← Book details Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 80

Sashe 5

Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kudin daya dora a cinyata kawai nake juyawa har ga Allah sai najini a tsorace tambayoyi nake so na yiwa Abban Nusrah amma bana so na rusa Farin ciki da yake ciki,a wanan zamanin har wane irin kudine da shi haka jiya ya bashi kyautar dubu dari biyu yau Kuma ya d'auko dari biyar ya bashi.

"Wai ya na ga ba kya farinciki ne Sajeeda Allah ne ya turo min shi ya taimaka min fa Allah yasan tsawon shekarun da na dauka Ina aikin wahala"

Murmushi yak'e nayi Ina "ba haka bane Abban Nusrah Mai zai hana ni murna kawai Ina ta mamakin yanda daga jiya zuwa yau ya iya baka kyautar dubu dari bakwai zugudum a wanan zamani ko dan uwan ka ke da wanan kudin ba lailai ya iya baka irin wanan kyautar ba"

"A wajen masu kudi kyautar dubu dari bakwai ba komai bane Sajeeda sabida dai bamu da kudin ne shi yasa kike ganin yawan kudin, ba za ki gane abinda na ke fada ba sai anjima idan mun je gidan Zaki tabbatar da ko miliyan daya ya bada kyautarsa ba zai ji komai ba"

"Allah ya saka masa da alheri"

"Ameen Ameen ai idan ya samo min aikin nan sai na siya miki tsalallen mota,su Saifullahi ma sai na bi su da motoci"

"Allah ya yarda yasa arzikin na alheri ne a gare mu Abban Nusrah kasan wani arzikin masifa ne,ni wlh a rayuwata rufin asiri kawai nake so bani da wanan burikan tashin hankalin indai zanci sau uku a rana yarana su kawo bukatar su na musu ba tare da na gaza ba wlh Alhamdulillah"

"Sajeeda kenan yanzu dai tashi kije ki boye mana kudin ki zo ki fada min Abubuwan da ake bukata a gidan"

D'aki naje na boye kudin na dawo wajen sa duk jikina a sanyaye bansan mai yasa ban ji Ina mugun Farin ciki ba shi kuwa sai zuba yake yana lissafa yadda idan ya samu kudi zai canja mana rayuwa ko girki da na so dorawa hana ni yayi yace yau bazaa yi girki ba Kuma bai yarda na Kara karbar aikatau ba.

Koda Yara suka dawo haka ya tara su Yana tambayar su abinda suke so.

Tuni duk suka haukace da murna daga Mai cewa machine yake so sai Mai cewa keke yake so Annur kuwa sai tsalle yake Yana mafarkin sa ya tabbata Abban su ya Zama Mai kudi,Abban Nusrah kuwa sai washe baki yake Yana su Kara saka su a addua ai Yana ganin nan da sati biyu zamu bar gidanan.

Ni dai da ido nake bin sa yanda ya hakikance Yana zuba lissafi Taya mutumin da ba shi da ko asi sai ya fita yayi buga buga tashi daya ya ringa wanan lissafe liisafen sai Kuma nayi tunanin Allah Kan iya azurta bawan sa a dare daya zai Kuma iya talauta bawan sa a cikin mintuna.

Bayan sallah isha yace na shirya mu tafi gidan abokin na sa na masa godiya na so ya bari zuwa gobe ya dage mu tafi.

Haka na shirya cikin dogon hijabina na haye machine din sa mu ka dau hanya.

Ni dai ban san wajen da mu kayi ba kalle kalle kawai nake har mu ka iso wani wawakekken gida da aka masa ado da fitilu masu haske kamar ba dare ba.

Haka kawai na ji tsoro ya Kara rufe ni na hau sallati a daidai lokacin da ya kashe machine d'in na sauko yayi parking a gefe ya hau buga gate d'in.

Wani ne ya bud'e yana ganin Abban Nusrah ya washe baki Ya rusuna ya bashi hanya tare da masa sannu da zuwa, nidai tsayawa nayi daga baya Ina mamakin yanda Mai gadin yasan Abban Nusrah har yake wani rusunawa.

Sai da Abban Nusrah ya juyo ya nuna min hanya na Shiga gidan da bismillah dan sai naji Ina karkarwa har Ina Jin sanyi na Shiga na.

Abban Nusrah kuwa kamar yasan gidan yayi gaba nayi saurin ruk'o hannun sa ya juyo Yana kallo na.

"Abban Nusrah tsoro nake ji ka ga girman gidan fa"

Nace Ina kalle kalle

Ya janye hannun sa Yana "mai abin tsoro ke dai kawai ki biyoni"

Kirjina na dukan uku uku na cigaba da bin sa a baya har Muka karaso wani k'ofar da gabad'ayansa glass ne.

Abban Nusrah ya danna wani waje k'ofar ta bud'e da kan ta,ya shige nima nabi bayan sa Ina zare ido,dan tunda nake a rayuwa ta ban tab'a ganin irin Wanan gidan ba.

Ba kowa a palon Abban Nusrah kuwa ya samawa kansa wajen Zama ya nuna min kujera akan na zauna.

Ni kuwa rawar da jikina yake yasa na zauna a kasa.

Abban Nusrah ya d'auko wayar sa daga Aljihu Yana "gamu nan mun zo"

Daga haka ya mai da wayar cikin jaka.

