Sashe 48
Rufaffen Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*WANAN NOVEL DIN NA KUDI NE NA HADA KU DA FIYAYYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALAM KARKU MIN SHARING NOVEL IDAN BANA KALLON KI ALLAH YANA KALLON KI KUDIN KARATU KIKA BIYA BANA MALLAKA BA IDAN KIKA FITAR NA BAR KI DA ALLAH GA MAI BUKATA SAI TA BIYA 500 ZUWA WANAN ACCT DIN 2029764071 FIRST BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08068484400 SAI A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANAN LAYIN 08033719070 KO WANAN LAYIN 08033719070 MUTANEN NIGER KUMA SU NEMI WANAN LAMBAR +227 96 82 89 84*
*PAGE 35-40*
"Karki Sha kinji umma wallahi ta zuba abu a ciki bari na tafi Kar tazo ta kamani naga ta hau sama wajen Abba"
Daga haka tayi waje da sauri.
Da ido na bita har ta fita sai na kasa gane Inda maganar ta ta dosa sai naji kwakwalwata ta kasa bani hadin kai nayi tunanin mai Yesmeen ke nufi da Kar na sha kunun da yayata da muke uwa daya uba daya ta kawo min,tana nufin abun cutarwa ta saka min kenan kirjina ya doka da k'arfi jikina ya dauki b'ari iya sanina ban yiwa Yaya Abu wani Abu da zata cutar dani akan me zata saka min Abu a kunu,maganar Yesmeen na karshe da na tuna yasa naji kaina ya sara min,wai ta hau sama wajen Abba,mai zata yi a sama wajen Abban Nusrah, shigowar ta dakin yasa na zuba mata ido Ina kallonta,sanye take cikin doguwar rigar atamfar ta cika rigar tam,har da dan kwalliya tana zuba kamshi,a haka ta hau sama wajen Abban Nusrah,sai na tafi tunanin yadda take zuba kwalliya tunda muka dawo Abuja,sai naji na kasa yarda shaidan ya raya min wai yayata so take taja hankalin mijina tunda yanzu a kwance nake bana iya komai,Koda ba a kwance nake ba taya zata tab'a tunanin Jan hankalin mijina bayan uwar mu daya uban mu daya ,a wane dalili zata zuba min abu a kunu iya sanina Kuma Yesmeen bazata tab'a mata sharri ba,kallon ta kawai nake inaso na hada tunanina waje daya
Ita kuwa room freshner ta d'auko a gaban mudubi ta fesa a d'akin ta zauna a gefen gadona ta hau mamatsa hanci tana "Sajeeda Allah ya yanke Miki wanan wahala da wanan rayuwar da kike na a kwantar a tayar wai ace jikinki ke fitar da wanan warin,Allah ya kawo Miki sauki na har abada wallahi da wanan wahalar da kike fama dashi,gwara ace ma mutuwa Kika yi Kika huta,kin zama hoto ba magana miji kuwa sai dai ki ganshi daga nesa,magani ba irin Wanda baa yi ba ba sauki,Allah ya yanke Miki wanan wahala kanwata wallahi Mai kaunarki bazai so ya ganki a haka ba, Allah yasa wanan jinya da Kika Sha ya zama silar shigarki aljanna sannu"
Kallonta kawai nake jikina na wani irin rawa maganganun ta sun matukar daga min hankali yayata ita ke min fatar mutuwa yayata ita takeso ta kau dani,mai nayiwa Yaya Abu da har take min fatan mutuwa,idan na mutu mai ribar ta,sai na tuna yadda take shishigewa Abban Nusrah idan ya shigo d'akin ta hau tambayar sa mai zaa dafa Masa,dama dan Abban Nusrah take wanan kwalliyar so take na mutu ta Aure shi kenan,?hawaye ya hau zubo min Ina Jin zafi a kirjina,wanan wane irin masifa da jarrabawa ne, mijina ya kassara min rayuwa yayata Kuma tana so ta karasa ni saboda kwadayin abun duniya, Mai na musu haka da zafi,
Kuka nake sosai kirjina na sama da kasa ita kuwa
Ta d'auko kunun tana "Sannu Sajeeda ya zaki yi da kaddara haka Allah ya rubuta miki"
Ta ajiye kunun ta matso kusa dani ta dagani daga kwancen da nake dan tsaf zata daukeni saboda rashin nauyi bama nama a jikina ta saka min pillo daga wajen kaina,tana "Kunun gyada ne nasan kina so shi yasa na miki"
Kallon ta kawai nake yaushe rabon da Yaya Abu ta kawomin abun karyawa da wuri,wani zubin ma mantawa take sai dai Yesmeen idan ta faki idonta ta kawomin,ko ta tashi kawo min haka za ta yi ta yamutsa fuska tana nuna kyankyamina take,a yau sai gashi da wuri ta kawo abin karyawar saboda ta zuba min abu a ciki,a daidai lokacin da ta kawo cokalin kunun bakina,na kau da kaina hawaye na cigaba da zubomin na hau addua a zuciyata Ina "Ya Allah nasan mutuwa dole ce ya Allah ka ara min tsawon rayuwa ka bani lafiya ka gwada ikon ka akan Abban Nusrah ka bani lafiya yaga na warke,ya Raheem bana iya ibada saboda ba abinda nake iya yiwa kaina,Allah nayi tawasali da kyawawan sunayenka ka bud'e min bakina na iya magana karka bawa yayata ikon cin galaba a kaina Allah nasan halin nan da na tsinci Kaina a ciki jarrabta ce daga wajenka Ina mai neman sasauci a wajen ka dan ban Isa na gujewa kaddara ta ba ka bani ikon cinye wanan jarrabawar ka bani tsawon rayuwa yayata ta gani a raye"
