya gane Ina bukatar wani abun ne,Yesmeen ma Yaya Abu ce ta koreta a ranar da ta shigo d'akin da dafa bango akan zata na kwana dani, Yaya Abu ta koreta akan me zata kwana ita da ba gani take ba ba Kuma wani abu za ta iya min ba.
Shigowar Yaya Abu ya katse min tunanin da nake na juya Ina kallonta,tana ganin su Annur ta hade rai tana "Uban me kuke nema a d'akin nan"?
"Ba komai dama munzo mu zauna da umma ne saboda ita kadai ce yau ma anan zamu kwana dan umma na bukatar kulawa tunda ba mai kulawa da ita daddare"
"Toh wanan ne baku Isa ba,bazaku kwana anan din ba,kaji min yaro da iyayi waye yace maka baa kulawa da ita maza maza tashi ku tafi dakinku zan bata abinci"
"Ai taci abincin tare muka ci abincin da ita dan Allah mama ki barmu mu kwana Yaya Saifullahi ma dazu da muka yi waya dashi cewa yayi mu ringa kwana da ita"
"Toh bazaka kwana ba nace so kake kace bana iya kula da ita har wani waya ake bugo ma ace ka kula da ita dalla tashi ku ficemin daga d'aki"
Annur da sauri ya dauki tab dinsa yayi waje,Hamza kuwa baa San ransa ba ya mik'e Yana kallona yayi waje.
Na hau zubar da hawaye kila ma kallon karshe Muka yiwa juna dan yau nasan Yaya Abu shigowa tayi ta kasheni,dan rabon da Kuma ta kawo min abinci na manta tunda ta kawo abinci har tana koran yayana da suka ce Mata naci abinci ta dage akan su fita.