Ni dai Sam ban ji hankalina ya kwanta ba dan Addu'a kawai nake a zuciya ta.

Takun da na jiyo yasa na daga kaina Ina kallon sama.

Wata mata ce mai kib'a fuskarta d'auke da murmushi bayan ta Kuma wani ne shi ma da kib'ar sa da Alama shi ne Abokin Abban Nusrah da matar sa sai naji hankalina ya dan kwanta har suka karaso wajen da mu ke.

Matar tace "Haba ya zaki zauna a kasa ki zauna a sama mana"

"Aaa nan ma yayi"

Duk yanda naso ta barni a kasa ki tayi har sai da na hau saman kujerun na hau gai da abokin Abban Nusrah da ya kura min ido ya na Kare min kallo.

Ku sha ruwa Mana"?

Matar sa tace dan suna Zama aka cika gaban mu da kayan ciye ciye ni dai tunda na zauna na rasa nutsuwa ta buri na kawai mu bar gidan.

Kaina a sunkuye naji Abban Nusrah na fada mi shi kawoni yayi na masa godiyar alherin da ya Masa.

A lokacin matar ta koma sama haka ne yasa na sauko daga Kan kujeran na hau Masa godiya cikin murmushi daya bayyana hakoran makkar sa yace "ba komai uwargida baxan iya biyan Kabiru alherin sa a gareni ba dan ya taimaka min sosai sabida ni maraya ne,abincinsa haka zai kawo mu raba dan na taimaka Masa ba wani Abu bane".

Godiya na Kara Masa yace ba komai ya Kara da "akwai wani gida da nake so na bar masa kyauta dan yace min gidan da kuke ciki ba naku bane haya ne,dan haka a satin nan ku fara shirye shiryen komawa na bar muku gidan halak malak,sannan zan d'auke shi aiki a company na zaa na biyan sa albashi miliyan daya kowane wata"

Tunda ya fara magana na saki baki Ina kallon sa dan gabad'aya ji nayi na girgiza da Abubuwan da yace zai yi mana.

Kamar an like min baki haka na ringa kallon sa Abban Nusrah kuwa sai godiya yake zuba Masa Yana ba komai.

Sai da Abban Nusrah ya kalleni na iya bud'e bakina Nima na hau masa godiya.

Ko da mu ka zo tafiya kudi ya d'auko Mai yawa ya miko min nak'i karba dan wlh wani irin tsoro naji ya Kara rufeni Kuma gabana bai bar fad'uwa ba idan dai na hada ido dashi.

Sai da muka fito na daga palon na fara samun nutsuwa nayi gaba na bar su a baya.

Kabiru

Yana ganin Sajeeda tayi gaba ya kalli Alhaji Rabiu yana "Kasan idan ba haka muka yi ba wlh haka zata tayi min tambayoyi"

"Nasan fa irin su haka sakeena ke da wanan taurin Kan,yanzu abinda za'ayi kayi k'ok'ari jibi ku koma gidan sabida ka fara aiwatar da abinda aka saka ka"

"Ba zamu wuce jibi ba"

Daga haka su ka yi sallama.

Sajeeda

Har muka isa gida Sam ban ji zuciyata ta kwanta da wanan sauyin rayuwar da muke neman samu ba hakane yasa sai da muka zo kwanciya nace "Abban Nusrah bansan Mai yasa hankali na bai kwanta da wanan canjin da muke neman samu ba,taya haka kawai zai d'auko gida sukutum guda ya mallaka ma dan kawai ka taimaka Masa Kuna Yara Anya mutumin nan ba dan yankan Kai bane?wane irin aiki zaka Masa da zai d'auko har miliyan daya ya baka a wata"a gaskiya!!

Wani irin tsawa ya daka min daya tilasta min yin shiru"Sajeeda dama bakya san na cigaba a rayuwata? kinfi so na dawwama a haka a talauci kina jinki kamar mai gidan tunda ke kike yin komai a gidan,kinfi so na zama kamar yaron ki ko? bakya so kiga na samu na kaina

Toh bari kiji na fada Miki da hannu biyu Zan karbi arzikin da ya tunkaroni idan Kinga bazaki iya ba sai kisan nayi"

Daga haka yaja dogon tsaki ya juya min baya.

Ko da na hau bashi hakuri inaso na fahimtar dashi nufina ko ta kaina bai bi ba.

A haka na kwanta a gefen sa ina sake sake da bacci barawo kuwa ya daukeni na hau Mafarki da Kabiru da abokin sa

Mafarki........

MG'S SKINCARE

Dame akafiki yar uwata?
Kyan fatar ko iya gyaran fatar?
Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata?
Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa?
Hajiyata miye matsalar?
Fatar takice abun se lahaula?
Kingwada kingwada harkinsare?
Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin?

Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu,
Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya,

Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah,

Ga product din kamar hka,
Sabulu 4k

Mg's beauty kit 14k
Herbal whitening soap
Body cream
Face cream
Scrub
Cleanser
Glow oil

Sannan akwai flawless skin beauty kit 16k

Tsakanida Allah kigafa
Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata,

Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba
Chat:08062991549,07046881166,07067210195,
Call,+2348064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Team glow😍

*RUFAFFEN SIRRI*

*NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*Page 4*

Mafarki
Chapter 5 · 0% Book details