Yaya Abu juyo da fuskata tayi tana "Ki Sha kunun Nan Sajeeda na fada Miki saboda ke nayi"
Turo k'ofar d'akin da akayi yasa muka kalli bakin k'ofar,Yaya Abu ta hau washe baki da taga Abban Nusrah ne ya shigo ya ci kwalliya da shadda ruwan zuma,shi ma bakin sa a washe ya karaso gefen gadon,na zuba Masa ido Ina kallonsa ya zauna a daya gefen Yana "Sannu da dawainiya Yaya Abu kina k'ok'ari sosai Allah dai ya biyaki ya saka Miki da alheri da bakya gidanan bansan ya zanyi ba"
Ba kunya ba tsoron Allah Yaya Abu ta kankantar da murya ta hau wani abu da ido tana "Ni Dan Allah ka daina cemin Yaya Abun nan ka kirani da Abu ko zainab ni idan kana Yaya Abu Nan sai naji kamar wacce ta tsufa bayan ni ba tsohuwa bace tunda haihuwa ta daya, matarka kuwa shekara daya kawai na bata"
Rufe Baki Abban Nusrah yayi Yana "Ai ko kwana daya kika bawa Sajeeda dole a baki girmanki na yayarta"
Kallon su biyun kawai nake Ina hararo Yaya Abu ta samu cikar burinta na kau dani, ta auri Abban Nusrah,dama Yaya Abu zata iya auren mijina,ashe ba abanza mahaifin mu ke mata fadan bakin Hali ba,dan lokacin da muke Yara indai na samu Abu ko nuratu haka zatayi ta fushi tana bakin ciki,akwai ranar da naci na biyu a islamiya mahaifinmu ya bani kyautar sabon littafi da fensir,daddare duk muna kwance ba bacci nake ba a kwance nake dan ba wuta da wuri Mu ke kwanciya Ina kwance da Nuratu a katifar dake kasa sai naga ta sauko daga kan gadon ta nufi wajen kayana har zan tashi zauna na fasa sai gashi ta bude akwatin karfen da kayana yake ciki,ta d'auko littafin ta yaga ta karya fensir din ta maida min akwati,har na girma na kasa manta abinda tamin da sai da na girma na gane bakin ciki yasa tamun haka, Haka idan muka samo kyautar abu ni da Nuratu sai ta yaga,ko auren Abban Nusrah da nayi murna take saboda tasan ba Mai kudi bane mijinta yafi shi hali, maganar Abban Nusrah ya katse min tunanin da na tafi,Sajeeda ki sha kunun Mana"
"Tun dazu nake fama da ita ta Sha tak'i sha Kuma saboda ita na dama kunun nan"
"Ko dai zafine da kunun"?
Girgiza kai Yaya Abu ta hau yi tana "Ina fa kunun yaga zafi"
Sai ta Kai cokalin bakinta ta fito da harshenta ta dandana tana ba zafi"
Sai a lokacin ta tuna dandana kunun tayi ta Kuma hadiye,ta mike da azabar sauri ta fara sallati tana tari da k'arfi tana kakalo amai tayi waje da gudu,
Lumshe idona kawai nayi Ina yiwa Annabi sallati,da kanta ta dandana kunun da take so ta kasheni dash,sai Kuma na fashe da kuka dana tabbatar da kasheni dai Yaya Abu ke San yi Abban nusrah kuwa ya bita bakin kofa Yana mata sannu ya dawo wajen da ta zauna ya Kara d'aukar kunun Yana "Ina ga tsarkewa tayi tashi ki Sha kunun Sajeeda ko wani abun kikeso kici"?
Ido na zuba Masa Ina Addu'a Allah yasa shi ma ya Sha kunun wallahi da zan ga abinda zai kashe Abban Nusrah Dadi zanji,kunun ya kawo bakina yaga na Kara kau da kaina sai ya ajiye kunun Yana "ko Tea Zaki sha,Wai bakya gajiya da kuka ne Sajeeda dan Allah ki bar kukan nan karki jawowa kanki wani matsala bari na hada miki shayi Ina ga kunun ne bakya so.
Ya mik'e yayi waje.
Kabiru.
Yana fita yayi hanyar kitchen Yana Shiga yaga Yaya Abu nata kakarin amai, gefen ta Kuma ga gwangwanin Madara ta bud'e ta lafta a kofi,
Shi kuwa cikin mamaki ya karasa wajen ta Yana "Yaya Abu lafiya kuwa mai ya kawo Miki amai Kuma"?
Yaya Abu kuwa hannu kawai take turawa bakinta tana kakarin amai,gudun Kar Kabiru ya zargeta yasa ta zuba ruwa a madarar ta kafa Kai ta shanye.
Sai da ta shanye ta kalli Kabiru dake ta jera Mata sannu tana "Wallahi bana San kazanta wari na shaka shine naji zuciyata na tashi"
"A cikin kunun warin yake"?
"Aaa Ina Kai kunun bakina na shako warin"
"Ai da kin fara gyarata kafin ki bata abincin naga yau ma ai warin da sauki Sannu bari na dama mata shayi Kamar kunun ne bata so"
Yaya Abu bata iya magana ba saboda cikin ta da taji Yana murda mata da ciwo,
Ta Kara dama wani madarar a daddafe tayi d'akin ta dan d'akin ta daban aka ware Mata,Yesmeen ma na da nata d'akin.
Tana shigewa daki ta daga Kai ta kwankwade madarar ta kwanta rub da ciki tana "da kaina nake neman kashe kaina banda rashin hankali da b'atar basira mai ya kaini dandana kunun duk wanan kabirun ne ma ya rudani naje na dandana